Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 30 of 31

Jamilu ya watsa mata kallon baki da wayo aranshi yana ayyana sonkai irin nata wato duk wannan Tashin hankalin akan Æ´arta take sabida Dukiya a fili yay dariya yace.
"Wannan Duk mai sauƙi ne Turomin Kuɗi masu yawa sabida wannan aikin dole sai da GUMBAR SUSA"
Babu wani tunani mama tai masa transper Kuɗi masu kauri sukai sallama ya tafi a ranar jamilu ya Nemo Gidansu saadah sabida akwai kwatancen Gidan ajikin kati sabida a ƙofar Gida za'a taru kafin a haɗu zuwa masallacin ɗaurin auren anan ya sami kwatance da komai.

Dariya yayi yana cewa.
"Nima wannan damar tawa ce ba za'a lalata auren sabida ya auri Æ´arki ba matsiyaciya kici Dukiya ke kaÉ—ai Ni ina miki wahala karkiga Cikinmu É—aya kowa yanzu kanshi ya sani Shafa Nima wannan dama ce gareni wadda zan kashe ANWAR da ita in yaso na kwashe Komai na cikin asusun kamfanin na gudu"
Yana faɗar haka yaja Motar shi yana dariya kai tsaye Gidansu saadah ya Nufa bai sha wahalar samun Baffa ba bayan sun gaisa babu wani Ɓoye Ɓoye Alhaji jamilu ya bayyana wa Baffa ƙudirinsa.
"Yaron nan Ya shigen hanci da Ƙudun dune ina son a matsayinka na wakilin yarinyar nan ka hanashi auren ta ranar ɗaurin aure Nasan wannan baƙin cikin zai sa shi ya haɗiyi zuciya ya Mutu saboda yana son yarinyar ance sosai sannan Kuma yana da ciwon zuciya ni kuma so nake naga bayan shi da wannan damar ga Miliyan Biyar cash inka cikan sauran zan baka Miliyan Goma kaga sha Biyar kenan"

Jikin baffa yahau rawa Yana kallon Alhaji jamilu tunda baffa yake Ko Dubu Ɗari biyar bai taɓa riƙewa tashi ta kanshi ba yau gashi ana masa tayin Miliyan sha biyar sai ya shiga Tunanin zama Miloniya inya sami waɗannan maƙudan Kuɗaɗe babu wata fargaba baffa ya amince suka ƙulla alƙwari ya amshi Kuɗinsa yayi Gida sai da ya adana Kuɗin sannan ya shiga Ɗakin Umma Lokacin ta rafka tagumi ta zubawa zubaida Ido wadda tun safe take zazzaɓi kuma duk akan damuwar wanda saadah zata aura ne wanda take masifar so ita Kuma umma tasan babu wata hanya da zata cusa ƴarta gare shi.

Zubaida na ganin baffa tabar É—akin zama yayi yana bawa Umma labarin Yadda sukai da Jamilu amman bai nuna mata ya amshi kuÉ—in ba.

BuÉ—a Umma ta saki tana cewa.
"Inusa ka amince dan Allah Ko bai baka kuÉ—i ba ni ama juya auren ya koma kan Zubaida kar Æ´arnan ta Mutu"
Baffa ya kalleta tare da cewa.
"To kamar yaya ba zubaida yake soba sannan mu bashi ita"
Umma tai Murmushin jin daɗi bata ɗauka zata sami Biyan buƙata farar ɗaya ba a hankali ta raɗawa baffa maganar sirri dariya sukai suka tafa kamar wasu yara.

Tofa Biki ya kankama kota ina shiri ake Daga ɓarin ango har na amarya.

Saadah tunda suka shiga Hidama bata tsayawa Cin abinci yau ɗaurin aure tunda ta tashi gabanta ke faɗuwa sai ta shiga gidan Aunty Murja tai kwanciyarta ƙarfe 11 na safe daidai tawagar ƴan ɗaurin aure ta fara sauka manyan Mutane daga sassa daban daban wasu jama'ar Abba wasu na Anwar Kafin kace me Ƙofar masallacin da za'ai ɗaurin aure ta shaƙe da ɗan adam.
Anwar da Khalid ankon shadda sukai mai kyau da tsada fara ƙar sun fito fes shaddar sai ɗaukar ido take yi Khalid ke jansu zuwa wajan ɗaurin auren wanda abokansu keta zubawa Khalid waya kowa ya hallara a wajan ba ango Anwar Kuwa wayar Aunty Murja yake Kira sabida a cikinta suke magana da saadah tunda aka shiga Hidimar Biki.
Koda ya kira saadah ta ɗauka Muryarta a dashe ya shiga tambayarta lafiya ce masa tai ba Komai ta kashe wayar sabida Ciwon da kanta ke mata baki a sake yabi wayar da kallo yana mamakin yadda ta kashe masa waya sai Kuma yayi Murmushi yana cewa yau zaki gane kuranki ƙaraso warsu wajan ɗaurin auren makiɗa da maroƙa suka baibaye su ga masu Hoto da Ƙyar ya kutsa kanshi Cikin masallacin zaman shi yay daidai da zuwan Baffa Kusa da Baffa Kuma Ƙanin mahaifin zubaida ne kasancewar ba ƴaƴan Baffa bane Su babansu ya rasu shine Baffa ya auri Umma tazo masa dasu amman shi baffa bai taɓa haihuwa ba.

Addu'a aka soma yi kafin Liman ya fara gabatar da waliyan Kowane ɓangare Za'a ɗaura auren Baffa ya fashe da kuka wanda Kukan nashi yaja hankalin Kowa na masallacin ya Dubi Malam da Abbah yace.

"Cikin mu É—aya da mahaifin saadatu Bata da kowa sai ni aduniyar nan amman yarinyar nan jiya har zagina tayi sabida nace sai ta auri ANWARU É—an albarka ta dinga aljanu tana zage zage har tana cewa in aka aura mata shi sai ta kashe kanta ta kashe shi dan bata son shi tunda yake zuwa wajanta Dole ce tasa take fita wajan shi"
Baffa ya kuma fashewa da wani kukan yana cewa.
"Tun asubah yau nake fama da ita akan ta kwantar da hankalinta Tunda ita ta kawo yaron nan tace tana so bamu mukai mata dole ba, amman taƙi daga ƙarshe Rijiya ta faɗa sabida haka ina baku haƙuri tare da fata da Roƙo agareku karku Ƙi don Allah zan Muku NA HUCE da zubaida ƴar matata ce yariyar arziƙi marainiya ce ga ƙanin mahaifinta a zaune in kun amince sai arufa asiri batare da kowa yasan bada waccan ƴar iskar aka ɗaura ba"
Abba Gumi ya sharce yasan Illar mata Musamman wadda tace bata sonka baze so Irin ƙaddarar shi ta kuma faruwa akan Tilon ɗanshi ba ya Juya yana kallon tarin mutanan da suka gayyato tabbas abin Kunya ne ace yarinyar taƙi aminta da auren ɗanshi Inda Allah yasa ma yadda Baffan ke magana ba kowane zaiji bayanin ba sai waɗanda Suke Kusa.

Malam ya kalli Baffa babu ta inda maganar shi tai Cikas dan babu wata alamar ƙarya a tare da shi.
"Alkairin Allah Muke Nema Liman a É—aura"
Ƙanin mahaifin zubaida ne ya amshi sadaki ba ɓata Lokaci aka ɗaura Auren Anwar sule Kurfi da Zubaida Salihi Ana shafawa Abba ya Dubi Ƙanin mahaifin Hanan tare da Fito da Kuɗi daga aljihunshi ya miƙawa malam ya kuma cewa ya Nema wa Anwar auren Hanan Ƴar matar shi a hannun ƙanin mahaifinta wanda yazo Ɗaurin aure wanda yana cikin waɗanda abba ya gayyata Jin sabon Ɗaurin aure a karo na biyu ya ƙara Saka mutane a Jimami.

Shaidu sun shaida É—aurin auren Anwar sule kurfi da Zubaida salihi sannan aka kuma É—aura wa da Maryam Muktar da Anwar sule kurfi

Lokacin Hayaniya ta kaure acikin masallacin kowa ya soma faɗin albarkacin bakin shi maganganu ne suka fara tashi a hankali khalid daya gama jin komai ya kama hannun Anwar sukai Mota wanda gaba ɗaya Anwar ɗin ya kasa gasgata komai gani yake kamar a mafarki lamarin ya faru mai yayi wa Saadah data zaɓi yi masa YANKAN ƘAUNA a ranar ɗaurin auren su hartasa a ƙaƙaba masa auren mata har biyu waɗanda basu da makama bare tushe a zuciyar shi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.