Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 64

BABI NA SHA TAKWAS.

A sanyayye na shiga cikin dakin yana tsaye kamar ba zai shigo ba, fita nayi na shigo dashi dakin ina cewa.
"Zauna a kan na shiga ban daki na fito."
Na zaunar dashi na shiga ban dakin na gama uzurina na fito, sannan na dauko mishi maganin shi, na nutsu na tofa mishi addu'a kafin na mika mishi, wani irin duba yakewa maganin cike da kyankyame.
"Ka sha maganinka ne" na fada ina tura mishi maganin a bakin shi, dakyar ya sha yana yunkurin amai, sororo nayi ina mamakin shi. Dafa goshinsa nayi naga ya rintsa idanun shi da karfi, alamar baya son na tab'a shi. Janye hannun nayi ina kallon shi, koda na dauko wanda nake shafa mishi ma, kamar ala dole nake mishi.

Ina gama shafa mishi nace mishi.
"Kayi hakuri kaji magani ne da alamun kafara samun lafiya shi yasa baka son ina tab'a ka, amma Insha Allah idan ka samu lafiya zan tafi na koma inda na fito, sabida kai nake nan" na fada ina shafa mishi ayatul shifa a kafar shi, kwalla na zuba akan gwiwar shi, ina gamawa na mike na mai da maganin sannan na fita niman abinda zamu ci.
Ina gamawa dan Ba'are yana shigowa gidan shi da Malik. Abincin na gabatar musu, kallon Hammah Mohan suka yi da yake tsaye astep ya kura musu ido, yaki saukowa. Mik'ewa nayi cikin rawan jiki zan tafi gurin shi Dan Ba'are ya dawo dani.
"Rabu da dan iska kar yazo taci ya zauna da yunwa dan Ubanshi"
Juya nayi gurin Hammah Mohan Gandhi tsaye, kan shi a sunkuye.
Kwace hannun nayi tare da nufar shi, yana tsaye bai matsa ba, gaban shi na nufa na tsaya tare da kamo hannun shi muka tawo gurin cin abincin. Na ja mishi kujera ya zauna, sannan na zuba mishi abincin. Kallon abincin yake yana kallon nasu, kamar ba zai ci ba.
"Banza dan iska karka ci dan kaniyar ka" haka yayi ta juya abincin sai da na hakura da cin nawa na fara bashi, yana yatsina fuska.
"Ayya abincin babu dadi ko?" D'ago kai yayi yana kallona, kafin ya ture hannuna ya shiga amsa dan ya lura da yadda kwalla yake cika min idanuna, sosai yake cin abincin yana gamawa ya mika min na kara mishi, shafa kan shi nayi tare da cewa.
"A'a ba zaka ci dayawa ba, kaji sha ruwa haka ya isheka kana magani ba a son kana cin da ya fita Muslunci."

"Ai da kin bashi, tunda shi ya zama tumbi iza hana gaya rub'a."
"Auchewww" inji Dan Ba'are, yana kallon Hammah Mohan, cikin takaici da zafi.
"Lafiya?" Na tambayr shi a rud'e.
"Ban da wannan dan iskan zai karya min yatsu shege ciwo bai saka ka daina mugunta ba, Mahaukacin banza kawai" ya faÉ—a lokacin da ya tashi a kujeran yana dingishi.
Rike kunnen shi nayi tare da zaro mishi ido, kawai sai ji nayi ya dauke ni cak ya daura akan cinyar shi da hannu daya. Ya saka ya matse ni.
"Sake ni! Kyale Ni bana son haka" na kwace kai na ina ajiyar zuciya. Make keyar shi nayi tare da kwashe kayan da aka ci abincin. Na nufi kitchen da shi.

Haka dai yanayin shi yayi ta sauyawa har Hammah Khalil ya bar garin, ina kuma kula dashi. Wannan karon karatu yayi zafi bana iya dawowa da wuri sai Malik ya je ya dauko ni, ga Malam Ansar ya taso ni gaba. Kamar zanyi kuka haka yake disgani a gaban jama'a. Bai tab'a sani naji a raina zan mishi yadda yake so ba.

Yau ma da wuri na shigo makarantar, na nufi ajin mu. Ina shiga na same shi yana karatu, dan haka na shiga tare da sallama.
"Zoka fita min a aji"
"Malam kayi hakuri na san sai bakwai da rabi kace zaka..."
Ban idar da abinda yake bakina ba ya kifa min mari, tare da daka min tsawa.
"Fitar min a cikin ajiye, dan iskan Yaro kawai" ya turo ni waje tare da rufe min kofa, gashi ana wucewa tare da kallon mu,haka na juya na bar makarantar sabida ko ina na zaga dariya ake min, danne kuka na nake har ba samu abin hawa, na nufi Jacader. Ina isa na samu sun bude min gidan, ina shiga na taradda sabon tashin hankali. Domin Matar ranar ce ta zo, ina shiga na same shi kamar Almajiri a gabanta yana zaune.
"Sannun da zuwa Hajiya" na fada ina danne kuka na,
"Takowa tayi tare da kifa min mari." Sai da na zube kasa.
"Akan me zaka na barin shi a gida bayan kasan bai da lafiya? Toh wannan ya zama na karshe kar a kuma, ga kuma maganin nan ka tabbatar ka yi amfani dashi maza dauka ka kai daki" jikina yana rawa na kwashe kayan na nufi sama dashi,
"Kai kuma a haka zaka kare, saura kiris burin mu ya cika ba sai kana raye zaka iya taimakawa iyayen ka ba, idan ka isa ka hana mu kashe Ubanka da ita mahaukaciyar Uwarka" ba iya Ni na kad'u ba hatta shi dai da naga ya girgiza, balle ni domin a haukace yake kallon shi, ai kuwa ta shiga marin kyakyawan fuskar shi, da sauri na iso gurin tare da had'a fuskar shi da kirjina, ina bata hakuri.
Nima duka na ta shiga yi tana gaya min.
"Idan baka min aikina ba, tabbas sai na kashe ka kai ma bayan na samu ka kashe shi matsiyata."

Can kuma ta mike tare da ajiye min kudi tana faÉ—in.
"Kayi hakuri raina ne ya b'aci ka dauka kayi min amfani da kome zaka gan shi a rubuce,kaji yaron kirki ka kula min dashi zan maka babban kyauta."

Gyada mata kai nayi ina kallon ta, bayan ta gama ta fita. Zama nayi a gurin na fashe da kuka, sosai. Sabida yau iya maruwa na maru.
A hankali na mike tare da riko hannun shi, muka nufi sama, yana kallona, muna shiga ya ga na fidda kayan baki daya, na zazzage shi a kasa. Daidai hancina yana zubda jini.
D'ago Ni yayi yana me lakutan hancin nawa.
"Kaga babu kome kawai jini ne yake diga."
Na kwace kai na, tare da kwasar maganin kaf na nufi ban daki dashi na juye a masai na tura musu ruwa suka tafi, sai wata yar karamar mutunmutumi a kwalba, ta rubuta.
*A saka a kasan gadon shi ko a yaga rigar katifar shi a cusa maganin lafiyar shi ce*
Dauka nayi tare da nufar bayan gidan yana biye da ku, na nimo fetur na watsawa kwalbar wanda aka soka allurai a jikin abin na watsa mishi fetur na kyasa Ashana. Na jefa bayan na yi kabbara, kwalbar ce ta fashe tare da wani irin bakin hayaki ya tashi sama, ihu hayakin yayi wanda ya haifar min da wani irin ciwon kai da daukewar gani na, na tafi zan fadi yayi maza ya taro ni, daukata yayi tare da nufar cikin gidan dani, da sauri.
Yana isa dakin kasa ya kwantar dani. Yana kallon yadda gefen fuskana ya sha mari, shafawa yayi. Yana kallon yadda nake kwance. Tashi yayi ya ma rasa me zai min, kawai ya fita can sai gashi da ruwan sanyi ya samu fuskana ya juye min baki daya, a firgice na farka tare da dafe goshina, kai na yana mugun sarawa.
Zama yayi tare da riko hannuna yana kallon yadda nake ajiyar zuciya.
Tashi nayi tare da nufar ban daki na, hada ruwan wanka, sannan na cire kayana na fara, tunawa nayi ban dauko wani abu ba, na fito daure da towel a kirjina. Da sauri na nufi inda dama kayana yake na dauki yar abin da zan dauka na na koma ban d'akin.
"Karka je ko ina ganin nan fitowa"
Na gaya mishi ina turo kofar, na cigaba da abinda nake, lokacin da na fito kusa gashina me bala'in yawa ban daure shi ba, na fito haka zube a kirjina, zama nayi ina tattara su,sannan na daure su baki daya, na kuma gyara shi yadda ba zaka tab'a dauka ina da sumar a kaina ba.

Kallon inda nake bai yi ba, alola na koma nayi sannan na zo na sashi yayi.
A tare muka yi sallah, muna idarwa na fito falo da niyyar niman abin da zamu ci na rana, sai ga Malam Ansar ya shigo gidan, daidai ba fito ina gyara wandona, kallona yake cike da tashin hankali lokacin da Hammah Mohan ya fito zip din gaban wandon shi a bude. Rigar shi botir din a balle. Cikin fusata ya nufe ni tare da zare belt din wandon shi. Wani irin mugun tsoro ne ya shige ni dan ba a tab'a duka na ba, kawai ya dage ya tsulla min belt din shi a gadon bayana sai da na daka tsalle, lokaci guda ya haukata Ni da duka.
Rarrafawa nayi ina ihu tare da cewa.
"Don Allah Hammah Mohan ka taimake ni" na nufi ne shi tare da k'amk'ame kafar shi. Jikin yana rawa, tare da kerma ilahirin jikina b'ari yake kamar za a zare ruhina, sabida yau ne karon farko da aka zane ni ban san dukkan ba.

Jin bulalar bata kuma dauka a jikina ba ya sani kara k'amk'ame shi ina kuka me shiga jiki. A hankali ya janye kafar shi daga rikon da nayi mishi, ya murÉ—e malam Ansar da bulalar a wuyar shi kamar zai kar shi, idanun shi sun yi wasu irin jajjur, jijjiyar goshinsa sun mike rad'a rad'a, jikin shi wani irin rawa yake kamar an saka mishi mazari.
Kakarin malam Ansar ya sani, d'ago kai na, ganin yadda Hammah Mohan ya shake shi, da sauri na mike.
"Sake shi ya hakuri bar shi na yafe mishi." Na fada ina kuka.
Sake shi yayi ya fadi, sannan Hammah Mohan ya dawo bayana ya rungume ni yana kallon Malam Ansar. Tare da mishi gargadi da idanun shi da suke cike da b'acin rai.
"Wato dan na hukunta ka shine zaka saka ya kashe ni?"
Bude baki nayi zan yi magana ya juyar dani muka koma cikin dakin. Zama nayi a bakin gadon ina kuka kamar me, ban san ya aka yi ba sai mika min hannu yayi tare da jana zuwa ban daki ya nuna min ruwa, gyada kai nayi. Na fara ƙoƙarin cire kayana ya fita daga ban ɗakin.
Ashe fita yayi bayan ya cire key din dakin ya rufe Ni ta baya, ya samu malam Ansar bai bar gidan ba, damke wuyar shi yayi tare da jan shi kamar kayan wanki ya watsa shi a waje, sannan ta nufi yake ya shiga kwallo shi, baki daya Sojojin ganin abinda Mahaukacin mai gidan su yake yasa kowa ya shiga hankalin.
"Yallabai karka kashe shi." Inji Malik yana rungumo Mohan. Ture su yayi domin ranshi yau yakai kololowar baci, haka ya wulakanta Ansar kamar yadda ya zane Almamoon. Sannan ya nufi cikin gidan lokacin na fito daga wanka zazzaɓi ya rufe ni, na kwanta tare da rufa bargo. Ina rawan sanyi. Fita yayi daga dakin ya nufi dakin shi, can sai gashi dauke da wasu abubuwan yana zuwa ya damu ina kwara amai zazzaɓi yayi mugun rike ni, kai hannu yayi zai ja bargon na rike ina girgiza mishi kaina, kyale Ni yayi tare da ajiye min maganin, har zai tashi na rike hannun shi.
Tare da juya mishi baya ya sha fa min. Musamman yadda bulalar ya fasa min jikina, yadda ya lakato maganin yana shafa min sai da naji hannun shi har cikin jini na yake yawo, tun daga tsoka har ɓargona ina jin hannun Hammah Mohan, yana gama shafa min ya mike tare da barin d'akin mik'ewa nayi na na cire towel din. Ina shafa maganin daga Ni dai pant, ina bin ko ina inda Bulalar ya fasa ina shafawa, sai a lokacin wani tunani ya zo min taya Hammah Mohan ya fahimci ina bukatar man zafi... Na d'ago kai zan yi nazari shi kuma ya bude kofar sai shigo baki daya na fasa wata irin ihu domin dai tsirara nake........😁🤣😜 Ayi sallah lafiya wallahi ko bashi naci sai haka kai Jama'a.... Babu ranar da ba zan ga Sakon Auta ba🙄🙄🙄 ga Yan Bororoji fans ga Mama Mai Voice! Ga Kawar Mommy na, ga Jikar kulu, Aunty Safiya Jos, Sister Fatima Sabo, Aunty Zully, Da My Kawata Mom Abdul, Da Rano 🤣 😂 Lalalala Aunty Mamieh shekaranjiya har da fushi, A'isha Durling har da kirana tsohuwa, Aunty Khalil kan cewa tayi ta hakura dai na gama rashin daraja na ta karanta😁🤣😂🤣😂 Wallahi wannan labarin da alamu sai ya ci kaniyar Kwarkwarah... Fatan Alkhairi 👏 ayi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ina jiran goron sallah....💞💓❤️Team One Love 😍😘❤️
Mai_Dambun ku ce har kullum.
8/19/21, 2:23 PM - My Mtn Number: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

*Barka da Sallah Ubangiji ya maimaita mana*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.