Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 10 of 64
BABI NA SHA BIYAR.
"Sake min hancina!" Na maza na kwace kaina a hannun shi ina lailaya hancin nawa, kamar zanyi kuka. Harara shi nayi tare da cewa.
"Maza zauna a nan na shiga ban daki na yi wanka." Na nuna mishi inda zai zauna na shiga ban dakin.
Sai da na shirya sannan na fito, na same shi yana zaune kwayam.
"Kayi hakuri kaji na Barka kai É—aya a daki."
Bai kula Ni ba, kamar yadda ban saka rai zai amsa ba, haka na cigaba da uzurin gabana, ban kuma bin takai shi ba, domin abubuwa da zanyi na maganin shi yana dayawa, dan haka na shiga haɗawa ina kaiwa ban daki nasaka shi ya cire kayan shima da kokuwa, haka na samu ta cire na fito na kira Hammah Malik yazo yayi mishi wanka Tunda suka fara yaƙe rawan sanyi.
  Har suka gama ya fito, na shafa mishi addu'o'in, sannan ya kwanta, ban yi tsammanin zai yi barci haka ba, sai gashi yayi dan haka ma na fita na barshi a dakin nayi sallah, ina idarwa na kuma leko shi, ina dawowa na samu bai farka na, dama Baba ya gaya min zai ta yawan barci.
 ***
Kasa zama yayi ya kasa tsayuwa. Kallon Mutallab yayi sannan yace mishi.
"Kasan me? Ba zan iya boye maka abinda yake raina ba, amma wallahi ina masifar kaunar Almamoon" ya faÉ—a a sanyayye, yana kallon yadda Mutallab ya sake baki, mik'ewa yayi zai fita Ansar ya riko hannun shi.
"Don Allah saurarre ni mana" fauce hannun shi yayi yana zare mishi ido.
"Shika min hannuna, da alamu ka haukace? Ba banza aka yi ta muku kallon masu soyayyar jinsi ba, ashe da gaske ne soyayyar jinsin kake ina zaka kai..."
"Dalla ka min shiru, ka bude banzan bakin ka sai maganar banza kake yaron nan mata maza ne!" Ya fada da karfi, zaro idanu Mutallab yayi tare da had'iye yawun.
"Kasan me yasa na gaya maka? Saboda ina son Yaron ne kuma zan taimaka mishi ayi mishi aikin ya tsaya a mace, wallahi ina masifar kaunar shi. Please my Friend kai É—aya ne zaka taimaka min shi yasa na maka maganar please"
  Ajiyar zuciya yayi yana kallon shi, Kafin yace mishi.
"Ban san me zan ce maka ba, amma na tausaya maka. Kuma idan na boye maka yadda rayuwa take yana da hatsari, idan yaron nan yana son ganin shi a mace falillahamdu idan kuma ya fison ganin kanshi a matsayin mata maza TOH karka tirsassa mishi ayi abin da zai saka kowa damuwa."
    Riko hannun shi yayi sannan ya ce mishi.
"Na sani, amma abin mafi alkhairi shine a dawo dashi jinsin da ya fi karfi idan aka ce lallai sai an jira ra'ayin shi ba zai yarda ba." Shiru yayi na wani lokaci kafin ya cigaba da cewa.
"Tukun kasan inda yaron nan yaƙe? Kasan a inda yake rayuwa? Yana tare da dan primer minister ne, kuma abin takaicin tunda yagan shi ya makale mishi.
   Wallahi ina tsoron kar yaje a lalata goben shi! Ina tsoron kar abin duniya yasa a lalata mishi mutuncin shi, don Allah ka taimaka min ta yadda zan shawo kanshi."
  Shiru Mutallab yayi yana gyada kai kamar kadangaren da ya sha rana.
"Yaushe kenan zamu hadu da Almamoon din, tunda kaga kun kusan komawa makaranta?"
  Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanun shi yana kallon yadda Almamoon shi zai koma da yan nonuwa a kirjin shi yana takun kauna a dakalin zuciyar shi. Tashi yayi zaune yana faɗin.
"Insha Allah ranar friday"
     Wani irin murna yake ji sabida yana hango yadda zai yi da Almamoon indan Allah ya nufa ya zama nashi. Kuma yadda zai sarrafa santalelen cinyoyin shi,(da gaske ashe su Mom Sayeed da Maman Sadeeq basu yi karya ba hauka kake tuburan team Ansar 🤣🙆ðŸ¾â€â™‚ï¸ï¿½?)
***
Zaune take tana ta haÉ—a aikan da ka kawo mata daga gidan ministan harkokin wajen tana gani tana murmushin mugunta domin haÉ—in na musamman ne, dan haka ta kira Babban matakin mai tuka jirgin saman fadar.
"Maza ku shirya gani nan zuwa Maradi zani"
Kashe wayar tayi tare da É—aukar jakarta tana me jin a ranta shi kenan daga wannan haÉ—in Insha Allah Mohan Mamman Nasir Aghali ya tafi har abada.
.... Dakin Hajiya Lateefah ta shiga daga bakin kofar ta shiga matse kwallar fuskarta tana faÉ—in.
"Hajiya yanzun don Allah ba zaki ki ga jikin Mohan ba? Hajiya abinda kike fa Allah"
"Fitar min a d'akina!" Inji Hajiya Latifah, tana nuna mata hanya. Kamar da gaske ta saka kai zata fita.
"Inda yaso ya mutu ko ya rayu, ohon shi" ta faÉ—a da karfi tare da jin kamar zuciyar ta zata buga dan bata kaunar a kira sunan Mohan a kusa da ita balle kuma sauran Yaranta.
   Da wani shu'umin murmushi ta bar falon tana jin a ranta shi kenan ta karewa Mohan Mamman Nasir, zata biya yaron da yake tare dashi kudi na fitan hankali.
 Â
Tana fitowa ya hadu da Primer minister, da Manyan yan jam'iyyar shi. Dake tana shirye da ta tozartashi tace mishi.
"Yallabai ina son zuwa na duba jikin Mohan"
Wani irin duba yayi mata tare da cewa.
"Ba yau ba"
Ya cigaba da abinda yake, juyawa tayi tare da komawa gida, har ta nufa gidan ya dawo tana cewa.
"Yallabai sai yaushe?"
"Jibi Insha Allah"
"Dama magani zan kai mishi, kuma yana da muhimmanci, tun da laluran nan hauka ce ai dole a duba lamarin don Allah ka barni na duba shi"
"Ba zaki ba nace" ya daka mata tsawa da yasa ta juyawa da gudu,
Caaa suka mishi da ido, yana jin numfashin sa yana hawa da sauka.
"Yallabai Mohan...."
D'aga hannu yayi alamar baya son jin koda kalma Daya ce daga bakunan su. Mik'ewa yayi yana me d'aga wayar shi ya mikawa Mai bashi Shawara na musamman.
"Ka musu bayani gobe zamu zauna yau bana jin dad'i."
Ya nufi hanyar da zai sada shi da cikin gidan shi. Yana jin kamar zuciyar shi zata buga.
Daga kasar zuciyar shi kaunar danshi yake kokarin tasowa mishi amma kuma k'iyayyar yaron yana kara danne mishi kin yaron.
  Yana shiga falon shi ya zube akan sofa, yana jin wani irin kewar yaron a ranshi, amma Yarasa me yasa yake jin zafin yaron.
Chef Judge ya fado mishi a rai, baya mantawa ko wancan juma'ar sai da yace mishi.
"Yallabai munufarka tana da kyau sai dai kuma da na jikinka ake maka yankan baya, sannan ake niman ganin bayanka, Yallabai nasan ba ilimina ya kawo ni nan ba, Allah ne ya kawo ni nan, kai a tunanin ka bayan mun hadu a Saudiya na gaya maka wannan yaron da kuke tafe dashi zanen ƙaddara zata iya raba tsakanin ku.
       Kuma kai ma baka manta ba, na gaya maka yaron ka yana da taurari masu karfi da zai hadu da wanda yake da irin taurarin shi da duniyar su. Yallabai Yaron ka yana cikin mawuyacin yanayi wanda a cikin gidan ka aka fara, sai dai kuma Allah yana sane dashi kuma yana sane da kome, idan yaso sai ya kawo mishi dauki kuma ya bashi wanda zai tsaya mishi. Ina tausaya mishi, duk da na daina na tuba amma bana jin dadin yadda rayuwar d'anka ya koma. Allah ya hada shi da mutanen kirki masu tsoron Allah. Yallabai Yaronka shine jigon mulkinka kayi wani abu akanshi ya dawo kusa da kai, Yallabai ina ga baka tab'a jin ana fadin Yan baiwa ba ko? Toh d'anka yana cikin su, domin kuwa idan yana tare da kai kowa tsoron shi yake babu wanda ya isa ya takaka, idan baya tare da kai kuwa wallahi jikin su na rawa zasu nemi bataka idan ka shirya zan duba Al'amarin shi Insha Allah za a dace"
  Duk da yana jin zafin kiran sunan Mohan da Shugaban alkalan alkalai yake amma haka bai hana shi jin abin a ran shi ba
.toh waye yake niman bayan shi? MEYE! Mik'ewa yayi bayan sun idar da sallah jumma'a ya mika mishi hannun shi.
"Nagode idan ina son karin bayani zan Nime ka, alkalin alkalai" inji Primer minister,
"Nagode sosai Allah ya tsare gaban ka da bayanka"
Lumshe idanun shi yayi yana kara nazarin abinda yake faruwa, na farko tunda Mohan ya fara jinya mutane dayawa suka shiga rayuwar shi kuma suna abinda suka gadama bai isa ya hana su ba
 Na biyu tunda babu Mohan aka fara mishi bore kamar zasu shi Office din shi.
Na uku kowa niman daura mishi laifi yake kome ya faru niman a cutar dashi ake? Ya rasa gane abinda yake faruwa,.ya rasa gane dalilin da yasa aka juya mishi baya, a yanzun yana da shekaru masu yawa akan mulki amma bai tab'a jin ko ya cutar da kowa ba, amma shi kullum niman hanyar cutar dashi ake, kasa fahimtar kome yayi, sai ma dage kirjin shi da yayi yana kara tausayin kanshi.
Yana kuma jin kamar akwai masu bibiyar rayuwar shi da ta iyalin shi, idan ba haka ba me yasa za a mishi wannan abun?
   ***
Maradi.
Addu'a ake mishi yana kara mingirawa kamar maciji, duk ya jima kamshi ciwo, sai rike kanshi yake, da sauri na mike zan kai mishi dauki domin yana cutar da kanshi, rike ni Malik yayi cikin wani irin sassayan kallo, ya rike hannuna. Fisgewa nayi na fada kan Mohan, wani irin duka ya kaiwa kirjina, sai da naji kamar raina zai fita sakamakon dukar nonuwana baki daya da yayi.
  "Hyaiiiiiiii! Haaaah" na sauke wata irin numfashi tare da jin kamar an cika min iska a bakina da kirjina, tafiya nayi zan zube Malik ya tare ni, daidai shigowar Dan Ba'are, shima ya kai mun wani irin riko, suka kwantar dani a kasa, yayinda Mohan yake ta amai.
  "Alhamdulillahi yau zamu bari zuwa gobe ku kula da Yaron yayi kokari wallahi"
    Bai kai aya ba,Dan Ba'are ya dauke ni da gudu ya fita dani Sakamakon jinin da nake fitarwa ta hanci da baki, baya ganin gaban shi domin kamar dirka yake a step din, har asibiti ya kai ni.
   A guje ya fita dani, Yaran shi da suka rako shi suna ganin shi aka bude kofar motar da sauri ya saka Ni sannan ya shiga yana me daura kaina akan cinyar shi.
"Taka motar"
Ya fada da karfi, haka suka fincike ta a guje.
    Daidai fitowar Malik da Malam.
"Yanxun ya za ayi da mara lafiyan?"
"Zan kula dashi" ya faÉ—a kamar zai fashe da kuka, domin wani irin yanayi yake ji na takaicin yadda Dan Ba'are ya mishi shigan sauri haka kawai zai wani dauki Almamoon ai haka bai dace ba ina laifin ya kuka da Mohan shi ya kai Almamoon toh idan kuma wani abu ya faru da.....
.......... Chaiiii.....🙄 Ga masu bukatar a tallata musu Hajar su kofa a bude yake a tuntube wannan Number,08130269641
8/19/21, 2:23 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1099611906?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=B2xbg56NQ%2Bj7itiadIMLq5S6mXv9S%2FsKyYdkh0H8PJKgwqgLqD%2Fo961ZM5LierkVHLwx3qEwMnG%2BOkvdE6rc9D1tbKk2fSwjLb0oWove1cVKshUkIo7LVOxrft0MhTCk
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.