Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 17 of 64

BABI NA ASHIRIN DA UKKU.

"Mohammed Mamman Nasir Aghali akwai abinda kake boye min" ya faÉ—a tare da kallon Almamoon da yake barci, dauke kai yayi yana kallon yadda Mohan yake kokarin barin gurin da Dan Ba'are yake. Rike hannun rigar shi yayi cikin damuwa yace mishi.

    "Ko akan matsalar shi ne na jinsin mata maz..." Fauce hannun rigar shi yayi tare da nuna Shi da yatsar shi. Kamar wanda aka gaya mishi wani magana mara dadi.
"Karka kuma, kayi abinda na saka bana son kowa ya rab'e shi ne, ni nace ka nisance shi idan kuma ba zaka iya min wannan Alfarmar ba thanks you can go away."

   Mamaki ne ya kuma rufe Dan Ba'are, sama da baya. Kafin ya kalli Almamoon.
"Shi kenan, but i'm in your side babu wanda ya isa shiga tsakanin mu ina tare da kai."

Bude mishi hannun Mohan yayi suka rungumi juna, duk da kowa yasan Dan Ba'are dan uwan Mohan ne ta gurin Uwa kuma sun tashi tare, kome nasu daya ne. Amma haka bai hana Mohan kafkafta mishi rashin daraja ba. Kuma bai tab'a fushi yace ya rabu da Mohan ba, domin kaunar su daga Allah ce.

      "Toh sake ni zan tafi maganar tafiyar ku, duk da mun gama rabin aikin kawai saura naje na karasa sauran ne" inji dan Ba'are,
   "Ok Yaron kirki kayi abu me kyau maza  kaje" inji Mohan ya faɗa cikin zolaya,
   Wani banzan kallo yayi mishi tare da barin d'akin, shi kuma ya koma jikin window yana kallon yadda ake training ta baya, kasancewar asibitin a cikin Barrack yake. Tsayawa yayi sosai yana kallon kome.

     Shigowar Dan Ba'are yasa shi juyawa yana kallon shi. Mika mishi wasu takardu yayi sannan ya kuma fita. Bayan kamar minti talatin sai gashi dauke har da jakar Mohan da kayan shi ya mika mishi. Sannan yace mishi.
"Toh na gama maka kome, Allah ya bashi lafiya"

        Bai rufe baki ba sai ga Nurse sun shigo da gadon marasa lafiya, daukar shi suke son yi, Mohan ya dakatar dasu ta hanyar daukar shi cak ya fitar da shi daga cikin ɗakin, lokacin da ya fitar dashi kallon su Dan Ba'are yayi tare da jin idanun shi na cika da kwalla.
*Karka manta Mohan yayi maka kome a rayuwa Mohan ya baka kome da kake nima! Dan haka ka bar shi da Yaron ko zai sake kamar kowa kafi kowa addu'o'in Allah ya sauya mishi murÉ—aÉ—É—iyar hali dan haka zaman shi da Yaron sai ka ga an dace*
Inji wani shashi na zuciyar shi yake bashi shawara. Ajiyar zuciya ya sauke tare da taka musu baya. Har gurin motar shi tun kafin Mohan ya isa sojoji sun bude motar tare da sara mishi kwantar da Almamoon yayi sannan ya shiga cikin motar dan Ba'are ya shiga gaban motar suka bar asibitin.

         Cikin abinda bai wuce awa daya na suna isa airport din, shi ya fidda Mamoon yana daukar shi tare da daura kanshi daidai kirjin shi. Mamoon ya sauke ajiyar zuciya. Cak ya tsaya tare da kallon fuskar shi jikin shi yana wani irin yanayi. Kallon fuskarshi yayi na few seconds kafin ya nufi cikin airport din dashi.

    "Kamar yayi motsi ko?" Dan Ba'are ya tambayi Mohan, karamin murmushi yayi tare da gyada mishi kai,
"Alhamdulillahi don Allah idan kuka isa ka saka ido akan shi kaji"

Wani banzan kallo yayi mishi tare da dauke kai kamar ba shi ba, haka yasa shi jan bakin shi yayi shiru tare da murmushi. Suna shiga dama kamar su ake jira. Dan haka suna bashi keken majinyata  suka tura shi a kai, sai  cikin jirgin, tare da Dan Ba'are.

Mika mishi wata jaka yayi tare da kallon shi. Da idanun Mohan ya tambaye shi.
*Meye a cikin shi?*

Shima ya mai da mishi da cewa.
_Idan ka tafi ka duba_
Gyada kai yayi tare da mika mishi hannun suka yi musabaha, kafin suka rungumi juna. Babu laifi sun ji babu dad'i da zasu rabu da juna.

       Leka Almamoon yayi da yake kwance a kujera.
"Allah yasa a dace"
Mika mishi hannun yayi a karo na biyu.
"Amin Friend zaka iya tafi" ya faÉ—a mishi tare da tsare gida dan yaga yadda yake leka Mamoon, shi a son shi kar wani yace zai kula Mamoon.

Dan haka Dan Ba'are ya juya yana dariya.
"Khalil Ibrahim Dan Ba'are Nagode da kome"
"Allah ya tsare ya kuma saka a dace."

         Dakyar suka rabu, (sai kace masu aljanun kafin zuwa wani lokaci cutar sanyin su ta motsa 🤣 Wallahi sun cika fada kamar masu ganin hanjin juna) bayan fitar Dan Ba'are, basu jima ba jirgin ya tashi.

            Ya juya a hankali yaji an bangaje shi ana dariya cike da mamaki ya juya, aikuwa Yarinyar ta koma bayan shi.
"Hammah kace kar Didih ta dake ni ba zan kuma tsokanar ta ba" d'ago kai yayi tare da tsare yarinyar da bata wuce shekara goma sha biyar ba ido sai hura hanci take tare da rike k'ugunta, ranta yana kara b'aci sosai. Sake baki yayi sabida wani abin mamaki yanzun yayi sallama da Mohan da Almamoon, amma ga wata yarinyar nan me kama dashi har da tsayin fuskar.

Cikin tsiwa ta juya shiga ƙoƙarin kamo yarinyar bayan shi ya kai hannun shi tare da kare ta, wani irin haduwa jikin su yayi tare da bada Wani sabon rikittaccen al'amari na daban. Kallon cikin idanun shi tayi, sai gashi ta kasa ko magana yayi mata Kwarjini. Idanun ya ne ya cika da kwalla.

"Wallahi Yumnah zan kama ki, sai na fasa bakinki mara kunyar banza kawai" ta faÉ—a tare da kwace hannunta.
"Toh Didih ba naga hoton ki da na Paul bane sai ki ce min solayinki ne Kinga ga Appa can muje."  Inji Ita Yumnah,

    Juyawa Yar budurwan tayi tare da barin gurin, shafa kan shi yayi yana kallon ikon Allah hatta tsayin da tafiyar. Daure fuskar sai dai ita wannan fara ce sosai. Kuma da alama girman kasar Turai ce domin kanta babu dan kwali riga da wando ne a jikinta sai jacket din da ta daura a k'ugunta. Idanun shi ne ya sauka akan Boom ɗinta, da sauri ya rintsa idanun shi.

  "Yumnah" ta juyo tare da kiran yarinyar, aikuwa idanun shi ya dauka akan dukiyar fulaninta, had'iye yawu yayi, tare da kura mata ido.. da gudu Yumnah ta fito a bayan shi zata wuce ya rikota.
"Meye sunan ta."
"Benazir!!" Ta fada a hankali,
"Daga ina kuke?"
"Paris" ta faÉ—a tana kallon shi,
"Yumnah" wata  mata ta kira ta, wacce zaka ga dai ba wata babba bace dan ba zata wuce talatin da yan kai ba.

"Na'am Nanny" ta amsa da gudu, rike hannun matar tayi tare da juyawa ta d'aga mishi hannu. Murmushi yayi mata. Da sauri yabi bayan su tare da kallon Number motar. Shafa kanshi yayi yana murmushi.
"Yar kwaila" shi da kan shi kuma ya kama dariya, tare da gyada kan shi. Yana tab'a gefen kirjin shi kodan kama da Almamoon zai iya sashi bibiyar rayuwar yarinyar.
"BENAZIR!" Ya ambaci sunanta yana kallon motar su, yarinyar tayi karama kuma fa, amma kuma ai bata mishi kadan ba, indai zai sake ta zai iya kuma zai koya mata son, a tunanin shi ba zata wuce 15 to 16 ba, dai dai ya kafa gwamnatin shi kenan. Dan bakin nan da idanun. Jan hancin shi yayi, Allah sarki ya rasa Mamoon Allah ya bashi Benazir! Gyada kai yake kamar kadangaren kafin ya isa gurin motar shi ya shiga tare da rufewa suka bar gurin.

      ***
Niamey.

Babban Ofishin primer minister, yana kallon Chef Judge.
"Yallabai Insha Allah kome zai wuce, sai dai ban da ikon Allah na gama kome Insha Allah babu abinda zai kuma faruwa kuma matsalar na gaya maka daga cikin gidanka ne idan har zaka iya taimakawa na gidan ka zai zama tarihi."

Mika mishi hannu yayi tare da mik'ewa yana faÉ—in.
"Nagode sosai, sai dai har yanzun bai tuntube Ni ba" ya faÉ—a a dame,
"Kai ka tuntube shi." Gyada kai yayi yana kallon shi.
"Ina kewar shi a kusa dani,.Insha Allah yana dawowa aure zai yi"

   "Allah yasa a dace, zan koma." Ya fada tare da mik'ewa.
"Alkali ka tawo da Iyalinka muci abincin dare mana yau" sunkuyar ka dai yayi cikin sanyin murya yace mishi.
"Bani da iyali"
"Ikon Allah sun rasu ne?"
"A'a Allah ne bai nufa ba"
"Sai yaushe? Baka kasan ka girma bane?" Idanun shi ne ya cika da kwalla, tare da jin tausayin kan shi da kanshi yace.
"Insha Allah zanyi" ya faÉ—a tare da barin Office din, cikin sanyin jiki.

           ***
Tafiyar awa uku ya kai su garin Dubai, kafin suka tsaya na tsawon awa daya, kafin jirgin su ya tashi daga birnin Abu Dhabi zuwa Riyadh, sun isa ƙarfe goma na dare, motar asibitin yana jiran su, tunda ya sa shi ya nufi wata motar ya shiga domin akwai wani kamfanin da suka bude shi da wani Yariman saudiyar anan kasar, dan haka suka nufi masaukin bakin su da yake cikin Kamfanin.

     "Mohan kai a ƙasar?" Inji abokin shi.
"Abeed gani nan." Bai gaya mishi gaskiya abinda ya kawo shi ba,.wanka tayi tare da saka jallabiyar shi cream colour..sannan suka nufi babban asibitin Riyadh, yana zuwa suka shiga tattaunawa da likitocin, kafin aka shigar da shi aiki.

      Tun da yayi Sallah yake zaune a gurin,.har kusan asuba. Basu fito ba, ya tafi masallaci ya dawo,   har gari ya waye kafin suka fito dashi babu laifi. A yanzun yana mai da numfashin sa.

         Wani daki akai shi. Tare da sauya mishi kayan shi.
"Alhamdulillahi mun yi aikin cikin nasara,. An tacce jinin shi yanzun sai huhun shi shima an saka allura da maganin zasu yi flushing dattin ko yayi amai ko yayi bayan gari."

Gyada kai yayi sannan yace.
"Mun gode" ya faÉ—a tare da kallon Mamoon.

  Tun daga ranar kome Mohan ya dauka, ranar Alhamis ya shiga macca yayi aikin Umrah,  ya dawo ranar juma'a da dare, rabin addu'o'in shi akan Almamoon da iyayen shi ne da yan uwan shi. Amma karfin addu'o'in shi akan Almamoon ne.
    
Duk da Asibitin ba a zama amma shi saboda yadda suka ga ya damu da majinyacin yasa suka kyale shi, yana kula da duk motsin shi. Amma ta bangaren goge mishi jiki Nurse ne suke aikin nan,  dan har zuwa lokacin bai yi amai ba bai yi kuma kashin ba. Ranar Asabar yana zaune ya kifa kanshi a gaban gadon.

             A hankali na fara bude idanuna, ina jin amai rike zanin gadon nayi tare da yunkurin tashi, amma na kasa jikin babu karfi. Dan haka na dan juya kadan nayi ta amai, kakarin yaji ya farka. Yana tashi ya rungume ni, na cigaba da sheka mishi amai a jikin shi da jikina, sai da nayi aman tas a jikin mu, sannan ya daura kaina a kirjin shi ina jin kwalla na zuba min. Shafa bayana yake tare da cewa.
"Sannun"
Murza kai na nayi a kirjin shi, ya tab'a wani abu, sai ga nurse sun shigo, dan haka ya basu guri suka gyara min jiki shikam fita yayi daga asibitin ya koma gida yayi wanka tare da wanke kayan, sannan ya mai da wasu kayan, ya dawo asibitin ya same ni jingine.

Gashi kayan ya fidda kirjina, sau daya ya kalle ni bai kuma kallona ba, ya mai da hankalinsa gurin rubutun da suka yi.  Kallon shi nake bako daya ya cika min idanuna. Hada min tea yayi tare da zama yana diba da karamin cokali yana bani a baki, amsa nake ina me kallon shi. Har ya gama ya bani magani, sannan ya dawo inda kafana yake yana matsa min su. Mamaki yake bani babu ruwan shi da magana tun sannun da yace min bai kuma magana ba.......

_🙄 Wallahi Na kusan fara rashin Daraja hmmm bana son na dauke labarin daga Wattpad kuma wallahi idan na cire zan dakatar da rubuta shi baki daya ne na Fara na kuɗi na shi kuma zai kai Okada Insha Allah ku bani had'in kai bana son ma fara book din kudi na dakatar da Wannan kuma bana son na sayar da labarin! Idan kuka bari na dakatar tabbas zamu ji babu dad'i bana son haka shi yasa nace kuyi comments da Vote idan babu Insha Allah Ranar Monday Zan fara KISHI a tsakanin zubda jini........iya comments da Vote kawai na bukata domin akwai mutanen da suke buƙatar Bororoji ya koma na kuɗi amma nace a'a kuyi wani abu ko nima na fara rashin Daraja kuma ba iya Pagen nan ba all Pages da masu zuwa👏🙄 Wallahi na iya rashin Daraja na fitar hankali musamman akan Zanen kaddara ta 🤸😒😏😡_
8/19/21, 2:23 PM - My Mtn Number: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

_Eh toh nayi ritaya daga Rashin Daraja! Sai dai kuma an koma Gaba gad'i🤫_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.