Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 53 of 64
BABI NA SITTTIN.
"Amma" rufe min baƙi tayi, bayan ta kashe karatun.
"Me yasa baki da Fahimta? Ki godewa Allah Kinji, abinda ya jarabce ki a kai kuma ki kara mishi godiya yana sane dake, karki yarda son zuciya ya saki, fadawa fushin Allah."
  Gyada mata kai nayi ina wasa da rigar jikina,sabida ina jin motsin abin cikina,
"Kina fushi da Abie har yanzun ne?" D'ago kai tayi tana kallona,
"Amma ai kina sonshi, tunda gashi har kina zaune a karkashin inuwar shi, kawai kuma shirya kanku ko kuma wannan abin ya shirya ku"
Mikewa tayi sakamakon shigowar shi, tana faÉ—in.
"Allah ya shirya ki"
"Amin Ya Allah" ya faÉ—a bayan ya zauna yana kallona, cikin murmushin jin dadi yace min.
"Ga Budurwan da nayi sunan ta, Grace" kallon Mommy nayi wacce ta tsuke fuska,
"Don Allah? Na ganta Abie amma ai babba ce ko" na tambaye shi ina leka wayar hannun shi.
"Eh talatin da biyu fa"
"La ba wata babba bace, toh gaskiya zamu je mu ganta."
"Haba Kinga kuwa baturiya ce, sai a haifa miki kane farare"
Cikin zolaya nace mata.
"Mommy kece babbar kawar Ango, tunda nasan bai da abokai sai ke"
"Karki kuma saka ni cikin shirmenku" ta wuce fuuuu, aikuwa muka saka dariya, sannan nace mishi.
"Abie me yasa ba zaka gaya mata kana Sonta ba?"
"Ina jin tsoron ta ne"
Kallon shi nayi kafin nace mishi,
"Babu wani tsoro kawai ka gaya mata gaskiya, itama tana sonka fa"
"Da tsufana"
"Itama ta tsufa ai"
"Toh Allah ya sa mu dace"
***
Agadaz.
Kallonsu tayi sannan tace mata,
"Kinsan girman baki uwa? Kinsan yadda Allah yake amsa bakin uwa? Da nace duk wanda ya shiga tsakanin Alhaji da Matar shi ban yafe ba shine kika kashe mishi aure yanzun kin dibo jiki akan Nuratu zata bar D'anta ya auri Kanwar Maimunari"
  "Nahnah yarinyar da Shegiya ce? Sannan taya ma zan so ya had'a zuri'a da mayu, tunda ya sake ta yaron nan bai kuma samun sukuni ba, dan haka nake zargin kama mishi kurwa tayi"
   Kallon tayi na wani lokaci, kafin yace mata.
"Idan har akan Shegiya ce toh ai kuwa Allah ne ya nufa zan haife ku a silar aure, har na auri buzu. Amma duk wanda yake cikin Zuri'ar mu yasan me ya faru a shekaru baya. Hmm Nuratu ki bashi yar ki Jalilah, Allah ya bada zaman lafiya"
  "Nahnah wallahi Mohan ba zai zauna da wata mace ba, Maimunari yake so ki saka baki ta barshi ya dawo da matar shi."
"Wallahi ba zai sake ta ba, Insha ALLAH ba zai sake miki yar ki ba na rantse da Allah." Ta fada jikinta na rawa. Cikin takaici Nahnah ta kalle ta, kafin tace mata.
"Dalla rufe min baki, Ni nace kar ku raba yaran nan amma sake baki da imani shine kika saka ya wulakanta yar mutane. Wallahi ki saka ido kiga abinda Ubangiji zai yi dake tunda baki da imani" shiru tayi cikin yanayin na jin haushi domin duk inda taje niman auren Mohan,kin bashi aure ake.
  "Ni dai ku taimaka min don Allah"
"Hmm! Allah ya gani ba zan yarda ya maida min Y'a bazawa ba, amma babu yadda na iya tunda Nahnah kin saka baki."
"Toh nagode"
"Nuratu kiyi hakuri"
  Kamar mahaukaciya ta fado d'akin, tare da shake wuyar Hajiya Latifah, tana kai mata duka.
"Kun kashe min yarinya na, wallahi sai kun mutu kuma, ba zan yarda ba." Ta fada tare da rufe Hajiya Latifah da duka, sosai ta haukace musu, sai da maza suka shigo aka fitar da ita.
"Wallahi sai na kashe su, tubda suka kashe min Y'a, wallahi sai kashe su wallahi ba zan yarda ba, idan har suka shiga hannuna sai sun mutu."
    Haka aka yi ta dambe da ita, cikin kuka Hajiya Latifah tace.
"Yau na shiga uku, meye nayiwa Karime da zata kashe ni?"
"Sharrin da kuka nemi kulawa yar mutane, shine Allah ya maida muku kaidin ku kanku, Alhamdulillahi da abin ya koma kanku. Wallahi Nahnah kin sani abinda ba zan ki ba. Amma da ba zan yarda Mohan ya auri Jalilah ba, yarinyar da tayi jinyar d'anki ma baki kaunace ta ba, sai yar da baki shiri da Uwarta sabida banbancin ra'ayi."
  "Kiyi hakuri"
"Shi kenan Nahnah" ta faɗa idanunta yana cika da kwalla, domin Uwa ce ba zata iya mata musu ba, amma wallahi da Latifah ne ba zata tab'a yarda ta bawa Mohan yarta ba. A cikin kankanin lokaci aka shirya kome, haka Hajiya Nuratu ta kira Mohan ta gaya mishi, sunkuyar da kai yayi sannan yace mata.
"Umma ba zan sake ta ba, sai dai har ga Allah wallahi Maimuna nake so, don Allah ki ce karta shige min, karta dame ni. Karta shiga rayuwata. Wallahi zan aureta ne kawai sabida ke da Nahnah da kuma Abba sai kuma Khalil ba zan iya cin zarafin ta ba, domin abotar mu dashi gaskiya ce. Kuma ba zan iya juyawa akan abotar mu ba, ba zan iya cutar da ita ba, dan kamar su Radiyah take. Amma ki bata hakuri domin zuciyata yana gurin Maimuna"
Yana gama fadar haka ya juya tare da barin falon, ita kanta ta san gaskiya ya gaya mata, ita kanta ta tausaya mishi, ta kuma tausayawa yarta, dan haka ta ce mishi.
"Insha Allah zan kokarta na nuna mata matsayinta." Ta fada mishi.
"Nagode sosai" ya mike tare da barin gidan, sannan ta kira Khalil ta gaya mishi, kin yarda yayi da nuna mata gaskiya haka cutarwa ce, domin da a bata mishi abotar shi da Mohan, mutuncin shi da Maimunari take gani ya zube.
  Bayani tayi mishi tare da gaya mishi gaskiya ita kanta bata son haɗin, dan haka suna gama wayar ta kira Jalilah ta ci Ubanta da kyau sannan ta gaya mata a abinda yake faruwa. Yar banza dai gata tana ihu da murna, tana faɗin.
"Nice zan auri Ya Mohan! Wayyo Allah na, dad'i kashe ni" ta faɗa tana ihu, takaici da bakin ciki ya sa Hajiya Nuratu ta kai mata duka, cuno baki tayi tana faɗin.
"Ni wallahi ina son shi dama"
"Kaniyar ki da soyayyar yaci kaniyarta, toh shi ba sonki yake ba sakarya kawai."
"Koma meye ni ina son shi" ta fada tana tura baki, dan babu abinda ya dame ta, takaici kamar ya kashe Hajiya Nuratu, domin bata jin a ranta wannan shine hanya bullaliya, abu uku da yake hana mace zaman lafiya a gidan mijinta K'iyayyar Uwar miji, k'iyayyar dangin miji, k'iyayyar miji, wallahi bata fatan ta zauna da Mohan a wannan yanayin na zuciyar shi tana tare da wata. Amma ya ta iya sam Jalilah bata da hankali.
  "Umma Idan na aure shi sai na sashi ya manta da Maimunari, wallahi sai na mantar." Make mata baki tayi,
"Kin ci gidanku, ana gaya miki gabar kina yamma, dan kaniyarki ba zaki tab'a iyawa ba, sadaukarwa da matar shi tayi shi kawai ya ishe shi mutuwa da rayuwar shi, ke kin san so? Kina son shi ne sabida yana burge ki ko? Toh ita ta sadaukar da kome nata ne domin shi, dan haka kar na kuma jin kince kina son shi zaki mantar dashi kome!"
  Cikin jin haushi ta mike tare da barin gurin ita ta sha alwashin sai ta mantar dashi kowa ma, balle kuma Maimunari. Dan haka ta juyar da kanta lallai zata mantar dashi kome har da soyayyar Maimunari.
**
Diffa.
"Ina sonta Baba, wallahi ina kaunar Maimunari, don Allah Baba ka gaya min me yasa kace na rabu da Ita" sunkuyar da kai yayi sannan yace mishi.
"Ka hakura da ita Hisham mahaifinta ba zai baka ita ba, koda kuwa zaka mutu ka dawo! Ka kyale su ba zaka tab'a samunta ba."
  "Baba don Allah ka gaya min meye yasa!" Shiru yayi sannan yace mishi.
"Kasancewar shi Baroro, mutum ne da yasan kan shi, kuma yasan abinda zai yi ya kare kanshi. Ni kuma Mahaifiyata bororo ce mahaifina Bazabarme, shima kuma yasan kanshi, sai dai shi yana rayuwa ne a daji mu kuma muna rayuwa a cikin gari, wani shakara ana bikin sallah, na hadu dashi. Wallahi da farko bani da burin zaluntar shi, sai dai lokacin mun nuna mishi muma bororo ne, yasa ya amince da mu.
   Dan haka bayan sallah mun bishi har inda suke anan muna zauna na tsawon wata shida sai dai muzo cikin gari mu koma, ba dan kome ba sai dai Allah yayi mishi baiwar Ilimi na iya sarrafa Alqur'ani yayi abu dashi, dan haka zaman mu bamu tab'a nuna mishi mun zo cutar dashi bane domin ma bama da wannan alamar a ran mu. Abinda yasa muka shiga wannan al'amarin sai dan yadda muke son mu shiga harkan siyasa da wasu abubuwan. Dan haka muka mai da hankali gurin daukar wasu sirrin Alqur'an, bayan mun gama sai muka fara zuwa muka yi fashi, bayan mun yi fashin shine muka gudu tare da kai cunen shi.
  Lokacin da ya samu labarin abinda muka yi, shine ya maza ya bar dajin. Aka yi ta niman shi. Bamu kuma haduwa ba, sai a hanyar Mali ya tafi da wata mace, itama kamar bafulatana ce. Dan haka matukar ka matsa kana son Yar shi zai iya tozarta ka, don Allah ka bar mishi yar shi."
Cikin bakin ciki ya kalli mahaifin shi, sannan yace mishi.
"Toh meye ya had'a ka da Abbun!" Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Shi wannan Sa'a yafi Ni, shi yasa nayi alƙawarin sai naga bayan shi"
  "Lallai ka fini son kai, dan haka koda za a dawo maka da gawata, wallahi sai na auri Maimunari, shi kuma Ubanta dole yayi hakuri ya bar Ni da ita."
   "Ka hakura ka bar mishi yar shi." Mikewa yayi tare da barin gurin.
"Na rigada na yanke hukunci sai dai a kawo maka gawata, amma tabbas sai na tafi ga abar kauna ta. Idan taurin kai da zuciya dabi'ar ka ce, toh ba makawa na gaje ka."
Daga haka ya fice daga dakin da Ubanshi yake, yana kara bibiyar layin Benazir, da ya karba a gurin yar ajin su. Tunda ya saka a kan google ya samo kasar, dan haka ya kwantar da hankalinshi ya gama hada kome zai nufi Zurich.
***
"Baba Mari Sannun kina ta hutawa!" Na fada ina zama, murmushi tai tare da kallona.
"Yo ni da kun mayar dani Nijar da na huta, na gaji da zaman garin nan" ta faÉ—a tare da kallona.
"Hmm! Babu inda zaki muna tare" shigowa Abie yayi Benazir tana kuka tare da fada mishi ita a'a, don Allah ya amince duk da bana jin English amma na Fahimci kamar an b'ata mata rai ne.
"Don Allah abie kasa baki wallahi na fasa auren shi" gutsiran apple nayi tare da kallon ta.
"Me yasa toh? Idan kinsan baki son shi me yasa zaki bar shi yayi ta wahala?" Na tambaye ta a fusace,
"Addah Munah, ban da bakin munafunci me yasa zasu hada kanwar shi da Hammah Mohan? Wallahi na tsane shi baki daya, ba zan kuma aure shi ba"
  Wani abu naji ya tsaya min a wuya, kafin na had'iye tare da sake murmushin takaici, sannan nace mata.
"A'a karki b'ata soyayyarki akan wani banza da bai san hakkin so ba! Dan haka ki gyara tsakanin ku da Dan Ba'are, bai da matsala" na cigaba da cin apple din, shi kan shi Abie dariya yake mata domin tun d'azun take mishi bori ita kuma gashi nan tazo na gwatsale ta.
"Addah Munah! Haka zaki ce?"
"Toh don Allah me zance miki? Shi yasan me yasa ya gaya miki ai? Tunda Kinga ya iya gaya miki toh sako ya baki, dan haka ki ajiye batun zaki b'ata soyayyar ki dashi, domin babu amfanin haka, tunda yana sonki kuma babu amfanin kiyi fushi dan kawai Mohan zai auri kanwar shi. Sai kiyi fatan Alkhairi ba wai kizo kina cewa kin fasa ba."
"Addah Munah!"
"Kinga karki b'ata soyayyarki, domin kuwa wasu na niman damar da kika samu amma basu samu ba."
  Ina gama fadar haka na tashi na bar musu gurin, na nufi can backyard, na zauna a kujeran da yake gurin, kwalla ce ta shiga zuba min ina sharewa amma kamar sake tulo shi ake wato har Mohan yana da kwarin gwiwar aure..
*Don Allah yau ku barni na huta na gaji baki dayaðŸ‘🼠wallahi*
#Mai_Dambu....
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1115269487?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=I5OLVif069AImr78w%2FlEumcHUFhhjB3GL%2BklLGDEG2mX72ge1I4j4pFlSrPzq7qgVMUX54J2flC9h4g6fi2m%2FvewJigtCSmbiskTJxpG%2BKNCCPD6AHygfMZwtAY2jz%2F0
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.