Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 7 of 31

"Dama ina fakewa ne da taimako ina Moruwa da Surar data Burgeni Sabida haka zo muji daÉ—in Juna na sallame ki kitafi abinki"
Yana faÉ—in hakan yayi tik haihuwar uwarshi yana shafa tumbin shi................Auta 09022260850

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*006*

Jikin sa'adah ya tsananta da rawa tunda take bata taɓa ganin Namiji a irin wannan yanayin ba Rintse ido tayi tana karanta duk addu'ar data zo bakinta Jada baya take tana Rufe idanunta da ƙarfi sanin Haramun ne kallon tsiraicin wani, Sabida duk da duhun Ɗakin hakan bai hanata ta gano shi tsirara cikin yanayin rashin tufafi ba.
Faɗuwa tai adaidai bakin Ƙofa ai Bata Jira ba aguje ta miƙe tana Gudu kamar ranta ze Fita sabida akwai tazara a tsakanin Falon da harabar Gidan Cikin Ikon Allah da tsarewar sa tana fita daga falon Taga Gate Ɗin a buɗe mai gadin nayin sallah ajiyar zuciya taja ta Zura aguje tana Gudu har takalminta ta yar Ummi data ga Gilmawar sa'adah Da gudu itama tabi bayanta Suna ƴar tsere wanda Ummi da ƙyar ta cimmata Ta kamata Se kawai suka faɗi ƙasa Tum sun Jima cikin Yanayin Hutu kafin Su Tashi zaune amman fa still Jikin sa'adatu rawa yake Ummi ta tsareta da Ido tana kallonta.
"Ummi ashe Mutumin nan É—an iska ne tsirara haihuwar Uwarshi yayi fa sabida naje neman taimako Ummi Allah ne ya tsare Mini Mutuncina"
Ummi ta Ƙunduma uwar ashar! tana cewa.
"Lallai Allah ya rufa mai asiri bani ya kira ba dase na datse masa Cilla wallahi dama haka suke tsinannu su fake da Guzuma su harbi karsana Allah yay gaggawar Tona masa asiri"
Se kuma ta miƙe sa'adah ta bita da kallo "Ina zaki?" tace mata Ummi tace "Zuwa zanyi Ya biyamu Kuɗin Motar mu kuma na tozarta shi" Sa'adatu tabi Ummi da kallo wani bin intai abu kamar mai Ƙwanƙwamai tai ƙasa da Murya sosai "Allah ya baki haƙuri ban faɗa dan Ki jamana masifa ba Shige Mu tafi Gida" ta kama hannun Ummi wadda har suka je gida Zage zage da tsinuwa take yi ga wannan Mutumin ga tarin takaicin ɓatar da ɗari huɗun da sukai a banza babu Biyan buƙata.

Sallah Ummi tayi Ita kuma sa'ada ta zauna tana Gogewa Hajiya Jikinta sabida zazzaɓin daya rufe mata Jikinta.
Ummi ta idar tazo Kusa da Sa'adah wadda ta zurfafa acikin Tunanin Neman kuÉ—in maganin Hajiya.

"Ummi kin san me?" cewar sa'adah Ummi tace "Ina ko zan san me Nida ba akuya ba" saadatu tai murmushi halin ummi se ita "Kawai Hajiya ce take bani tausayi" Ummi tace "Bake kaɗai ba naki ne yafi nawa Fitowa Fili amman a zuci kamar na fiki dan na gama yanke shawarar bada Jikina dan Hajiya ta sami lafiya tunda mazan sun zama Mayu" Buge mata baki sa'adah tayi "Karki Kuskura Ummi wannan shine abu mafi Muni da zaki sema Hajiya ta Mutu Kuma kin riga kin yada Ƙimarki Mu cigaba da addu'a dama duniya kurkukun Mumini ce"

Ummi hawaye ta soma tana cewa.
"Ina tuna yadda Hajiya kafin ta soma ciwo take yi mana hidima Ki duba koda sallah Mune abin kallo tunda mahaifinmu ya rasu Hajiya bata taɓa bari Munyi Kukan rashin saba tana cewa Mu amana ne a wajanta bata da kowa se Mu amman yau Mun kasa sai mata maganin Dubu ashirin" Sa'adah tai Murmushi mai ciwo.
"Haka Allah yaso Haka Allah yaga dama Wannan ma dan ya gwada imanin mune amman Nina fiki damuwa Ummi Ina kukan gazawa ta ga ciwon hajiya to ya zamuyi Allah ya bawa Hajiya Æ´aÆ´a maza amman dasu gwara babu Ki duba fa kamar ba ita ta haife suba"
Ummi tace.
"Ni share babin suma nake yi wallahi Gobe ma fita zamu yi da wuri Muga abin da Allah ze mana dan Allah kima daina batun waÉ—ancan marasa amfanin"

Daga tsakar Gida suka Jiyo Muryar Umma da Jamila Umma tana tuhumar Jamila daga Ina take tun safe ta fita bata dawo ba se yanzu Jamilar ce take cewa Umma.
"Fita nai don na ciko Cikina da abinci Na gaji da zaman yunwa ko anyi Girkin ma bama Ƙoshi Ke Umman nan kowace mace tana sana'a amman ban da ke Duk maƙotan ma Kinbi Kin ɓata dasu sabida faɗan ki In ke kin Jure Yunwa nikam bazan iya ba"

Umma ta É—aga Murya.
"Jamila daga gidan uban wa kike Ba tambayata yunwarki ba Tambayarki nake daga ina kike tun safe kin saka ƙafa Kinbar Gidannan se yanzu zaki shigo mini Gida so Kike ki jamana abin faɗa maƙiya su mana dariya"

"Kai umma kai umma abin fa sirrine Kinga dai ga wannan nasan baki ci abinci ba Ƙila tunda Baffa bai Shigo ba amman karki sake ki bawa cima zaunan can waɗanda basa cas basa as niko kasuwancin kai da kai na soma mai tarin riba"

Umma ta soma Murmushi kasancewar ta mace mai bala'in son abin duniyar tsiya da kwaayi.
"To jamila duk dai abin da zaki kada ki kuma kaiwa dare"
Zubaida ce ta fito a fusace tana Cewa jamila "Da wa kike naji kina maganar cima zaune to in ma damu kike Mu dai Alhamdulillahi Tunda bama bin maza" Umma seta hau salati tana tafa hannu "Zubaida sharri zaki wa jamila maƙota suji To Ta Allah ba taki ba Kasuwanci ta fara kema In zaki cire girman kai ki fita ki nemi kuɗi to dan na gaji Kuba aure ba kuba sana'a ba inji da kaina mana"

Zubaida tace "Lallai Umma sabida jamila ta baki Kuɗi yau ni kike gayawa haka to a makkan dazan biya Miki idan nai Kuɗi" Dariya jamila tayi "a haka zaki ƙare buri ne ze kashe ki Ina kika ga kuɗin zuwa makan kai sarki Kullum kina ɗaki riƙe da waya mai kyauro Buri da ƙarya sun cika rayuwarki kina geto area amman Fake life ya cika Miki Kanki wadda in za'a ƙureki ba lallai Ki iya karanta ABCD zuwa Z ba"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.