Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 64

BABI NA GOMA

   Fita yayi ya nufi gurin su, tare da gaya niman shugaban yan dakon.
"Don Allah kasan mahaifina  ya kone, ko zaka taimaka min na shiga cikin mutanen ka, don Allah don Allah" ya shiga rokon shi tare da jin kamar kwalla zai zuba Mishi.
"Yanzun kai saurayi! Toh shi kenan, Haliru ga dan gidan Malam Sanda nan a yi aikin dashi"
" Toh shugaba, kai saurayi zo nan"
Da sauri ya nufi gurin su, ya tsaya aka ciro buhun alkama suna tambayar shi.
"Zaka iya kuwa?"
"Insha Allah"
Daukar bugun suka yi tare da daura mishi a kafad'ar shi, sai da yaji kamar zai fadi, amma da ya tuna dusa yaga Innar shi take sakawa da sauri ya cira,  cikin mugun yanayi da rashin sabo, ya nufi hanyar inda zai ajiye, abinka da kuruciya, sam baya tuna kowa sai Iyayen shi, haka suka yi ta kwasar kayan, har asuba tayi, dake bai da tsarki, tattarawa yayi ya nufi gida, bayan an bashi kudin shi da suka ga yadda yayi aikin ma kara mishi kudi suka yi tare da mishi fatan sauki na Babansa.

           Yana isa gida ya zube a gaban Baban shi yana sauke ajiyar zuciya.
"Almamoon! Meye ya faru?" Suka tambaye shi a tsora ce. Cikin sansanyar murya yace.
"Dako" sannan ya ciro kudin ya mika musu.
"Inna Kafadana da wuyana ciwo" ya fada a sanyayye.
"Maza daura ruwan zafi akan wuta, a gasa mishi jiki" inji Baban shi.
"A'a Inna zauna kawai" ya kuma mikawa dakyar ya nufi wajen, ya haɗa wuta, sannan ya daura ruwan zafi, yana zaune sai gyangyadi yaƙe. Har Innar shi ta juye mishi ruwan ta dawo tace mishi.
"Tashi dan arziki irin albarka dan da aka haifa tsiya tana barci ba ta farka ba balle ta rab'e shi"

           "Inna muje ki gasa min jiki don Allah" ya faɗa tare da marairece fuska.
"Toh muje"

Mikewa yayi ya shiga dakin shi ta cire kayan shi, ya dauki jallabiyar shi ya saka, sannan ya nufi ban dakin, ya cire rigar shi tare da zama ya juya bayan shi.
"Innah ki shigo" ya faɗa a gajiye, tana shiga ta kalle shi, cikin tausayawa. Hannunta ta kai kanshi ta shafa gamon da ya tufke gashin kanshi a keyar shi, ita kanta gashin sai da Innar ta warware shi. 
Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halittar farko da karshe, Allahu Akbar. Shi kansa gashin baki ne wuluk, har kasa domin idan ka ce zaka kimanta zai yi wuya.
"Innah don Allah ki saka almakashi ki yanke gashin nan damuna yake,"

"Kul na kuma jin haka daga bakin ka" shiru yayi yana kallon yadda take wanke gashin kafin ga dauki tsuma ta shiga gasa mishi kafad'ar shi, sai lumshe idanu yake.
" Innah"
"Idan ana ban daki ba a magana"  shiru yayi, har ta gama gasa mishi jiki, shima yayi wankan tsarki, sannan ya dauki zanin sa ta kawo mishi ya nad'e gashin. Kafin ya wanke tsumar jinin shi. Ya fito tare da kaiwa dakin shi ya shanya.

   Sannan ya gabatar da sallah asuba da ya tsare mishi, kafin ya kwanta a gurin, sai barci. Wunin ranar a gajiye yayi shi, shi yasa bai farka na sai uku saura ya tashi yayi alola a gurguje yayi Sallah azhar, yana addu'o'in ya fita gurin iyayen shi ya zauna.

   "Sannun ku." Ya fada me jan kwanon abincin, ya fara ci a hankali. Yana gamawa ya tattara kayan kaf ya fita ya wanke su, sannan ya koma dakin shi yayi Sallah la'asar, kwanciya yayi dan har yanzun bai warware ba. Dakyar ya ke takawa, sabida ciwon jikin shi.

        Karfe biyar ya fara shirin zuwa kasuwa, kowa yaje bai zauna ba, haka ya shiga niman aikin yi dakyar ya samu wani kwashe kwata,. Lokacin da ya isa bakin kwatar, kallon gurin yayi kawai ya fara jin amai, babu shiri ya matsa tare da nufar gefe ya zubda yawu, sannan ya nutsu yana tuna hiran da yaji su Innah suna yi.
"Malam maganin ya kare kuma babu kudin saya, wannan kudin na makarantar shi da."

"Adana mishi, karki tab'a Allah zai kawo yadda zamu yi"
Kwalla ne ya zubo mishi, sannan ya shiga ramin bayan ya saka takalmin aiki, ya fara kwashe kwatar, cikin juriya yake aikin har ya gama, sannan ya fita ya wanke jikin shi suka dauki CD dubu biyar suka miki mishi. Saboda sun nime mutane dayawa sai su yanka musu kudi shi kuma cewa yayi aba shi duk abinda ya samu.

   Kamar ya kwanta a.kasa dan murna  dauki kudin ya saka a can cikin wandon shi sannan ya koma inda suke zaune, kasancewar a bakin kofar kasuwa ne a nan yayi Sallah bai bi masalaci ba, yana idarwa yace me shayin da yake Baban Salihu Bukar.
"Baba Ina son na je na sayo maganin Babana, don Allah idan malam yazo ka gaya mishi."
"Toh babu kome" ya faÉ—a bayan ya amshi bayanin shi.

    A gurguje ya nufi gida, ya shiga da sauri yace.
"Innah bani kwalin Maganin Baba"
"A ina"
"Inna babu lokaci bani don Allah" ya faÉ—a mata a wujilance, dole ta bashi tare da kallon shi, ya fita bayan kamar minti goma sha biyar ya dawo, sannan ya dauki abincin shi na dare ya tafi, duba Maganin yayi sannan yace mata.
"Yaron nan da iyayen shi sun tallafi al'amuran shi tabbas sai sun fi kowa moran shi, ina tsoron ranar da zai fahimci ainihin waye shi? Ina jin shakkar tambayar da zai mana, ban san amsar da zan bashi ba"

"Allah ya rufa asiri" inji Innah.

***
Maradi.

    Kurawa wasikar idanu yayi sannan yace mata.
"Baba Almamoon mata maza ce"
"Bana tunanin haka, idan har mace ce abubuwa dayawa zasu bayyana mata, kama da cikar halittar jikin ta, sauyawar ta na girma ko na wani iri. Eh kuma na fahimci wani abu mata maza ce shi yasa jikinta bai nuna alamar mace ce ba sai dai jinin da take."

         Kallonta yayi na wani lokaci kafin dafe goshinsa, idan yace baya kewar Almamoon yayi karya, bai san lokacin da son Yaron ya kama shi ba, amma tabbas zai iya kome dan samun damar rayuwar shi,

Mik'ewa yayi tare da fita daga gidan yana faÉ—in.
"Baba zan fita"
Ya ce mata,
"Allah ya dawo da kai lafiya"

      Koda ya fita makarantar ya nufa, gidan kwanan dalibai ya nufa tare da niman wani abokin karatun. Kallon shi yayi bayan ya fito yace..
"Malam gani" shiru yayi kamar mai tunani, kafin ya juya ya kalli Yaron.
"Tambayar ka zanyi" ya faÉ—a haka yana kallon yaron, kamar yayi shiru. Sai kuma is very important, yasan halin da Yaron yake ciki kowa sunan garin su ne.
"Daga wani gari Yaron nan yaƙe?" Ya tambaye shi yana kallon shi.
"Eh toh gaskiya yace mana daga Damagaram yake, yayi makarantar Annur,"  ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce mishi.
"Bai gaya maka sunan unguwar shi ba?"
Shiru yayi sannan ya kuma kallon malam Ansar, kafin yace mishi.
"Kamar yace gidansu na kusa da makarantar ne."
"Nagode" ya faÉ—a har ya juya zai tafi yace mishi.
"Karka fassara da wata manufa, naga ya tafi ne babu sallama" ya faÉ—a tare da muzurai.
"A'a wallahi."
Ya fada ina murmushi, dan shi bai tab'a shiga wannan shiga cikin shirmen da ake yi a cikin makarantar ba, asalima shi tausayin Almamoon yake, dan haka yayi tafiyar shi.

      ***
Watsar da kayan wardrob din shi yake, watsarwa yake yana wasu irin surutai wanda baka gane abinda yake fada, ga bayan shi kuwa wasu mutane ne cikin bakakken kaya, juyawa yayi tare da niman inda zai cusa kanshi, sake juyawa yayi yaga tabbas matsowa kusa da shi suke.

            A mugun tsora ce, ya fara kokarin shiga wardrob din. Yana daidai sun tawo zasu caka mishi wukar har ya rutsa idanun shi, kawai yaji kamar an tare shi.... Karar da yaji tare da zuɓewa a jikin shi yasa shi bude idanun shi da sauri, ya had'a zufa sosai zama yayi yana kallon cikin kasuwar, sanan ya mike tare da ɗaukar karamar buta ya zaga bayan gidan yayi alola bayan ya kama ruwa, sanan ta dawo ya fara sallah nafilla, yana idarwa ya fito, sakamakon motsin da yaji. A hankali ya zuba ido akan Baba Nasiru.
"Zauna Mamoon" zama yayi yana kallon dattijon.
"Wato kaga rayuwar mun nan! Cike yake da al'ajabi, wasu na farin ciki, wasu na dariya da ban mamaki, wasu kuma masu saka kuka. Karka yarda Allah ya jarabce ka da laluran da bata da magani, karka yarda Allah ya daure maka kaddara da bata da iyaka, duniya cike take da mugaye, kowa da ka gani son kanshi yake, kowa da ka gani son abin duniya yake, kasan dai rijiya mai gaɓɓa dubu, idan ka fada kafin a ciro ka ai kasan ka sheka lahira, toh haka tafiyar ƙaddara take, na farko ba a tanada mata guri, sannan baka shirya mishi lokacin dawowa, sannan tafiya ce da motar da baka da matuki, tafiya ce da ko kana hanya ko baka hanya idan motar ta lalace tafiyar kafa zaka koma.

Kasan yadda tafiyar yake a cikin tsannanin zafin sahara? Toh lallai wannan shine zanen ƙaddara, tafiya a cikin sahara ha zafi, ga babu guzuri, shi babu takalmi da zai rage mak ga zafi sahara, yunwa da ƙishirwa. Sai ya rage maka taki kad'an domin cimma manufar ka da burarrakinka na rayuwa, sai kuma kayi katari da alkalamin ƙaddara, wacce take rubuta fari da baƙi. A lokacin zaka ji duniya tayi maka zafi, kowa ya koma ya zuba maka ido. Allah Sarki sai ka ga lokacin duk inda zaka nufa cike yake da azzalumai.

Duk inda zaka dafa mugaye cike suke da gurin, kowa kokari zai yi domin a sami dama daya tal! Kowa yunkuri yake yaga ya shiga cikin lamarin mutum, amma sai ka tadda zuciya ta kangare sakamakon jin bakon lamari, ƙwaƙwalwar mutum ta gigita. Fansa da rashin adalci ya girmama zukatar mutanen. Miyagun mutane suna karawa juna ilimi suƙa, masoyan asali sun koma a abokan gaba, taurin zuciya da ɗaukar zafin rai, zai zama linzamin farko na jagorancin zuciya, kafiya da rashin makusantan kwarai zai zama janabi na tunkarar mutanen da suke fadi tashi domin kaucewa kusakuran su.

Yaro karka sake lokacin yayi kana me jin haka tabbas zai faru, karka yarda duniya ta baka damar amsar wasikar jaki, Rayuwar da aka gina bayan an saka Allah a cikin shi, bata lalacewa. Duk mutumin da ya dogara ga Allah baya tab'a tab'ewa, idan kaga Abu ya same shi, Ubangiji yayi haka ne domin ta tura mishi wani irin yanayi domin gyara alamarinshi.

Allah ya kawo mu lokaci ne da mutane suka rufe idanun shi da yagar namar wasu, suna taunawa. Allah ya turo mu karnin da bamu da abinda zamu yi domin kaucewa tafarkin mugaye sai Addu'a, ina ma da zaka rike wannan tatsuniyar tawa, da ka kaucewa kuskure mara iyaka. Yaro mutanen da basu san darajar damuwa ba, a duk lokacin da damuwa ta faÉ—a musu, sun kan dimauta su gigita, Yaro kaga duniyar nan tsoro yake bani, gani dai a cikin ta amma ina shakkar mulkin da duniya take.

Wasu mutanen basu da kirki, kana son aikata abin alkhairi, amma sabida sharrin zuciyar su, haka ,zasu yanyayemak da mugun nufin su, irin su basu barin mutanen kirki zama a kusa da mutum sabida sharrin su ya fi ta bakin maciji, fitinar su ta fi ta fitinar karni, bala'in su tafi ta annoba, kai yaro nasan ba fahimtatta kake ba.....

_Don Allah kuyi hakuri 👏👏👏 wallahi na fita ne kuma fitar gaggawa ce ya kama ni! Kuyi hakuri ban cika muku alkawari ba amma muyi Abu daya mu sauya tsarin Posting ku fada min lokacin da ya dace na muku Posting naga kamar zai fi dad'i ayi da daddare sabida kowa ya gama busy na rana, kunga sai ina baku page me yawa ya kuka ce? Ina jiran ra'ayin ku idan kuma zan cigaba da rana ne shi kenan amma idan na shiga busy ba zan iya Posting ba ina jiran ku nagode sosai_

Hmmmm Wattpad ANYA?🙄🙄 Gaskiya toh wallahi zamu sake lalle domin zan bar Posting iya Whatsp.....🚶🏾‍♀�? Maneji....
8/19/21, 12:43 PM - My Mtn Number: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
    Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris

Wani Al'amari...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.