Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 64

BABI NA TARA.

Muhammad Mamman Muhammad Nasir Aghali. Shine asalin cikakken sunan shi, kasancewar sunan shi sunan babans shi da Kakan shi na Uba, yasa aka mishi lakani da Mohan.
   Duk inda kake niman mutum me tsaye akan ra'ayin shi Mohan ya kai gurin, yana da dadin mu'amala. Ga son mutane da yawan Alkhairi, sai dai mutum ne da bai da fara'a sosai , wani hali da mohan yake dashi wanda ba kowa yake iya zama dashi ba wato murɗaɗɗan hali, duk wanda zai zauna da shi sai tayi mugun hakuri dashi, kafin wannan lamari babu me iya gane abinda yake so sai Abokin shi daya tal a duniya wato.
   Captain Khalil Ibrahim Dan Ba'are, kaf duniya bai da Amini sama da dan Ba'are, bai da abokin arziki irin Dan Ba'are shi yasan Meye Mohan yake so, shi yasan Meye baya so, gashi Allah yayi mishi farin jinin Yan mata, shi kuma baya da lokacin su.

   Sau dayawa Yan mata har kawo kansu suke gurin shi, amma haka bai tab'a burge shi ba, gashi da mugun miskilanci kamar wani Balarabe,  ga wani baiwa da Allah yayi mishi na kwarjini, duk lokacin da zai tsaya a gaban ka baka iya koda motsi. Sannan duk da haka baya cin abincin kowa sai na Dadda kakar shi na gurin Uba. Itace kawai yake cin abincin ta.  Sai na Chef Hurayyah, wata yar Kasar Libya da ya dauko ta domin cika mishi cikin shi da abincinta. Domin ta iya girki sosai, balle shi da mahaifiyar shi ta girma cikin Larabawa.
      Babban matsalar Mohan yana da damuwa amma baya iya gayawa kowa sai Dan Ba'are, TOH shima basu cika zama guri daya na, dan haka yakan zauna yayi ta rubutun shi.

       Kafin faruwan Al'amarin da ya same shi, akan ganshi yana yawan zama shi daya ko kuma yayi ta yawo a gonar shi da yake cikin gidan shi, baya cika magana dama kuma halin shine. Wani lokaci kuma zai fito afujajjan ko wanka yake zai fito yana zare idanun shi, mutum me yawan ibada da tsare hakkin Allah sai gashi an wayi gari baya Kaunar jin kiran Sallah, karshe sai dai ya koma daki ya kwanta, ko kuma a sayo mishi wani abun da zai saka shi barci.
Ranar da ya zama mafi muni a gare shi....
Biki ake tsakanin fadar shugaban kasa zuwa inda ake bikin, ko ina ka leka an cika makil, haka aka gama wannan bikin me cike da farin ciki. Kallon shi dan Ba'are yayi sannan yace mishi.
"Muje na kai ka gida" shiru yayi kamar me tunani. Can ya kalli Khalil Ibrahim Dan Ba'are.
"Kace me?"
Ya fada cikin rashin kuzari,
"Muje na kai ka gida" kurawa Dan Ba'are ido yayi, na wani lokaci kafin ya jinjina kanshi.
"Muje" ya kuma nuna mishi hanya, haka ya shiga cikin motar, a sanyayye. Koda ya shiga motar kallon waje yake,.kamar akwai abin da ya manta. Haka kawai ya fara jin kamar ana harbe harbe,. Duk da ya san karan bindiga haka bai hana shi firgita ba, har yana faÉ—in.
"Taka motar zasu harbe Ni"
Ya fada da karfi, abin mamaki shi dai Khalil bai ga kowa ba, haka ya tadda motar babu shiri suka bar gurin sai rike kanshi da kunnen shi yake, har suka isa gida.

Aikuwa a lokacin ne yayi karamin hauka, yayi ta fasa duk abinda ya kai hannun shi, haukacewa yayi sosai, koda aka kira likita, daukar shi aka yi zuwa asibiti, da farko yana gane kome yana magana, har yana faÉ—in zasu nan da bindiga ku bani bindiga na, na harbe su. Haka za ayi ta danneshi ana mishi allura.

  Tun daga lokacin ya daina himm balle humm, baya magana kuma baya fahimtar me kake fada, duk abinda zaka yi sai kayi babu wanda zai ce maka ga abinda yake so. A hankali iyayen shi suka manta dashi, domin yana cika sati biyu zuwa uku, suka ajiye batun shi. Suka saka duniya a gaban su. Hatta yan uwan shi babu wanda ya iya tunawa da shi. Sai dan Ba'are, shima dole ya barshi sabida aikin da yake fama dashi.

Dan haka baya nan kawai sai jin labarin yayi a gurin Hajiya Safiya ta gaya mishi ai an maida Mohan Maradi, shima dalilin da ya sani sabida ya shiga cikin gidan nan ya nufi shashin Mohan, aka ce mai baya nan,. Koda ya nufi gurin Firaminista yace ya fita baya son jin sunan Mohan, itama haka Hajiya Latifah, dole ya nufi Hajiya Safiya ita ta gaya mishi ai Mohan an maida shi can, dan haka akan lokaci ya iso Maradi. Yaga kofar gidan babu masu kula da lafiyar shi, babu kowa sai yan sanda biyu da sojoji biyu, yana zuwa ya ga yadda gidan yake dama Mohan ya sha bashi labarin irin dukiyar da aka zuba a gidan bai tab'a zuwa ba, dan haka yana ganin yadda gidan yake kawai ya shigar da wani bayanai sai ga shi an rundunar sojojin sama da na kasa, da sauran jami'an tsaron,.masu kula da lafiyar shi.

        Haka ba ƙaramin samawa Dan Ba'are nutsuwa yayi ba, dan haka Yasaka aka dauko Hurayyah, da wasu ma'aikata da zasu kula da lafiyar Mohan.

     Wannan kenan....

A hankali yake tafiya ya jika jikinshi Jagwaf, a hankali yake rab'e rab'e, duk inda ya wuce sara mishi suke, haka ya shigo cikin falon tare da sake murmushin jin dadi, duk ma'aikatan gidan suka fito suna kallon shi, sunkuyar da kai yayi tare da haurawa sama da gudu kamar zai tashi sama, cikin tsannanin takaici da bakin ciki Hurayyah ta fashe da kuka, kasancewar tunda ta fara mishi aiki basu tab'a samun sab'ani ba, idan suka mishi laifi baya kula takan su, asalima sai ya daina shiga harkan su, kuma basu isa su daina girki ko kula da shsshin sa ba, abu daya yake musu idan suka mishi laifi, shine kara musu kwanaki a saman wanda suke misali idan yana biyan su duk bayan sati hudu ne, zai mai dashi sati biyar, kafin ya basu albashin su, daga baya ya bari sakamakon wani me mishi wanki da ya rasa Kanwar shi sabida bai biya shi akan lokaci ba, dan yayi mishi laifi.

         Tun daga ranar idan suka mishi laifi sai ya zuba musu na mujiya. Zama tayi ya ci kuka sosai kafin ta kira Bilal, suka haura zama. Sai da suka dauki hodar da Hajiya Safiya ta bada ana saka mishi, sabida idan ya tirje, idan zasu saka mishi kaya dambe ake dashi kamar za a tashi sama, amma idan ya kama mutum sai ya sumar da kai yake kyale ka, haka ba karamin tashin hankali bane. Shi yasa suna shiga suke hura mishi iskar hodan.

    Haka ce ta faru, suna shiga dakyar sha a hannun su, bayan ya musu dukar kawo wuka,sannan suka watsa mishi hodar ya fara barci, ita ta fita Bilal ya saka mishi kaya, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi.

     Suna fitowa dan Ba'are yana shigowa gidan.
"Barka da zuwa Yallabai"
"Yawwa ina Friend yake?" Ya tambaye su,
"Yana sama, barci yake."
Kallon agogon falon yayi sannan yace musu.
"Akan me zaku saka shi barci a irin wannan lokacin? Ko kunsan cewa bayi da lafiya kara mishi wani cutar zaku yi?"
"Kayi hakuri"
"Akan me zanyi hakuri? Jiya ma haka nazo ban ganshi ba, yau ma haka nazo har na tafi ban samu ganin shi ido biyu ba, me yasa kike saka shi barci?"
"Sir"
D'aga musu hannun yayi sannan ya wuce abinshi,ranshi yana barci dakin shi ya shiga tare da zama a kusa dashi, yana kallon kamilalliyar fuskar shi me dauke da kwarjini, rike hannun shi yayi.
"Friend!" Ya kira sunan a hankali.
"Kana cikin wani irin yanayi, ga Abbinka ce makiya sun sako mishi fitina a gaba" kamar wanda aka tashe shi ya bude idanun shi, kafin ya mai dashi ya rufe.
"Friend ka tashi haka, Mahaifinka yana bukatar ka, duk da bai san kome akanka ba amma yana bukatar ka a kusa dashi" ya faÉ—a kamar ya zubda kwalla,
Shafa kanshi yayi yaga yadda ya tara gashi yasan shi ba mutum ne da yake son zama babu gashi ba, dan haka ya shiga cikin ban dakin shi ya fara. Diban shaving cream, yazo ya shafa mishi sannan ya koma gefe ya duba jikin shi zuwa maran shi yasan da hankalin Mohan baka isa ganin dan kamfen shi ba, balle kuma jikin shi da yake riritawa.

Haka ya aske a shi tass, sannan ya gyara mishi kwanciyar shi. Kana yayi shi sai da safe. Koda ya sauko damuwa ya shiga saura kwanaki ƙalilan ya koma gurin aikin shi, dan ma sanadin rashin lafiyar yasa an dakatar da Mohan har ranar da zai sami lafiya.

    Shafa kanshi yayi yana nazarin abinda ya dace yayi akan Mohan yana son niman Mutum me gaskiya da Amana ya bashi kula da Harkokin lafiyar shi amma gani yake kamar babu wanda ya dace da kula da Mohan sai shi. Toh a ina ya dace a fara nima mishi wanda ya dace. Dan haka a cikin kwanakin da suka rage zai maida hankali sosai gurin niman wanda zai kula da lafiyar shi. Da wannan tunanin ya bar gidan.
***
Washi gari.
Da sassafe Almamoon ya bar gidan, ko karyawa bai yi ba. Abinda ya d'aga mishi hankali, mahaifan shi da yake mafarki dasu, haka ya mugun d'aga mishi hankali, shi yasa yaji gwara ya tafi yasan halin da suke ciki. Tun a hanya yake kuka haka kawai yana jin wani irin yanayi mara daÉ—i. Har suka isa garin Damagaram.
Daga tasha ya sami abin hawa zuwa gida. Haka kawai jikin shi ke kara sakewa, har ya shiga cikin gidan. Ya hango Innar shi tana sura hatsi.
"Assalamu alaikum"
Sake tabaryan tayi tana me dafe kirjinta.
"Almamoon?" Ya tambaye shi tare da kura mishi ido. A hankali ya taka jikin shi yana wani irin rawa.
"Innah!" Ya kira sunan a hankali,
"Na'am Almamoon"
Ya isa gaban ta tare da fashewa da kuka.
"Ya aka yi?" Cikin kuka ta fara magana,
"Ina Abba? Me yasa ya haife ni tunda yana son duniya tasan Ni? Na gaji sai zagi na ake ana aibanta ni?"

Daga bayan shi yaji gyaran muryan Baba daga daki.
"Baba na" ta juya tana me zare idanu, sakamakon kallon yadda wuta yayi mishi illar, amsa sallamar da yayi ya dakyar, zaman yan bori Almamoon yayi tare da sake wani irin kuka.
"Innalillahi wa'inna ilahirajoun,.dama abinda ya faru da kai kenan, wayyo Allah babana" ya rarrafa da sauri kamar zai kifa akan shi. Sai kuma ya zauna, tare da hade hannun shi,.mik'ewa yayi tare da bude jakar ya shiga zazzage kayan ciki..ya ciro kudin da yake samu a gurin malam Ansar ya juya zai fita.
"Zo nan" dawowa yayi da baya, ya zauna tare da kallon shi.
"Meye zaka yi?"
"Baba magani zan sayo maka"
"Barshi ka bawa Innarka kudin a kara mana a cikin abincin da zamu ci ko?"
Gyada kai yayi tare da sake wani irin kuka, d'aga labulen dakin yayi sannan yace mishi.
"Baba kana son wani abu ne?"
Ya tambaya hawaye na zuba mishi, sake kallon baban nashi yayi sannan yace mishi.
"Ko kana jin zafi ne?"
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Almamoon! Bana jin zafin kome sama da hawayen ka, ka daina kuka bana son ganin kukan ka"
Gyada kai yayi tare da rike rigar shi. Ya wani ja hancin shi, tare Sake shashekar kuka, muryan shi a raunane yace.
"Baba zan fita niman aikin yi ne"
Yadda yake maganar zai d'ago maka da sallar yarinta shi, yana yi yana wani murɗa yatsun hannun shi. Lips din shi sai wani irin rawa yaƙe. Yana kallon Abban shi.

Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Karka damu, Allah yana sane damu."

"A'a ko Allah yace a fita a nima don Allah ka barni na fita Insha Allah."
"Kana hauka ne? A kananun shekarunka zaka fita wahala, ai rayuwar mu dan kayi farin ciki muke, bawai dan kayi wahala ba, babu inda zaka"

Kallon su yayi tare da sake baki.
"Toh ni me yasa baku barina nayi rayuwa irin na kowa ne? Me yasa kuka tsani nace zan fita ne?" Ya fada yana ihu, sabida takaici.
Baki daya suka taru mishi, tare da rike hannun shi.
"A'a Almamoon! Karka mana haka, tsoro muke ji kai yaro ne, tsoro muke ji kar wani ya cutar da kai? Ka"

"A'a wannan ba hujja bane, kawai ku bari na koma aikin baba Insha Allah babu abinda zai faru" ya faÉ—a yana share kwalla,
"Don Allah" ya kuma fada a karo na biyu, haka ya cigaba da rokon su yana kuka,rike hannun shi suka yi tare da cewa.
"Zaka koma makaranta dan shine"
"Insha Allah zan kama kai na, amma don Allah ku barni na tafi aikin kun ji" 
"Shi kenan" suka fada tare da kallon shi, basu so amma saboda kaunar da suke mishi yasa suka amince, rike hannun shi suka yi sannan suka ce mishi.
"Don Allah karka bari wani rudin duniya ya rufe maka ido, ka tuna da mu,.muna raye ne sabida kai. Don Allah ka yi abinda ya kai ka"

      Gyada kai yayi sannan malam  Ya gaya mishi inda zai tafi, a dace.
   Cikin farin ciki ya tafi kasuwa da wata ƙatuwar rigar shi irinta Bugaje, sai uban rawanin da ya buga. Da takalmin roban shi, yayi mugun kyau, yana zuwa inda baban shi yake zama yayi musu bayanin waye shi.

     Kai shi ruwan chairman aka yi, yayi mishi bayani. Murmushi chairman din yayi sannan ta saka aka mai da shi kan aikin baban shi,

    Haka wunin ranar yaki zama a bakin kofar kasuwa, dako ya shiga fafa, duk da bai saba ba amma duk inda ka ganshi yana mugun gajiya, dakyar yake ɗaukar kayan, bai bar kasuwa ba sai dab Magarib ya dawo gida ya basu duk kudin da ya samo, yaci abinci yayi wanka ya sauya kayan jikin shi da tsumar jikin shi, sannan ya kuma komawa kasuwar bayan yayi musu sai da safe.

          Kirga kudin suka yi CF dubu biyu, kamar su zuba ruwa a kasa.
"Dakon yayi mishi nauyi halittar shi ba irinta maza bane idan ya cigaba da irin wannan abun." Kura mishi ido tayi sannan tace mishi.
"Wani abu zai faru dashi ko? Ban taba jin haka a raina ba, kamar yadda yake rayuwa cikin maza" ta fada tana share kwalla,
"Addu'a zamu mishi Allah ya kare shi."

  ...
A kasuwa kuwa cikin dare aka kawo kaya, haka ta tashi yayiwa abokin aikin baban shi bayanin zai tafi aiki, bai hana shi ba. Haka ya nufi kasuwar ya........
Kuyi maneji, wallahi na saka shiririta ne a gabana wallahi 😜🤣 Yawwa masu tambaye account ɗina zasu sayi Aliyu Asadullah gashi nan, 0472282105 Ramlat Abdul Rahman Manga GTBNK...
#Comments!Share!Vote...
#Mai_Dambu,
8/19/21, 12:43 PM - My Mtn Number: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
    Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris

  *Hmm! Kalma ce da take kunshe da ma'anoni bila'adadin! Koda yake bana ce ba! Ba kuma zan fadi ba Amma idan har zan fadi gaskiya ku din masoyan gaskiya ne ba masoyan bogi ba. 🤣😜 Wato masoyan Mata maza, #Team Majnunu! Mukan Yan tawaye ne❤️🙄 Team Malam ANSAR*

Wata Rayuwar..
BABI NA SHA DAYA..

Dariya ce ta so subuce mishi, ya kalli Baba Nasiru, sannan ya ce.
"Ina fahimtar ka, kawai maganar  ce tayi min nauyi sosai. Na gaza gane me kake son ka fahimtar dani"
 
Tashi yayi dakyar ya nufi ban daki yayi alola sannan ya fito yana faÉ—in.
"Wata rana zaka tuna da haka"
Ya fada tare da nufar masallacin. Shima sallah yayi a cikin dakin, sannan ya zauna yana nazarin, mafarkin shi da. Can ya tuna da halin da yake ciki, iskar bakin shi ya ja, yana kallon hasken da rana da yake hudowa ta  gabar. Ranar yayi wani irin kyau ta bada Wani irin yanayi, a hankali ya fito waje yana kallon yadda garin yake washewa. Shaƙar iska yayi me dad'i da ni'imar safiya.

   Ya lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi, yana cikin nutsuwa.
"Kasan wata ƙaddaran tamkar hudowar rana ce, idan ta shigo bata tab'a barin ka har sai tabbata akan ka."

    Kallon inda hasken ranan yake murmushi yayi sannan tacewa Baba Nasiru.
"Zan koma gida" ya dauki kayan abincin shi ya juya tare da fita a kasuwan, yana isa gidan wanka yayi, Almamoon akwai tsafta ga son kwalliya, dan haka ya gama kome yana kallon Innah, sannan ya shige dakin ya kwanta. Barci me nauyi ya dauke shi.

    ..... Haka rayuwar su, take tafiya cikin ikon Allah da kuma matsin rayuwa, ga jikin Baban shi sai ruruwa yake, Nana cikin wannan yanayin aka yi sata a kasuwa, ai kuwa aka kama Almamoon. Aka rufe halin kunciin ya kuma rub'anyan sama da haka, rayuwar ta kuma ta'zara.

   A wannan gaɓɓar halin da Innar shi take ciki kawai ya isa ya karya maka zuciya, domin wallahi ba karamin matsanancin rashin hali take ciki ba.

Ga ciwon Baban ya matsa mishi, wasa wasa sai da Almamoon ya cika sati biyu, sannan aka sake shi ya dawo ya daku, yayi laushi ko magana baya iya yi. Kwana shi uku yayi bai san inda kanshi yake ba, sai da ta haÉ—a mishi ganyen Tsamiya da wasu sassake ta dafa mishi yayi wanka, yana sha kafin Allah ya bashi lafiya. Sai dai kuma halin da yake ciki na rashin abinyi ga rashin abinci sai Innar shi ta tafi Bara suke samun abinda zasu ci.

     A hankali kwanaki suke tafiya, watanin suna kara nisa, abin mamaki Almamoon ya cinye zangon karatun shi a gida.

     ----
Burin shi nason zuwa ya duba Almamoon bai samu ba, sakamakon tura shi wani yanki da kayi na aikin zaɓe,yana dawowa kuma yayi ta faman zirga zirgan asibiti da Umman shi, baki daya yaron ya tsaya mishi a ranshi, ya rasa gane wani irin kauna yakewa Dalibin shi, a iya sanin shi. Dai kaunar da yake mishi bai kai yadda yake ji ba a baya, amma rashin dawowar shi makaranta Yasaka shi jin kamar zuciyar shi ce a Damagaram.
  *
Yau ta kama lahadi.

Gyara mishi gashin kanshi dan Ba'are yake, cikin kulawa da nutsuwa. Duk da yaki tsayawa amma kuma haka bai hana shi gyara mishi sumar da yake kanshi buyayya haka nan ba.

         Wayar tafi da gidanka na shine yayi kara. Dauka yayi sannan yace.
"Kaga Bama bukatar mace? Namiji muke bukata don Allah kar ya wuce nan da kwana uku, matukar ya wuce haka da akwai matsala bana son tafiya na bar mara lafiyar ne"

Kome aka gaya mishi sannan tace.
"Alhamdulillahi, ku taimaka min daga fadar shugaban ne kuma albashin akwai kyau Insha Allah babu matsala, Nagode sosai"

      Sannan ya katse kiran, yana jin kamar ya janyo kwana ukun zuwa yau, dan an addabi rayuwar shi da kira, ya dawo bakin aikinshi. Bayan ya gama mishi gyaran gashin kanshi ne ya kuma dawowa kan fuskar shi, a nutse yake gyara mishi fuskar. Shi dai yana zaune sai yadda aka yi dashi, yana gamawa ya kama mishi gyaran farcen shi, har ya gama sannan ya mike ya haɗa mishi ruwan zafin wanka.

   ***
Ofishin shugaban jami'ar, shiru yayi sannan yace mishi.
"Yallabai yaron nan haziki ne, idan aka kore shi ba a mishi adalci ba, don Allah karka yanke hukunci Ni zan tafi garin su na duba bashi, don Allah yallabai ka du..."

Daukar wayar gaban shi yayi ya fara waya, ya jima yana magana kafin ya ajiye. Har ya manta abinda Malam Ansar yake rokon shi nan ya shiga rabtabo bayanin.
"Wai ana niman wanda zai yi jinyar wani na hannun damar shugaban kasa ne, kuma namiji matashi, sun hadani da aiki ina zan samu me wannan yanayin kuma wai basa son mace, don Allah ka taimaka min ka tayani cigiyar."

"Toh yallabai ya batun Almamoon?" Ya fada a marairece,
"Zan duba ka fara duba min yaron idan ma ta kama ma waye ka kawo min   zaka nima akan aikin shi kenan, albashin sa na farko nawa ne, sauran kuma zamu yi ta kashe mu raba"

  "Hmm! Toh zan duba maka. Mun gode da alfarman da kayi mana daura dari biyu a fara jarabawa, dan haka Insha Allah zan tafi har Damagaram ɗin." Ya fada tare da gyada kanshi.

       Mikewa yayi tare da ɗaukar kayan shi ya fita, yana me cewa.
"Insha Allah ba zan koma gida ba dai na nimo inda kake" ya faÉ—a cikin motar shi, ya bata wuta. Gidan mai ya fara tsayawa ta cika tanki, sannan ya dauki hanya.

---
Karfe shida na yamma yana zaune a kofar gidan su, dake basu da nisa da Makarantar da yayi, yana hango motar kamar ya santa, Amma haka ya kura mata ido, har ta iso gare shi. Mik'ewa daga kan dakalin ya tunkari malam Ansar.
"Barka da zuwa Malam" zuba mishi ido yayi ya kara lalacewa bakin shi ya karu ainun. Fitowa yayi yana kallon shi, sunkuyar da kai yayi yana wasa da hannun shi.
"Baka iya tarba'n baki bane?"
Da sauri yace mishi,
"Kayi hakuri mu shiga daga cikin gidan."

Almamoon yana gaba Malam Ansar yana baya, har cikin gidan. Inda yayi mishi shimfid'a a kusa da inda Malam Sanda yake zaune, yana fama da sauran mikin wutar da ta kona shi.
"Barka da zuwa malam" inji Innar Almamoon tana kawo mishi ruwa, "Yawwa nagode Inna"

  Gaishe gaishe suka yi, kafin dai ya kawo dalilin zuwan shi. Mik'ewa Almamoon yayi Tare da cewa.
"Ni dai bani komawa ko ina, zan zauna da iyayena babu wanda yafi dacewa da kulawa da lafiyar su sama da ni, sannan babu me taimaka sama dani, idan na tafi waye zai kula da lafiyar su? Idan na tafi waye zai nima musu abinda zasu ci? Ba kowani lokaci ake samun abinda ake so ba.

         Koda zaka samu dole sai ka dandani azabar da kowa ke sha, Na gode sosai malam" ya faɗa cikin sanyin murya, duk sai son shi da kaunar shi ya cika mishi zuciya, ya kuma jin yaron ta cancanci yayi rayuwa me kyau da tsada, toh amma shima ga halin da yake ciki, mahaifiyar da duk wata take cinye sama da rabin albashin sa, ga bikin kanen shi biyu da aka saka. Duk sai yaji babu dad'i Meye ma ya kawo shi?

     Kurawa Baban Almamoon yayi ido, kafin yace musu.
"Ku saka baki ya koma makaranta Insha Allah zan nima mishi aikin da zai rike kan shi da kuma baki ɗaya"  dukkan su a lokaci guda suka zuba mishi ido, sabida rashin yarda da ya shiga zukatar su. Ganin irin kallon da ake mishi yasa shi gyara zaman shi sannan ya fara da basu labarin yadda suka yi a ofishin shugaban jami'ar.

"Idan har daga jikin firaminista ake niman shi toh ba makawa ba iya kune kuka huta ba, hatta wasu zasu huta a jikin ku, bawai dan na rena muku bane sai dai ina son yayi rayuwar da zata saka shi farin ciki ne, kar ku damu ni ma kamar dan ku nake, don Allah ku fahimce ni".  Shiru suka yi kafin ya cigaba da cewa.
"Wani sana'a kike anan?"

     Sunkuyar da kanshi yayi tare da labarta mishi ko sati biyu bai yi da fitowa ba daga ofishin yan sanda, sakamakon abinda ya faru. Idanun shi sunyi jajjur,
"Dako fa?" Ya kuma tambayar shi.
A hankali ya saka hannun shi a cikin aljuhun wando shi ya ciro kudi masu kauri, ya ajiye musu.
"Ku dubi girman Allah ku taimaka gobe ya dawo makaranta, ba nazo dan na tilasta ku bane, a'a nazo ne dan na tsayawa dan uwana kanina zan tafi Nagode ga wanna Ku sayi magani"

     Duk da suna cikin damuwa da matsin rayuwa, bai hana su ce Mishi.
"A'a , bawan Allah mun gode Insha Allah zamu turo shi amma ka dauki kudin nan kai Almamoon dauka ka bishi da abinshi mun gode"

    Cikin sanyin jiki ya zuba musu ido kafin yace musu.
"Baku yarda dani ba kenan?" Yadda yayi maganar yasa Malam Umaru yace mishi.
"Allah ya kara budi mun gode sosai, Allah ya tsare hanya Ubangiji ya jibanci alamarunka"

Cikin wani irin jin dadi yace mishi.
"Amin Ya Allah Nagode sosai baba Allah ya baka lafiya, Toh sai an jimanku Almamoon sai na ganka kenan" mik'ewa yayi suka fita. Mika mishi hannu yayi, amma fir ya coge, sai ma yayi kamar bai da lafiya.  Shiru suka yi dukkan su.

    ...
Bayan fitar su, a kidime Innar Almamoon ta kalli Malam,
"Malam!" Ta kira sunan shi a sanyayye,
"Kabo, bana son damuwa akan Almamoon. Ba wai dan ina cikin tsannanin rayuwa bane, sai dai ba zan ji dadin yaron ya kare rayuwar shi anan ba, kamata yayi ya tafi koda babu aikin da zai yi a jikin masu kuÉ—in."

"Malam ba haka bane, na hango tashin hankali a kwayar idanun malamin, na hango kaunar Almamoon a cikin idanun shi."

    "A'a ki kyautata zaton ba wai ki munanan zato ba, ban ji dadin abinda kike tunanin ba."  Tana son yin magana amma sabida yadda malam yaki amsar uzurin ta, yasa tayi shiru.

....
"Almamoon!" Kasa d'ago kai yayi dan yasan yana nan yana kare mishi kallo,
"Almamoon dama irin wannan rayuwar ne ya hanaka zakewa a ko ina? Me yasa baka gaya min ba tun farkon zuwanka makaranta a nima maka aikin yi yadda zaka rike kanka da iyayen ka? Me yasa baka tab'a gaya min ba?" Ya tambaye shi cikin wani irin yanayi. Tar ya kalle shi kafin yace mishi.
"Bana niman taimako a gurin kowa sai Allah, bana son wanin da ba Allah ba ya goranta min, sannan idan daga haduwar mu nace maka ina son ka nima min aiki ya zaka ji? Dan haka ya yankewa kaina damuwar Kowa sai na iyayena, yanzun ma zan yi shawarwari dasu idan suka amince na dawo shi kenan, idan basu amince ba kayi hakuri. Na iya talaucina" ya faÉ—a kai tsaye ba zaka tab'a tsammanin zai iya fadar haka ba, domin babu shakka ko wani abu a ranshi sai ma tsantsar gaskiya wanda daga kin shi sai b'ata.

     Shafa kan shi yayi tare da hura iskar bakin shi yace mishi.
"Ba zan yi kasa a gwiwa ba, idan har baka zo ba gobe jibi Insha Allah zan zo" daga haka ya juya tare da shiga motar shi. Har ya bar Unguwar, kallon motar Almamoon yake.
"Hm" ta faÉ—a tare da shiga cikin gidan. Yana shiga ya lura da Innar shi fushi take dashi.
"Inna" ya kira sunanta,
"Wato baka jin maganar mu ko? Me yasa ba zaka gane yanayin ka da na sauran mutane bane? Sai da muka baka shawara kan babu ruwanka da mutane amma kayi kunnen uwar shegu damu, Allah ya baka sa'a tunda ka jajjubo shi."

         Kamar wanda aka dasa, haka yake tsaye bai tab'a ganin irin haka ko ji ba, sai gashi lokaci guda kome ya sauya.
"Kai Almamoon zoka dauki kudin nan kasayo sabulu ka wanke kayanka gobe ka koma makaranta ko baka yi aiki ba, ai bamu ke daukar dawainiyar ka ba, tallafi ka samu, ina me rokonka da ka kame kanka. Insha Allah babu abinda zai faru sai Alkhairi babu ruwanka da kowa, don Allah ka rufa mana asiri. Ka ji"

"Baba ni ba zan koma ba" ya faÉ—a kan shi a sunkuye, shiru ne ya ratsa tsakanin su, kafin Malam Umaru ya sake wata magana kamar saukar aradu.
"Aminatu kenan, ba sai kin gwada min karfin ikon ki akan Jinin Sama'ila ba" ya fadi haka tare da mik'ewa, ba ita ba hatta Almamoon sai da ya mike tsaye.
"Malam!!!" Ta kira suna shi jikinta na rawa.
"Ayya Ayya Ayya Malam, Ayya Malam me yasa? Malam alƙawari bai ce haka ba, Malam me yasa zaka nemi kifar min da miyar da na jima ina wahalar had'a shi? Malam me yasa zaka kunce min zani lokacin da ban shirya kuncewa ba, Ayya Malam Ayya Ka yi min adalci kuwa? Malam me yasa baka Cigaba da YAKANA ba? Malam karka tulamin kasa a idanu mana, karka sare min gwiwa ta mana, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji."

  Shi kanshi bai zata maganar zata iya fitowa a bakin shi ba, kallon su Almamoon yaƙe, kafin yace.
"Waye Sama'ila da nake amfani dashi a makaranta?"
"Sunan Baba nane" inji Malam, sabida ya dauke hankalin Almamoon daga batun, ita kuwa Innar had'iye kukan tayi lokaci guda, haka kawai Almamoon yaji a ranshi, akwai abinda suke boye mishi, amma koma meye wata rana zai fito. Daukar kudin tayi tare da yafa mayafinta ta fita, sayo sabulu, kafin ta karasa ta tsaya a wani lungu. Ta fashe da kuka, sai da ta durkusa a kasa tana wani irin kuka. Me yasa malam yayi mata haka?  Me yasa ya zab'i cilla rayuwar Almamoon wata duniya, me yasa ya aikata haka? Komawa tayi tare da zama.

   Tayi kuka kamar ranta zai fita, kafin ta goge idanunta, sannan ta nufi shagon, ta sayi abinda zata saya. Sannan ta juya tare da komawa gida.

        Ita da kanta ta ware kayan Almamoon ta wanke mishi aka kiran magarib tana shanya kayan, sannan ta zauna bayan ta ga Almamoon yana alola.
"Gama ka bani butar na taimakawa malam"
"Toh ina"
Haka ya gama ya mika mata bayan ya cika ruwa a cikin butar, ya shiga dakin sallah.
"Malam gashi" ta faÉ—a tare da dauke kanta daga gare shi. Riko hannunta yayi cikin nashi yana faÉ—in.
"Nasan nayi laifi, amma haka ba yana nufin b'ata miki rai bane, idan har sabida kin yi fushi yace ba shi komawa makaranta waye zai gaya mishi yaji? Rayuwar shi zaki duba? Waye shi ba shi bane me muhimmanci ba, rayuwar shi na gobe shine mai muhimmanci.

     Idan da ace sabida ke ce wallahi ba zan saka baki ba, amma dake saboda yaron ne dole na saka baki, yana miki wata irin kauna ce ba iya ke ba hatta ni, kaunata yaƙe, sabida mu ya sadaukar da karatun shi ashe ba zamu tsayawa rayuwar shi dan wata dama ta same shi ba? Kinsan mutanen da suke niman dama irin da ya samu yau? Wallahi ba kwadayin abin duniya ya sani amsar wannan batun ba, sai dan rayuwar shi, ai ko babu kome zaki duba ki ga waye shi?

     Ina zai shiga? Meye Allah ya ƙaddara mishi, shin zai iya jure ƙaddaran shi? Shin meye mizanin ƙaddaran shi? Wannan shine abinda nake son ki Fahimta, amma idan kin fahimta idan baki fahimta ba, ki barshi yayi ya zama. Allah yayi mishi baiwa amma zai kare ta a matsayin dan dako, nasan waye na ke zaune dashi. Tunda nake da yaron nan bai tab'a ɗaukar abin wani ba, amma lokaci guda an daura mishi laifin da bana shi.

    Idan muka ce kullum gudun ƙaddarar shi zamu yi wata rana ba zamu iya gudu ba, kyale shi ya fita yayi rayuwar shi kamar kowa, ya fahimci muhimmancin rayuwa, ya san yadda Goben shi zai kaya, idan muka cigaba da boye shi wata rana zai iya tambayar mu me yasa? Ina jin kunyar na gaya Mishi waye shi.

Don Allah Karki Cigaba da abinda kike aikatawa, don Allah na hadaki da shi karki kuma abinda ya sani magana."

Share kwalla tayi tare da SUNKUYAR da kanta.
"Malam don Allah karka kuma haka"
"Insha Allah ba zan kuma ba, leka karki kuma ki barni nayi iko da shi." Ya faÉ—a,
"Inna yau ba zaki mana abinci bane?" Ya fada tare da tura baki,
Tashi tayi tare da cewa.
"Ga tsakin can dambu ne" zama yayi tare da kallonta,
"Innah dambun kuma?"
"Ina da zogale da busheshen lawashi"
"Inna da magarib zaki mana dambun?"
Ya fada kamar zai fashe da kuka, haka ya mike.
"Toh zoka sayo maka makaroni." Da sauri ya mike, tayi mishi lissafin, bayan ya mike ya dauki kudin ya nufi shagon unguwar.

Tun daga nesa ya hango yan daban, sunan shi Shege. Cikin shi ne ya cika da ruwa, haka ya isa shagon ya gama sayayyan shi, sannan ya juya zai tafi, yaji an matse mazaunin shi. Maganar gaskiya Almamoon yana da halittar mazaunai, duwawun suna nan masu dan tudu, ba laifi abinda yake jan hankalin matasan yan daban suke bibiyar shi.

Shege dan iska, yana bin mata da maza. Tun shekara daya da ya wuce yaga Almamoon yake Masifar son ya kusanci bayan shi. Amma haka bai samu ba, sai da magarib nan yake ganin kamar zai iya shigar shi da karfin tsiya.

Kwace jikin shi yayi tare da kallon shi.
"Malam Meye haka?" Wani nishi ya sauke tare da takowa gabansa.
"Kamshin mace naji a jikinka"
"Malam bana son damuwa" ya faÉ—a da sauri yana ja da baya, ganin Almamoon zai subuce mishi ya kara kai mishi cafka Allah ya bashi sa'a, ya arta a guje.

Shi da yaran sa, suka mara mishi baya Allah bai basu Sa'a ba, har ya shiga cikin gidan, tare da rufe kofar gidan yana haki, kamar Mahaukaci haka ya shiga gidan yana haki.
"Lafiya?"
Nan ya basu labarin biyo shi da shege yayi, shiru Malam sanda yayi sannan yace mishi.
"Insha Allah gobe zaka bar garin nan"
Innah da cikinta ya duri ruwa kamar zata fashe da kuka.
"Eh gwara ka tafi, zaman ka a nan masifa ce gwara can"

Shima munafikin da yaji haka, ai amincewa yayi babu shiri a daren suka tafasa taliyar suka ci, wajen asuba. Ya shirya kayan shi. Sannan suka mishi addu'a, kafin suka sanya shi yayi Sallah tare da niman dacewa.

Karfe bakwai na safe ya bar gidan, cike da zulumin rayuwa,
Haka ya nufi tasha, yana zaune har motar su, ta tashi. Anan ya sauke ajiyar zuciya.

**
Karfe hudu na yamma ya same shi a quarts din malaman jami'ar, a hankali ya shiga buga kofar get din, dake yasan Almamoon zai zo shi yasa ya bude da kwarin gwiwar shi, yana buÉ—ewa, ya shigo. Bai san lokacin da ya fisgo shi tare da rungume shi ba, yana wani irin jin dadi da nutsuwa yana saukar mishi.

(Labarin zai koma bakin Mata maza🙄🤣 Salon da na saba 🙆🏾‍♂️�?)

Cikin wani irin takaici na kalli Malam Ansar.
"Toh meye haka? Idan Baba Mari ta ganmu ta zarge mu da wani abu ko?"

Kamar zai sake min kuka yace min.
"Kayi hakuri nasan babu dad'i amma kuma nayi kewar ka ne sosai."

Ƙaramin tsaki kayi a raina sanan nace mishi.
"Toh Ni gaskiya bana son haka." Na ture shi tare da juyawa zan fita.
"Don Allah kayi hakuri"
Banza nayi dashi. Kamar dani yake ba,
"Toh shi kenan, ba zan kuma ba." Ya fada a sanyayye, shiga cikin gidan nayi ina wani hura hanci irin ganin nan an min laifi.

"A'a ba nan ba, BQ" na wuce da jakata ina shiga na kalli Baba Mari. Cikin wani irin murna ta taso tare da amsar kayana.
"Dan mutum kai ne a gari"

Kaunar tsohuwar ya taso min tun daga cikin raina har jinin jikina, ba zan iya cewa ga yadda nake ji akan ta ba, kwalla ne ya cika min idanuna.
"Wallahi matar gani nan". Na zauna ina kallonta, kura min ido tayi, sannan tace min.
"Idan na kalle ka sai na tuna da Abuh, yanayinku, kayi hakuri na tsare ka da surutu.."

Tashi tayi ta fara hada min abinci, tare da duk wani abun da take dashi a dakin. Cikin kauna da gata, take min.
"Maza zauna kaci" haka ta hada min na fara ciki ina janta da hira, har ma gama na kwashe kwanikan na wanke, na dawo dakin nayi sallah,haka na tattara kome na koma dakin da aka bani, na gyara shi tsaf.

Sannan na dawo dakin ta muka shiga hira, har malam Ansar ya kuma zuwa, wani shegen kallon yake min, dan haka na dauke kai na tare da b'ata rai. Haka muka sha hiran mu tare da basu labarin halin rayuwar da muka sha, wanda ma na bar su.
"Yanzun ma ai bawai na dawo bane saboda kaje, wani gantalallen mutum ne ya dame ni shine Inna da Baba suka yarda na zo."
Ya fada tare da tsume fuska, dan bakin nan ya cuno shi gaba, alamar wannan Almamoon da mace ce (🙄😜🤣) tabbas zata yi tsiwar bala'i, ina dalili dauke idanun shi yayi daga kanshi, domin kowani seconds na bugawar agogo jin bugun zuciyar shi yake yana fita kamar da sunan Almamoon, tsabar kaunar da yake mishi (Dalla can mata mazan🙄😠😏) kasa sakewa yayi dan gani yake kamar Baba tasan abinda yake yi akan Almamoon, ya tashi ya bar gurin tare da cewa.
"Baba bari na fita na dawo"
"Allah ya tsare"
Ta faÉ—a mishi.
***
Abinka da mara lafiya, ganin yadda agwagwan ke wanka haka shima ya tawo da mugun gudu ta dirka a cikin ruwan ji kake famjammm, ya fashe da wata irin dariya yana gurnani kamar Mahaukacin kare, bakin shi yana zubda yawu, sai buge fuskar shi yaƙe alamar kuda na binshi.
"Hrmrmrmnnnnnrrr" masu kula da lafiyar shi, ne suka taru a gurin da hodar da suke shaka mishi.
"Ku nutsu a hankali"
Inji Hurayyah, sadaddewa suka yi tare da shaka mishi hodar ta bayan shi, anan suka yi a rangama daukar shi, kai ciwo makiyin mutum.
"Amma Hurayyah idan Dan Ba'are yazo da?"
"Toh kai da mu bari ya dake mu ai gwara mu shaka mishi tunda naga ai ba laifi bane, kuma idan ba haka muka mishi ba kana ganin zamu sha lafiya ne, gwara mu shaka mishi."

Haka suka dauke shi zuwa dakin shi, aka kwantar dashi, suna kokarin cire mishi kayan Dan Ba'are ya shigo. Ganin halin da suke ciki ya shi musu wani irin banzan kallo, babu shiri suka bar d'akin, tare da nufar waje, suka shi ya kintsa shi sannan ya zauna yana kallon shi.

"Mohammed Insha Allah zaka samu lafiya ina jin haka a jikina, sai dai ta inda lafiyar zata samu ne ban sani ba" ya faÉ—a tare da rungume hannunsu guri guda. Tausayin shi yake, yasan idan ya samu lafiya bai zama dole ya koma bakin aikin shi ba, tunda ga halin da yake ciki. Koda ya ji sauki sai dai ya nemi wani aikin kawai. Kiran wayar shugaban jami'ar yayi suka yi magana, shafa kan shi yayi yana murmushin jin dadi.
"Nagode"
Ya fada cikin wani irin abu yaji ya tsaya mishi a raina,

Dan haka ya mike tare da nufar waje, ya kalle su dakyau.
"Insha Allah jibi za a kawo wanda zai na kula da lafiyar shi, ku sai ku tsaya akan aikinku,."

"Toh" suka fada lokaci guda, sannan ya juya tare da barin gurin su.

Ko minti biyar ba ayi ba aka kira shi, daukar wayar yayi tare da mannawa a kunnen shi.
"Akan me zaka ce su tsaya akan aiki su? Karka yarda ka kawo min wani mutum da zai kula da lafiyar Mohan domin kome na shi yana hannuna."

Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ko Ammi bata da ikon hana ni abinda ya dace akan Mohan balle ke, dan haka ki fita idona na rufe idan na rufe dake mmm" ya kashe wayar yana tsaki, fitowa yayi tare da tara su,

"Wallahi sai na kore ku kuma na kwana lafiya, kunyi na farko kunyi na karshe kar na kuma kama wani dan iska da min tsurku, idan kuma na sami haka"

Nad'e hannun rigar shi yayi tare da kallon su, yana lashe lashe bakin shi, cikin zunzurutun masifa da bala'i. Ya tsani renin hankali. Shi yasa ake ganin kamar baya son mu'amala da mutane kananun magana ne ce ya tsaya, yan iska kawai sai ya hana Hajiya Safiya shigowa gidan da shi take zancen fita yayi tare da danna wani kararrawa, kafin kace kwabo.

Kafatan jami'an tsaron sun halara a filin gidan, haurawa saman wani dakalin yayi yana kallon su.

Kafin yace musu.
"Jibi Insha Allah zan bar garin nan zan koma gurin aikina, kuma jibin zan kawo me Kula da lafiyar Mohan, idan yazo ina bukatar a kula da lafiyar shi! A kula da duk wani abun da zai zo dashi sannan ina kyautatta zaton zai zauna anan ne zai na tafiya makaranta a bashi driven da zai kai shi ya dawo dashi. Ina son kuma a saka ido akan masu zuwa daga Fadar firaminista da sunan duba lafiyar Mohan, kowaye matukar Ba Hajiya Latifah bace ko Daya daga cikin Yaranta ko Mai Girma Shugaban kasa ban yarda a bude kofar gidan ba, idan kuka ga mutum ya matsa zai shigo ku bude mishi wuta. Sannan ku kara saka ido akan masu aikin kicin da sauran bangarorin akwai munafukai. Da fatan zaku bawa Major General Mohan Mamman Nasir Aghali Kariya da Yardan Allah"

Duk suka hada baki da cewa sun amince, zasu yi aiki tsakanin su da Allah tare da bawa shugaban su kariya da yardan Ubangiji. Sanan ya gaya musu duk wanda ya karya dokan shi tabbas shima zai karya kafaffun shi. Dan haka su bi doka da oda. Suka kuma yarda tare da amincewa.

Kafin ya sallame su, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya kira su baki É—aya.
Kallon shi suka yi dan sun fara razana da al'amarin shi. Duk da sun zai bai da dad'i amma kuma basa tsammanin har ya kai yadda suke tsammanin.
" Idan mai aikin yazo zan tambaye shi matukar ya iya girki ba zaku kuma dafa mishi abinci ba" a rude suka d'ago kai suna kallon shi, a ransu kuwa ba karamin kwashe mishi albarka suke ba, ayi mutum da zunzurutun masifar tsiya, kome sai ya sauya musu tsarin su yake, Ashari'a kuwa yasha babu iyaka da Tsinuwar su akan ya sauya musu alkibla....
Please if you read hope me sharing to family and friends😭😭😭 karku manta da komens da bote, ko muje hutun kwana uku 😛😁😜🙄😩
#Mai_Dambu...
8/19/21, 2:19 PM - My Mtn Number: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
    Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Batool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azi_zat

*Gaisuwar ce wannan shafin Aunty Safiya Jos, Ummi Ilham Gombe, Mom Sayeed Kano, Mrs Faruq matar kakana Nagode sosai*

Sai da rai....
BABI NA SHA BIYU.
Da'go kai yayi tare da kallon su, cikin nutsuwa da yanayin shi na cin Uban kowa ya kwana lafiya, yace musu.
"Matukar wanda zai kula da ya iya kome dukkan ku barin gidan nan zaku yi domin ban yarda da fuskar ku ba. Ku b'ace min da gani marasa mutunci"

      Rabil da Hurayyah suka wuce kitchen, Bilal da Moussa suka wuce gurin wanki, Sarah da Nouhu suka wuce bayan dakin da ake ajuye kayan aikin cikin gidan.

Hurayyah da Rabil girki suke, Bilal da Moussa, wankin da guga suke. Sarah da Nouhu sharan gidan suke da goge goge. Kusan idan ya cire Hurayyah itace Mohan ya kawo ta da kanshi sauran kuwa. Daga can fadar gwamnati aka kawo su. Kuma yana kyautatta zaton Hajiya Safiya ce. Ya tsani matar nan kamar me.
      ***
Niamey.

Shige take da fice, tana hango yadda Hajiya Latifah ta harde ana mika mata wasu takardu, zata saka hannu. Murmushi tayi sannan tace.
"Da Sannun zan ruguza ki, tunda nai babban nasara kawar da wanda ya tsaya muku"

       Fitowa tayi cikin shigar Alfarmar ta nufi gurin da Hajiya Latifah take.
"Barka da hutawa ranki shi dade"
Sai da ta b'ata lokaci kamar ba zata amsa ba kafin tace mata.
"Hmm"
Ta cigaba da aikin ta, kamar bata san da tsayuwarta a gurin ba.
"Hmm, dama ranki shi dade akan batun matsalar Mohan"

     Ta faɗa tana kallon yanayin da Hajiya Latifah ta shiga, ganin yadda Jikinta yake rawa yasata sake murmushin mugunta, sannan ta cigaba da cewa.
"Dama naga"
"Kije bana son jin sunan shi tashi ki bar min nan"
Ta daka mata wani irin tsawa, wanda yasata mikewar dole, domin babu karya ta razana. Bayan tabar gurin kan Hajiya Latifah ya shiga sara mata kamar zai rabe biyu.

        Tsaki tayi tare da mik'ewa, ta nufi cikin gidan, koda ta shiga har ta manta kome akan shi. Itama Hajiya Safiyar dadi ya sata bata kuma bin wani abu akan Mohan din, sai dai tana da kudirin jibi Insha Allah zata dira a Maradi ta cirewa dan Ba'are rashin mutuncin da yake kan shi.

       Kuma wallahi ta isa sai ta ganawa Mohan azaba, dan duk cikin Yaran Hajiya Latifah ta tsani Mohan sama da kowannen su,, shi yasa bata yi kasa a gwiwar gurin tsayawa sai da kome ya faru dashi kafin hankalinta ya kwanta. Shima dan Ba'are sabida ba haka kawai yake ba da ta jijjiga shi da karfin ta. Ta kuma nuna mishi Allah daya ne.

***
Washi gari
Kamar ba zan shirya ba, amma sabida irin yadda Malam Ansar yake bina da idanun yasa ni hada kayana, na raba biyu. Na saka rabi a cikin wata jaka, rabi kuma na barshi a dakin Baba Mari, sanan na tsaya tare da cewa.
"Baba idan aikin da sauki zan na zuwa duba ki, Insha Allah."

      "Allah yayi miki albarka, ya kuma kare ki daga sharrin shaidanun mutane da shaidanun Aljanu, karka yi wasa da ambaton Allah a duk inda kike, gurin da zaka shiga haka kawai nake ji a jikina akwai babban Al'amari a gurin. Dan haka a rike Allah babu wasa sallah nafilla, walaha da duk wani sallah bayan sallah farillah, ba ayi da La'asar da magarib, amma ana yin shafa'i da wutiri, karka manta Alhamis da Litinin kayi azumi ka nemi dacewar Ubangiji.."

     Rike hannu na tayi tana kallon fuskana tace min.
"Wallahi nayi mafarkin inda zaka  cike yake da ƙaya masu matukar hatsari, shi yasa na mike da nima maka kariya, Insha Allah zaka yi nasara amma karka manta gaskiya tafi kome tasiri kar manta da karatun Alqur'ani domin itama haske ce s duk inda mutum yaƙe."
Wato matar nan jinta nake kamar ita ta haifi Innata, zunzurutun kulawa. Sannan ta bani addu'o'in.
"Baba zamu tafi makara muke"

"Allah yayi muku albarka" ta faÉ—a tare da juya mana baya, mu kuma muka fita, ina lura da take taken shi magana yake son min, amma na wani b'ata rai, sai da muka fita daga gidan ya rufe Kofar gidan sannan ya tako har zuwa inda nake, ya bude motar ya shiga. Shiru ne ya gifta tsakanin mu. Kamar ba zai yi magana ba.

         "Ina rokonka don Allah don sonka da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka kame kanka, tunda kasan yanayinka ba irin tamu bace, yanayi biyu ne a tare da kai don Allah karka yarda wani ya fahimci halin da kake cikin har yayi kokarin cutar da kai, Wallahi idan wani abu ya same ka, kashe kaina zanyi da bakin ciki,"

"Ai makabarta bata cika ba, dan haka Allah ya jikan musulmai wanda ya kashe kanshi kuma Ubangiji ya san yadda zai yi dashi" (hali a jikin rai yaƙe Bakar magana)  kallon shi Malam Ansar yayi tare da cewa.

"Wai meye nayi maka ne ka bi ka tsane ni haka?" Ya tambaye shi kamar zai yi kuka,
Wani banzan kallo na mishi, kafin nace mishi.
"Kawai naji a raina na yi ta kafta maka rashin arziki ne" ya bashi amsa.
"Indai akan dan rungumo ka da nayi jiya ne Allah ya baka hakuri." Dauke kai nayi kamar ba dani yake ba, gidan shugaban makaranta muka nufa, daga nan shima ya koro min jawabin shi da abinda zamu yi kallon shi nayi kafin nace mishi.
""Toh" sanan muka bar gidan, ina ji kamar na rufe su da dukka, kiran dan Ba'are yayi ya gaya mishi gamu nan mun iso amma akwai jami'an tsaro sosai.

Bayan kamar minti goma sai gashi ya zo da kanshi, suka yi magana kafin ya leko cikin motar ya kalle ni.
"Kai fito" ya faÉ—a babu wasa a fuskar shi. Ganin shi dirkeke, ga fuskar nan babu sassauci ya sani fitowa ina kamkame jakata.kallon na yayi sannan yace min.
"Koma cikin motar"
Komawa nayi, sai lokacin na lura da fuskar malam Ansar, ya b'ata rai ainun. Fuskarshi har wani ja yayi.
"Malam Ya naga yaron kamar mace?"
"Almamoon namiji ne, haka kowa yake gani kamar mace amma namiji ne"
"Toh ince bai da matsala, irin dauke dauke da sauran su?"
A wannan gaɓar kamar malam Ansar ya daka mishi mari, amma ya rarrashi kanshi yana kallon shugaban jami'ar.

"Yaron bai da matsala, kuma ban tab'a jin malam Ansar ya fadi wani abu akan shi ba, ko abokan karatun shi basu tab'a koraafin yayi musu ta'adi ba."

"Toh Shikenan, kuje dashi Insha Allah gobe idan ya taso makarantar yazo Insha Allah kafin lokacin an gama mishi kome nashi na gidan domin babu me tsallake wancan shingen babu alamar kai É—aya ne daga cikin gidan."

"Mun gode" d'aga musu hannu yayi tare da juyawa ya bar gurin su.
"Gaskiya ban da dole da Almamoon ya hakura da wannan aikin kawai raina bai kwanta da wannan gida me cike da murÉ—a murÉ—an maza ba"
Inji malam Ansar, jin haka shugaban Jami'ar  ya lullube shi da faɗa, har suka isa makarantar. Kamar zai ajiye Almamoon sai ya dawo dashi gidan. Sannan ya nufi makaranta domin fushi yake sosai kuma ba kome ke damun shi ba sai kishin bala'i da ya daurawa kanshi akan Yaron. Dan shi har kwanan gobe kallon da Yakewa Almamoon ba na wasa bane.

     ....
Bayan tafiyar su, ya koma cikin gidan. Zama yayi yana hasashen fuskar Almamoon, haka kawai yaji yaron yayi mishi kuma ya kwanta mishi, bai da nutsuwa da wata shirme irin n yaran yanzun,

     Kallon Mohan yayi tare da cewa.
"Bana son barin ragamar rayuwarka a hannun mutane da suke kewaye da kai ne" shiru yayi sannan ya cigaba da shafa kanshi yana jin tsannanin tausayin halin da Aminin shi yake ciki. A hankali ya mike bayan ya nufi inda ya ajiye kome ya fara shirin shi da yasaka a ranshi, yayi ta aiki yana connect din na'ura a cikin gidan. Bayan nan ya fito.

Akwai wani yardadden Yaron Mohan mai Suna Malik, har yau bai tab'a jin Malik yace mishi ga wani abu na Mohan ba, dan haka lokacin da Mohan ya fara jinya da zai zuba jami'an tsaron Malik ya bawa rikon su. Dan haka ya fita tare da kiran shi suka nufi lambu. Zama Dan Ba'are yayi yana me kallon Malik da ya sara mishi.

     "Gobe Insha Allah yaron da zai kula da Mohan zai zo, kasan me ina son ka zuba ido akan Yaron! Daga yau zan mai da kula da gidan a hannun Fahad, kai kuma ka zauna a cikin gidan kana taimaka mishi da wasu abubuwan. Akwai abinda nake zargi a cikin gidan amma ban tabbatar ba, don haka zaka ajiye unifoam. Nasan kai ɗaya ne kasan kome akan Mohan har da abinda ya shafi dukiyar shi, naji dad'i da ka zama mutum mai Amana da gaskiya, Insha Allah zaka ga sakayya a gurin Ubangiji. Gashi nan wannan key motar da zai na kai shi makaranta ne, wannan kuma duk wata zana cire CF dubu dari bakwai kana bashi katin bankin shi na kamfanin shi da yake doso ce, babu abinda zai yi da izinin Ubangiji. Don Allah ka zama me amana da na san ka dashi, bayan ku duk mutumin da ya nemi shigowa gidan nan"

Jan hannun shi yayi kamar wanda ya ke jan bindiga ya dauke kamar yayi harbi, "ku gama dashi, idan ka fahimci Yaron yana da dauke dauke ka kira Ni ka gaya min zan zo na mai dashi, sannan duk bayan sati biyu kana ciwo mishi dubu hamsin kana bashi, sabida kashe wasu kannan bukatar shi. Idan kaga wani sauyi kai min magana, idan na samu lokaci Insha Allah zan zo na kai shi sokoto gurin kana na"

    Gyada kai yayi sannan yace.
"Insha Allah"
Daga nan ya bar gurin dan ya sallame shi, zuwa yayi inda motar da zai na kai Almamoon makaranta, yake ya duba yaga BMW ne, jinjina kai yayi sannan ya nufi sansanin su, ya saka sunan wani daga cikin su aka kira shi. Ko minti biyar ba ayi ba. Ya shigo tare da sara mishi.
"Gashi daga yau aikin ka shine kai yaron da zai na kula da lafiyar Yallabai Mohan makaranta da duk inda yake buƙata."

"Insha Allah" ya sara mishi, tare da juyawa ya fita..daga nan shima Malik ya haÉ—a kayan shi yayiwa Fahad magana, gyada kai yayi tare da rungume shi yana faÉ—in.
"Allah ya baka sa'a"
"Amin Abokina Nagode" suka tafa sannan suka bar gurin.

        ***
Sake shirya kayana nayi, sannan na kalli Malam Ansar da yayi ciki ciki da fuska.
"Wallahi karka sake abin duniya ya rinjaye ka"
"Toh ai kai ma da abin duniyar ka janyo ni" na fada tare da gimtse fuskana,

"Baba wannan Yaron ya rena ni, duk abinda nayi dan na kare shi nake amma ban da kwashe min albarka babu abin da yake." Ya gayawa Baba,
"Almamoon bana son rashin kunya mana, me yasa ka rena malamin ka? Dan ya taimaka maka sai yayi laifi? Toh kul bana son haka, idan ka sake na kuma jin haka sai na sab'a maka"
"Kiyi hakuri, kayi hakuri ba zan kuma ba" ya faÉ—a kamar zai fasa ihu, wuni ranar har dare suna manne a dakin baba.

   Washi gari da ya tafi makarantar, ya samu zasu fara jarabawa yayi rashin test da wasu abubuwan, dole zai maimaita wannan zangon da haka dake karatun a ranshi yake nan ya amince tare da yarda yayi duk abin da zai yi, yana tashi daga makaranta, ya nufi gida. Malam Ansar da kanshi yazo ya dauke shi suka nufi can gidan.

      Karfe biyu da rabi yayi mana. Kofar get din farko, dan haka ya kira mutumin , ko minti goma ba ayi ba sai gashi sun fito tare, da wani mutum, suna zuwa shi mutumin jiya yana sanye da kayan sojoji, sai jar hular da yake kanshi, yana zuwa ya mikawa malam Ansar hannu suka gaisa, sannan ya leka Ni.
"Ban rike sunan shi ba"
"Almamoon Isma'il Wodaadabe"
"Ai kace Bororo ne?"
"Eh haka nake tsammanin" inji malam Ansar,
Bude min kofar suka yi na fito a hankali, ina kallon su.
"Don Allah ku saka ido akan shi yaro ne, dan har yanzun bai cika sha tara ba, don Allah kar wani abu mara dadi ya same shi. Sannan Insha Allah zan ina zuwa duba shi"
"Malik bashi Number ka, idan kazo ka kira shi, Insha Allah har cikin zai kai ka, Mamoon kai kuma mu wuce."
.kasa tafiya nayi na tsaya a gaban shi, kwalla na cika daga idanuna.
Riko hannuna yayi tare da kallon yadda nake kuka.
"Baka son rabuwa da ni ne?"
Gyada mishi kai nayi.
"Me yasa?"
"Babu" na fada ina jan dogon hancina.
"Maza wuce Allah ya bada sa'a" ya faÉ—a min, kuka ne ya zo min na toshe bakina, haka suka sani a tsakiyar su, muka nufi inda wata mota take, wanda aka kira Malik ya bude min baya, juyawa nayi ina kallon Malam Ansar har. Na shiga motar, leken shi nake ta bayan motar, kwalla na zuba min. Kawai sabon da nayi dashi ne yasa haka, a hankali muka bar gurin ina kallon jami'an tsaron da aka girka a kofar gidan kafin ka shiga gidan ma tukun, Ashe ba karamin tafiya bace idan da kafa ne, kallon gidan nake me dauke da aljannar duniya duk inda muka wuce sake baki nake har muka isa cikin gidan sosai.

   Tun ban shiga gidan ba gabana yake faduwa, har muka shiga cikin gidan, a hankali suka shiga gaba. Ina bin su a baya har muka fada wata babban falo. Hoton wani soja ne yayi mana mara ba da zuwa gidan, ina d'aga ido na kalli hoton. Kamar wanda aka daki kahon zuciyata, wani irin bugu yake duk wani dakika jin shi nake kamar zai fasa kirjina, dafe kirjin nayi tare da saurin dauke idanuna akan hoton ba mamaki kodan kwarjinin da hoton yayi min me yasa na ji wannan yanayin a raina. Har muka fara haurawa sama, sake juyowa nayi na kalli hoton naga ya kura min ido, da sauri na bi bayan su da gudu, har suna juyowa.
"Lafiya Mamoon?"
Dakyar numfashina ya dai-dai ta, na girgiza musu kai.
"Toh muje" haka suka kai Ni falon sama, sannan suka ce na tsaya. Suna shiga can sai gasu tare da mutumin hoton nan ne,

Zuba mishi ido nayi, abu biyu naji a lokaci guda, wani mugun tsoron shi da kwarjin da yaji min, sai wani abu da na hango a tattare dashi, yadda ya kafe ni da ido ya sani sunkuyar da kai na kasa, jikin yana kerma sakamakon hango shi da nayi cikin fararren kayan barci.

    Zama yayi sannan ya kalle su, bai ma san me ke faruwa ba.
"Yawwa Almamoon ga shi nan mara lafiyar mu, shi yake bukatar kulawa, wannan shine Malik zai taimaka maka a duk lokacin haka." Gyada musu kai nayi, domin ban san me zanyi musu bayan haka ba.

         "Kayi hakuri nasan kai dalibi ne ka iya abinci, sabida zan amshi kula da abincin shi a hannun masu yi na dawo dashi hannun ka ne?"
"Na iya"na fada ina kallon kasa,
"Shi kenan, and ka kula da lafiyar shi don Allah duk sauran bayanin yana gurin Malik. Shi zai taimaka maka"

     Haka ya mike tare da mika min hannu, kasa karb'a nayi sau da ya kuma min alama na mika mishi a karon farko a rayuwata da nayi haka dan ko da nake makarantar ban tab'a yarda ba, amma yau nayi. Sai naji kunya ya addabi ni, har ya fita sannan Malik yayi mishi rakiya.

"Ka ciro kudi ka kai shi ya zab'i kayan da ya dace da shi, wancan kayan da ya saka sai kace wani Bugaje,. Ka nima mishi kananun kaya masu kyau da tsada, sauran kuma a hada mishi da takalmi da duk wani abun da zai fito dashi gari. Zaka iya tambayar shi dai ka sayo mishi.

         Haka suka tafi suna tattaunawar...
Baya bata da kaÉ—an.
Wato suna barin gurin, kaina  a sunkuye, ba zan iya fahimtar yadda abin ya faru ba, amma tabbas sai dai nake kamar ba a duniyar mutane nake ba, domin wata irin shaƙa da Mutumin yayi min, ya sani fara ganin wata duniya na daban.
Gashi ya  danne ni akan kujeran, kamar zai kashe ni. Wutsul wutsul nake, kafin Allah ya bani nasarar buga mushi kararrawan sadarwan shi, zuɓewa yayi a kaina tare da dauke wuta. A lokaci guda muke kallon idanun juna, lumshe idanun shi yayi tare sake jikin shi alamar ya suma a jikina, wallahi gashi kaman gumgumemmen dutse, kasa motsi nayi.. a hankali na kuma kallon fuskar shi, naga yana lumshe sai kwalla da take bin fuskar a hankali yana diga a daidai saitin zuciyata. Kasa jan numfashi nayi, tare da jin wani abu ya cika min wuyana.

      A hankali na shiga janye jikina, amma kamar bana kome, gaskiya mutumin nan kato ne, dakyar na iya d'aga hannun shi da kanshi, shigowar Malik yaga yadda nake kiciniya sai da ya tintsire dariya, har yana nuna ni.
"Sannun Kaji, da fatan bai maka kome ba?"
"Da yanzun sai dai wani ba ni ba domin shake ni yayi zai kashe ni." Na fada kwalla na zubo min,
"Kayi hakuri"
Yazo ya had'a karfin shi guri guda ya dauke shi tare da sab'a shi a kafada,"biyo Ni" da sauri na ji bayan shi. Muka shiga cikin É—akin.. haka kawai naji kaina ya sara, ina jin wani irin kauri kamar an gasa wani abu, kallon dakin kake naga yana fidda wani irin hayaki, me dauke da bakin duhuwa, lumshe idanuna nayi ina kallon yadda dakin yake fidda wannan yanayin. Hatta shi ma hakan ce,.da sauri na fita ina dafe kai na.

          "Mamoon" zuɓewa nayi akan kujera kamar danyen nama, ina sauke wata irin ajiyar zuciya, kafin wani lokaci zazzaɓi ya sauko min,
"Mamoon" ya kuma kwala min kira.
"Na'am" sai ga amai, sosai nayi ta kwarawa a falon, kafin na iya rarrafawa zuwa d'akin.
"Ina ka tsaya? Baka da lafiya ne?"
"Eh.." sai ga Amai, wani irin wari da dauyi yasani kwara amai. Kafin kace kwabo, zazzaɓi da wani irin firgita ya kamani,  haka nayi ya dungure a dakin shi kam Malik komawa yayi gefe yana kallon ikon Allah. Sai da na kai minti talatin kafin na bude idanuna.
"Ciwon shi nan ba daga Allah bane, ciwo ne na mutane." Na fada muryana yana rawa,
Kura mishi ido muka yi, a hankali ya tako inda nake yace min.
"Kamar Ya? Ban gane ba?"
"Nima abinda ban gama fahimta ba kenan, amma don Allah karka bari a sani, Allah ya bashi lafiya"

Ni kaina ban san me ya kai ni irin wannan katob'arar ba, sai dai na tsinci kaina da yarda da Malik din ne zuciya daya, shi yasa na gaya mishi. A hankali na gyara saman tsaf sannan na share ko ina, na saka wasu turaren zamani na gwangwani..

Sannan na kalli Malik nace mishi.
"Kar mu kuma barin shi babu alola, ya zama jikin shi kullum da  alola"

      "Amma kasan me? Wallahi nima tun farkon ciwon na fara zargin ciwon kamar ba ta Allah bace"

Nan muka yi ta hira akan matsala duk da kasancewar shi ba me yawan magana ba.

     Bayan mun gama mishi alola, kallon shi nayi, ina kallon fuskarshi naji kamar an dake ni, sai da na kusan faduwa, sabida kwarjininsa, ga wani uban kyan da yake cika min idanuna.

  Fuskar shi nan kamar madubi, har hango shi nayi yana kyalkyali, da sauri na fice a d'akin. Ina hararan shi, ko yaushe na fara jin wannan shirin oho, haushi ma ya bani Dan ta cika kyau dayawa, na tsani namiji kyawawa. Tab'e baki nayi ina me jin haushin kaina, daga yanzun ba zan kuma yarda zuciyata ta buga akan wannan katon basamuden ba, mutum sai kace wani katon bishiyar kuka.

             ***
Malam Ansar.

Ya kai minti talatin a cikin motar shi bai tadda ita ba, dan ji yaƙe kamar zai tafi ya bar zuciyar shi a gurin, ya zaune ya kifa kanshi  da sitiyerin motar, yana ji kamar ya shiga ya dauko Almamoon, yace ya fasa aikin. Ji yaƙe kamar ya kira Shugaban jami'ar yace sun fasa, amma baki daya bashi da confidence din yin haka. Bai san waye din shugaban kasa ba. Amma daga nan ya fahimci wanda yake cikin gidan ba karamin mutum bane.

    Ya kwana da sanin cewa sojoji basu da mutunci, yanzun kana musu wata shirme zasu sake maka wuta, shi yasa ba zai iya daukar kasadar komawa gidan ba, balle su bude mishi wuta, har Dan Ba'are ya wuce yana nan a gurin.

   Murmushi yayi a karo na farko da ya tuna yadda Almamoon yake tura mishi bakin shi alamar dai yaji haushin abinda yayi mishi. 
"Ina son Yarona".ya faɗa yana tadda motar. Ya bar kofar gidan cike da kewar Mutumin nashi....  Kusan weekend sai a hankali... Ayi maneji
8/19/21, 2:21 PM - My Mtn Number: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
    Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima batool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azi_zat

Duhun Damina....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.