Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 15 of 31

"Allah sarki Yaya sai haƙuri fa da mahaifi karka fasa fita Office dan Allah"

Ya juyo yana mata Murmushi wanda ta jima bata gani a saman kyakykyawar fuskar shiba.

"Hajiya shafa'atu kin taɓa ganin ɗa yayi fushi da ubanshi Akan me zanyi Fushi da dukiyata bayan ni ake tattalawa"
Ya faÉ—a mata yana zira idanun shi cikin nata ya É—age mata girar shi Guda kafin yabar mata falon Cikin tafiyar shi ta Jaruman maza

Zaman dirshan tayi tana yarfe zufa da ƙyar ta saita kanta ta nufi part Ɗin Abba kuma tana tunanin maganar shi mai kama da harshen damo.

Tana kuma zama a falon saƙon haihuwar Husna ya ziyarce ta wanda Mijin Husnar ya sanar da ita umarni ta bashi akan ya sama wa Husna ticket ɗin Kano ya amsa yana kashe wayar ƴan uwa ta shiga kira tana sanar Musu Husna ta samu baby boy kafin a hankali ta Kira Hadiza mai kawo musu ƴan aiki ta ce mata tana son yarinya Budurwa wadda zata dinga Kularwa da Husna jaririnta da sauran Hidimar Mai jego daga haka sukai sallama akan Hadiza zata kawo mata wannan Haihuwar ita ta mantar da Mama tunanin maganganun Anwar wanda tuni Gida ya ruɗe da shirin zuwan mai jego Tun kafin ma ta diro Gidan ƴan uwa suka soma zuwa da ƙawayen mama sabida harka in aka ce maka ta mai shi ce to ko ba dan Allah ba sai anzo.

Da matiƙar farin ciki Hadiza ta shirya zuwa gidansu sa'adah sabida daman tunda suka rabu take Nanata tausayin yaran acikin zuciyarta to yau dai Allah ya nufa Gidan Alhaji Sule Kurfi suna neman mai aiki zata gwada kai wannan yarinya ko Allah yasa a dace.

Da wajan la'asar hadiza ta fito daga gidanta ta hau mota zuwa Gidansu sa'a wanda yau suka tashi da farin cikin Mijin Aunty Murja ya sai wa Hajiya magani sabida haka sai suka kasance cikin walwala da farin ciki a wannan rana duk da tarin habaici da Umma take yi Musu amman su hakan bai dame suba.

Ana yin la'asar sa'adatu ta fito da wanki tana yi a bakin Rijiya ta sunkuya tana saɓe kayan taji Muryar Hadiza tana sallama a tsakar Gidan nasu.......

*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*12*

Da murmushi a saman fuskar sa'adatu take amsa sallamar Hadiza Bayan ta tsame hannunta daga cikin ruwan wankin.
"Lahh Baba Hadiza ce a gidan namu? sannu da zuwa" ta faÉ—a tana Dariya Hadiza taja kujerar gaban Sa'adah tana cewa.
"Nice Sa'adatu yaya gida da Jikin Tsohuwar taku?" Sa'adah tace "Alhamdulillahi Hajiya jikin nata da sauƙi Mu shiga daga ciki"
Hadiza ta miƙe suka ƙarasa ɗakin su Sa'adah Ummi tana bawa Hajiya abinci Tana ganin Hadiza ta faɗaɗa Far'a tana gaisheta Ruwa Sa'adah ta miƙowa Hadiza ta fita da sauri ta ƙarasa wankin ta dawo Lokacin Ummi da Hadiza suna ta hira wadda rabi akan yanayin ciwon Hajiya ne Sa'adatu ta zauna bata ce komai ba tana ta murmushi dama ita bata da yawan surutu ummi ta fita magana.
"Ƴata wajan kifa nazo,Dama akan maganar aikin da muka aje ce wadda nace idan na samu zan gaya miki"

Sa'adatu ta gyara zama tana sauraron Hadiza.
"To An samu anan gaban ku Layin Muhalli Gidan Alhaji Sule Kurfi shahararran É—an kasuwar nan Æ´ar sace ta haihu uwar ke son wadda zata ke taimakon mai jegon wajan raino da sauran hidindimu"

Sa'adatu tace "To Alhamdulillahi aikuwa nagode Yanzu zamu je ko sai Gobe?" hadiza ta gyara zamanta tana cewa "Ai da yake na kwana ne yanzu zaki haɗa kayanki Mu tafi gudun kar a kawo masu wata" Jin aikin kwana yasa sa'adatu ta sauya yanayin Fuskarta nan da nan ta ɗaure Fuskarta "Ni dai bana son aikin kwana Baba Hadiza inna tafi Waze dinga kula da Hajiya Ummi abubuwan zasu yi mata yawa bayan haka ma ban taɓa Nisa dasu ba tun da na taso" Hadiza tai Murmushi tare da cewa "Yaro yarone Ko baki tare dasu ai kina da abin da zai riƙe su wannan aikin da zaki yi zai taimaki mahaifiyar ki dan ina miki kwaɗayin zakkah da sauran alkairai Kuma bama jimawa zaki ba ina ga daga ta gama wanka koma kafin Lokacin kin gama fa sai dai a ƙara samar Miki wani sannan kuna kusa daga kin ji kina son gida zaki tambayi Hajiya ki zo damma gidan akwai jami'an tsaro amman ni zan mata bayanin Komai da Komai"
Ummi ita ma duk jikinta yayi sanyi amman sai ta daure dan ta ƙarawa sa'adah ƙarfin gwiwa "Dan Allah Sa'adatu kije ko dan ma kuɗin maganin Hajiya in danni ne karki damu Zan mata komai In sha Allah dama in da nice zan tafin ke zan ke tunani kodan Mutan gidannan amman ni kam karki damu Babu abin da zai gagare Ni Da yardar Ubangiji Allah yasa ki shiga a sa'a Allah yasa silar ƙarshen wahalar mu ne aikin naki dan wani abun in yazo ka ƙishi sai kaga ya zame maka alkairi"

Da wannan ƙarfin gwiwa da Ummi ta bawa sa'adah suka samu harta haɗa ƴan kayanta a Ledar Viva baƙa Aikuwa data fito daga ɗaki da Ledar kayan idanun nan nata sunyi jajir tasha Kuka ta Ƙoshi zuwa tayi gaban Hajiya ta rungume ta tana kuka Hajiyar ma hawaye take a fili sa'adatu take cewa.
"Wallahi zuciyata ciwo take Mini na rabuwa dake Hajiya amman yaya zanyi rayuwar tafiya take Lokaci Gudu yake bamu da mataimaki sai Allah kullum Jiya i yau, akan dole zan tafi na nemi Halak ɗina don na taimake ki bamu da kowa sai Allah Hajiya Allah ya baki lafiya Haƙiƙa zanyi kewarku"
Ummi ma duk yadda taso danne nata kukan Hakan bai samu ba domin sai ta fashe da kukan itama Rungume Hajiya sukai Hadiza sai barin ɗakin tayi tana Share hawaye haƙiƙa Ƴammatan ababan tausayi ne rayuwar su abar tausayawa ce shiyasa tunda taji halin da suke ciki ta kasa samun kwanciyar hankali har sai da ta ga Sa'adah ta sami aiki sannan hankalinta ya kwanta tasan koba Komai zata rage wasu abubuwan sosai da Kuɗin albashin nata.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.