Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 27 of 31
Sai da Aunty murja tai wa saadah jan ido sannan ta saka hijabi dan da cewa tayi babu inda zata Bishi.
"Meye haka saadah ni banga wani aibu a tare da bawan Allah'n nan ba yana da Nutsuwa kuma ba yaro bane daga gani"
Cewar Aunty Murja.
Ummi tai dariya kaÉ—an tana cewa.
"Ko shine ya kawo ki Jiya ne? ni a ƙofar Gida na ganshi yace Ina mami na kasa ganewa sai da ya kwatanta Min ke sannan na gano ki"
Hararar Ummi saadatu tayi tana cewa.
"To in ba shi ba waye ne ni ya wani takura ni tunda naje Gidansu ya hanani sukuni kinji wata yaudara wai aure na zeyi Kuma bai ce yana sona ba dama ana aure haka?"
Aunty Murja da Ummi dariya sukai kafin Aunty Murja tace mata.
"Taso kar yaga Mun zaunar dashi mayi maganar a gida ai ba zamu bar wannan damar ba"
Tashi sukai tare da tattare abubuwan su A motar ma sai da saadatu tai masa taurin kai don yace ta shigo gaba tace ita a baya zata zauna sai da taga ranshi yaɗan ɓaci sannan ta shiga aikuwa har suka je Gida bai yi mata magana ba Ko kallonta bai yiba yana dire su yabar wajan faɗa Aunty Murja ta rufe ta dashi tana cewa.
"Ke bada ban soyayya ba uban me wannan Mutumin zai dake ba ajin ki bane shine zaki watsi da damar Ki, Wannan fa wani LuÉ—ifi ne Allah yayi Miki Karki wasa da damarki saadah Ki gwada bashi dama baki san abin da Allah ya Æoye ba"
A bakin Ƙofar Gida suka rabu da Aunty Murja suka shiga gida ita kuma ta shiga nata Gidan.
Gidan nasu kamar babu kowa ɗaki suka buɗe suka shiga Hajiya duk ta ɓata Jikinta sabida haka basu zauna ba saida suka gyara Hajiya tas sannan Suka Shiga sabgar gabansu.
Saadah ta kasa gayawa Ummi abin da Anwar yayi mata ta dai ce mata shine ya kawo ta Jiya ya nemi ta daina aiki agidan su yau kuma yace mata auren ta zeyi yadda Ummi ta shiga Murna ne ya bawa saadatu mamaki.
Har dare saadah tana zuba ido ko Anwar zai dawo ya dubata amman shuru babu shi babu Ɗuriyar sa wasa wasa har tsayin kwanaki Uku babu Anwar Babu labarin sa suna samun abinci wajan Aunty Murja sannan Kamalu yana basu ɗari biyar Kullum Tunda ta dawo Gida Kamalun daya zo Taga yanayin sa kamar yaɗan sauko Har faɗa yay ma Abbati na dukan daya mata to wannan Rufin asirin ne yake riƙe dasu saboda har zuwa wannan kwanaki Anwar bai kuma zuwa wajanta ba Tun tana shiga ɗaki tai kuka har ma abin ya zame mata Jiki Dan wani Bin ko zama tai sai taita tunanin shi A yanzu ta yarda da soyayyar shi ta shiga zuciyarta tun ranar data ganshi taji Tana yi masa wata irin soyayya mai wuyar a fassarata.
Yau Kimanin kwanaki Biyar rabonta da Anwar Aunty Murja ce ta shigo Gidan da yamma sabida Aunty Murja bata shakkar Umma kai tsaye take Shigowa gidan.
Zama Aunty Murja tayi a kusa da Saadah taÉ—an kalleta kaÉ—an.
"Ni kam saadah kina fama da zazzaɓin dare ne?"
Saadah tai Murmushi mai ciwo tare da cewa.
"Mai kika gani wallahi lafiya ta ƙalau"
Ummi ta kalli Aunty Murja tana cewa.
"Nima na rasa me yake damun ta Kullum sai ta Æoye kanta taita Kuka nasha kamata tana Kuka to amman naga kamar bata son nasan damuwarta ne shiyasa nai mata shuru"
Saadah ƙasa tai da kanta bata Iya cewa komai ba saboda ita kaɗai tasan yadda take ji acikin zuciyarta game dashi.
"Saadah meke damun ki? sannan ina wanda ya É—auko mu daga asibiti ina maganar ku ta tsaya?"
Ƙirjin saadah ne yaɗan Buga kaɗan ta ɗago ta kalli Aunty Murja sai ga hawaye na zuba daga idanunta anan Aunty Murja ta gano bakin zaren Damuwar saadah Cikin Hikima Aunty Murja tace mata.
"Kodai tun daga ranar bai Kuma zuwa ba?" saadah ta É—aga mata kanta alamun "Ehh"
Aunty Murja tace "Shine kika rame haka lallai soyayyar taki da gaske ne Hajiya saadah an faɗa soyayya ai maganin ki yayi Ko nine haka zan Miki haba ai Nima kaina naga alamun ranshi ya ɓaci Ƙiri ƙiri Kika ƙi shiga motar shi fa Kuma Shine ya biya Miki Komai na asibiti dan da Mijina ne zai Biya zuwan shi yaje wajan likita ya biya Komai amman dan baki da Kirki agabanmu Kika dinga Nuna halin taurin kanki zuciya yayi ina ga baki da Number shi da se Ki masa waya"
Saadah ta É—an zaro ido tana cewa.
"Ni bani da Number shi Aunty Murja ina ganin fa dama Yaudarata zeyi Ina shi ina Aure na ÆŠan Gidan Alhaji Sule Kurfi ne fa naji Wadda ta kaini aiki gidan tana gaya Min To Aunty ina wannan mai KuÉ—in ina ni"
Ta faÉ—a cikin karaya.
Murmushi Aunty Murja tayi.
"Ni kuma gaskiya banga yanayin shi yayi kama da mayaudari ba, sabida daga gani ba yaro bane Kuma yana da Nutsuwa nafi zaton Fushi yayi ko wani uzirin kin san manya fa sai an Musu uziri Ko kuma Hidimar Gida"
Murmushi Saadah tai.
"Bashi da mata gaskiya ni dai ban san mai ya hana shi zuwan ba"
Aunty murja ta zaro ido.
"Bai da mata tabb Allah yasa rabonki ne wannan ai Kika aure shi zaki Shagwaɓarki son ranki dan naga yana da shekaru kawai dai bamai Kule Kule bane amman ai yaci ace yana da ƴaƴa ma Kita addu'a kuma ki kwantar da hankalinki Kinji"
Aunty murja ta dinga kwantar mata da hankalinta.
Har ta É—an sami Nutsuwa sallama sukai Aunty Murja ta koma Gida daran ranar Saadah labarin Anwar taita bawa Ummi wadda Ummin ta lura Anwar yayi wa Æ´ar uwarta Shigar sauri cikin zuciyarta.
*************
Yana tunanin anya bai shiga haƙƙin taba baya son takurawa Mutum sabida haka sai ya yanke shawarar rabuwa da ita Ko hakan zai sa ta samu Nutsuwa sabida haka koda yaje Gida ya tarar da Æacin ran Abba sosai na sallamar da yayiwa Alhaji jamilu haÆ™uri ya bawa Abba wanda ya Umarce shi akan lallai lallai ya mayar da Alhaji jamilu kan Kujerar shi.
Daga cikin Gida Duban Duniya Kande tayi wa Saadah bata ganta ba, sabida ko kaɗan bata kawo cewar Da Anwar suka Fita ba Ganin har dare yayi babu Saadah yasa ta sanar da Mama wadda mama ta kira Hadiza tace mata ba'aga Yarinyar data kawo ba Hadiza tace bata nan tana ƙauye amman In ta dawo zata Je Gidansu Yarinyar da haka Suka bar maganar sabida Hidimar Sunan Husna da suka Shiga Ita ta ɗauke hankalinsu daga Bibiyar Ina saadah tayi.
Kuɗin data bari ma Da kande ta kaiwa Husna cewa tayi ta Riƙe Kande taita Godiya Hanan kuwa data ji Saadah ta tafi har Rawar Murna tayi sabida dama bata ƙaunar yarinyar Ko kaɗan.
Anwar ya shiga sabgar gabanshi sai dai duk yadda yaso ya cire saadah a zuciyarshi abin ya faskara ko Rufe idanunshi yayi Hotonta yake gani Gaba É—aya jiyay ya shiga damuwar rashinta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.