Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 31 of 64

BABI NA TALATIN DA BAKWAI.

Idan na fahimci Innalillahi tana nufin, keb'ewa da nake da Hammah Mohan ba haka kawai bane ina barshi yana wani abu dani? Hmm tashi nayi tare da kallon shi.
"Tsaya a can zan sayi abu!" Na gaya mishi. Tsayawa yayi bakin hanya daidai kofar wani shagon sayar da maganin, sauka nayi tare da É—aukar kudi a jakata, ban san nawa bane kawai ina zuwa shagon nace mishi.
"Bani maganin mura" na ajiye mishi kudin, yana gani ya shiga dibo min su, ya tara min, sunan su nake bi, zuba min yayi a laida. Sannan na dauki daya na bude take na shanye a gurin, na ajiye mishi kwalbar, na dauki sauran zuwa motar, tunda na shiga na zauna na juya mishi baya, haka nayi ya shan maganin nan bai tashi sanin abinda nake aikatawa ba sai da na kwalbe Kwalba uku, da na farko biyar yaji karan zuɓewar kwalabe a kasa, wani taka birki yayi tare da birkito ni.

Ganin saura Kwalba biyu ina bude É—aya yayi maza ya gangara bakin hanya, ya kalle ni. Ranshi yayi mugun b'aci, kifa kai nayi sabida maganin ya fara tasiri a jikina.
"Ka gaya min me yasa duniyar take shirin juya min? Innah tace kana samun damar kwanciya dani zaka gudu kabarni, Ansar Yace min kana kwanciya dani zaka gudu kabarni me yasa tunanin su yayi daya ne?"

Jan numfashi nayi, sannan ba cire hijab dina nace mishi.
"Ka tab'a ganin mace a tube? Toh yau zaka ganin ni full naked." Na shiga cire kayana ina faÉ—in.
"Kawai zan baka kaina a wuce gurin, idan nayi haka zamu fi samun nutsuwa daga ni har su."

     Raba rigar jikina nayi gida biyu, kafin na juya na kalle shi. Kwantar da kujeran nayi baya, kafin na shiga ƙoƙarin cire zanin jikina. Komawa nayi na kwanta, sabida na kasa cire zanin sai na shiga ƙoƙarin cire bra din, anan idanun shi ya sauka akan dukiyar fulanina. Da na fitar da dayan shi. Dayan yana cikin rigar shi.  Tausayin ta ya kuma ninka sama da baya, cire rigar shi yayi ya lullube ta, sannan ya motso da fuskar shi, yana kallon yadda take mutsu mutsu da bakinta, kunnen shi ya kai yaji tana faɗin.
"Ba zan tab'a kashe iyayena ba, Innah amma zan iya sadaukar da rayuwata domin shafe tarihina, ina son Hammah Mohan!"   Gyara mata kwanciya yayi, sannan ya tadda motar tare da barin gurin da gudu, ina son ya isa Niamey akan lokaci.
*
Damagaram.

Shigowa malam yayi ya same Innah tana fadar abubuwan da suka faru, akan rayuwar Moonah, kasakai yayi da bakin shi yana kallonta.

"Me ya faru?" Ya tambaye ta,
"Waye ban da wadannan lalatattun, yazo ya dauke ta har yana gaya min maganar banza ashe na cancanci wofantarwa Maimuna?" Ta fashe da kuka tana kallon shi.
"Baki cancanci haka ba, amma kuma daga ke har Sama'ila kun so kanku dayawa, ai dama na gaya muku dole gaskiya zata bayyana kanta. Ai ba yau aka fara ba. Ai ba yau Sama'ila ya fara ba, ba kuma sabon abu bane.

    Dan haka ki ha bakin ki kiyi shiru, kiyi addu'a kawai Allah ya takaita hakkin iyaye akan ku. Kin zata yaran da ya raba da iyayen su, hakkin su zai tafi a banza ne? Ba zai tafi ba. Shima gudun tafiyar Ƙaddara yasa shi bai tab'a tunanin aure ba, da ya kuskura yayi auren da yaji yadda ake yinta na gaji da halin ki Allah ya gani, yar dan Uwanki? Zaki wulakanta ta, kamar ba jinin ki. Ai ko da Sama'ila yace ki rike ta karta tab'a bayyana kanta sai ya dawo ce miki akayi zaku yiwa Allah yawo? Ai baba Nasiru yayi gaskiya, dalilin soyayya ta bayyana kanta, yau dalilin SOYAYYA yarinya karama tana kuka. Ki barta ta rayu da abinda take so abu ya ci tura, toh Ni dake muzuba mu gani Allah yabawa mai rabo Sa'a."

      Daga haka ya juya ya bar gidan ranshi yana soya, sabida zunzurutun bakincikin, ita kanta sai da tayi al'ajabi da abinda malam yayi mata, kasa zama tayi ta kasa tsayuwa.

   ***
Karfe shida na yamma ya shiga babban asibitin Niamey,  wayar shi ya dauka ya kira Khausar.
"Kina cikin asibitin ne?"
"Eh Hammah ina ciki" da sauri ya fito tare da bude motar ya dauke ta, bayan ya rufe motar da kafar shi, ya shiga asibitin da mugun sauri, yana kallonta da yanzun bata da bambancin da gawa, yana shiga suna karo da Khausar.

      "Ku kawo gado" ya faɗa da karfi, da sauri aka kawo ya daurata, aka Wuce da ita dakin gaggawa. Fitowa tayi da sauri tana niman wasu likitocin, aka nufi dakin da Moonah take, aka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar ta, abin tausayi. Yana zaune yayi zugun. Har kusan awa daya kafin Khausar ta fito, ta zauna akan bencin da yake kai, ta daura kan shi a kafad'ar shi.
"Alhamdulillahi, Hammah mun yi nasarar ceto rayuwar ta, sai dai karta kuma aikata haka."
"Yarinyar tana cikin damuwa ne, kuma ni ne me laifin domin naga ta fita, amma kuma ban san me taje yi ba, ashe maganin mura tayi ta sha."
"Ba laifinka bane! Yanayin kaddara ce, mun yi mata alluran da zai lalata tasirin maganin."

       "Nagode kanwata karki bari sauran su sani don Allah"
"Haba ai ciwon ya mace na ya mace ce, dan haka babu wani abinda zai faru, Insha Allah"ta faÉ—a tare da gyara zama. Suna zaune aka fito da ita bayan an canza mata kaya. Suka kaita wani daki na daban.
Zama yayi a jikinta tun karfe shida, Khausar ce ta kira kanin mijinta ya kawo mishi kome, bayan ta gama aiki ta nufi gida wajen karfe tara, ta kawo musu abincin. Lokacin yana addu'o'in. Bayan ya idar da sallah da ake bin shi.  Jin ana turo kofar yasa shi juyawa.

Murmushi suka sakarwa juna, tare da kallon inda Moonah take.
"Hammah Sannun ya jikinta?"
Shafa kan shi yayi yana shafa addu'a, yace mata.
"Da sauki." Ajiye basket din tayi tare da kallon shi, kafin ta durkusa ta fara zuba mishi.
"Karki zuba dayawa, bana son cin abin dan dai naki ne"

     Ajiye mishi tayi ya kalla kadan sannan ya dauka yana ci yana kallon Moonah.
"Hammah kana Sonta da yawa, tun ranar da ka gaya mana da Hammah take kiranka ya sani sauya maka daga Yaya zuwa Hammah, haka kawai nake ganin kun dace da juna"

    Kallonta yayi sannan yayi murmushi, yana kallon Beauty ɗin shi. Idan ya tuna abinda ya faru kuma sai yaji ranshi ya b'aci sosai, dakyar ya cinye abincin yana ji kamar yayi ta fasa ihu. Domin jin kishinta yaƙe, musamman idan ya tuna yadda ya gansu a yau din nan kamar zasu shigewa juna, ajiye flet din yayi yana jin daci a ranshi.

      Hiran da Khausar ke mishi ma kamar dole ce, karshe da taga baya son magana, tashi tayi ta mishi sai da safe, har gurin motar ta ya rakata, sannan ya koma cikin asibitin, tunda ya koma yayi alola, duba jakarta yayi ya hango karamin Alqur'ani, ya fara karatu kasa kasa, har kusan karfe biyu na dare, kafin ya ajiye ya kifa kanshi gefen inda hannunta yake.

            Karfe uku saura ya farka sabida ya saba sallah a lokacin, dan haka ban daki ya nufa yayi alola, ya fito. Ya shiga kaiwa Allah kukan shi dan yayi Imani dashi babu me musu maganin taurarrun iyayen su, sai Allah Sarkin sakarakuna.

    Yana gurin har karshe hudu, sannan ya nufi masalaci, yana can har aka yi sallah asuba, ya dawo cikin asibitin, yana jin barci amma babu yadda ya iya, dole ya jingina kan shi akan gadon ya fara barci. Karfe bakwai Khausar suka shigo ita da Radiyah, ganin yana barci, ya suka koma tare da rufe kofar.

Abin mamakin basu tashi ba sai karfe É—aya na rana, sai dai Khausar ta shigo tayi abinda zata yi a hankali, tana gamawa zata fita. Kofar ma a hankali take jan shi.
           Yana tashi ana kiran sallah azhar, dan haka ya nufi masalaci. Zama yayi a can sai karfe hudu ya dawo domin lokacin da zai fita sun hadu da Radiyah. Dan haka ya zauna a masalaci, yana dawowa suka gaisa, tare da zuba mishi abincin, yana ci yana mata yan tambayoyi, tana bashi amsa, haka suka zauna har dare sannan tayi mishi sallama.

Wasa wasa sai ga Moonah har ta shafe kwana uku cur, a cikin kwanakin nan kuwa. Idan ka ga Mohan zaka rantse da Allah shi yake jinya domin ya firgita tayi wani zuru-zuru. Sai ka zata shine ai da lafiyar ma. Sam ya manta da kowa sai Moonah, ranar da ta cika kwana uku, likitocin sun taru akanta. Suna tattauwana. A hankali nake bude idanuna. Da nake gani dishi dishi, lumshe su nayi tare da jin wasu irin yarerrika ake a kaina, tsikara min wani abu ya sani cewa.
"Wash" suna cewa "masha Allah" sake lumshe idanuna nayi sannan na kuma buÉ—e su, wani irin haske na gani ya wuce min. Daga nan ban kuma dawowa hayacina ba,

Sai washi gari na bude idanuna, yana barci cusa hannuna nayi cikin gashin kanshi, ina wasa dashi. Murmushi nayi tare da jin kome na raina da damuwa ta ya gushe, take kuma abinda na kaita ya dawo min kaina, dafe goshina nayi fa jikina babu kwari.
"Hammah" na kira sunan shi,  a hankali ya d'ago kai yana kallona fuskar shi a daure.
"Kayi Hakuri"  na mika mishi hannuna. Tashi yayi ya zauna a bakin gadon sannan ya rungume ni.
"Mahaukaciya waye ya gaya miki maganin mura yana rage damuwa, kinsan halin da kike jefa zuciyata kuwa? Kece kike kwance ni nake miki jinyar karki kuma min haka domin zan mare ni, ya faÉ—a bayan ya had'a goshin mu guri daya."

"Kayi hakuri, duk ranar da na rasaka a rayuwata tabbasa mutuwa ce ta dace dani, Hammah na, ina jin tsoro! Ina jin tsoron ranar da ba zaka iya taimaka min da kome ba sai ido, ina ji a jikina abubuwa dayawa suna tunkaro ni, Hammah Mohan kayi hakuri. Idan aka samu akasin ƙaddara karka juya min baya, idan aka samu sauyin ƙaddara karka guje ni, idan aka samu yanayin ƙaddara karka tafi ka barni, Hammah idan ka juya min baya daga zanen ƙaddara ta, wallahi billahi azim mutuwa ita ta dace da rayuwata ba, ba rayuwa ba." Kukan naja tare da kallon shi.
"Hammah! Kasan me wallahi wallahi wallahi mutuwa zan yi, domin kirjina kamar yana ci da wuta , Hammah ina da damuwa. Hammah ina ji kamar banbanci zama fa kai ba, me yasa na shiga rayuwar ka? Me yasa na takura maka. Hammah kayi min addu'a idan mutuwa xan yi na mutu a hannun ka, Hammah ina jin kamar nan gaba kowa zai guje ni! Amma kai! Zuciyata ta ki gaya min zaka guje ni.  Hammah me yasa nake kuka? Kawai dan nace sai na zama mace ce ko kuma dan nace ina son kane ya kawo haka! Hammah!" Na kira sunan shi ina jin wani irin tari a daga zuciyata irin me kaikayin nan. Tarin na fara tare da jini,, gogewa nayi tare da kallon shi. Kamar wanda aka dasa shi, ya rasa gane meye yake mishi  dad'i. Ji yaƙe kamar baya duniyar baki daya. Tarin ya tafi da karfina. Kwanciya nayi a jikin shi. Ya kuma rungume ni. Goge bakina nayi tare da bude baki zan yi magana, ya rufe min bakin da hannun shi.
"Ya isa haka, zaki yi dariya wata rana ki daina kashe ni da raina."
*HMMM! A KARAN KAINA BANI DA HAUFI AKAN YADDA ALMAMOON KO NACE MAIMUNARI BA ZAN SO TA TAGAYYARA BA! AMMA A YADDA LABARIN YAZO TAFIYAR KADDARA SHINE MADUBIN LABARIN BOROROJI INKIYAR LABARIN CE, AMMA SUNAN LABARIN SHINE TAFIYAR KADDARA! BANCE YA FARU DA GASKE BA. AMMA TOH DAYAWAN MU BAMU SON MUGA JARUMIN LABARI YANA SHAN WAHALA! TOH GASHI TAFIYAR MU NA DAN NISA KUMA KUN FARA SAREWA TAYA ZAKU ZAMU JI RAYUWAR JARUMAR AMMA TOH BANSAN ME ZANCE BA AMMA KUYI HAKURI KUYI HAKURI KUYI HAKURI SHINE ABINDA ZAN CE DA WANDA XAI ZO GABA da wanda zai wuce duk yana cikin tafiyar ƙaddara 💓❤️💞*
*Yau lalaci nake ji wallahi! Wai meye nufin Ku? 🙄 Anya ba zan yi rashin daraja ba toh Shikenan mu hadu nan da sati Uku masu zuwa tunda ba zaku yi voting ba🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀�? sai na tafi hutun baba ta gani domin dama hanyar tafiyar nake nima kuma kun ki bani damar haka ba*
#Mai_Dambu.
8/19/21, 6:53 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1109544279?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=jfVhi7eN9HoToyWK2IK1Om6sqMtZf1yyZ%2Bne%2FvH0bt9GhZlc9FG1phyPxEZrvJ9chyYJ%2FCfRfvUMri3Zq3pk4FzYixCktvZE2JvpFYpj4wiO1rqTM%2FpB2xa010KtsSOd

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.