Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 56 of 64
BABI NA HAMSIN DA UKU.
Yana son duk abinda zai yi da amincewar mahaifiyar shi, yana son ita da kanta tace mishi ya je ya auro Radiyah, yana bin duk wani sharadin ta, dan a zauna lafiya.
  Shi yasa baki daya yaƙi d'aga hanaklin shi, shi yasa yaki damuwa da irin hukuncin da ya yanke, baki daya ya ki mai da hankali kan Radiyah. Burin shi Mahaifiyar shi, ta ji dadin biyayyar da yayi mata, wannan dalilin da yanayin ya saka shi dauke kai akan Radiyah, kuma ita kanta tana mamakin yadda tunda tace bata son ganin su, har yau bai kuma mata magana ba, bai kuma kallon ta da batun ba.
Dan koda tace ya nime auren Yar kawarta amincewa yayi jikin shi har da rawa, haka da yayi ne yasa ta jin lallai zata barshi ya auri Radiyah, amma sai ta nunawa mahaukaciyar uwar su basu da hankali zata amince mishi.
*
Gefe Mohan ya motsa sosai kuma ya maida hankali, duk da yaki zuwa gurin Jalilah da sunan zance haka bai hana a fasa kome ba, Maimunari ce dai yasan ya rasata kenan. Shi yasa ya rungume auren Jalilah bawai dan yana da bukatar haka ba, kuma yau da gobe yana bukatar kulawar mace, idan ya dubi shekarun shi kara hawa suke, matar da yake so baya tare da ita.
  Dan haka ya watsar da damuwar shi, domin yayi imani da Allah. Tunda mahaifiyar shi taki Maimunari ba zata tab'a kaunarta ba, ya kan zauna yayi dogon nazari akan me yasa kome yazo mishi a jagule! Me yasa kome yake bukata sai ya rasa? Shin ko dan bai kyautatawa mahaifiyar shi ce? Ya rasa gane abinda yake faruwa da al'amarin shi.
       Da sallama ya shigo falon mahaifin shi, sanan ya nemi guri ya zauna, kafin yace mishi.
"Abbu kana jin labarin Maimunari kuwa?" Yayi tambayar a sanyayye.
"Baka tambaye ni, me yasa naki auren Yar Sarkin maradi ba?" Sunkuyar da kai yayi yana wasa da capter din falon.
"Abbu kayi hakuri, nasan tun wata biyu da suka wuce ya dace a ce anyi bikin kuma Allah bai nufa ba, ban san me ya faru ba. Kuma bana son na tambaye ka kar na shiga abinda bai dame ni ba. Ba wai damuwarka bata dame Ni bane sai dai bana son na cika bincike ne!" Ya fada mishi.
"Eh toh da farko yarinyar ta amince amma daga baya taki, wai na mata tsofa, na zata ko wani abu nayi ashe iya kawai girman da nayi ne, shine nace mata toh babu damuwa, kuma Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ya fada yana kallon Mohan da ya sunkuyar da kanshi.
"Mohan Maimunari ta kusan haihuwa, domin cikin ta ya girma. Sai dai kuma tana cikin damuwa ne, domin ko kwana biyu da suka wuce naji labarin bata da lafiya jininta ya haura." Da sauri ya D'ago kan shi yana kallon mahaifin shi.
"Abbu don Allah, ka hada ni dasu, dan girman Allah ka taimaka min, ina son sanin halin da Mata ta, take ciki ne idan ma cire abin cikin za ayi a cire. Ta huta wahalar tayi yawa"
"A'a yanzun take da wata takwas, idan aka cire karfi da yaji, abin cikin ba zai rayu ba..Insha Allah sunce nan da sati Uku zasu mata aikin shi." Kamar Ya fashe da kuka,yana faÉ—in.
"Abbu don Allah" ya zube gwiwar shi a kasa, idanun shi jajjur.
"Kayi hakuri! Insha Allah akwai lokuta da zaka ganta."
"Abbu kafin nan na kuma rasata kenan, na rasa ta har abada, ina kara hango nisan da take min, Abbu kayi wani abu, sabida ni Khalil ya hakura da Benazir, an tace ba zata aure shi ba dan zan auri Jalilah, don Allah Abbu kayi wani abu, don Allah ka taimaka min kar ya rasa yarinyar da take so, na yarda zan dauki kome amma ban da na zama sanadin rasa masoyin shi."
"Insha Allah ba zai rasa ta ba, ba zai rasa ta ba."
    Sam iyayen su basu san abinda yake faruwa ba, sai da Mohan yayi bayani, kuma koda Hajiya Nuratu taji labarin bata ji zafin Benazir ba, sai ma burge ta da tayi tana son taga mutum na kishin dan uwan shi, uwa uba son kai ƙarara da aka nuna musu,idan wasu ne zasu ga kamar dama haka shiryayyen al'amari ne.
Dan haka ita da kanta ta sami Abban Khalil tayi mishi magana shima ya gaya mata ai ya samu labarin, dan haka suka kira Abie tare da tuntubar shi. Dariya yayi musu sannan yace musu.
"Ai shi ya biye mata ne har da d'aga hankalin shi? A'a kar ya damu tana taya yar uwarta kishi ne, shi yasa take ganin idan tayi haka shima zai ji zafi, itama tana can a dame balle shi, dan haka ku kwantar da hankalinku. Insha Allah Benazir matar Khalil ce."
  "ALHAMDULILLAHI, mun gode sosai da wannan Alfarmar da kayi mana."
   Haka suka tattauna abin su, sannan suka yi sallama, wani abu da mutane ya dace su fahimta, duk wata tushen matsala daga mace yake, mazajen da suka san ciwon kansu, zai yi wuya su zama tushen matsala, sai dai su zama ƙarshen matsala. Dan haka bayan sun gama tattaunawa ne Abbu da Abba suka kara tattaunawa akan matsalar matan su, shi Abba ya isa da gidan shi kuma ya san matar shi bata da matsala akan wannan maganar,
Dan haka bayan sun rabu kowannen su ya koma gida, koda Abba yasa mi Umma da maganar dariya abin ya bata, tace mishi.
"Ai tayi mishi da kauna shi yasa naga kamar bai da lafiya, ashe inda matsalar yaƙe kenan! Ai karka nuna mishi kunyi ma, kunyi maganar yanzun ya wani sake ranshi."
  "Ba zan iya sitirin asibiti ba, idan zaki iya boye mishi ki yi, amma zan gaya mishi wallahi domin ba zan iya kallon shi cikin damuwa ba." Ya fada yana kallon ta.
"Toh babu matsala duk inda kace haka za yi.
  **
A gidan su Mohan.
Wayar shi yana kara, duba wayar yayi ya ga babban limamin masallacin Niamey, dauka yayi suka ka gaisa.
"Yallabai, na maka karambani, na daura maka aure da kanwata shekaranjiya ta fita takaba, mijinta ya rasu, kuma ba yarinya bace can dan shekarunta talatin da biyu. Kayi hakuri amma bai zama dole ka rike ta ba, idan bata maka ba"
  Murmushin jin dadi yayi sannan yace mishi.
"Babu Matsala Allah yasa haka shine mafi alkhairi, nagode sosai na amshe ta baka gaya min sunan ta ba."
"Sunanta Ummu Aimana"
"Alhamdulillahi, Nagode sosai Insha Allah anjima zan turo a dauke ta, nagode ka taimaki dan dattijo"
Wallahi labarin yayi mishi dad'i, dan haka ya shiga kiran yan uwan shi da yaran shi yana gaya musu, Aikuwa Khausar ta nufi kasauwa aka shiga hidima sosai, zuwa dare Umma suka zo aka dauko amarya, mace mai mutunci da sanin ya kamata.
Washi gari kuwa aka buga walima na manyan mutane, anyi nasiha tare da tsoratarwa akan aure, sannan aka yi rabo dan abin yazo a gaggauce, bayan an watse amarya aka kaita part din Hajiya Sahiya, sannan aka watse. Sai fatar Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba,domin bata taɓa haihuwa ba.
  Da alamu su Mohan za ayi kane (🤣🙄 Wallahi ban ce kome ba)
Danne Hajiya Lateefah sosai Umma take domin kuwa, ba karamin haukacewa tai ba, domin kuwa kuka tayi musu.
"Ni zai ciwa mutunci? Ya auro sa'ar Salman Meye ya rasa idan yace min yana bukatar hakkin."
"Kinga wannan ya zama son kai, bayan baku tare Kice kar ya auro wata, wallahi baki isa ba."
"Nuratu! Bayan shi ki ke bi? Toh na fasa aurawa Mohan Yarki wallahi na fasa! Kuma zan kira Nahnah na gaya mata yanzun."
Mikewa tayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi, haka nake so domin ina son farin cikin yarana sama da na kowa musamman Ibrahim akan son zuciyar ki zai rasa yarinyar da yake kauna Kinga maza gaya mata wallahi ban ki mata biyayya ba"
   "Ni zakiwa rashin mutunci? Toh fitar min a gida, ko na ci mutuncin ki" ta faɗa tare da kumfar baki.
"Sai me? Fita kan zan fita wallahi kawai ina farin ciki ne zaki raba wannan sharrin da zaki kula"
Fada Sosai suka yi sannan ta kira mahaifiyar su, ta ce ya fasa aurawa Mohan yar Nuratu, sannan Umma ta bar gidan, kusan hauka Hajiya Lateefah tayi a daren, domin bakin ciki ya hanata barci kuma ba auren shi bane a kanta zunzurutun kishi da haukar banza.
Washi gari.
Nahnah ta kira Abba ta bashi hakuri sannan ta ce su janye maganar auren, bai damu ba domin yasa karshe haka zai iya faruwa a fasa auren, Allah sarki Jalilah ce ma tayi karamar jinya, sabida an fasa auren Mohan da yaji kan shi kamar ya sauke nauyin da ya dace.
Dan haka yayi maza ya bar ƙasar domin matukar yana ganin ta tana ganin shi ba zata tab'a barin shi ya huta da batun auren ba.
*Kuyi hakuri muna fama da rashin wuta da babu gwara babu dad'i!*
*Hmm ku Cigaba da ɗaukar labaruna kuna juyawa! Daga free har na kuɗi bai isa ba? Sai an kwashe wannan ma. Daga yau tambarin littafina zai kasance kwanar Wata Insha Allah idan kuka ga labarin da yayi daidai da nawa Fasaha ta aka dauka! Kowa mai dambu muguwa mai_dambu Shegiya amma kuma labarin mai dambu ba zai tsari ba!? Kome da lokacin sa na saka abinda ya shafi kishi amma haka aka yi ta zagina na dauki fasahar wata Toh wannan karon a bar min labarina! Masarautan JORDAN bai tsira ba, Bahaushiyah bai tsira ba HABEESHAH bai tsira ba! Yau an diro Bororoji na gama shan bakar wahala da asarar data bincike akan abu wasu dan rashin Imani sun dauka! Na hana idanuna barci ina bincike amma ban tsira ba! Ban da ma hauka idan aka dauka ba a sauya tsarin labarin haka za a tafi dashi! Yadda Safina ta shiga Jordan a spy haka aka dauke shi aka rubuta! Yadda Husnah Habib Manga ta shiga Rayuwata Family Abubakar Moddibo haka aka dauke min Bahaushiyah Na Bature Yohanna Chibok labarina ne Dr Yohanna Chibok! Shima HABEESHAH an dauke shi an mai dashi Noorah uku. Kuma ɗan rashin mutunci sayarwa suke! Munafukai da suke karanta books dina suke saya suna shiru ana zuzzuta hauka da jahilci Allah ya isa Ban yafe ba kalmar turanci nayi amfani da shi a Kwarkwarah sai da aka ce nayi satar fasaha 😓 Ni kuma an dauke nawa an hana Ni magana Allah ka bi min hakkina Bororoji ma bai tsira ba haba mana*
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: HAKKIN MALLAKATA
#sun-Aug-2021
BOROROJI
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.