Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 19 of 31
Kafin ta hankaÉ—eta da sauri Sa'adah ta takure a bango tana raba idanunta Yi yayi kamar bai ga abin da Hanan É—in tayi ba.
"I told you to come here, ko zan cinye kine kin wani tsare ni da ido....." sai Kuma yayi shuru Lokacin Hanan takai ga Bedroom É—inta.
Iya ko zan cinyeki ne ta gane da kin tsare ni da ido amman sauran bata fahimta ba.
A hankali take jan ƙafafunta zuwa wajan shi ga falon babu kowa.
Tana zuwa gaban shi Kwarjinin shi ya cika mata Ido zubewa tai jagwab ta zauna agaban shi tana sauke Numfashi.
"Kin iya dafa shayi"
Bai jira mai zata ce masa ba.
"Ki dafa ki kawo Min wannan ɓangaren da kika shigo ɗazu"
Daga hakan yabar falon da sauri.
Sabida yana matiƙar Buƙatar shayin Kuma yasan yanzu Inna tayi bacci bare yace ta dafa masa shi kam bai iya komai ba bare ya dafa da kanshi shiyasa ya zaɓi sabuwar mai aikin da bai san wani aikin take taka maimai agidan ba data dafa masa ganin da yayi kamar zatai tsafta.
Sa'adah tai tagumi Cike da tsoro Hajiya tana gargaɗinsu Da kada su sake su Keɓanta da Namijin daba muharramin suba a duk inda suke su kare Mutuncin su.
Tun kafin Allah ya jarabci Hajiya da lalura take gaya Musu hakan Gaba ɗaya Gidan sunyi bacci kawai sai ta kama hanya tayi ɓangarensa dan bata da Ƙima.
To kuma in bata kai masa ba hakan zai zama laifi dan daga gani Yana da muhimmanci acikin Gidan.
Ajiyar zuciya ta saki domin ko hanyar Kitchen É—in ma bata sani ba.
Sai kawai ta tashi ta Nufi ɓangaren su alwala tayi tai kwanciyarta sai dai Ƙirjinta cike yake da tsoron abin da zaije ya dawo.
"Sa'adatu ki tashi kici abinci naga kin ɓata Lokaci wajan Hajiya Husna"
Da ƙaramin sauti tace.
"Baba na ƙoshi"
Tsaki taÉ—an ja wanda yasa Baba kande tace mata.
"Sai haƙuri Sa'adatu amman kika kwantar dakai zaki ci arziƙi"
Sai ta tashi zaune.
"Baba kande bama wannan ba, Wanine yace wai na dafa masa shayi nakai masa ɓangaren shi Ni bamma sanshi bafa Kuma dare yayi kina kallon ɓangaren babu kowa"
Baba kande tace.
"Waye kar dai Alhaji Ƙarami ne?"
Taɓe baki Sa'adah tayi.
"Wani dai mai faÉ—an tsiya mai ido kamar na Mayu"
Dariya Baba kande tayi.
"Ki rufawa kanki asiri Ki kai shayin nan Alhaji ƙarami ne lallai Yarinya kinzo Gidannan da ƙafar dama Tunda nake ko ruwa bai taɓa cewa na bashi ba Sabida haka maza tashi Muje na Rakaki Kitchen Ki dafa ki miƙa masa Ina wa Muhammad Anwar kyakykyawan zato ba zaki same shi daga cikin lalatattun maza ba In sha Allah yadda kika kai lafiya haka zaki dawo"
Badan taso ba sai dan bata son yiwa baba kande Musu ne.
Taja hijabi ta ɗora saman kayanta tana data sanin Gayawa baba kande maganar suka tafi zuwa babban Kitchen Ɗin Gidan wanda faɗin tsaruwar shima ɓata bakine Wasu Irin sinadaren haɗin shayine daga saudi ake kawosu baba kande ta nuna mata tana tsaye A kan sa'adah ta kammala haɗa shayin wanda dan tsananin Ƙamshi da kayan haɗi har kauri yake da mazarƙwaila aka dafa da zuma bada suga ba ta Juye a wani Dogon Kofi mai ƙananun Ƴaƴa ta ɗora a tray Baba kande ta Nuna mata Part Ɗin Anwar ta Nufi kai masa ciki sai dai Duk Notikan Jikinta sun saki sabida fargaba.........*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*
*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*
*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*
_A WANI ÆANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ÆANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCIÂ MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*
*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*
*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO
*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
​*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*15*
Jikinta a matiƙar sanyaye wanda yayi kama da wanda aka tsoma ta acikin ƙanƙara haka ta buɗe Ƙofar falon nashi ta shiga, wawiyar ajiyar zuciya ta saki Lokacin data ƙarasa shiga Cikin Falon Sanyi ne da ƙamshi suka cika ta, Kamar mai tsoron wani abun haka tai saurin aje tray ɗin hannunta tana Ƙoƙarin Juyawa domin ta koma sabida bata Ji alamun da Mutum cikin falon ba sai kawai taji sautin Muryar shi ta fita a hankali.
"Kawo mini shi nan matsoraciya kamar wani zai kamaki"
Gabanta ne yayi wata irin faɗuwa harda dafe Ƙirji tayi kafin ta ɗan zaro idanunta kaɗan wanda hakan yayi matiƙar yi mata kyau.
Ɗauka tayi ta ƙarasa gabanshi yana zaune ya miƙe ƙafafun shi ya ɗora ƙafar shi ɗaya akan ɗaya.
Ta ajiye a gaban shi.
"Zuba min ki miƙo min"
Ya faÉ—a a dake.
Sosa idanunta tayi tana hamma! kafin ta ɗauki Cup ta tsiyaya masa aciki Ta miƙa masa Tsirawa hannun shi ido tayi kaɗan, Abin ya birgeta ko ina gashi ne kwance hatta a saman yatsun shi.
Tana miƙa masa ta Miƙe zata tafi.
"Zauna har na gama sai ki tafi da kayan" ya faÉ—a yana Kurbar shayin batare daya tsaya firfita shi ba.
Wani irin haɗaɗɗan Ƙamshi da daɗi mai ratsa zuciya ne ya shiga Kwanyar shi ya Lumshe ido yana kurɓar shayin cike da mamaki dama ance yawanci ƴaƴan da suka taso Cikin rashin wadata sunfi Ƙoƙarin iya komai saɓanin ƴaƴan da iyayensu keda hannu da shuni waɗanda Suna kwance ake Musu komai
Jingina kanta tayi da Jikin Kujera duk jinta take a takure ita gaskiya hakan ya zama takura a gareta sai dai bata da damar yi masa Musu Ya É—auki wajan Minti Goma sha biyar kafin ya sallameta tana tafe tana haÉ—a hanya tsoro fall zuciyarta sabida yadda Ko ina yayi tsit a gidan.
Tana aje kayan a kitchen ta Rufo Ƙofar part ɗin Maman ta nufi nasu Koda taje Baba kande tayi bacci Ƙwan ɗakin ta kashe ta kwanta ba jimawa bacci ya ɗebe ta cike da Wani irin yanayi a tare da ita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.