Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 41 of 64

BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI.

_SANNUN MUTANE 🤡🙋🏾‍♂�? INA GAISUWA MUSAMMAN MUTANE ANSAR DA HAJIYA LATEEFAH DA HAJIYA KARIME 💓😘 ANA TARE 🤝_

Kallon gown din nayi ina Kuma juya shi.
"Amma ai wannan bai yi kama da gayyatar ki yayi ba, sabida."
Kallonta nayi domin bana jin a raina ba gayyatatta yayi ba. Watsar da kayan nayi tare da kwanciya ina jin babu dadi.
"Na tsane shi!"
"Da gaske"

       "Allah ina gaya miki na tsani Hammah Mohan!" Na kuma fadar haka ina kallon kayan,
"Zan yarda kina jin haushinsa amma banda tsana, meye laifin shi? Dan kawai za ayi baikon shi da wata mace?" Tashi nayi zaune na kuma kallonta.
"Amma dai...."
Shiru nayi tare da komawa na kwanta, ina jin daci a raina, tsaki nayi tare da juya mata baya, raina na kara b'aci, ina zan iya samun kamar shi, sai dai nasan na rasa shi kenan har abada.

  Da haka na tsunduma cikin tunani.
**
Diffa.
Sanye yake da irin kayan sakin nan, yana zaune a kujeran guragu. Ya saka hoton Maimunari a gaba yana kallon ta.

"Appa!"  Watsar da abubuwan da suke gaban shi yayi, cikin fushi da damuwa.
"Yarinyar kawai nake bukata! Amma ka gaza niman soyayyarta, meye amfanin kiranka da sunan D'ana soyayyarta ma ta gaggare ka! Dan ina nakashe" ya faÉ—a da karfi. Sai da mutanen gidan suka fito.

   Zuɓewa yayi a gaban shi. Ya rsa yadda zai mahaifin shi ya fahimci abinda yake faruwa.

"Yarinyar da tun tana namiji yace min nata sona, duk lokacin da na shirya mata wani abu bata tab'a faduwa sai nasara, yarinyar ta rike Allah sama da yadda kake tunani, Appa Munnah ba gama garin mutane bace domin yar baiwa ce tana da tawwakali don Allah kayi hakuri, idan tana rabon mu zata shigo cikin gidan nan, tunda itace kake bukata zan kawo maka ita indai zaka yi nasara a rayuwar ka."

      Sanarwan baikon Mohan da Hanan ne ya katse mishi sauran bayanin, murmushi yayi sannan ya ciro wayar shi zai kira Munnah sai ya fasa, dan haka ya shiga garin ciki babu iyaka. Dan haka yake jin yanzun zai iya tura mata sakon da zai saka ta amince da shi ta wata fuskar,dan haka ya tura mata da wata wayar.

**
Da Asuba bayan na idar da sallah, ina kwance na janyo wayata na kunna, bayan na bude data. Na duba Internet, abu daya ne wato sake hotonan Hanan da Mohan, babu karya babu hassada sun dace da junar su. Kamar zanyi kuka haka na ajiye wayar, ina shafa kai na da ya fara tohowa da gashi, ina jin haushin kaina. Dan ma ina da kafar gashin ne shi yasa har ya fara tohowa.
       A hankali na koma na kwanta ina hararan wayar dan itama yanzun haushi take bani, hango sako yasani dauka na bude. Zaro idanuna nayi, cikin tashin hankali da fargaba, tare da jin cikar kwalla a idanuna. Sake wayar nayi a hankali ya fadi kasa, bayan na rike kowacce harafi da kalmomin jikin hoton da aka turo min.

*_Ina ga wannan al'amari ya gani ya juya miki baya ko? Toh ina da kuma ya kara fahimtar an shiga cikin an juye bakin mai fa_*

Daga
           Malik Dalhat.

Wani irin kuka ne ya kwace min tare da cusa kaina a tsakanin cinyoyina, ina rusa kuka, kamar raina zai bar jikina, haka nasha kuka ma more, har gari ya waye ban fita ko ina ba, ina ganin kiran Mohan naki dauka, karshe goge abin nayi tare da kashe wayar baki daya.

    Ina jin shi yana buga kofar amma naki budewa, karya kofar yayi ya dame ni zauna akan abin sallah..na takure guri guda,  takaici ya sashi takowa har inda nake yana kallona.
"Toh wannan haukar da kika min zai sa na fasa abinda nayi niyya ne? Bari na gaya miki koda aurenki nayi wallhi baki isa ki juna ni ba, wacece ke da zan kira wayar ki, ba zaki dauka ba? Dan ina sonki sai ya zama na haukace akan ki? Wacce irin daukaka kike  nima ne? Meye zan baki? Meye kike bukata na miki?"

Mikewa nayi ina kuka tare da riko hannun shi.
"Don Allah ka yarda dani! Shine kawai abinda nake bukata idan kayi min haka har abada ba zan kuma ba, ka amince ba zan maka abinda za a gaya maka ko zaka gani ba, Mohan na yarda da kai matukar zaka saka ni a jerin matanka, koda zaka iya fushi dani don Allah ka yarda dani"

      Jikin shi ne yayi mugun sanyi, yana kallon yadda nake kuka, janyo ni yayi tare da rungume ni.
"Kina boye min wani abu da ya faru dake? Me nene shi?"
"Kayi hakuri dani!" Na fada bayan na rike rigar shi.
"Insha Allah zanyi hakuri dake"
Haka yayi ta shafa bayana yana, faÉ—in.
"Ina tare dake, amma idan akwai wani abu ki gaya min, bana son daga baya muzo muna samun matsala"
"Babu matsalar kome Insha Allah"
"Ina jiran ki, ki shirya na ajiye ki a gurin saloon."

Murmushi nayi tare da kallon shi.
"Na aske gashin" na nuna mishi kan. Jan hancina yayi tare da cewa.
"Gaskiya ina son gashinki nan me kyau da tsantsi, dan haka muje a hada miki mayukan da zasu fito nan da wata uku insha Allah."

Fita yayi na shiga nayi wanka tare da kwalliya, sannan muka fito. Gurin karyawa muka fara tafiya. Bayan mun karya sannan ya kai ni gurin Saloon, aka had'a min mayuka masu kyau, sannan yasa aka min jan lalle, tare da gyara min fuskana.

         Bayan an gama ya kai ni gurin aiki, yana bawa Abie hakuri. Cikin harshen buzanci suke magana, sai su kalle ni sai su cigaba da magana, kafin yayi mishi godiya da sallama ya fita.

"Ashe za yi baikon shi?"
"Eh Abie"
"Toh Allah ya tabbatar da alkhairi!"
"Amin Ya Allah,"

Daga haka bai kuma magana ba, nima haka sai dai hankalin mu ya raja'a akan abinda yake gaban mu ne.

"Me yasa kika sare akan sha'anin ku?"
"Abie shi din dan masu kudi ne, kuma uwa uba, dan shugaban kasa ne, taya zan kai kaina gurin shi, kawai ina jin rabuwa dashi shine mafi alkhairi, sabida kamar bamu da ce da juna ba"

   "Ni kuwa sai nake ganin kun dace da juna, kuma kunsan halin juna, zaku iya zama da juna koma yayya ne, kawai ki daina saurin karaya."

Dariya nayi domin yadda yayi min maganar sai da ya bani dariya,
Toh Abie kana ganin Mahaifiyarshi zata yarda? Matar da tayi mishi matar da zai aura, kawai daga ni har shi b'ata lokacin juna muke, ka duba al'amarin mana, mahaifiyar shi tana son nasaba ni kuma ko mai kwasar shara bamu dashi ni daya ne nake karatun boko, sannan kuma."

"Kin yarda da Allah?"
"Sosai ma kuwa!" Na bashi amsa,
"Toh ki yarda da ƙaddaran ku, yace na baki hakuri gaskiya yana kaunarki,sosai kuma yana tare dake don Allah karki juya mishi baya"

   "Abie bani da wannan burin, amma idan ya cigaba da Zafaffa kishi babu bincike alaƙar mu bazata yi nisa ba." Na d'ago kai ina kallon tv dake office din ana kuma saka sanarwan baikon, da Yaren fillaci, anan kan sai da na dauke kaina.
"Masu hakuri suna tare da Allah." Ya fada tare da mik'ewa ya kashe tv.
"Na sani Abie" haka wunin ranar maganar da zai gaya min na kwantar da hankali ne, da nuna min.
Ba wai na d'aga hankali na bane, amma kuma maganar gaskiya, bana jin dadin raina,.kawai ina daurewa ne dan kar na d'aga mishi hankali,

   Domin abin saura kwana uku, kuma nayi kokarin ganin na dauke kai na akan Mohan, amma na kasa domin komen kashin laifi idan yayi min, yanzun zan tsaya nayi ta balbale shi da masifa, zuba min ido yake na gama masifar sannan na fashe da kuka, toh a nan ne zai ta bani hakuri.

      Duk da haka bana iya dogon fushi dashi, a cikin saura kwana biyu, har gidan Khausar sai da ya kai ni, ya kuma kai ni gidan yan uwan baban shi da suke yan uba, Alhamdulillahi na samu kyakkyawar fahimta a tsakanin mu dasu, kuma sun mana fatan Alkhairi, dake mutum ne mai matukar ilimin dan adam, bai yarda na tafi hannu rabba ba, domin duk inda zan shiga yana min sayayya yace musu nice na kawo, wannan abin ya kara min matukar daraja a idanun dangin baban shi har suka fara adawa da Hanan. Musamman yan matan family din su, dayawa sun ki marawa Hanan baya, karshe suka shiga rokona.
"Don Allah Addah Munari ki amince ki auri Hammah Mohan, don Allah karki ki amincewa wallahi muna sonki". Wannan abin ya kara sani samun kwarin gwiwar son kasancewa da MOHAN. Sai dai abinda basu fahimta ba, duk soyayyar su matukar mahaifiyar shi bata yina ya zama na banza, matukar bata kaunata babu amfanin  zama dashi.

   Haka ana gobe za'ayi baikon ya kai ni gidan su dan Ba'are sabida akwai wasu daga cikin Familyn su da zasu zo, koda suka zo da kan shi ya kai ni. Domin har da Kakar shi ta gurin Uwa. Koda muka shiga gidan. Ba dukkan su bane suka yi na'am da ni ba, sai dattijuwar mai suna Nahnah. Ina shiga cikin dakin da take ta zuba min ido.

      "Ke bafulatanar ina ce?" Ta tambaye ni,
"Libya-Nijar" na bata amsa,
"Daga wacce kabilar kike?"
"Wodaadabe Bororo"
Rike hannuna tayi tsam, tana me lumshe idanunta. Kafin ta bude idanunta.
"Ya sunanki?"
"Maimunari!" Kura min ido tayi, na wani lokaci kafin tace min.
"Allah yayi miki albarka, ya kuma had'e kanku."

   Na kalle shi, murmushi yayi min tare da lumshe idanun shi, yana gyada min kai. Kafin muka fito tare da mika musu laidar da nazo musu dashi, ita kuma Nahnah na bata katon laida mai dauke da kunshi takarda a cikin shi kilishi ne.

Koda muka fito kallon juna muka yi tare da sakarwa junan mu, murmushi.
"Gaskiya kai dan babban gida ne, kawai baiko sai kace wanda za ayi bikin shi"
Hannun shi cikin aljuhun wandon shi yace min.
"Eh ya za'a yi dan ma sauran basu zo ba, amma da kin ga family mu ba karamin yawa ne dasu na, muna dayawa ainun. Kuma duk da haka Abbu yana ƙoƙarin kula dasu baki daya, duk da haka kawai manta."

"Idan naki fa? Amma dai gaskiya Allah yana son ka da ya kawo ka babban zuri'a gashi kowa yana sonka."

   "Sabida nima ina sonsu ba dan yanzun ba, ai da ina zuwa can na zauna. Toh aikin soja ba irin na kowa bane baka da lokacin kanka sai na kasarka. Insha Allah wani sati zan koma office."

"Lallai kace mazaje za a saka unifoam!"  Na fada mishi.

     "Wai haka" ya ce min yana murmushi,
Baki daya mun kashe lokacin yau a tare da juna, kuma mun yi dogon tafiya, kafin ya kira aka kawo mana mota, tunda ya kawo ni gida nayi sallah tare da cin abincin, muke hira har kusan sha biyun dare, kafin yayi min sallama.

    Washi gari
Baiko...

Ina kwance bana jin dadin raina, kawai dai ina kwance ni, gashi Abie ya ce ba sai nazo aiki ba yau, ina jin a raina kamar na rasa Mohan baki É—aya.

     Wayata na lalluba ka kira Hammah Mohan.
"Hello!"
"Hmmm"
"Yau ne baikonka ko?"
"Eh"
Toh Allah ya yasanya Alkhairi, ba zan sami zuwa ba, Innah bata da lafiya zan je dubata a Damagaram"

"Karya kike! Ba zaki zo bane kawai nagode, kuma wallahi na fasa"
"Hammah Mohan, ka fahimce ni"
"Ba zan tab'a fahimtar ki ba, dan haka kiyi tafiyar ki, na gode dana na jima da fahimtar ni nake hauka nake ba, maza jeki Allah ya baki sa'a"
Ya kashe wayar, ajiyar zuciya na sauke na fito daga dakina ina sanye da riga da wando. Na kayan barci. Tura baki nayi tare da cillar da wayar na zauna ina dafe kaina.
....

Hidimar da ake zaka rantse da Allah biki Mohan din za ayi zunzurutun yadda aka kawata kome, a cikin gidan shugaban kasa ake kome, dan haka Hajiya Latifah an shirya a bangaren Hanan kawayenta Æ´aÆ´an manyan mutane sun halara,

*_Gaskiya mura ya sani a gaba! Ba zan samu typing É—in na dare ba_*
#Mai_Dambu...
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1112326619?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=b5uzlwrsmnjDJy16UxrP%2B6c%2F7MtDoc5iAfHC4HQyJIms0PfUCslcpjPlXla74C0IG9WLlc5Su6cieJVelxnZUaqj64NLFkeQVg24jiQwUO0LftfuKKKLW5VGghOyRdvm

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.