Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 55 of 64

BABI NA SITTIN DA BIYU.

Dan haka dole ki koyi mu'amalar irin mutanen wani lokaci ma sa masoyanka kake fada, sai ta kwab'e maka zaka Fahimci haka, sannan da gaske ne dole ki koyi hakuri, domin duk inda zaki zauna dole ki koyi hakurin nan shi yasa Allah madaukakin sarki yace masu hakuri yana tare dasu, dole ki koyi kawar da kai.(🌚🤣wallahi sai ina jin kunya idan na rubuta maganar hakurin nan 🙄domin ban da ita da rashin daraja ce zan iya fada akwai ta buhu buhu 🤨😒😏🌝🤸) mahaifiyar Mohan tana da zafi da fada, kuma irin su dole ka zama ruwan sanyi, sai a zauna lafiya. Bari na gaya miki wani abu, duk yadda aka kai da zaman aure dole ki samu positive and negative, dole cikin biyu ayi daya imma dangin miji su kauna ce ki bawa, umma miji yaki ki. idan aka yi dace kuma kika hada soyayyar dangin miji da namiji kin dace, idan kuma aka yi rashin dace uwar miji taki ki.
(Kuyi hakuri bawai babu Yaren Novel bane a labarin amma ina son ku fahimci wani abu ku mata ne! Kuma dole a gaya muku rayuwar wasu dangin mijin baka san da wanda Allah zai had'a ka dasu ba, amma yana da kyau mu fahimci kan rayuwa ba wai nace babu Sex bane a'a kawai labarin na gina shine akan wannan yanayin 🙄🤨 yan buta roro, idan aka barku da shugaban karamar hukumar wandon cinye shi zaku yi. Wallahi ba sex story bane labari ka fahimci sakon labarin shine damuwar, idan naso sai nayi labarin kamar Kwarkwarah 😂🤣 lami kenan a gaban Uban kowa ma za a karanta labarin babu jin kunya ko rufe fuska 👏🏼)

    Ba wai na gaya miki mugun hali ne ko muguntatta ba, a'a tana da fada amma tana da kirki, kowani dan adam yana da kirki yana da banzan hali, idan Allah yaso halin kirkin ya danne banzan halin ka huta idan kuma halin banzan ya danne na kirki ka banu, domin duk wanda zai fadi wani magana akan ka toh halin banzan zai fada akanka. Ba zai tab'a duba tarin alkhairirronka ba, burin shi ya fadi wancan mugun halin."

Rike hannuna tayi sosai, tare da kallona.
"Jinki Allah ba zai tab'a jarabtarki ba? Ko yayi dake ne ba zai tab'a jarabtar rayuwarki ba? Maimunari idan har namiji zai dauke ni ranar aurena bayan an daura min aure da wani yaje yayi rayuwa dani meye yafi wannan muni da jarabta? Maimunari idan har zai tafi dani bai tab'a mu'amalata ta cikin nutsuwa ba meye yafi haka cin rai?" Damke hannunta nai hawaye na wasan tsare a fuskana,  "kinsan me ya faru? Hatta rayuwar ki nice na lalata miki, domin ba zan manta ba bayan na gama tsine mishi, sai da nayi furucin da nasan shi yake dawainiya dake." Riƙe hannun juna muka yi, kwalla na zuba mana.

    " Nice na jefa ki a ƙaddara, da a lokacin ban ce wani abu nakanki ba da yau rayuwarki bata cikin matsala. Kiyi hakuri da dangin shi da kuma Mahaifiyarshi."
"Mommy ba zan koma gare shi ba, shi daya yayi aure uku bayan Bana nan? Mommy wallahi ina son Mohan, Mommy kinji zuciya tab'a kiji yadda take bugawa, Mommy Mohan wani shashine na rayuwata, amma haka yayi watsi da ni, wallahi ina son shi. Mommy ban san yadda zan gaya miki yadda nake kishin sa ba, shi din mijina ne, Mommy ki min addu'a ko zan sami sauki a zuciyata. Mommy Mohan kamar zinari ne a cikin tsakiyar taku.

   Shi din Kamar ruwa ce min a zafin sahara, kyauta ne da na samu bayan na rasa kome na, Taya ba zanyi kuka ba, amma nagode zan koyi hakuri zan kuma koyi dauke kai, amma Tabbas ba zan iya hakuri a min irin abinda aka miki ba, ba zan iya dauke kai a cutar dani ba, wallahi zan yi magana, kuma idan ka takani zan rama, sai dai idan ba zan iya ba."

Dariya yayi tare da isowa gurin mu.
"Yar Baba gaya mata dai ke ba irinta bace, zaki iya yaki dan kwatar kanki. Karki yarda wani ya taka ki, kina da Uban da zai tsaya miki, ko ita uwar Mohan kyaleta nayi sabida Mohan amma da na mata abinda zata nime ki da kanta, amma bana son haka domin xan fi son ki sami soyayyarta da zuciyar ta, shi kuma Mohan ba yadda kike tunani bane, Yaron yana sonki"
Mikewa nayi ina kunkuni.
"Haka kawai ai da ya damu da Ni, ba zai zauna ba sai ya nimo ni amma bai zo ba yana can ina soyayyar shi da yan mata dama ai nasan nice na takura mishi toh na fita a rayuwar shi. Allah ya bashi hakuri ya cigaba da zama da Kanwa dan Ba'are, Allah zai saka min"
Na fada ina kuka.

    Su kansu dariya na basu domin ba dage sai faɗa nake, zaunar da Ni Abie yayi ya mika min ruwan addu'o'in da kullum yake bani, nasha sannan na sauke ajiyar zuciya.
"Kiyi hakuri" kallon shi nayi kafin, nayi kwafa.
"Wallahi da zan ganshi sai na sashi ya dauki cikin shi nima na gaji, tunda bai da."
"Ai ke kika da hankali tunda gashi zaki sauke mishi cikin ya dauka, rigimammiya kawai" Mommy ta zungure min goshi.

Cikin sabon bakin ciki na kuma fashewa da kuka.
"Abie ka ganta ko? Ni aka yiwa laifi amma ita haushina take ji, wallahi sai na rama akan Mohan duk abinda aka min tunda ya cuce ni"

       "Kyale ta, Uwata haka take bata da kirki, kinji babu wanda zai kuma sa min ke kuka kina da Jarumin Uba irina, ko na miki kiranye Mohan din ne duk inda yake ya sussuce ya fito niman ki"

"A'a!" Na fada,
"Yawwa Yar albarka Ubangiji yayi miki albarka Insha Allah zaki yi kyakkyawan karshe da kyakyawan sakamakon hakurin ki."

   Gyada mishi kai nayi, tare da mik'ewa a hankali. Wato lallabani da Abie yake kamar wata kwai, amma ba zai hana idan nayi rashin hankali ya taka min birki ba. Ashe Benazir ta haukacewa Khalil. Allah Sarki baki daya ta nuna ba zata aure shi ba. Babu wanda ya sani.

***
Niger.

Baki daya ya Surkukurce idan ka ganshi ba zaka dauka Khalil din da ka sani ba zaka yarda shine ba.

"Mohan yarinyar taki fahimtar ba da gayya aka hada auren ba, wallahi duk yadda naso na mata bayani taki, yanzun haka ta yi ta rufe Ni a WhatsApp É—inta. Mohan ban san inda take ba balle na je."

   Wallahi duk sai ya bashi tausayi, ya rasa yadda zai yi dashi.
"Khalil ban san me zance maka ba, domin kuwa nima ina cikin yanayin da kake ciki, kuma nasan maganar baki ba zata wadatar ba, dole sai da rarrashi. Kayi hakuri Insha Allah zaku dai-dai ta."

     "Ba zata yarda ba, wallahi ba zata yarda ba, duk yadda na bata hakuri taki asalima cewa tayi ba zata aure ni ba, ni da zasu amince da sun duba alamarina "

"Zasu amince mana." Inji Mohan,
"A'a na hakura da ita, sabida itama Umma Umarnin Nahnah take bi, sabida soyayyata ba zan hana Mahaifiyata yiwa nata Mahaifiyarta biyayya ba, Allah ya zab'a min wacce ta fita, akan dangina ba zan zab'e ta, dukda ina kaunar ta, amma na zabi Mahaifiyata na barta"

Wani irin sanyi jikin Mohan tare da kallon Khalil, wani irin Tausayin Khalil yayi wani irin mutum ne shi da yake cike da sonka kowa ya zauna dashi sai tayi rashi mai girma, duk wanda ya rab'a sai ya rasa wani na jikin shi yanzun Khalil ya rasa yarinyar da yake matukar kauna. A hankali ya mike tare da barin gidan su, tunda ya shiga cikin gidan su. Ya sami mahaifiyar shi tana fada da Radiyah, zama yayi tare da daura kanshi a zaman gwiwar Hajiyar shi.
"Ammyn na amince zan auri Jalilah!"
"Haba? Lallai ka kyauta min, Nagode kuma kaga ta samu tarbiyya na gari"

"Ammyn don Allah ki so Maimunari mana! Don Allah ki kaunace ta, wallahi zan miki biyayya"
"Koda zaka dawo da ita, sai naga yadda ka zauna da ita ta kuma samu kwanciyar hankali a rayuwar ku zan duba yadda zaku zauna."

   Lumshe idanun shi yayi tare da sauke ajiyar zuciya, a kai akai yana kuma kara jin kamar ya gama rasata kenan, tabbas ba ji bane ya rasata baki daya, domin yasan ya rasa ta baki daya. Kwallar da yake danne shi, a hankali yake jan numfashi, sabida yadda yake jin kirjin shi tayi nauyi, Yana ji yana gani ya rasa yarinyar da ya kaunata.
"Ammyn me kike so nayi domin ki Huce!"
"Ka hakura da Ita" ta faÉ—a tana shafa kanshi, d'ago kai yayi yana kallonta.
"Ka hakura da ita bata dace da kai ba! Bata damu da kai ba, asalima matar da ta kai iyayen ta kotu meye zata haifa maka tsiya da bala'i, ba matar zama bane."

"Amma da baki tozarta ta ba, ai ba zata kai iyayen ta kotu ba, me yasa kike manta laifinki hmm Ammyn Kenan,  wallahi abinda aikata shi yake kore min manema na, zan koma gurin Haddir, domin idan na cigaba da zama bakin cikin ki ne zai kashe ni, gashi nan ana zaman lafiya yarinyar da Hammah Khalil zai aura tace ta fasa sabida rashin adalci irin naki, sai ki Cigaba Ni sai ba zan cigaba da zama da wannan abin ba."

      Ta fada tana kuka, sabida tausayin Yan uwan ta, tana kallon abinda mahaifiyar su, amma babu halin magana, babu wanda ya isa ya dakatar da ita..

  Haka ta tasha kuka sosai domin  tana son Safwan amma mahaiyarta,, tayi mata sanadin rashin sa, har abada domin ta samu labarin ya kusan aure, shi kan shi ma ya turo mata hotunan amaryan shi, kuma ya gaya mata yana sonta har kwanan gobe, kawai Mahaifiyarshi yake son yayi mata Biyayya, yana son ta rabu da Mahaifiyar shi lafiya, yana son idan zata sauko karta sauko...
Wannan Pagen yana magana ne fa akan biyayya ga Uwa.... Alhamdulillahi Ubangiji ya jikan Iyayen da suka rigamu gidan gaskiya, wallahi biyayya ga Iyaye shine babban kalubalen wannan zaman kuyi kokarin rabuwa dasu lafiya! Don Allah Karki yarda karka yarda rayuwar ta tashi babu ka tashi zero! Iyaye ba abin wasa bane, iyaye ba abin yarwa bane, karka yarda aci kasuwa a watse iyayen ka basu ribanci kasuwancinka ba, Karfin nasarata Addu'o'in iyayena, karfin Cigaba na Fatan Iyayena, bani da shekaru masu yawa. Amma Alhamdulillahi na rabu da mahaifana lafiya Yar uwa, ki gwada rabuwa da iyaye lafiya sai ki wayi gari ki rasa me kika yi Allah yake rufa miki asiri..... Addu'ar Iyaye ce.... Alhamdulillahi.....
_Kuyi hakuri babu lokaci yau din nan ne, yau addu'ar arba'in makociyata. So dakyar na samu damar typing É—in su, kuma idan nace sai dare wallahi zan manta daki domin aiki zan shiga_
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number:  https://www.wattpad.com/1115798063?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=H4PLUmmQMtRivq0LpRHlS38%2Fr1hLcjzt2XEZ3yHCmyzI3xoWStQC02%2FROcdRbxcPubxgSNp7F%2BbsI7AVD0kyhHL5jlei18XLmYIFmbPXjnlRmUgtZXxtCYJkkmcIRyXT
#sun-Aug-2021
HAKKIN MALLAKATA
BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.