Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 47 of 64

BABI NA HAMSIN DA UKKU.

"Wannan wayon fa? Kawai ka manta  da batun Mohan zan duba al'amarin Khalil Insha Allah. Sai maganar gaskiya, so nake ta Fahimci yarinyar yana da daraja a rayuwar D'anta. Domin nasan Lateefah sanin hakika bai zama dole ta saduda ba, nasa Lateefah kwanton bauna tayi"

"Wallahi tayi laushi." Saboda girman juna da suke gani yasa shi hakura, tare da sake musu lokacin, ba tare da iyayen sun fahimta ba,  a cikin yan kwanakin Aka nimo Auren Maimunari inda aka biya sadakinta mafi girma da darajar, domin da zinari Baban Khalil ta biya, Itama beenah Primer minister da kanshi ya tafi har Maradi aka nimawa Khalil auren Benazir, inda aka saka bikin su Khalil wata shida masu zuwa, shi kuma Mohan sati biyar sabida halin da yake ciki.

         A cikin kwanakin suka roki Maimunari tazo ta ga halin da Mohan yake ciki, haka suka tawo har da Innah da Baba, wani abin takaici koda suka iso ta nime Abie wayar shi baya shiga karshe da ta je kotun aka ce yayi tafiya. Su kuma kwana ɗaya zasu yi kamar zanyi kuka haka na hakura. Washi gari har gida Khalil yazo daukar su, dake na mishi kwatancen gidan.

Bayan tafiyar su ban kuma bin takan Mohan ba, oho su suka sani. Domin ba zan je ana min kallon wata aba ba. Satin shi biyu kwance, wanda yayi daidai da dawowana kwana goma, Mahaifiyarshi ta kirani. Na gama tattara abubuwan da suka dace ba abinda ya kawo ni. Daukar wayar nayi.

"Hmm! Bayan abinda ya faru ne zaki zo ki duba shi ba sai an roke ki?"
"Ammyn ni fa banyiwa kowa dole ba, idan yaga zai tashi ya tashi idan kuma kwanciyar ce tayi mishi bismillah, banda ina ganin girman Abban Khalil da Abbu. Allah na tuba ina zan kai sauran hauka."

"Kome aka yi da jaki sai ya ci kara,"
"Hali zanen dutse, kamar yadda aki'data take linzamin na, haka kema ba zaki sauya ba, dan haka ki aura mishi matar da aka haife ta domin darajar duniya, kuma kika kara gaya min magana sai na gayawa Abbu domin ya bani Number shi, sannan wayar da muke dake ina É—auka, idan kika dame ni na tura mishi, kuma kika iya tunanin balle ni da nake karanta shara'a"

Na kashe wayar abuna, na cigaba da aikina.

"Maimunari dawa ake rigima?"
"Abie mahaifiyar Mohan ce zata zage ni, ni kuma ba zan iya hakuri ba"

    "Toh ai babba ce! Kar ki kuma mata rashin kunya kinji! Bana son jin haka"
"Toh Abie"
Mika min wasu takardu yayi, sannan yace min.
"Maimunari zaki tafi baki gaya min kome akanki ba, sanan nima kuma ban gaya miki kome a kaina na, wannan takardun dukiyata ce, da wasu kadarorrin duk da ba dukka na tab'a ba, amma gasu nan na saka sunanki a kai, ina da Yaro ban sani ba ko namiji ne ki mace ce, amma na tafka laifukan cin zarafin mata, na nadamar abinda na aikata, Maimunari Yarinyar da naso na wulakantatta ta hanyar daukar ta ranar aurenta." Kasa fada min yayi yana share kwalla da suke zuba min.

"Har yau Zainab tana raina, har kwanan gobe ina son Zainab, ta tafi tabar ni da abinda ya haifa, bata kuma waiwaye ba, haka nima na tafi na bar abinda aka haifa ban kuma waiwayen shi ba,  don Allah ki sanyani a addu'o'in ki, wallahi na tuba na daina zaluntar al'ummar Annabi."
"Abie kunyi Kuskure babba, ta yadda kuka watsarb da jaririn da bai ji ba bai gani ba,. Allah ya yafe mana baki daya, sai dai gaskiya ba zan amsa ba, idan Allah ya nufa zamu yi aure da Mohan zan zo na amsa da kaina, idan kuma wani ne ma zan zo dashi. Nagode zan ajiye shi anan."
Na bude wani drowe na saka, sannan na mika mishi key,.nace.
"Abie ka bar kuka, Allah yana tare da da masu tuba domin shi. Kuma gashi kaki kayi aure, balle nace zan zo gidanka na kwana biyu. Abie kayi aure don Allah"

   "Toh ai Zainab nake so" ya faɗa yana murmushin jin dadi.
"Toh Yanzun don Allah, a ina zaka samota? A gari me girma irin Nijar?"

Dariya kawai yayi tare da rakoni har inda motar shi take yasa aka kai ni gida, ba zan tab'a manta wannan lamari ba, nayi farin ciki nayi bakin ciki. Nayi kuka nayi dariya.

   Da yamma lis na nufi asibiti, na same su, na gaida Umma bayan mun gaisa da Khausar da Radiyah, gefe can su Salman da Haddir ne, sai matan su. Karasawa nayi na gaishe su, sannan na amshi yar wajen Haddir, mai suna Widad.

"Ki shiga ki duba shi mana! Har yau bai san waye akan shi ba, ya shiga coman su Khausar suka ce." Mikawa Matar Haddir yarta nayi mai sunan Nabilah, na shiga jikina a matukar sanyayye, yana kwance mahaifiyar shi tana goge mishi jikin shi....

"Yarinyar tana da nutsuwa da kamala, gashi duk sanda zan ganta cikin shigar mutunci da kamun kai."

"Hmm!" Khalil ya faÉ—a bayan ya kalle su.
"Shima bai da mutunci, yarinyar nan tasha wahala da dan iska amma karshe zarginta yake, wai cewa ma tayi su rabu yake kwance, da shi ya kunshi bakin cikin da suka kunsa mata ba mamaki da lahira tayi baki."

"Gaskiya Khalil baka da imani, meye na wani cewa da lahira ta yi baki" inji Salman.
"Kasan Allah, babu dan iska irin Mohan,ni yarinyar ta min daidai dan Uban shi ko babu kome gashi kwance zuciya tayi laushi" ya faÉ—a yana dariya.
" Da fatan zaka maimaita a gaban shi."
"Bar dan iska idan ya tashi zaku ga iyayi da kinibini irin ta shi. Inda nice Maimunari ba zan tab'a yarda na aure shi ba sai ya tashi a jinyar da yake."sake mishi duka Umma tayi tana hararan shi.
"Kai dai ka zama sai du'a'i, amininka kake binshi da sharri?"
"Kai Umma kina ganin bai da mutunci shima." Fitowar Ammyn yana share kwalla yasa su zuba mata ido.

   Duk sun fahimci wani makircin ne.
"Yanzun sabida nafi kowa laifi idan nayi magana ba za a yarda dani ba, d'azun nakira ta tayi min rashin kunya yanzun ma ta shiga tayi min rashin kunya. Ni da d'ana bani da iko dashi"
"Ammyn ai duk abinda zata miki tayi miki da kauna ce, idan wata ce billahi azim ba zata zo ba sai dai ya mutu."

Jin abinda Radiyah ta faÉ—a yasata yin shiru, Nairah tace.
"Da nice wallahi ba zan zo ba, kai Ni ba zan aure shi ba, zan yarda ni matsiyaciya ce amma kuma nafi karfin mai kudi ya wulakantani ba Mohan ba, ko Uban Mohan ne ya mutu i don't care" ta wani ware hannunta (🤷🏼‍♀�?)

   "Toh ai abinda zaku duba yarinyar tasan darajar iyayenta da Mana, dan lokacin da Abba ya je, mahaifinta yace shi ba zai hana Mohan Maimunari ba, sai dai matuƙar aka tab'a mishi ita toh wallahi ta rabu da Mohan kenan har abada, ita kuma yarinyar da aka kira ta, cewa tayi duk abinda aka yanke ita mai biyayya ce. Kaji irin yaran da nake fatan Hur ta zama, koda Abba ya kuma tambayar ta, cewa ta kuma ita mai biyayya ce duk abinda aka bata zata amsa hannu bibbiyu, bayan Abba ya kuma tambayar ta, ya kira Abbu ya gaya mishi dama ya tafi Maradi niman auren Budurwan Khalil karshe privet jet din shi ta kuma bi yaje har Damagaram ya tambaye ta, ta kuma cewa.
"Abba duk abinda kuka bani ni mai biyayya ce, don Allah ina zaka so rasa wannan kyautar. Sai dai wanda duniya ta aure shi ba laifi zai iya nimar yar da take shan giya."

Inji Salman. Da yake basu labarin yadda aka yi gurin Niman auren Maimunari, Hajiya Latifah duk tana jin su, hmm bata ce musu koma ba. (Ni kuwa nace hmm zaku ci kaniyar ku🤷🏼‍♀️😏😒☹️�?)

      Lokacin da na shiga na same ta, kallona tayi sannan tace min.
"Kun nace!"
"Da alamun rayuwar dakin yana cikin hatsari amma bai dame ki ba?"
"Hmm!" Shine ta fita. Ni kuma ba zauna a jikin shi tare da rike hannun shi,  duk da laifin shi daya ne na zargina da yake amma har yau ina jin son shi yana sosa min zuciyata. Sumbatar hannun shi nayi, sannan na taka a hankali, na isa daidai goshin sa na manna bakina a kai, kafin ya sumbaci idanun shi, na dawo kan dogon lokacin shi ba sumbata, sannan na sauko bakin shi. Jan numfashi nayi sannan daura bakina akan nashi, sai da na jima ina tsotsar bakin shi tare da janye bakina daga na shi, na juya zan fita. Na tuna ranar da aka yi baikon mu, daidai zuciyar shi na sumbata, dan haka na isa gurin na sumbaci inda aka saka wani igiyar da karfe na sumbata, sannan na mike tare da barin. Dakin.
"Allah ya bashi lafiya zan tafi" na sallame su,

   Tana fita a dakin yayi wani irin jan numfashinsa na'urar da suke makale da jikin shi suka bada wani irin sauti. Da gudu Khausar ta shiga dakin tare da kiran likitocin, aka rufa mishi.

   So yake ya farka amma ina abu daya yake yawo a ranshi da ƙwaƙwalwar shi, sumbatar da ta mishi ranar da zasu rabu, sak irin shi yaji, a wata duniya, yana mishi.

    Haka suka mishi alluran barci Bayan sun tabbatar da bugun zuciyar shi ya daidaita.
"Kun gani ba! Idan ba maita ba meye daga fita zai kama!"

"Amma Latifah baki da hankali,  godiya za kiyi da Ubangiji ya bashi lafiya ba wai ki zargi wata ba, idan ma itace. Ai ta miki gata tunda ke baki hankali" yaranta babu wanda ya damu da abinda take yi.
      Fitowar Khausar tana yiwa likitocin godiya dayan yace musu.
"Akwai abinda ya tsaya ranshi kafin faduwar shi, kuma ina ga shi din ne ya kuma dawo da bugun zuciyar shi."

         "Mun gode! Insha Allah zamu bincika" bayan nan ta shiga yi musu bayani tare da gaya musu abinda ya faru.

   "Dan iska mara mutunci! Zan muku bayanin abinda ya faru, amma ku shiga family room" kallon shi suka yi, take ya bude data yana tura musu hoton emoji na saurayi da budurwa suna kiss, yace musu.

*Wannan shine abinda tayi mishi kafin su rabu. Kuma daga shi bata kuma yarda sun hadu ba. Ina da yakinin ta kuma sumbtar shine. Allah ya barsu tare amma gaskiya Ammyn bata hakura ba gani nake kamar akwai abinda yake shiryawa! Amma Allah yana sane da kome*

Take kuwa Family room din. Ya kuma hargitsewa. Haka suka yi ta fadan albarkacin bakik su.

      ***
Washi gari kafin na koma Maradi na kuma zuwa asibitin Ammyn bata nan sai Salman da Haddir, a mutunce muka gaisa har nake tambayar su.
"Ya jikin na shi har yanzun babu canji." Murmushi suka yi sannan Salman yace min.
"Eh toh jiya bamu san me kika bashi ba, daga tafiyar ki kawai malamin mu ya farka, yana barci dai yanzun."

_Kar dai sun fahimci na sumbace shi ne? Wayyo Allah na kunya_

"Amma bai ce wani abu ba ko?"
Na tambaye su ina zare ido.
"Eh toh! Ya dai ce sumbataaaa!"
"Ya ilahi!" Na daura hannu a kai.
"Amma bai ce muku na sumbace shi ba?"(🙆🏽‍♀�?)
"Ai ya gaya min kome, kai Maimun!"
"Amma me yasa Hammah Mohan yayi min haka? WALLAHI ba sa gayya na sumbace shi ba, ince babu abinda ya faru dashi"

"Salman don Allah ka kyaleta haka wallahi ta fadi gaskiya! Shiga abinki Karya yaƙe miki"

"Wayyo Allah na, ka sani nayi subul da baka!" Na fada ina shiga dakin da sauri. Har bakin gadon na nufa, tare da rike hannun shi.
"Ina jiranka! Ina jiranka a karo na babu adadi!  Ni kamar baiwar ka ce! Zan koma Maradi na gama abinda ya kawo ni, amma ina fatan zaka tashi daga dogon barcin da kake min ya isa haka! Maimunari mallakar kace, taka ce har abada ba zaka tab'a raba kaso da kowa ba, Maimunari kason kace! Ina kaunarka da fatan zaka tashi da izinin Ubangiji."

    Ina gama fadar haka na kuma sumbatar goshin sa, sannan ya juya zan fita naji ya rike hannuna. Juyawa nayi tare da kallon shi, komawa nayi na zauna a bakin gadon, tare da kallon shi.
"Karki tafi" ya faÉ—a min a hankali.
"Kayi hakuri! Daga wannan satin sati biyu masu zuwa ina karkashin da'iran mulkin ka ne sai yadda kayi da Ni!"
"Zaki Aure Ni?"
"Mun wuce wannan maudu'in!"
"Da gaske?"
"Da gasken gaske!" Na fada mishi ina share kwalla.
"Ki tanada min sumbatar ranar da kika min, ki ajiye min duk wani kwarin gwiwar da na gani a cikin idanun ki ranar, ki adana min dukka wani irin nau'in kulawa a daren mu, ni kuma zan gina miki daren da ba zaki manta ba!"

   Murmushi nayi tare da hade goshin mu.
"Na tara maka kome na wannan daren na adana maka kome a wannan daren, zan hada maka kome kuma zan sayo jarunta a wannan daren sabida kar na hanaka sukunin aiwatar da muradinka, Hammah Mohan daga wannan daren karka tausaya min ka fanshe duk wani soyayyar ka, a cikin shi ka nuna min sakamakon kaunar da kake min Ni kuma zan boye kuka na da kome zan baka kyautar daren, zan tsara maka daren ya zama mafi girma da darajar, zan Kawata maka shi. Zanyi kome domin ka, hmmm sannan zanyi kuka da!"

    Murmushi yayi tare da zungure goshina yana dariya.
"Idan kika yi kukan zan rarrashe ki, zan baki kyauta na musamman, nan dan mallaka miki zan baki dukkan shi zuciyar taki ce, zan zame miki farin dare zan raya miki daren da so da kauna, zan shirya miki shagalin da ba zaki tab'a Mantawa, ranar zan baki kyautar kaina baki daya, zaki ganin iya ganin idanunki, zan tsaya a gaban ki na juya ki ga irin mijin da kika aura. Ubangiji ya bamu yawan rai yadda zan share miki kukan ki, Ubangiji ya nuna min yadda zan sanyaki farincikin a wannan daren ya rabbil alamina ya nuna min yadda zan kayata miki daren ki! Ina addu'ar ki same ni a yadda kika sannin kika yi  fatan haka, akwai shagali yarinya babu tausayi babu ruwana da Yarantarki! Zaku hadu da katon tuzuru ne!" Rufe mishi baki nayi ina zare ido....
#Mai_Dambu...
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1113398663?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2BxTW4N%2Fi3%2B1dAQX5gbjmfTxgxiRMRb8Nl%2F50OD4pV94UP35Ih%2FrlfzEmYSOqSePFjk4F6wQI4BmDexcUn1v%2B6q7S5wMuA0Uc%2FC5OPGYtcFd9ON0zvTrtgtJg8WkJ5LAn

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.