Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 26 of 64
BABI NA TALATIN DA BIYU.
"Na gaji wallahi na gaji, ina son na rayu da abokin tarayya, babu amfanin boye ni da kike yi. Don Allah ki barni na rayu kamar sauran Yan matan don Allah kinji na had'aki da Allah dan girman Manzon Allah karki hanani rayuwar da ta dace dani" na fada cikin kuka, ina me rokon ta ina kuka ina. Bata hakuri amma bai saka Innah tausaya min ba, duk da tana dukana amma ban fasa rokonta ba,, sai yau zancen Baba nasiru ya dawo mata. Lokacin da Malam ya ke gaya mata zancen sai yanzun ta kuma kara fahimtar dalilin da yasa Munari take sake kin zama wajen ta,ashe soyayya ya faɗa.
_Duk abinda zai sanya shi bayyana kanshi tabbas shi zai sanya shi kuka! rayuwar shi zagaye take da zanen ƙaddara dan haka babu wanda ya isa sauya ƙaddaran wani_
Kura min ido tayi sannan tace min.
"Ba zan baki damar ki salwarta da rayuwar wasu sabida naki ba. Soyayyar da zata zame miki masifa? Ko ba soyayyar da zata zame miki Bala'i ba, Munari ina miki kallon mutuniyar kirki ashe idanun ki sun bude har kina yarda namiji ya dauke ki ko ya rungume ki, Munari tunda kika iya haurawa katanga ya sani fahimtar soyayyar da ta saka ki kika iya haurawa katanga, soyayyar da tasaki kika tambaye ni zaki rayu akan jinsin ki ba karamar abu bace ko ya kwanta dake ne? Kike tsoron kar ya gudu ya barki"
Dariya nayi domin yanzun kam na fara hango tsagwaron zalinci da son zuciya na fara fahimtar abinda Innah take nufi dani?.
"Innah zargina kike dan ina son shi! Abinda na sani na haukace akan shi. Innah ina son Muhammad ina mishi mahaukaciyar so ne. Amma duk da haka ban tab'a kusantar zina ba, Innah wallahil billahi azim ban tab'a zina ba, amma kike tambaya na ko ya kwanta dani? Innah tun ina yar miciciya nake kare kaina, Innah na shiga jami'a na kwana a dakin da maza suke ban yi zina ba sai yau rana tsaka ai wallahi ko wani ne ya gaya miki zan iya bazaki yarda ba, balle balle kuma ke da kika da na dauke ki kamar Uwar da ta haife ni"
Da mamaki take kallona, kafin taja wani itacce ta rufe ni da duka. Tana kuka tana dukana, ban yi mamakin dukar ba, amma yadda nake jin zuciyata ko zata kashe ba zan fasa ba.
 "Ki dake ni, ki zage ni matukar zaki barni a raye toh wallahil ba zan fasa ba, kuma ba zan bar kaina a matsayin namiji ba, Ina son rayuwa dan haka duk abinda Kiyi min matukar zaki bar ni da shi ba zan tab'a zama a ?matsayin namiji ba da bakinki kike kirana karuwa bayan ban tab'a ba, ko ciki nayi na kawo miki bazaki kirani da karuwa ba sai dai ki min Uzuri. Innah kawai rayuwa nace zanyi mike min haka ina kuma da nace zan gudu sai kin kashe ni duk abinda zaki yi kiyi
  "Ni zaki tozarta kamar yadda Iyayen ki suka tozarni, ni zaki wulakanta kamar yadda iyayenki suka wulakantani, bakar ƙaddara, ai tunda iyayenki suka gudu suka barki babu wanda zai iya zama dake, Shegiya yar iska, ni zaki watsawa kasa a idanu?"
  "Nasan da iyayena suna raye ba za su bar ni haka ba, kuma da suna nan ba zasu wulantani haka ba, zasu bani abinda nake so ki dake ni idan har dukar zai cire miki bakin cikina Innah ki dake ni, na gaji ina son Yancin."
  Shigowar Baba yaga yadda take dukana kuma ban fasa fadar abinda yake raina ba, yasa shi amsar itaccen.
"Baki da hankali ne? Kan me zaki tirsassa mata? Dole ne?" Ya fada da karfi, tare da tasowa ya d'aga ni.
"Baba don Allah ka barni na rayu kamar kowacce mace, wallahil zan kama kaina, don Allah ka Amince min na rayu."
 "WALLAHI ba a cikin gidan nan ba, sai dai a wani gurin ba zaki zauna min a gida ba, sai dai ki zab'a mu ko shi wanda kike son?"
 "Innah korata kike?" Na tambaye ta hawaye na zuba min, shiru tayi, ba ita ba hatta Baba sake baki yayi yana kallon ta.
"Ina kika ce na fita na bar miki gidan dan kawai nace ina son Mohan? Innah ba zan tab'a tafiya ba, ba zan zama butulu ba. Amma zan baki lokaci idan kika huta zan dawo." Na saka kai na shiga d'akina na hada kayana, har bana ganin gaba na.
 Â
       Wayata na dauka na shiga niman Number Mohan, amma da na tuna kar wata rana yayi min gori yasani kiran Ansar, na tambaye shi yana ina?
   "Ina diffa!"
"Ok gani nan a hanya" kawai so nake na nisanci Innah ne, dan haka na fito da kayana, hijab ne da katin bankina da Mohan ya bani. Ina fita na sami Innah ta kafe idan ban hakura da Mohan ba na bar mata gidan ta, sake kiran shi nayi, tare da tambayar shi a ina Baba Mari take, ya gaya min tana gidan shi na Maradi, dan haka na duba jaka na, na dauki key din gidan da Mohan ya saya min, na nufi Maradi dan na gaji bana son na cigaba da zama da Innah dan zan gaya mata magana..
   ***
Niamey.
 Karan cikala a yadda ake gudanar da cin abincin ban da Mohan, domin juya cokalin yake. Har suka gama,
  Kallon shi tayi kafin tace mishi.
"Mohan meye yake damunka?"
Murmushi yayi sannan ya mike tare da cewa.
"Babu"
Ya bar gurin su, tare da kara sauri.
"Meye alaƙar ka da Yaron nan? Naji an ce mace ce ko mata maza ce" cak ya tsaya ya kasa motsi, a hankali ya juya tare da kallon ta.
"Hmm hmm, kawai karya mutane ne" ya faÉ—a tare a barin gurin da sauri,
     "Yallabai Mohan yaki zuwa gurin Hanan, ita yarinyar tana son shi amma shi yaki zuwa ban san me yake nufi ba!" Ta fada a dame.
"Babu abinda yake nufi sama da ki bar shi ya zab'i macen da yake so Mohan ba yaro bane, kuma tunda yaki zuwa yana bukatar matar da yake so ne" ya bata amsa yana kallon tv,
  "Amma ai zab'in shi bai zama dole ba, tunda yarinyar da zai kawo bai zama dole ta cika abinda ake bukata, ina ga kawai a fara shirya kome kafin zuwan ranar da kasa zatayi murnan zagayowar samun yanci" kallon ta yayi tare da cewa.
"Toh! Amma ke me yasa baki son ya zabi wacce yake SO?"
"A'a kasan bai zama dole ya kawo yar masu kudi ba, ko wata yar manyan nafi zargin yaran talakawa yake niman kawo mana"
"Meye banbancin mai kudi da talaka? Gani nayi dukkan mu bayin Allah ne amma sai ki ta nunawa kamar baki yarda da Allah ba."
   "A'a nifa ba haka nake nufi ba, kawai dai bana son ya dauko mana yar karamar gida ce, kawai kome ayi shi a cikin harkan arziki."
"Latifah kenan,gani nayi ba a haifi kowa da dukiya ba a duniya ya samu me yasa kike nuna son kan ki dayawa, me yasa baki tuna gobenki?"
Dariya da tayi sosai, kafin ta mike tana faÉ—in.
"Wallahi ina da buri akan Mohan, matar da Mohan zai aura ba karamar mace bace, matar da Mohan zai aura zata kasance mai nasaba wacce duk inda zan shiga da ita ce kyawawan tsaro zan hada shi da ita, wacce duk inda muka shiga za a gane yar babban gida ce kamar Hanan"
   Abinda ya fahimta matar shi tayi nisa a don duniya, matar shi tana da mugun son kai, dan haka ta mike bai kulata ba ya barta tsaye tana bayanin abinda take son akan Mohan.
  ....
"Munmohan" ya kira sunanta a sanyayye,
"Na'am Hammah na" ta amsa a hankali, tare da jan hancinta alamar tana kuka, ko kukan yana son zuwa mata. A rud'e ya shiga tambayar ta.
"Babu kome, kawai dai ina hanyar Maradi ne na ma kusan shiga."
"A ina zaki sauka?"
"Gidan nan na kusa da Makarantar"
"A'a zan kira malam ya dauke ki." Ya fada can kuma yace.
"A'a ki kirani idan kin isa"
Baki daya ya rude, ya rasa gane wanda zai kira ya gayawa ya dauki mishi Moonah,
"Moonah! Insha Allah kome dare zan zo gare ki"
"Toh ina jiranka"
Kashe wayar yayi, tare da niman Dan Ba'are.
"Kai zoka kaini Maradi"
"Professor Ibrahim Dan Ba'are, idan ban kai ka ba zaka iya tsine min ne? Dan Ubanka a yanzun ne zamu tafi Maradin ko ce maka akayi Ni sallamamme ne.
   "Kazo idan ba a sallame ka ba ai ni na sallame ka, dalla kazo muje ina jiranka"
"Mohan bana ciki da Iskanci, a wannan daren zamu fita?"
"Kayi hakuri" karon farko da Mohan ya bashi hakuri tabbas ba karamin abu bane. Cikin sanyin jiki yace mishi.
"Ina zuwa Insha Allah" domin tunda ya iya bashi hakuri yasan ba karamin abu bane, dan haka cikin wani irin yanayi, ya shiga had'a kayan shi.
  Kafin dan Ba'are yazo har ya gama, koda yazo babu wanda yasan baya gidan dan sun fita daga cikin gidan.
  **
Karfe tara na isa garin Maradi, dan ma mun tsaya a hanya, gidan da yake kusa da makarantar na isa, ina ganin kiran malam Ansar. Da kamar ba zan dauka ba sai na dauka.
"Kana ina ne?"
"Na shigo Maradi zan tafi gidana da yake kusa da makarantar, kuma Hammah Mohan zai iso an jima" na faÉ—a a sanyayye,
"Ok toh idan dai da wani abu ka min magana."
"Allah Sarki nagode sosai, Insha Allah idan da wani abu zan maka magana."
"Toh" ya faÉ—a min.
"Da fatan ba wani abu bane ya faru?"
"A'a babu kome" kiran Hammah Mohan ne na ga ya shigo min.
"Don Allah kashe zan dauki wani kiran."kashe wayar yayi na dauki kiran Hammah Mohan,
"Kina ina ne?"
"Hammah yanzun na shigo Maradi."
"Insha Allah zuwa sha biyu saura zan shigo kinji"
  "Toh Allah ya kawo ka" na fada tare da tare abin hawa, ya kai ni har kofar gidan, na biya kudin sannan na shiga cikin gidan har yau da jami'an tsaro a kofar gidan.
  Ina shiga cikin gidan wanka nai tare da salallolin da suke kaina, babban addu'a ta, Allah ya sanyayya min zuciyar Innah, amma ban ji dadin yadda tayi ta min miyagun kalamai ba, ko babu kome Innah ce ta reneni, ita ta min kome, Innah ta min gatar da babu wanda zai min bayan shi. Dan haka na zauna nayi kuka nayi kuka har sai da kai na ya fara sarawa ban san ya akayi ba wani irin jiri ya kwashe ni a sallayar na zube.....kuyi hakuri wallahi na gaji ne....
*Nagode sosai Maman Humairah da kawo min ziyara Allah ya bar zumunci ðŸ˜ðŸ’ƒðŸ’ž Ubangiji ya bawa Humairah lafiya Nagode sosai*
#Mai_Dambu..
8/19/21, 6:53 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1108262550?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=cavWiGGyBrCAo%2BWqCLglY3Gs%2BgN1rFoDPpKB0zWz6PoxIH7kodf8pwkn%2Bapj%2BNu2jcr3lLRQ1jZyx3x0Y0w3eVNqEUJhy%2FQFfQ%2FqU6I47IboRfk%2Fq6JpeUV04y6Fe%2BIf
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.