Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 42 of 64

BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.

"Toh ki shirya muje mana!" Kallonta  Auta nayi a shagwaɓe,
"Auta ina jin tsoro ne, kar naje a sami matsala."

"Ba gani ba" ta faÉ—a cikin tsokana,
"Kai Auta me zaki iya, keda ba karfi ne dake ba, balle ni"

Harara ta tayi sannan tace min.
"Baki da mutunci kona miskala zarati, na yarda bani da karfi..dan haka maza ki shirya muje lokacin na tafi karfe biyar za ayi fa!"

     Buga kofar mu akayi, ita ta tafi a hankali ta bude kofar.
"Kina niman waye?"
"MG Mohan ya aiko ni nayiwa. Maimunari kwalliyar"
"Toh shigo mana" ta bude kofar ta shigo. Juyawa nayi na kalle ta.
"Laa! Aunty Uwani shigo mana"
"Ya haka karfe hudu saura amma baki shirya ba, gashi can ya addabi rayuwata da kira. Uwani ki tabbatar kin fitar min da ita, Uwani ki gyara min fuskarta."

     Murmushi nayi domin indai Mohan ne zai rina.
"Aunty bari na watsa ruwa."
"Ok! Amma tsaya ga wannan"
Ta mika min wata jaka.
"Ki duba zaki ga yadda ake anfani da shi."

    "Toh nagode"
Tunda na shiga ban daki na shafa wannan, na goga wannan. Kai har su gashin hammata duk dai da na fitar, sannan na yi wanka da wani sabulu na musamman, na fito, zan goge jikina sai ga auta da wasu mai.
"Malama zauna na shafe ki!"
"Wallahi baki isa ganin jikina ba."
"Toh ko nakira Hammah Mohan ne dan nasan shi zai iya gani har can birnin lintsin" ta fada tana min dariya.
Bayana na yarda ta shafa min, sauran na shafa da kaina, bayan na gama na saka doguwar riga naje na zauna. Aka fara kwalliyar. Tun karfe hudu aka fara bamu gama ba, sai biyar saura minti biyar, sannan na mike na saka doguwar gown din da ya bani ranar, sai yanzun nake yabawa da shi,  dauko min wani set na bracelet diamond ja mai mugun kyau da tsada, dan kunnen shi da abin hannun shi, da wata zobe mai mugun kyau duk nashi. Sai yar siririn agogo duk nashi. Kallon shi nayi da kyau.

   Ina jin kwalla na cika a idanuna, jan hancina nayi sannan nace mata.
"Ban san iy adadin soyayyar da Mohan yake min ba, amma kyautar tayi min girma"
"Ke dai Allah ya tabbatar da alkhairi" inji Auta. Wani hula me kyau ta saka min bayan an shirya ni, sannan aka shiga daukar hoton, tare da tura mishi.

Sannan ta gyara auta itama tayi kyau sosai, buga mana kofa aka yi. Auta ta bude,
"Barka da zuwa Khalil"
"Yawwa Auta, kun shirya?"
"Eh! Uwani ai ba dan Surukata karta ga nayi azarbabbi ba da na je na dauko Beenah amma babu kom.."
Daukar wayar yayi yana faÉ—in.
"Banza kawai idan kayi hakuri zan kawo ta, kafin a saka maka. Shege mayyen mata"

"Zan ci Ubanka!"
"Na yarda, ku tashi kafin Mohan ya tawo dan ba kunya ce ta ishe shi ba."

Takalmin da aka ciro min na gani kamar zanyi kuka nace musu.
"WALLAHI tunda Uwata ta haife ni dau daya na saka irin wannan takalmin don Allah ku barshi, zan fad'i" jan kafana Aunty Uwani tayi sai da ta daka min ta daure min belt din, sannan ta mika min yar pose din, sannan ta shiga fesa min turare, sannan ta saka auta ta riko hannuna. Muka fito.

    Motar da ina da yakinin bai tab'a shigar ta ba, domin naga alamar sabuwa ce, bude min baya Khalil yayi sannan na shiga auta ta zauna kusa dani, muka fara ajiye Aunty Uwani a shagonta. Mika min wata jacket yayi tare da cewa.
"Mutumin ki yace ki saka."
Amsa nayi, tare da rikewa har muka shiga kofar farko na fadar shugaban kasa.

   Rike hannuna Auta tayi, tare da cewa.
"Sabida ke yau zan shiga fadar shugaban kasa, anya sunanki ba Noor ba!" Murmushi nayi tare da rike hannun ta. Muna shiga yayi parking, sannan ya kira shi.
"Gamu nan"
"Ok ka shigo da ita"
"Toh amma tare suke da kawarta."
"Ka hada ta da Radiyah"
"Ku fito" haka muka fita, sai da ya kira Radiyah ya hadata da Auta, sannan yayi min jagora, har shashinsa ta baya, muka shiga ya gama shiryawa yana saka links, na shiga da sallama. Duk falon da abokan shi, na wuce su, Hammah Khalil ya nuna min dakin na shiga, tare da sallama a karo na biyu.  Kaina a sunkuye, "ki karaso" yace min, a hankali na karasa inda yake.
"Me yasa kike wasa da hankalina?"
.hararan shi nayi sannan nace mishi.
"Ni banyi wasa da hankalin ka ba"
"Ok dan ina sonki sai ki ta wulakantani?" Shiru nayi, domin ya fara bani haushi.  Wayar shi ya tab'a sannan yace.
"Zoka tafi da ita"  duk wannan jarabar da yake wallhi ya juya min baya, yana shiryawa. A hankali na juya sakamakon kwankwasa kofar da aka yi. Mamaki na bashi da bance yayi hakuri ba, har na juya zan fita naji ya ce min.
"Baki iya bada hakuri bane?"
"Kayi hakuri"
Na fada, tare da barin d'akin, bin bayan ta yayi da ido, tare da tab'e baki, Munarih akwai ji da kai, hakurin ma a kasaice aka bada shi.  Dafe kirjin shi yayi yana faɗin.
"Wannan yarinya duk ranar da ta ga girma na.. na shiga uku"
"Baka shiga uku ba dan iska. K'ugun kawai na gaya maka a shirye suke ka auna min Ash'aria, ina kuma da macen da take gaban ka. Yarinyar sai kac.
"
"WALLAHI ka fadi surar matana sai naci mutuncin ka, billahi azim." Ya fada kokarin cire kayan zai daku da dan Ba'are.
"Kwantar da hankalinka, wallahi ba da manufa ba, akan me zan fadi wani abu, ai ko lokacin tana mata maza ma banga girman kirjin ba sai yau da aka saka."

Cire takalmin shi yayi tare da jifar shi da shi, yana faÉ—in.
"Ka tsaya mana dan Ubanka, na nuna maka rashin arziki. Mayyen mata kawai, kai kan ranar da ka kwana akan mace toh Billahi azim sai mun kaika turu."

Daga waje yace mishi.
"Eh na yarda ba laifina bane laifin kayan da suke bawa amaren ne, kai kuma ina da yakinin duk ranar da ka tabo dukiyar fulaninta, sai ka kwana goma kana hauka."

"Dan Ba'are!!!"
"Aghali!!"
"Zamu hadu dai na gaya maka rashin mutunci zan nuna maka bani da daraja!"

    Haka ya shiryo tare da fitowa, yana hararan su, kusan dukkan su abokai ne na family.
Wato suna ganin, shi suka kwashe da dariya, tare da cewa.
"Hammah Mohan!" Suka kira sunan kamar yadda Maimunari take kiran shi. Cikin nutsuwa da wata irin sanyi, ya yi gaba. Tare da nufar inda ake taron.

    .
Lokacin da  muka fito, ya kai ni inda aka tanadar domin mutane su zauna, bayan tafiyar shi dai ga Jalilah. Tana zuwa kawai ta watsa min ruwan a jikina. Allah yasa akan jacket din ta zuba, dai da na bari zata wuce kawai na saka mata kafa, faduwa tai sosai kamar yarinya karama, mik'ewa tayi yana kallona tare da nufo ni, nima na mike, mermaid   trappist gown  saka, take na taka Jelar gown ɗin tare da kallonta.

"Idan kika sake kika yi wani shirme zan ja takalmi na, kuma zai yaga kayan jikinki, ba zuwan ku nayi ba, dan haka wuce babu ruwana dake"

           A hankali na d'aga kafana kan Jelar gown din, babu musu ta wuce, jikinta yana mugun sanyi,. Sannan na koma na zauna, a hankali gurin ya shiga cika, manyan mutane da ga gwamnatin kasar suna shigowa.

   A hankali idanuna ya kai kan Abie, lokacin da yake gaisawa da manyan mutane, sannan na ciro wayata na tura mishi sakon.
"Abie kayi kyau cikin suite"

Duba wayar yayi tare da juyawa yana nima na, d'ago mishi hannu nayi ina murmushin jin dadi,  takowa yayi har inda nake ya zauna.
"Kinyi kyau"
"Nagode sosai"
Na fada ina risinawa, "taso muje na gabatar dake a gurin mutane."
"Toh " nace mishi, daidai isowar Mahaifiyar Hanan, tare da Hanan tana rike da hannun Mahaifiyarta. Sanye da wani masifaffen gown Royal blue, sanye da whiter gold kan nan babu mayafi balle dan kwali, ganin kishi zai sani na kauce hanya, nayi maza na dauke kai na. Tare da barin gurin baki daya.

  Na nufi wani gurin na zauna ina jin kwalla na zuba min, ina jin ka fara fadin ga Mohan nan, lokacin da suka saka kidan sojojin kasar tare da taken sojojin kasar, kafin aka fara gabatar da manyan mutanen da suka halarci taron, bayan babban Chef Imam ya gabatar addu'o'in, sannan ya sakawa baikon albarka.

Kafin MC din ya bayyana wasu abubuwan da suka danganci Mohan, a katon majigi. Tare da cewa.
"Muna bukatar  Khalil Ibrahim Dan Ba'are yazo ya gabatar mana da wannan bayanin akan MG Mohan"

   A hankali ya fito bayan ya gaida iyayen da yan uwa, sannan yace.
"Mohammed Mamman Nasir Mohammed Aghali, wanda muka fi sani da Mohan!."
Yadda yake bayanin abubuwan Cigaba da ya karu sosai da Mohan, da abubuwan. Sannan ya maida abin maganar.

    Nan a ka saka kidar taushi, wato (Cool music) kafin aka kira Mohan da Hanan iyaye suka saka musu albarka, tare da bayanin yanzun za ayi baikon tare da musayan zobba. Ina ganin haka na cire jacket din na ajiye musu a gurin, sannan na juya.
"Kafin ayi musayar zobe don Allah a bani minti biyar kacal!"
Ya fada yana kallon Dan Ba'are.
"Khalil tawo min da ita"
Nima na ya shiga yi,  kafin ya hango ina ƙoƙarin barin gurin, cikin sauri ya tawo tare da riko hannuna, cikin karfin hali da danne kukar da ya taso min na juya.
"Yana kiranki"
A hankali na juya tare bin bayan shi, muna isa kuwa hasken wutar da aka saka a gurin da na Cameras ya cika fuskana. Tun kafin na isa gaban Hanan ya gama faduwa.

"Ammyn ina me baki hakuri da abinda zanyi amma, iyakar gaskiya ce daga zuciyata.  Maimunari itace zab'ina amma duk da haka zan amshi Hanan a matsayin zabinki"

A hankali ya tako cikin wani irin izza da mulki, uwa uba kwarjini da isar shi tana kara bayyana akan fuskar shi, yana zuwa ya zuba gwiwar shi daya a kasa daya.
"Zaki Aure Ni.......
*_Wallahi mura ya dame Ni dakyar nayi wannan fa! Hahhhh Hajiya Lateefah! Hajiya Karime! Hanan! Jalilah! Zata fashe fa! Wai ina An Niger ne? Yasin ku fafata ko na tafi jinyar mura🤷🏽‍♀️🤷🏼‍♀️🏃🚶🤸_*
#Mai_Dambu......
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1112737045?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=Zioa4Y%2F3Hu%2BHlUSk66YueQO%2BpbPAhg0irEJcowTIrXaYPT9Z1eBnkRuAOXMIzo1imod4QTdXoGp%2FGjSekGkrqI9y9tm6Kgi%2FKpQsmzrrREW8q3mkPoldIzQqc5mqaVfv

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.