Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 24 of 31

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *18*

Tunda ta doso wajen shi yake binta da kallo ta ƙasan idanunshi wanda ba lallai itan ta gane irin kallon ƙurullar da yake yi mata ba.
A hankali ta ƙaraso gabanshi ta tsaya daga nesa dashi ta sunkuyar da kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
"Wuce muje"
Ya faɗa mata a taƙaice.
ÆŠago idanunta tayi tare da yin raurau da su kamar zatai kuka! kafin tai magana cikin sakarci kaÉ—an tace masa.
"Nifa ban gama shirya wa ba"
Tsira mata kaifin idanunshi yayi wanda yasa ta yi saurin Kauda kanta tana jin wata irin faÉ—uwar gaba.
Cikin ƙaramin sauti ya furta.
"Muje ko"
Ya faɗa lokacin daya juya domin fita daga falon bata da wani zaɓi face na bin bayan shi ko Kuɗin bata mayar wa da Husna ba haka zalika bata ɗauki kayanta ba, Bare tai wa Baba kande sallama.
Sai da ta ƙara da Gudu sannan ta cimmasa sabida saurine dashi ba ɗan kaɗan ba a bakin wata farar Mota ta tarar dashi sai da ta ƙaraso sannan ya shiga ɓangaren driver ya sa hannu ya buɗe mata kusa dashi sannu a hankali ta shiga cikin Motar ta zauna.

Ya kunna ya tashi Motar suka bar wajan a bakin gate ya danna Horn masu gadi suka BuÉ—e masa suna É—aga mai hannu ya fita daga harabar Gidan gaba É—aya saman kwalta ya cilla hancin Motar tashi.
Tafiya ce suke kamar ta Kurame yana sane daya zo layin yaÉ—an wuce da sauri tace.
"Ga layin namu fa"
YaÉ—an kalleta yana cewa.
"Nina É—auka Kurma ce ay"
Dariya ta saki kaÉ—an tana sa hannunta tana rufe fuskarta.
Cikin layin nasu ya shiga yana tafiya a hankali har yakai daidai inda ta Nuna masa ya kashe Motar ya É—an kalleta.

"Ki shiga gida to sai da safe"
Magana take son yi masa amman kwarjinin shi ya hana ta furta abin da take son gaya masan.

"Ko na rakaki?"
Ya faÉ—a yana É—age girar shi guda É—aya.
Sunkuyar da kanta tayi tare da kama Murfin Motar zata buÉ—e ta fita.
Da sauri ya kamo hannunta.
Itama da sauri ta ɓamɓare hannun nata daga Cikin nashi.
"Ashhh kin fama min Ƙunata"
Ya faÉ—a mata a hankali.

Da ɗan ɓacin rai ta juyo gareshi zata yi masa magana, Yay saurin hanata furta maganar ta hanyar Rungumeta ta baya yana zuba mata dukkan Nauyin shi Kokawa suka shiga yi acikin Motar hankalin Saadatu yayi Mugun tashi.

Sai da tayi da gaske sannan ta iya Rabashi da Jikinta sai faman Nishin azaba take Ranta a tsananin ɓace ta kalle shi da Manyan idanunta waɗanda suka Sauya launin su zuwa jajir.
"Dama haka halin ka yake? mai yasa kayi min haka daman dan ka lalata min rayuwata ka rabo ni da Gidan dana ke sa ran samun halak É—ina?"
Sai hawaye! shaaa suka soma ambaliya a saman fuskarta.

Dafe kanshi yayi yana Ƙoƙarin saita Nutsuwar shi a hankali ya zira Hannu Cikin Aljihunshi ya ciro kuɗi masu yawa wanda bai ma san adadin suba ya kama hannunta ya damƙa mata gaba ɗaya ya kasa magana.
Watso mai da KuÉ—in tayi Jikinsa.
"Allah ya kiyaye na amshi KuÉ—in ka ko zan rasa komai bazan iya amsar KuÉ—in kaba Kuma sai Allah ya saka Min abin da kayi Mini"
Daga haka ta fita daga cikin Motar tana wani irin Kuka mai tsuma rai da zuciya.

A guje ta faÉ—a Gidan ko sallama bata iya yiba

Da kuka ta shiga É—akin su Ummi na sallah Ummi tana idar da sallar ko addu'a bata tsaya yiba ta Juyo tana tambayar sa'adatu.
"Lafiya kika shigo da kuka! menene mai ya faru?"
Ummi ta faɗi maganar a firgice ganin yadda saadatu take Gursheƙen Kuka!

Baffa yana bakin dakalin Ƙofar Gida yana kallon sanda motar ta sauke saadatu har zuwa sanda saadatu ta fito daga cikin Motar Murje idanunshi yayi yana kuma Buɗesu tabbas saadatu ce ta fito daga Motar Jikin Baffa har tsuma yake wajan takewa saadatu baya zuwa Cikin Gidan daga tsakar Gida ya soma ƙwala mata kira.

"Saadatu! saadatu!! fito nan Munafukar Allah, yau Allah ya tona miki asiri dama na jima ina zargin ki yau dai Abin Ɓoye ya fito Fili"

Saadatu daga cikin É—aki ta Matse Ummi jikinta sai rawa yake tana tsiyayar hawaye!
Ummi ta ɗago tana kallon Yadda saadatu take kuka! adaidai nan Baffa ya ƙaraso gaban Ƙofar ɗakin yana Bugawa da ƙarfi yana kuma nanata Kiran sunan saadatu.

"Idan baki Fito waje ba zan tona Miki asiri a cikin unguwa kowa yaji"
Da sauri Ummi ta kama hannun saadatu suka fito tsakar Gidan.

Suka zube a gaban Baffa.

"Dama ni na jima ina zarginku to yau na ga komai da idanuna saadatu ashe ba wanke wanke da shara kika jeba ashe yawon iskanci kika je uban waye ya sauke ki a mota?"
Ya faɗa cikin ƙaraji.

Wanda faÉ—in maganar tashi tayi daidai da sanda Abbati ya shigo gidan Umma dasu Jamila kuma suka fito daga cikin É—aki.

Yowa kanta baffa yayi kamar zai daketa yana kuma tambayarta.
Toshe bakinta tayi tana wani irin kuka!
"Ba magana nake Miki ba uban waye ya sauke ki a mota? wato mu zaku mai da marasa tunani Kin tafi wajan namiji ya kwana dake, Shine zaki fake da tafiya wajan aiki"
Kuka saadah take sosai a wannan karon.
"Wallahi Allah Baffa Babu wani Iskanci dana je É—an gidan ne yace na dawo Gida na cigaba da Kula da Hajiya wallahi Iya gaskiyata kenan Kuma shine ya kawo ni har nan"
Baffa yayi wata irin dariya.
"Bayan ya gama lalata dake Ko? babu wanda zaku rainawa hankali kawai kawaliya ce tai Miki Hanya kika je kikai kwana biyu kika dawo Gida To bari Kiji ba agidana wannan abun Kunyar ba wallahi bazan É—auka ba sabida haka tun wuri Ku haÉ—a ina ku ina ku Kubar Min gidana danni ba zakuja Min zagi a cikin Unguwa ba"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.