Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 21 of 31
Saadah na tafiya tana tunani haka ta Nufi sashin Anwar tana ƙoƙarin shiga taga Giftawar wani ya fito daga Falon Tana jiyo sautin Muryar Shi yana cewa.
"Khalid ka dawo mana Mu gama kallon" wanda take tunanin wanda ya fita É—inne Khalid.
Da Murmushi a saman Fuskarshi ta same shi a zaune a ƙasan carpet sallamar tace tasa yaɗan Sauya Fuska zuwa yadda take a Kullum wato a ɗaure.
Ta aje masa Flask É—in zata tashi yace mata.
"ÆŠan bani Cup a dining mana"
A ranta tace ya cika Saka aiki sai ta Miƙe ta ɗauko masa.
"Zuba min"
Da alamun shi bai ma Lura da sauya Flask ÆŠin ba.
Ta zuba mai ta miƙa masa.
Tea É—in yana turiri ya É—auka zai kai Cikin bakinsa Da sauri ta sanya hannu ta ture Cup ÆŠin wanda ruwan zafin bai sauka a ko ina ba sai a saman Fatar hannun Anwar...........
*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*
*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*
*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*
_A WANI ÆANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ÆANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*
*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*
*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO
*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
​*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
    Â
     *NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
           *16*
Ji tayi kamar Ruwan zafin a nata hannun ya sauka sabida haka sai ta saki ƴar ƙaramar ƙara tana Rintse idanunta, Da sauri takai hannunta saman Nashi hannun tana Murzawa wanda hakan Yayi daidai da sanda Fatar Hannun nashi ta Kwaye baki ɗaya wajan yayi wani irin ja naman wajan har wani farin ruwa ya tara.
Toshe bakinta tayi da hannunta tana zaro idanunta waje gaba ɗaya Jikinta rawa yake hankalinta yayi matiƙar tashi.
"Dan Allah kayi haƙuri"
Ta faÉ—a Muryarta tana wani irin Rawa hawaye na bin saman fuskarta.
"Ya isa tashi kije"
Ya faɗa a hankali kanshi yana sunkuye sai faman taune ƙasan laɓen shi yake da alamun zafin na ratsa shi dan dai kawai namijin duniya ne shiyasa ya daure amman in da mace ce babu abin da zai hana ta saka Ihu.
"Dan Allah kayi haƙuri"
Ta kuma faÉ—a tana share hawayenta gaba É—aya tsigar Jikinta tashi take.
"Jeki abin ki"
Ya kuma faÉ—a, Lokacin ya É—ago idanunshi wanda yayi ja kamar zeyi aman wuta tsoro ne ya kuma kama zuciyar Saadatu.
Sai ta matsa can nesa dashi tana Leƙensa.
A hankali ya tashi yana yarfe hannun ya shiga Bedroom É—insa Minti Kusan Goma ya fito sanye da wasu kayan wannan Karon Farin yadi ne mai shara shara ba Hula akan shi sai Makullin Mota.
Bai ce da ita komai ba ya ratse ta gefenta ya wuce sai tashin Ƙamshin mayen turaren shi na Tom ford Oud wood daya bar mata acikin hancinta.
Shi kam fita yayi zuwa Wajan Motar shi ya shiga da hannu ɗaya yaja kanshi zuwa wani ƙaramin Clinic Domin ayi masa dress ɗin hannun nashi sabida kawai dauriya yake amman ya Ƙonu iya ƙonuwa sai dai ko kaɗan bai ga laifin ta ba, sai ma mamakin shi daya ƙaru wanda ya zurfafa acikinsa mai yasa zata kare shi ai da ta bari yasha tea ɗin da gaske ya gane An sauya Tea flask ɗin kawai ya nuna kamar bai gane bane, Yasan da Biyu ta tankwaɓe Shayin dan kar ya sha ne to mai ya ruwanta da Kare shi Mamakin abin da tai shine ya tsaya masa acikin zuciyar shi yasan komai dake faruwa acikin Gidansu kawai nuna wa yake bai san Komai ba Domin a zauna lafiya.
"You will have an hour's rest because of your body and symptoms of fever but I will give you an injection now"
Cewar Likitan bayan ya gama duba masa wajan daya ƙone ɗin.
Anwar dake zaune saman Kujerar dake facing likitan yaÉ—an Girgiza kanshi.
"Bani son allura Doctor dama bani jin daÉ—i kwanakin nan"
Ya faɗa a taƙaice.
Murmushi Likitan yayi.
"To amman dai ka É—an kwanta ka Huta tunda kaima ka zama yaro Gudun allura kake"
Ya faÉ—a yana Dariya Æ´ar kaÉ—an.
Bai yarda ya kwanta a clinic ɗinba bayan ya kammala komai sukai sallama da Likitan ya fito da ƙyar yake driving Haka ya ƙaraso Gida a daddafe yayi sallar azahar aikuwa zazzaɓi yace mai salamu alaikum a nan saman carpet ya kwanta abin tausayi ya cure Jikinsa waje ɗaya yana ta rawar sanyi dan ko bedroom ɗinshi bai iya kaiwa ba so yake ya kira Khalid ma yazo ya kira mai Likitan shi amman ina ya kasa.
Da wani irin farin ciki na cin nasara Mama take waya da Hajiya turai matar yayanta Alhaji jamilu.
Daga ɓangaren Turai ta ɗauki wayar tana dariya tare da kirari wa Mama.
"Kin ci gida kinfi ƙarfin matar Gida ƙanwata ta kaina yaya ake ciki?"
Mama tana dariya tace.
"Da saura Hajiya turai yau dai Allah yayi aure da marar kwabo, Husna ta sami wata yarinya mai aiki Jiya tazo to ina tunanin dutse yayi tunbuɓe da farar fata harya shagala, Ni kuma nai amfani da damata na shigar da Ƙoƙon barata"
Hajiya turai dan dariya har ƙwarewa tayi sabida jin Yadda Ƙiri Ƙiri Shafa'atu ta mayar da sunan ɗan Mijin nata dutse.
"Ki gayan yadda zan fahimta mana shafa kin bani maganar a rabe"
Mama ta gyara zama acikin Bedroom Ɗinta ƙafa ɗaya kan ɗaya gefenta yankakkiyar tufa ce take cinta ga sanyin Ac tana ji ajikinta.
"Husna ta ba tazo ba, To shine jiyan aka samo mata ƴar budurwa saboda taimako danni Abban su yana nan Kin san ina tare dashi Lokacina bai da yawa, To gaskiya yarinyar Tana da kyau dan bama zaka ce zatai aiki ba to Nafi zaton Wancan Dutsen son yarinyar yake koma dai meye bani da masaniyya dan in ba waccan matsiyaciyar baraka ba, Baya yarda da kowa agidannan sai ko ɗanta Amman abin mamaki shine jiya Yasa yarinyar ta dafa masa shayi yau ma haka tun Jiya Hanan tazo tana Kuka tana shaida Mini Nace tai Haƙuri zan ɗauki mataki, Na kama yarinyar ta fito daga sashin sa da bakinta tace Shine yace mata ta dafa masa shayi Jiya yau ma haka, Inda na yarda da ita nasan ba Munafuka bace shine data gayan jiya ma yace ta dafa masa Kinga banga na jiyan ba na yau na gani amma ta gaya Min sabida haka zanyi amfani da ita wajan Cimma Burina zanyi amfani da ita wajan ganin bayan ANWAR"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.