Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 15 of 64

BABI NA ASHIRIN DA D'AYA.

Cikin ihu da masifa yake bin bayan Mohan tare da niman riko rigar shi, amma zaratan sojojin da suke bin bayan MG Mohan suka cafke shi, tare da shiru suna jiran Umarnin shi.

"Ku kyale shi ya rayu. Na barshi ya rayu domin idan kuka dake shi sai ya leka lahira ya dawo." Ya fada tare da cigaba da tafiyar shi,

     Ganin Almamoon baya motsi ya sashi karawa da sassarfa, yana kallon fuskar shi, hular kanshi ne ya zame, lallausar gashin sa da yake tufke baki wuluk wanda yake warware. Kallon shi yake yana kara mamakin yadda namiji dashi yake da uban gashi haka.

       Yana fitowa ya ajiye shi a cikin motar su, kallon Fahad yayi tare da kallon bike din shi, sara mishi yayi sannan ya koma, gurin bike din ya ja machine din da gudu, yayi da suma suka rufa mishi baya. Tab'a bluetooth din shi yayi tare da cewa.
"Malam turo min wani likita daga barikin sojan maradi."

   Tab'e abin yayi tare da sauke wani irin ajiyar zuciya.
"Yallabai an tura masu wani motar da zata kwaso su."

          "Hmm" ya faɗa, yana me kallon zoben hannun Almamoon,  a hankali yake me jin kamar ya rufe Ansar ku baki daya, amma bai san girman da yake dashi a duniyar Almamoon ba, sai ya farka.
Suna isa gidan ya sauke shi cak, har yana mamaki.
*Dube bakin shi da ya iya zungure min goshi, nan kuwa tsiwa ce zallah babu wani karfi dube shi kamar ba namiji ba*

Ya fada a kasan ranshi, yana jin wani dariya yana niman kwace mishi, yanzun ma idan ya farka zai koma kamar da yadda zai cigaba da rena mishi hankali, dan yana son haukar yaron baki daya ya kam manta da batun shi din wani ne yayi ta shirme.

  Shigowar wani likita tare da wasu mata biyu, suka fara aikin su a kan Almamoon, tashi yayi ya bar musu gurin. Can suka ci-gaba da aikin su, sai kallon juna suke musamman bayan da likitan ya gama nashi suka fara nasu. Abun mamaki ya basu. Me yasa haka?

       Dan gulma sai da suka yi ta duba shi har cikin, tsoro ne ya kama su lokacin da Mohan yayi gyaran murya, da sauri suka bar shi. Juyawa suka yi. Likitan ya fara magana.
"Yallabai mun debi jikin shi, zamu bincika muga abinda yake cikin shi. Nan da awa daya."

    "Amma Likita mara lafiyan yana"
"Na Fahimta muje Insha Allah zamu kara dawowa, sannan na sami sauran birbidin maganin da aka shaka mishi zamu yi bincike akai."

Suna barin gidan likitan ya balbale su da faÉ—a, yana gaya musu.
"Dan baku da hankali taya kuna gaban MG na soja zaku saka bakin ku a cikin maganar mu kusan waye shi?"

    Shiru suka yi dan sun san halin shi masifaffen ne, har suka isa asibitin, cikin abinda bai fi awa daya ba aka gama binciken. Yana karanta abinda ya kusan da sauri ya kira Dan Ba'are ya gaya mishi.
"Don Allah ku tawo da majiyancin nan rayuwar shi tana cikin hatsari"

        Zunzurutun tashin hankalin da  dan Ba'are ya shiga kamar zai dira a maradi, dan haka ya kira Mohan a hanzarce.
"Yaron nan yana cikin hatsari a kai shi asibiti gani nan zuwa."

    Kashe wayar Mohan yayi mishi.
"Hello Hello! Kai kai katsaya mana" babu shiri ya dauki kayan shi bai tsaya wata wata ba. Ya kira wata wayar da take cikin Office din shi, ya faɗa musu abin da yake bukata, cikin kankanin lokaci suka hada mishi kome, yana fita ya daga Office gidan shi ya nufa, ya haɗa abinda zai hada, 

....

A dakile ya watsar da wayar tare da shimfid'a dogayen kafaffun shi a samar table, yana kallon Almamoon da fuskar shi yayi wani irin fayau kamar wanda aka kwashe mishi jinin jikin shi. Bakin shi kuwa fari yayi fayau.

     Idan ya cigaba da rike yaron mutuwa zai yi, dan haka a zuciye ya dauke shi, yana fitowa dauke da Almamoon, sojojin da suke gidan suka mike, tare da nufar inda motar aikin su yake, suka yadda saka shi yayi tare da shiga ya zauna ya daura kanshi a kan cinyar shi.

       Lumshe idanun shi yayi yana tuno yadda ya birkice yau ganin halin da ya shiga, duk yabi Cameras na cikin gidan yaga  yadda yaron yayi ƙoƙarin kula da lafiyar shi. Da yadda aka yi ta had'a mishi mugun abu a cikin gidan a saka Hajiya Safiya tayi ta dukar shi. Ya rasa inda zai saka zalincin Hajiya Safiya baki daya.

         Sai dai wani abu daya da ya lura dashi. Bude fararren idanun shi yayi akan kofar asibitin. Ga Nurse da suka tsaya suka jiran fitowar su, a hankali ya fita tare da bude inda Mamoon yake kwance. Ya fitar dashi,

   Tunda aka shige dashi wani daki bai kuma ganin wani ya fito ba.  Tun yana kirga lokacin da aka shiga har ya kai ya daina duba agogon lokacin sallah nayi suke fita da Malik.

   Bayan awa biyu sai ga Dan Ba'are, kallo daya Mohan yayi mishi ya dauke kai Kamar bai tab'a ganin shi ba. Asalima haushin yadda yake bashi umarni yake sai kace irin shine a kasar shi. Wani b'ata rai yayi yana shan kamshi kamar bashi ba.

    Shi kuwa bawan Allah bai fahimci halin abokin shi ba, abu daya zuwa biyu ya tambaye shi.
"Ya jikin ka? Ya jikin Almamoon?"
Wani basarwa yayi tare da mai da smart watch din shi hannun shi yana wani cin magani, dakyar bakin shi ya motsa da cewa.
"Da sauki"
Ka sake Dan Ba'are yayi yana kallon shi. Kafin jikin shi yayi wani iri, komawa gefe yayi ya zauna tare da É—aukar wayar shi yana latsawa,shi kuwa Mohan sai wani tsare gida yake irin ba zai yiwu ba.

     Fitowar likita ya sa dan Ba'are mik'ewa ya mikawa Dr Faruq hannun suka gaisa.
"Faruq meye a ke ciki?"

     "Yallabai rayuwar shi ta fita daga matakin tsari, sai dai bamu da kayan aikin da zai tacce jikin shi."

"Dama kunsan baku da kayan aikin uban waye ya ce kuce a kawo ta?" Ya fada tare da watsar da su baki daya gefe yayi wucewar shi cikin dakin.
"Mohan ka tsaya ayi magana kaji yace idan da za a fita dashi kasar waje ko Saudi za a dace."

"I fuck nonsense words, taya zaka gaya min maganar banza kaniyar kasar waje hell You da kasar wajen" ya faÉ—a a tsawa ce. Yana bankawa dan Ba'are hararar.

           Dan ya tsani duk wanda zai mishi iyayi akan Mamoon.
"Amma dai meye na zagi? Kamar wanda aka mishi wani abu? Yaron nan dai ni na kawo shi dan lura da lafiyar ka, so it's my responsibility na tsayawa rayuwar shi if not me kake tsammani za a dauke ni, don Allah kayi hakuri a dauki matakin da ya dace."

      Kura musu ido yayi cikin nutsuwa ya juya zai fita daga asibitin, zuciya kawai yake dawainiya da shi, yana fita ranshi ya kuma b'aci dan haka bai tsaya a asibitin ba ya nufi gidan shi, dakin motsa jikin shi ya cire kayan shi ya rage daga shi sai farin wando. Daukar karfe yayi yana nazarin yadda dan Ba'are ya nuna mishi fin karfi akan Almamoon ne. Ba zai kuma shiga damuwar su ba.

Dan haka abinda yake gaban shi zai yi ya cigaba da boye matsalar shi,.kiran Malik yayi tare da zubawa kofar idanun shi. Wanda suke cike da masifar rikici.

Yana zuwa ya zuba mishi wasu files a gaban shi, tare da kamewa ya sara mishi tare da yin alamun yana da magana.
"Humm" yace a hankali,
"Yallabai! Na gama tattara bayanan baki daya, sai dai yaron bai da matsalar kome, kuma ba shi da alaka da Ansar Yusuf. Wancan kuma akan case din su.."
D'aga mishi hannu yayi tare da kafe kofar shiga da idanu.

Sara mishi ya kuma sannan ya juya tare da barin d'akin, yadda kan shi ya dauko zafin nan idan ya cigaba daukar magana ji yaƙe kamar zata fashe shi yasa ya bar asibitin dan ranshi ya fara b'aci.

A hanyar fita suka haÉ—u da Dan Ba'are.
"Ina mara mutuncin yake."
"Yana dakin motsa jiki"
A fusace ya shiga tare da banke kofar, ya d'aga ruwa yana sha.
"Kai wani irin mutumin banza ne haka? Akan wannan maganar sai kayi zuciya da Yaron?"

" Kasan kanin Ubana ne da zan zauna muku" ya faÉ—a bayan ya ajiye goran ruwan,
"Banza kawai waye ya kawo batun Iyaye?"

Bai kula shi ba, zama yayi tare da sassauta murya yana faÉ—in.
"Mohan yaron yana bukatar kulawa"
"And so what?" Ya tambaye shi yana zare mishi ido,

"Jinin shi bai da karfi, kwayoyin sinadirin kulorin da kuma Cocin aka hada ya shaka, Kuma shi sinadarin yana lalata huhu da makogaro, don Allah kayi wani abu a fitar dashi kar ya rasa rayuwar shi, gashi ban san inda Iyayen shi suke ba Ansar Yusuf ne kawai ya san inda yaron ya fito"

A matukar tsoro yake amma kuma a yadda ya nuna rashin mutunci akan fuskar shi sai ka rantse zuciyar shi bata rawa akan abinda aka gaya mishi.
"Wani hali yake ynzn?" Ya tambaya fuska a daure,
Gyara zama É—an Ba'are yayi Y
Tare da cewa.
"Yana nan dai sai a hankali, ina tsoron kar wani abu ya same shi ne wallahi"

Mik'ewa yayi ya fita tare da nufar dakin shi ya shiga ban daki, wanka yayi sannan ya fito ya bude wardrob din shi ya dauki kayan shi wani riga da wando, rigar ja ce sai wandon baki. Sakawa yayi tare da rufe closet din shi,bai cika amfani dashi ba, kasancewar akwai Abubuwan sirrin shi.

Lumshe idanun shi yayi lokacin da ya gama shiryawa ya fito, yana saukowa tare da nufar inda Dan Ba'are yaƙe. Ya dauke kai Kamar bai ganshi ba. Haka yasa dan Ba'are jan tsaki me ƙarfi. Bai kula shi ba dan yasan ya shaka ne yasa yayi tsaki.

Ko a motar babu wanda ya kula wani asalima dauke kai suka yi dan kowa da jin haushin dan uwan shi, suna isa asibitin Office din likitan suka shiga, suka samu yana duba wasu sojoji.fita suka yi tare da zama.

"Ko zamu je kaga yadda yake?"
Kamar ba dashi ake ba, shiru yayi yana latsa agogon hannun shi.
"Amma kai kan anyi dan iska idan ba zaka ba kayi min bayani mana ka tashi ka share ni kamar wani abu mara daraja" kallon shi Mohan yayi tare da tab'e baki yace mishi.
"Idan kai ne da kafana dauke ni ka kaini"
"Ok ince kai maganar bakin ka kashi yafi shi daraja"

Sanin bai son magana yasa shi dauke kai yana kallon yadda Asibitin yake. Mik'ewa yayi tare da nufar hanyar da zai kai shi cikin asibitin Dan Ba'are yana gaya mishi bi nan can zamu shiga har suka shiga inda Mamoon yake, Ya kai hannu zai bude kofar Dan Ba'are shima ya kai nashi hannun, a lokaci guda suna kalli juna. Tsuke fuska Mohan yayi dole Dan Ba'are ya cire hannun shi, koda ya shiga cikin dakin, rufe kofar yayi yana me jan tsaki.

Jingina yayi da kofar tare da kura mishi ido, tausayin yaron yake ji. Haka kawai ƙaddara ta kawo shi inda bai da muhalli, inda yana da gata babu me tozarta shi, amma yau gashi ana watangaririya da rayuwar shi.

A sanyayye ya mike daga jikin kofar, ya nufi inda yake a Mamoon yake kwance, ya dafa kujeran da yake gaban gadon, tare da juya shi a hankali sannan ya zauna yana fuskarta shi.
Riko hannun shi yayi tare shafa, shi a hankali yana me jin tausayin shi a ranshi, kara rike hannun yayi yana kallon shi zara zara, kafin ya kai hannun fuskar shi. Yana tuno abinda ya faru kafin wannan lamari d'azun da safe. Musamman yadda yake zaro mishi ido, murmushi yayi tare da cewa.,
"Allah ya baka lafiya" ya faɗa a can ƙasar makoshin sa......
*Har na bude data sai naga Yan Baroriji fans 😂 suna nimana ido a rufe kamar ka sace Mamoon na b'oye🙄😠😏 ku gode yau bana jin rashin daraja da ban muku typing ba🙄 Insha Allah na kusan fara muku rashin darajar nan.... Ban sani ba ko zan sami damar typing gobe, idan nayi zakù gani idan bai yi ba toh na tafi leka Gyatuma ce kusan abinka da mai kaka sai anayi ana leka su thank You so much 💓💞*
8/19/21, 2:23 PM - My Mtn Number: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.