Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 1 of 64
*BOROROJI*
~The Journey of Destiny~
 Mai_Dambu
Littafi na D'aya...
Sadaukarwa ga
 Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
Mafarin labari...
BABI NA ÆŠAYA
Niger Republic.
Tayi makotaka da wasu ƙasashen har guda bakwai.
Chad
Burkina faso
Benin republic
Libya
Algeria
Mali
Nigeria.
Kuma dukkan su ƙasashen a zagaye suke da kabilar Wodaadabe Bororo da wasu dangin Fulanin...
2000/ May/08
Nishi take a hankali, tare da cizon bakinta. Iska ta kuma ja alamar tana cikin tsananin zafin nakuda, juya kai tayi cikin tsannanin takaici da bakin ciki, ga wani abu da ya tsaya mata a makogaronta. Yau kimanin wata goma sha biyar kenan da take jin abin a ranta, har yanzun bata ji saukar shi ba.
  "Sannun Abuh ga ruwan addu'o'in sha Insha Allah zaki sauka akan gwiwar lafiya." D'ago kai tayi ta kalle shi cikin tsannanin k'iyayya da bakin ciki, sannan ta sunkuyar da kanta, tare da had'a kai da jikin itaccen da akayi gadon kara dashi. Ta kuma sauke wata ƙatuwar nishi a hankali jariri ya fado daga kasanta, cikin wani irin kakkarin kuka bayan ya zabga atishawa, Allah da idon shi ya diro da uwa baki daya.
    Murmushi tayi lokacin da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da wuccewar abinda ya tokare mata kirjinta. A hankali ta mike tare da ɗaukar wani mayafi da zani ta daura sannan ta dauki babban zanin da yake sayo mata, tayi kunzugu dashi. Kafin ta isa gaban shi tace mishi.
"Kowacce rayuwa akwai samu akwai rashi, akwai nasara akwai faduwa. Kamar yadda ka zalince ni Ya Allah Ya ninka maka abinda kayi min. Kamar yadda ka saka ni kuka Ya Allah Ya sakaka kuka.
  Kamar yadda ka hanani farin ciki Ya Allah Ya hanaka, zan so Ubangiji ya jefa ka, kasar jahannama. Ya turaka ƙarƙashin fir'anuna da hamana, Ubangiji ya haɗaka da masifa da bala'i, Ya Allah Ya sanyaka bakin ciki sama da yadda ka saka ni."
     Takowa tayi gaban Jaririn ta juyar da shi, tana me kallon Mutumin da yake tsaye, ta sake murmushi me had'e da kuka, tace mishi.
"Ba zan yi fatan kayi irin na wancan mujirimin ba, zan so kayi rayuwa cikin salama, wannan mutumin da ya samar da kai mugu ne, mugu mara alkibla, fasiki mara imani, kazami me dauke da datti da kazamta na bala'i da masifa da jahilci ya goga maka bakin fanti na har karshen rayuwar ka. Iya haka ma ya ishe ka, ka tsani wanda ya bada gudummawar jazaman ƙaddararka"
  Sannan ta tako gaban shi cikin bakin ciki mara iyaka, tace mishi. "Sama'ila kenan, gamu ga ka ga duniya ga Allah ya tsayawa me gaskiya." Ta juya ta nufi kofar dakin zata fita. Riko hannunta yayi tare da zuba gwiwar shi a kasa, cikin tashin hankali yace mata.
"Don Allah ki rufa min asiri, ki dauki Yaronki, bai da gatar da yafi naki, Zainabu zan gyara kuskuren da nayi a shirye nake na isa gaban danginki don Allah ki rufa min asiri karki juya mana baya a daidai lokacin da muke bukatar ki"
    Cak ta tsaya tare da sake wata irin kuka da sai yanzun ta samu damar yi, tare da shasheka.
"Aminci Allah Rahaman Allah, jin kan Allah Ubangiji ya hanaka su tun daga duniya har lahira" sannan ta saka ta bar dakin da rugar baki daya, tana tafiya tana kuka dukda sulisin dare ne, bai hanata tafiya ba, sai da tayi dogon tafiya kafin ta isa wata iyar karamar gari, tun daga nesa take hango kamar fili ne sahara babu kome sai rairayi. Kurawa gurin ido tayi alamar kamar ba nan take nima ba, dan haka ta cigaba da tafiya har alfijir ya keto sanyin Asuba ya kuma gabatowa zama tayi a kasar wata bishiya tare da kusa hannunta kasar cikin ta da yake murÉ—a mata jini na zuba a hankali. Barcin gajiya ce ya dauke ta.
 Kamar yadda Zainabu ta fita daga dakin da rugar baki daya, zama yayi yana kallon jaririn da yake ta kyankyara kuka kamar zai shiɗe, a hankali yake jin muryan jaririn zaaa a kunnen shi. Har ya kasa jure kukan jaririn, ya dauki wata zani ya lullube shi, tare da kallon fuskar shi, kamar ya shake shi. Amma ya fasa, can wata zuciya ta kuma bashi shawaran ta kashe shi ya huta da godon abin kunyan da ya aikata. Zama yayi tare da kurawa jaririn ido, babu abinda ya bar mishi. Domin kwayar idanun shi tarr akan na Ubanshi, kwallar da yake cikin idanun shi ce ta sauka akan na jaririn, ya kuma ware idanun shi tare lumshe nashi. Kwayar idanun yaron kamar an ja shi da kwali, cikin idanun zaiba ce kamar wanda aka zana da ruwan zinari. Sai dan digon bakin tsakiyar ya Kawata kwayar idanun Yaron goshinsa kuwa cike yake da gashi me shegen laushi da tsantsi. Gashin giran shi a haɗe yake da juna, karan hancin shi har bakin shi, bakin shi karami me kyau dai-dai ta jarirai, wanda Uban yake hangowa sakamakon hasken fitilar kwai da take ci. Hannun shi ya saka a bakin shi yana tsotsa cikin hakuri da juriya, wani irin kukan danasani ne ya shiga saukarwa Uban. Me yasa ya aikata abinda yake ganin dai-dai ne, me yasa bai hakura da Zainabu a ranar ba, me yasa ya rushe mata na ta farin ciki.
    Yana sane da iyayen ta, sun bar gurin su, ina zasu kuma haduwarl bayan yasan suma Bororoji ne, ba ma zauna bane kuma ba zasu tsaya ba. Zai yi wuya su tsaya tunda su din Fulanin tashi ne. Bai ga amfanin fitowar shi a cikin kabilar Wodaadabe Bororo ba, bai ga amfanin amsa sunan Bororo ba. Ya zai yi da rayuwar jaririn nan?
   Ya rabata da kowa nata, ya raba ta da farin cikin ta, ya kawo ta inda yayi ta gasata da bakin ciki da tashin hankalin, me yasa bayiwa rayuwar shi adalci ba? Me yasa bai tuna da wannan lokacin ba? Ya lalata rayuwar jinjirin shi, ya lalata kome nashi, me zai cewa duniya me zai gayawa mutanen da suka bugi kirji suka amsa karyar shi a a madadin gaskiyar shi? Wacce irin son zuciya ce ta kai shi da aikata wannan kuskuren! Lallai tafiyar shi rugar Alu yaja mishi bakin cikin da zai mutu yana danasanin kuntatta mata da yayi. Kukan jaririn da kiran sallar farko ya sa shi, fahimtar asuba yayi. A hankali ya mai da jinjinrin kamar ya kashe shi amma yana jin kamar haka ba zai yiwu ba. Tunda yasan makotan bukkar su. Wani irin tausayin jaririn ne ya kuma kama shi. Dan haka ya mike tare da d'aga labulen ya fita a hankali lokacin har anyi Sallah asuba.
   ---
Bayan yayi alola ne ya dawo D'akin ya rasa yadda zai yi da jaririn, domin ya cikawa mishi kunne da ihu, har ta kai makotar shi sun fara zargin ko uwar yaron ta gudu ne yaki gaya musu, kuma har zuwa lokacin bai raba yaron da cibiyar shi ba, dan haka yayi ta zaman dakin yana kallon jinjirin.
"Gafara dai Sama'ila, me nake ji a gari ana ta fadar cewa Abuh ta gudu ta bar maka jariri ba dai abinda su.?" Yadda ta kalle shi cikin tashin hankali, shima kuma ya sunkuyar da kai tare da mika mata jinjinrin yasata fashewa da kuka. Tare da cewa.
"Kaico wannan wacce irin ƙaddara ce? Me yasa kayi haka? Gashi nan abinda kayi ya lalace ya Barka da kunya me yasa ka aikata haka? Me yasa ka rushe yarda da ke tsakanin mu? Meye muka gaza maka? Ni mijina Hamma Sama'ila ka cuci wanna abin ka zalince me zaka ce mishi idan ma abinda ake zargin ka dashi haka ne me yasa?
Me yasa ka tozarta baiwar Allah, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun." Ta kuma fashe da mugun kuka tana kara rike dan jinjirin. Tana kuka kallon shi, sannan ta fita da jaririn tana wani irin kuka me ban tausayi, duk bukkar da ta shige sai taji sun ce mata "tir" har ta isa bukkar ta, mijinta me suna Sanda ya fito tare da kallonta da dan luɗi, yace mata.
"Kabo lafiya?"
 "Sanda me zanyiwa Hamma Sama'ila ya fahimci abinda ya aikata? Me yasa yake da mugun son kanshi? Meye ya saka shi aikata abinda zai saka mu kuka har karshen rayuwar mu.". Shiru yayi sannan yayi kwafa. Kafin yace mata.
"Shiga da jaririn ciki an fara cika mana" juyawa tayi ga wasu daga cikin mutanen da suke kewaye dasu har sun fara fito mishi, dan haka ya shiga cikin dakin, tare da sake labulen. Ta saka jaririn a gaba tana kuka..
Shi kuma ya nufi bukkar Sama'ila.
  Yana shiga ya same shi zaune ya cusa hannu a cikin gashin kanshi, yana nazarin makomar rayuwarsa da na abinda aka haifa.
"Sama'ila meye ya faru? Ina Abuh?"
"Ta tafi, kome ya lalace kuma nayi farin cikin faruwar haka. Domin ta haka ne zai saka na girbi abinda na aikata, kuskuren ne babba ka kalubalanci kaddarar wani, amma babban tashin hankalin yadda rayuwa zata juya maka idan har duniya ta san waye kai? Meye matsiyin shi a cikin al'umma? Meye zance mishi a cikin al'umma,? Me zan mishi idan ya min tambaya daya tak? Sai yaushe zamu daina aikata laifukan ci da karfi? Yaushe kuka zata daina wanzuwa a zukatar mutanen da suka fada irin abinda na aikata?
  Yan mata nawa ne zasu daina kuka? Yan mata nawa ne zasu daina gudun kabilar Wodaadabe? Me yasa muka yi kaurin suna ta hanyar lalata farin cikin wasu? Me yasa na san wani sirri har na saka Iyaye da yawa kuka? Sanda nayi tir da Allah wadaran halin irin nawa, a wancan ranar abinda take so ta zab'a amma na kasa Fahimtar haka,.
Iyayen ta sun gudu sabida abin kunya, mijin da zata aura ya tare ni naashi dukar da sai dai wani ba shi ba. Tir tir tir da halina." Ya fada yana me fashewa da kuka. Can kuma ya shanye kukan yana kallon Sanda wanda yake kallon shi cikin tausayi.
"Babu kome ya yaron yake ka duba min shi"
Ta faÉ—a tare da juya mishi baya, yana kuka sosai, haka sanda ya fita daga dakin, shima idanun shi yana cika da kwalla, sau daya ake aikata kuskure amma sai ka kai sau dubu kana danasani mara amfani.Yau ga abinda ya nusar dashi ya faru karka zama mara adalci a rayuwarka domin goben ka zata maka rashin adalci.
   Koda ya koma gida ya samu tayiwa jinjirin wanka tass, sannan ta kuma yanke cibiyar da ba a yanke ba. Ta binne shi sannan ta nad'e shi cikin farin mayafi, kallon jinjirin take tana mamakin yadda bakin jinjirin ya bayyana tun bai sha iskar duniya ba, dan haka ta dauko kasko ta fara gasa mishi cibi yana ihu da kuka. Kafin ta gama ta kuma kwantar dashi dan ya sha ruwa ainun.
   ---
Bude ido tayi tare da kallon dakin da take, kokarin tashi take taji alamar an saka mata abu a hannunta, kallon gurin tayi taga ƙarin ruwa ne. Da sauri ta bude bakinta zata yi magana.
 Wani farin dogon mutum ne ya shigo, cikin farin labcoat. Ya kalle ta yana murmushi.
"Sannun ya jikinki?"
"Da sauki" ta faÉ—a tare da juyar da kanta gefe
  Safar hannun ya saka tare da nufar kanta, zai duba ta tace mishi.
"Karka tab'a" jan kujeran yayi yana kallonta, kafin ya nutsu ta fara kokarin dubata.
"Kin haihu baki tsaya duba matsalarki ba, kika baro can din jini na zuba miki, me yasa kike haka?"
"Me yasa ba zan yi haka ba? Me yasa kowa ya guje ni? Kai ma ai sabida ina kawo tallar nono nan yasa"
"Zainab!" D'ago kai tayi tare da kallon shi.
"Har yanzun babu abinda ya sauya! Kuma ban ga laifin su dan sun gudu ba, sai dai akwai matukar ciwo abinda ya faru dake, kuma ba dukkan iyaye bane zasu fahimci girman kaddarar da ta."
"Me yasa ita ƙaddarar bata biyo ta kan kowa ba sai ni? Me yasa babu wanda ya gane akwai ƙaddara sai da ya faɗa min, idan har da gaske batu ne na kaddara jeka dawo da da ahalina da suka tserewa ƙaddara ta, idan kayi haka zan Fahimci girman abinda kake nufi da ƙaddara."
 "Kin jahilci ƙaddara amma zan barki nan da kwana uku idan kin ji sauki muje a dauko abinda kika haifa, ko ya mutu ne?"
Cikin wani irin bakin cikin tace mishi.
"Bai mutu ba,amma kuma ba zan dauke shi ba, ya zauna ya girbi kuskuren da uban shi yayi."
  "Me yasa baki da tausayi? Me yasa baki da hankali? Me yasa baki da imani, toh zamu je mu dauko shi."
  Cikin fushi ya fice daga dakin , ta fashe da kuka wanda take tun daga kasar zucuyarta. Tasan tunda ta ganta a cikin asibitin tabbas ta shigo garin Maradi ne, tunda dama a wani kauyen Maradi suke....
   **
Yau kwana biyar da haihuwar Yaron, amma baki daya kauyen an tsangwame su, musamman Sama'ila wanda shi ya fi kowa fuskarta matsa kai ko masalaci, ya je ba a sallah dashi, wannan dalilin yasa aka daina ganin shi a masallacin baki ɗaya.
   Shiru da ta daina ganin dan uwanta shine tazo duba shi, dake ko aika ne an hana yara mata, tana tafe tana jijjiga yaron, wanda nonon akuya ake bashi yake sha. Abin tausayi, yana ta kyankyara kuka, tana isa bukkar ta d'aga labulen wayam ta gani, cikin tsoro ta kuma shiga dakin Babu Sama'ila babu dalilin shi, sai wata yar tsohuwar fatar rago da yayi rubutu da harshen ajami da shi ya rubuta mata.
كي ØÙ‚ر مثني مك ل٠بذ أي ذم ا غرنني يثن بر غرا اني إكا قام Ø§Ù„ØØ±
Kuka ne ya kuma kwace mata, tana gani da sauri ta fitar dashi wa mijinta domin bata san me ya rubuta ba, kuma duk abinda ya rubuta ba zai wuce bankwana ba. Dan haka ta fita tana gudu ana kauce mata a hanya, koda ta isa gidan tana shiga ta mika mishi. Yana dubawa yaga sakon.
"Kash! Sama'ila me yasa baka da kirki? Me yasa baka da hankali kana tir" ya faÉ—a da karfi dan ya gama jin haushi kamar zai yi wani abu.
"Ina fama da matsalar Ardo ya sallame mu a garin. Kuma haka shine mafi alkhairi domin idan muka cigaba da kallon wannan yanayin zamu iya shiga tashin hankalin da yafi wannan abin kunyar, kuma wannan abin zai fi mu shiga tashin hankalin da yafi ba mu. Dan haka zamu wuce Maradi kawai."
"Wannan shine adalcin da zamu yi mishi."
  *_Toh gamu nan a wata tafiya! Me kuka gane_*
8/19/21, 12:41 PM - My Mtn Number: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
   '''Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haÉ—in kayan amare da na uwargida...🗣ï¸ðŸ—£ï¸Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃ðŸ»ðŸ’ƒðŸ»'''
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀Â
         Â
~The Journey of Destiny💔~
 Mai_Dambu
Littafi na D'aya...
Sadaukarwa ga
 Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
Akasin ƙaddara.
BABI NA BIYU
_Da alamu Jumma'a da zata yi kyau tun daga laraba ake gane ta, sai dai zaku yi hakuri sosai domin wannan tafiyar ba kamar sauran tafiyar bane bana ce yakai Kwarkwarah ba, amma ba mamaki zai iya kunnen doki da haka tafiya ce me matuƙar tsoho da bukatar hakuri Insha Allah zaku same Ni me cika alkawarin da na dauka naso na sayar da labarin amma kuma gashi nan dai mu karanta shi a kyauta! Idan Ubangiji yayi maka ni'ima ta wani gurin kai ma sai ka gwada taka azancin da fatan zaku amshi wannan lamari da girma is FREE BOOK_
Sab'a jaririn tayi a baya, tana me ce mishi da harshen fulatanci.
"Kayi hakuri! Bawan Allah ƙaddarar kace tazo a tsakanin zukatar mugayen mutanen karshen karni, shi yasa ka fuskanci tozartawa, Ya Allah ga Al Mamoon, ka azurta rayuwar shi ta farkin da ban zata ba, ka mishi ni'ima da ilimi, ka daukaka darajar shi Ya Allah ka bashi juriya da hakurin ƙaddarar shi.
Ya Allah ka rangwamta mishi tsangwama da hantara na Al'umma, Ubangiji ka sanyawa Al'umma soyayyar shi ta yadda ba zasu guje mishi ba, Ubangiji ka sa ya zama zakarar gwajin dafi Ya Allah ka raba shi da akasin ƙaddara." Ta faɗa tana kuka, sabida Allah bai bata haihuwa ba, sai take ganin kamar sun zo kan su ne da suka wofantar da Al Mamoon, dan haka ta gyara mishi goyon shi. Sannan suka fita da mijinta.
"Yanzun kin ga na tambayi Babayo ya bani shanuna ya hanani, sai wata karsana ce ya bani. Mu dauka mushiga gari idan yaso sai na sayar na nima mana haya" ya faÉ—a cikin sanyin murya.
"Toh babu kome nima tun d'azun na kama dabbobina, muje na sayar da su, dan nasan Hamma Sama'ila ya tafi da shanun mu"
Haka suka hada kayan su baki daya. Suka bar rugar duk da zaman amanar da aka yi bai hana a musu koran wulakancin ba, dan har wajen rugar aka bisu, dakyar suka sami keken shanun suka hau, tare da lullube fuskar su.
 Suna fitowa wata mota kiran honda ta shiga garin garin, da gudu. Har sai da suka juya tare da kallon motar, jaririn da yake hannun Kabo ya fashe da kuka. Har da shashakewa, haka tayi ta jijjiga shi har suka bar yankin rugar Ardo bako.
Suna shiga rugar Ardo bako, suka tsaya kallonta yayi tare cewa.
"Kika ce mun iso sama a farkon gari suke."
Lumshe idanunta tayi sakamakon rungume nonuwarta da tayi har suna wani irin cika da tsirta da ruwa.
"Yaron yana bukatar ki sosai"
Kallon shi tayi cikin kuka tace mishi.
"Da fatan ba zaka tab'a juya mana baya ba, kar na dauko shi kuma kace ba haka ba, babu da Uwa bani da Uba, duk sun tafi sabida zanen ƙaddara ta, don Allah karka juya min baya, kai ne Ubana kai ne Uwata don Allah karka juya min baya."
"Insha Allah ba zan juya miki baya ba." Ya fada tare da murmushi domin karfafa mata gwiwar ta, a tare suka fito daga motar domin yara sun yanyaye motar suna kallon kansu da ihu.
  "Laaa Abuh ce! Yaran suka fada tare da watsawa a gurin, a hankali take takawa, zuciyarta yana rawa, tsoro da tararradi ya zauna a fuskarta. Tana isa bukkar Sama'ila ta samu baya nan, juyawa tayi a kidime zata nufi gidan Kabo, wata dattijuwar mata tace mata.
"Ayya ita ƙaddara sau daya takan fada maka, amma zafinta sai ta shekara dubu tana bibiyar ka, da lokacin da kika haihu kin dauki abinki bakin ki alekun babu wanda zai kuma ganin ki sai tsananin rabo. A yanzun kuwa abu biyu suka haɗu a guri daya.
Tafiyar kaddara wacce baka iya tsayawa dole sai kayi, sai kuma akasin ƙaddara wacce idan ta same ka sai hakuri, ko minti talatin basu yi ba da barin garin nan sai wata rana." Dishi dishi, ta fara gani kafin ta ankara har ta zube a kasa, da gudu ya iso gare ta, bai tsaya ba wata dogon nazari ba ya dauke ta, suka bar garin baki daya. A mota yayi ta watsa mata ruwa bayan sun bar garin.
"Wayyo Allah na, wayyo Allah na wayyo na shiga uku, meye nayi ne haka? Meye na aikata da Ubangiji ya sab'a haduwar mu, meye yasa ban hakura na dauke shi ba, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji na tuba Ubangiji, ina son jinjirina ina kaunar jinjirina, ya Allah na tuba ya Allah na tuba, na shiga uku me yasa nayi haka? Me yasa bani da zuciya na imani, Dr Khalid bani da tausayi na rasa Yarona na barshi a hannun mujirimi, ya rabani da Uwata ya Rabani da mijin aurena, ya rabani da Ubana ya kuma rabani da Yarona Wayyo Allah Ubangiji ka tsinewa Sama'ila, Ubangiji ka hana shi jin dadin rayuwar shi."
Kuka yake tana buga kanta tare da dukar cinyarta, duk hakurin ka sai ka zubda kwalla haka har suka iso garin Maradi, gidan Mahaifiyarshi ya kaita dama a can ya kaita. Kallon su tayi cikin tausayi tace mata.
"Kiyi hakuri Sama'ila yayi laifi amma laifin shi bai kai naki muni ba, da yayi miki sai kiyi hakuri da shi ki dauki d'anki ki dawo."
    Dauko wata jaka tayi tare da mika mata.
"Wannan jakar Mero ta kawo ranar da abin ya faru, tace baffanki ya hana Sama'ila nisan zango dake ta hanyar da yayi amfani da ke, sai dai kabilar Bugaje basu cika zama ba suma, ba kamar Fulanin mu na yau da kullum ne ba, gashi dukiyar cikin shi sunce kiyi karatu kamar yadda kika so tunda har kinyi primary school da Secondry, since kiyi karatun da zaki amfani al'ummar Fulani, da wayar musu da kai. Domin sun tabbatar da zaki dawo, amma girman abin kunyar da ya faru dake ba zai iya sakawa su amshe ki ba, domin tunda suka ji labarin juna biyu gare ki, da shi Mijinki ya kai musu takardan sakin ki, shima yana cikin shi. Kiyi gudun abin kunya yasa suka tafi bawai basa kaunarki bane"
  Wani irin kuka ta kuma fashewa da shi, tana yi tana karawa, tare da k'amk'ame jikinta, meye yasa aka fidda al'adun da basu da tushe? Me yasa ita ƙaddara bata zab'i kowa ba sai ita? Ji take kamar an cinnawa zuciyarta wuta yake ciki. Kuka take tana kuma wa, har yamma lokacin da aka juye ruwan wankan ta nonuwarta sun kuma cika da zubda ruwa.
 Haka ayi ta watsa mata ruwan idanunta a lumshe bata buɗe ba balle kayi tsammani bata jin zafin ruwan ne kuma tana ji har cikin ruhinta da gangan jikin ta.
  ***
Damagaram.
Anan suka fara yada zango, kuma sun ji dadin yanayin garin domin sun sayar da saniyar su, yar kudin ce, Sanda ya kama musu haya. Gidan da ya kama musu akwai mutane dayawa, musamman kabilu mabanbantar harsuna dabam dabam, yan kudin hannun su, dashi suka saka ledar tsakar daki, da kuma taburma, sai yar tukunyar da zasu amfani dashi, dan basu iya daukar wani shirgi ba, sabida fitar bata nutsuwa bace kuma ma basu san inda zasu fada ba.
Dan haka suka auno hatsi da zasu ci, dan ma sun shigo garin da yan dabbobin su. Ta watsa a tsakar gidan, bayan sun tambaya aka ce zasu iya saka kiwon su.
   Wani abinda ya Kum burge su da gidan akwai rijiya da wata tsohuwar turmi, dan haka ta nemi Izni gurin daya daga cikin matan gidan zata yi daka. Cikin kallon tsoro ta nuna mata inda turmin yake, ta wanke hatsin sannan ta zuba ta fara dakawa, ta surfe shi tass, sannan ta kuma wankewa har ya tsane ta koma ta dake shi sai da ya zama gari, lokacin Sanda ya shigo, da sauri ya amshi Jaririn bayanta.
"Kabo bana son haka, taya zaki zo kina daka da goyon dan luÉ—i a bayanki, idan tabaryan ya fado daga hannunki fa?"
"Kayi hakuri mai gida" ta faÉ—a cikin wani irin farin cikin, sabida yadda ya nuna kulawa kan Al Mamoon, yayi mata dad'i. Haka ta gama dakar tazo dakin ta same shi.
"Ki dama mana kunu mana tunda na samo mana madarar Rakumi shi yafi yawa a garin nan"Â Â "toh me gida,"
  Haka ta fito tana kallon yadda suke ta harkan gabansu.
"Iya isuhu kunyi bakin Bororoji ne?" Matar da aka kira Iyar isuhu tace.
"Eh wallahi, d'azun suka zo"
"Toh kuyi a hankali" matar ta faÉ—a dake tana saman katanga ne, jikin kabo ne yayi sanyi, ta koma daki.
"Maigida bari su gama nasu sabgar idan suka gama na fita nayi mana" dake shima yaji abinda aka fada, bai takura ba, haka suka zauna a dakin shiru, suna tarerayyar Almamoon.
   Sai da suka ji tsakar gidan shiru ya fito ya fara kokarin niman abinda zata hada wuta, sai da tafita ta sayi itaccen tazo ta haɗa musu wuta aka daura kunun nono. Bayan ya gama ta wanke jikin tukunyar ta itaccen.
Komawa daki tayi, suka zauna tare da shan abin su. Tana jijjiga yaron su.
      Hakuri yayi ta bata taɓa gaya mata abinda suke so, rayuwar Yaron shine kan gaba, dan haka ba zai yi kasa a gwiwa ba, Insha ALLAH sai yaron su ya taka muhimmiyar rawa a duniya...
   **
Duk inda take tsammanin ganin Sama'ila da Aminatu bata same su ba,haka ta dauki kudin tai ta bin ƙauyuka da wanda suke iyakar Nijar da Najeriya, haka tayi ta b'atar da kudin ta, ta lalace sosai, bata da aiki sai na kuka, idan ta zauna kuka da kaunar danta take, yau ma tun sassafe take shirin fita Dr Khalid ya hana a barta ta fita. Yana sane da jininta yana yawan hawa.
"Khalid me yasa ka hana Musa ya barni na fita?" Kallonta yayi sannan yace mata.
"Sabida ina son na kilace ki daga fita ko ina, so nake na kuma sabunta rokon ki akan na baya. Ina son aurenki, kuma ba wasa nake miki ba, wancan ranar da kika tawo har kika kwanta a kasar bishiya, ba dan Allah ya nufa zan tafi niman ko zan ganki ba me kika san zai faru dake? Don Allah ki taimaka min aurenki zanyi ba wani abu ba, idan muka zauna a inuwa daya Insha Allah Ubangiji zai kuma baki wani Yaron ki duba lamirina."
  Hawaye na zuba mata ta kura mishi ido, tun lokacin da suke shigowa gari da nono yake Bin ta yana Sonta amma take gaya mishi ita tana da wanda zata aura, zama tayi dab'as tare da fashewa da kuka. Ta rarrafa gaban shi tare da rike kafarshi.
"Don Allah karka manta ka tayani niman Yarona wallahi ina son shi"
.d'ago ta yayi tare da cewa.
"Insha Allah zan tayaki niman Yaronki Insha Allah."
Da wannan shawaran ya sami mahaifiyar shi, dake itama dattijuwar arziki ce mai kaunar Ƴaƴan wasu da nata, tace mishi.
"Allah ya tabbatar da alkhairi"
   Dan haka a cikin satin aka daura auren Zainab Hamza Bugaje, tare da Dr Khalid Agla, akan sadaki CF dubu arba'in da biyar.
   ***
A hankali zaman garin Damagaram yake niman fin karfin su, kasancewar yadda mutane suke tsoron su. Yasa suke dan fuskar halin rayuwa.
  "Iyar Mamoon, naga kin iya surfe da daka ko zaki mana mu biya ki"
"Kai Iyar isuhu zan yi mana," ta faÉ—a tare da amsar hatsin, kafin awa daya tayi musu daka cass, ta kuma daka musu. Ta tankad'e musu. Sannan ta basu,
    "Laaa. Iyar isuhu kiga yadda yayi laushi. Nima Iyar Mamoon zaki min" take mata suka shiga kawo mata surfe, matan maraya suna da banbanci da matan karkara, sabida matan karkara suna juran aiki, matan maraya kuwa basa iya juran ire iran wannan aikin.
    Shi yasa har makota kawo mata surfe suke, tare da bata aikin.
   Aminatu tana da mugun hakuri, ga dauke kai akan abubuwan da suke faruwa, idan yaron ta yana kuka zata goge shi. Du buga surfen su.
   ***
Tunda aka daura auren kawai yasan da auren ne amma babu wani abu na auren sai yawan rikicin da take mishi dan haka ya shawarci mahaifiyar shi zasu bar kasar. Bata ki ba tayi musu addu'a, dan haka ya haÉ—a mata kaya suka nufi Faransa,. Zuciyar ta cike da kewar D'anta. Ranar da zasu bar garin Maradi, kuka tayi ta yi tana kallon yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta ko iyayenta basu dame ta ba karma yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta.
  Wannan shine sanadin Kenan da ta bar garin Nijar.
***
2011/August/04
Idan kace rayuwa tabbas Aminatu da Sanda sun ganshi,kuma suna kan ganin shi. Duk wani abin da zasu yi domin amfanin Almamoon suna yi, kuma Alhamdulillahi.
Yaron ta taso babu tashin hankali, sai dai idan ka tsokane shine fa bai iya fada ba kamar kurma.
    Shi yasa yaran da suke gida daya dasu basa fada dashi sai dai idan an fi karfin su, shine zai shigar musu. A wannan yanayin har suka saka shi a makarantar boko, da arabiyya dan ma yana karatun Alqur'ani a gaban Baban shi Sanda yayi nisa.
  Almamoon Allah yayi mishi baiwar Ilimi, tun yana shekara biyar ya fara shiga musabaka, kuma yana lashewa, gashi da wani banzan hali shine karka nuna mishi ka damu dashi domin da wannan yanayin yake iya saka damuwa, idan kace kana son shi da abota, wayyo Allah..ka shiga uku domin zai ta baka wahala ne, yana share ka.
     Gashi da farin jini idan turawa yan yawon bude ido suka shiga makarantar su, har rige rigen daukar hoto ake dashi sabida bakin fatar shi, wanda idan ya shiga rana har wani kyali yake, idan ka cire kwayar idanun shi da hakoran shi sune fararre tass a jikin shi sai harshen shi ja, bayan nan babu wani abu da zaka ce fari ne a tare da shi..
Yanayin fatar shi ta janyo mishi soyayyar mutane, sai dai abu daya yake mugun bawa kowa haushi a tare shi a yanzun yana da shekara goma a duniya idan ya yab'a maka bakar magana sau ka rasa inda zaka saka kanka.
A yanzun haka yana tare da wasu yan ajin sune. Amadu Bukar sai Salihu Muhmuda jarabawar suke ta gama primary.
   "Mamoon don Allah taimaka min da amsar nan mana?" Inji Amadu Bukar, Banza yayi dashi. Can Salihu Muhmuda ya taba shi.
"Don Allah taimaka mana abokin mu"
"Ai kusan ni na kawo ku makaranta shi yasa zan baku satar amsa," ya faÉ—a mu....
8/19/21, 12:42 PM - My Mtn Number: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
   ```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haÉ—in kayan amare da na uwargida...🗣ï¸ðŸ—£ï¸Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃ðŸ»ðŸ’ƒðŸ»```
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀Â
         Â
~The Journey of Destiny💔~
 Mai_Dambu
Littafi na D'aya...
Sadaukarwa ga
 Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
_🙄 Daga farawa naga yadda kuke sakawa Dan baki namu ido fa😛🤠Wallahi ko hmm_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.