Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 20 of 31

Anwar sai wajan 2 na dare bayan ya kammala nafilolin shi ya shiga Bedroom ya kwanta bacci washe gari ranar Sunday babu Office sabida gaba É—aya ma'aikatan Kurfi Tex basa fita ranar Sunday Hutu suke Baccin shi yasha dan sai wajan 12 ya farka shima Khalid ne ya shigo ya tashe shi daga baccin suka fito falo suna kallon Ball.

Baccin Saadatu rabi da rabine a ranar sabida rashin sabo ta saba kwanciyar ƙasan tabarma yau gata a lafiyayyen gadon daya sha katifa wai a haka ma gadon mai aikine ina ga kuma masu Gidan Da asubahi baba Kande ta tayar da saadatu akan ta tashi tayi sallah Miƙewa tayi sabida bata sallah tana fashi wanka tayi da ruwan ɗumi ta gyara Jikinta sosai Ta koma tayi kwanciyarta wajan ƙarfe Goma suka tashi daga ita har Baba kande Bayan sun gaisa Baba kande ta fita Ɓangaren su Mama ita kuma ta zauna gyara Musu ɗakin da wanke Musu bayin su da yake bata da saurin aiki sai wajan 11 ta kammala sannan ta fita ɓangaren maman ita ma tuno Wannan Budurwar ta jiya taji gabanta na faɗuwa addu'ar Neman tsari daga sharrin abin tsoro ta shiga yi taɗan sami Nutsuwa kaɗan kai tsaye ɗakin Husna ta Shiga suna zaune su Huɗu acikin ɗakin Husna tana bawa Bassam Nono sauran ukun kuma ko wacce ta miƙe ƙafa da waya a hannunta a ɗarare Saadatu ta ƙarasa gaban Husna ta rissuna har ƙasa Muryarta a sanyaye tace.
"Maman Bassam ina kwana?"
Da murmushi akan saman Fuskar Husna tace mata.
"Lafiya lau nanny Bassam, yaya kwanan baƙon waje amman Kin ɗan makara Bassam yayi Kashi da tumbuɗi Suna toilet suna jiranki"
Lokacin ɗaya daga cikin Ƴammatan taɗan Juyo tana kallon Saadah kafin tace.
"Ke baki ga mutane bane a wajan Husna wannan wace Irin mai aiki kika samu marar tarbiya ni bamma ga amfaninta ba tunda muna da washing machine a gidannan wankin me zata yi?"
Husna ta É—an haÉ—e ranta.
"Ni bana buƙatar Inji ya wanke Mini kayan yaro na sabida Masu kyau da tsada ne Zasu lalace wankin hannun Mutum yafi, Ke kuma Saadah baki ga mutane bane karki yarda a ƙara kawo Min ƙarar rashin gaisuwar Ki dan Jiya Aunty Hanan tace kin ture ta sanda zaki fita daga nan da yamma dan Allah Ki lura"
Saadatu tai ƙasa da kanta.
Tare da cewa.
"In sha Allahu, Suyi haƙuri hakan baze ƙara faruwa ba"
Sannan ta juya ta na gaishe dasu.
"Wow Saadatu ko ma sha Allah dama nice da kyanki Gaskiya kina da kyau" Cewar É—aya daga cikin Æ´ammatan wannan ta jiyan ce ta aje wayar hannunta tana kallon wadda ke yabon kyan saadah tsaki taja tare da cewa.
"Kedai anyi banza ina wani kyau anan aba kamar Nunar rana dallah tashi ki bani waje" da sauri Budurwar ta fita tana Gunguni Ita dai saadah tashi tayi tabar wajan ta shiga Toilet Ɗin sai da takai zuciyarta nesa wajan wanke kayan sabida harda panties ɗin Husna da suka ɗan ɓaci da Jini Aikuwa tana wankin tana tara Miyau acikin bakinta zuciyarta na wani Irin tashi haka ta kammala da ƙyar ta wanke toilet ɗin tass sannan ta fito Husna ta shiga wanka ita kuma ta soma gyara ɗakin Bassam ne ya ke Kuka sosai Husna ce ta fito Jikinta duk Kunfa tana wa Saadatu faɗan tabar mata yaro yana kuka "To naji Kince karna taɓa shine shiyasa ban yi Gigin taɓa shi ba amman Kiyi haƙuri" Ta ɗauki yaron tana Jijjigashi, Husna kuma ta koma wankan sai da ta fito sannan ta miƙa mata shi ta fita Kitchen ta shiga wajan Baba kande ta taimaka mata wajan kammala girkin tana Miƙa kayan zuwa dining.

Bayan sun kammala komai suka Ɗibi nasu zuwa ɓangarensu Suna Karyawa baba kande tana Yi mata nasihar kwantar da kai tare da yin biyayya ga ƴaƴan gidan baba kande ta ƙara da cewa.
"Duk ƴaƴan mama basu da matsala sosai su kawai Ka basu Girmansu in kana binsu zaka ji daɗin zama dasu, Mai bala'in matsala Hanan Ita ce babba a ƴaƴan Mama kuma ba ƴar Gidannan bace a golace Fiƙe ake gaya Miki kafi ƙaya tsini, Nima kaina bata ganin ƙimata amman Husna Khairat Ihsan Gaskiya ba sosai Suke da damuwa ba sabida haka Ki kula sosai Saadatu naga Kina da hankali"
Saadatu tai wa baba godiya anan suka cigaba da zama Baba kande ta kawo Musu ƙarshen zaman nasu ta hanyar kamo Musu tashar Arewa 24 Suna kalla Ga kuma sauran Ƙwai da farfesun da suka rage nan Saadah tana kallon Ragowar abin karin Hajiya da ummi suka Faɗo mata wanda Tun Jiya ta shiga damuwar rasa wayarta bare ta Kira Ummi taji yaya suka kwana ƙwalla ce ta taru a idanun saadah tashi tayi ta fita kai tsaye ɓangaren Sa ta nufa tana Tunanin Ko zata ga wayar tata Jin sautin muryoyi na tashi daga cikin falon nashi yasa ta Juya zata Koma wanda adaidai nan taji sautin Muryar shi.
"Wacece anan wajan?"
Tai tsuru Har zufa na karyo mata.
"Zonan ina zaki tafi bayan na kamaki"
Gabanta yana faɗuwa ta Juyo shi kuma lokacin har ya buɗe Ƙofar falon ya koma to tayaya ya gano ta bayan Ƙofar falon tana rufe.
Ta jima tana kokonton binsa tare dajin faɗuwar gaba kafin tai Shahadar Bin bayanshi wanda shi tuni har ya Koma cikin falon Taja ƙofar ta buɗe ta shiga a Lokacin taga wani farin namiji ya shiga Cikin wata Ƙofa da waya a kunnen shi tai saurin ɗauke idonta daga kallon shi tare da mayar da akalar Idanun nata zuwa ga Masifaffan Jiya wanda yake kwance a saman Doguwar Kujera Jikinshi sanye da Baƙar jallabiya.

"Ina kwana"
Ta faɗa bayan tai ƙasa da ƙwayar idanunta.
"Mai ya kawo ki nan ko yanzun ma ɓatan kai kika yi?"
Anwar ya jefa mata tambayar.
Girgiza kanta tayi.
"Tom ina jinki"
Tayi masa shuru.
"Okay ba zaki magana ba? Ko Abin break kika kawo Mini dama kin barni da kewar baƙin shayin ki"
Ta maimaita maganar a zuciyarta.

Da sauri ta Kuma girgiza kanta.
"Tab duk rashin maganata yau naga wadda ta fini yaya sunanki ma?"
A hankali ta furta.
"Sa'adatu"
Ya É—an sauke ajiyar zuciya yana Lumshe ido.
"Wow Nice name Mamina!"
Ita dai shuru tayi masa.
"Yanzu ina so ki kawo Min irin wannan shayin na jiya amman ki tafi da wancan Flask É—in sai ki zubo man aciki"
Ta maimaita hausar tashi a bakinta tabbas hausar bata ba kano bace hausar tai kama da katsinanci.
Ta tashi kamar wadda ƙwai ya fashe acikinta wurga ido take ko zata ga wayarta amman bata gani ba.

Ta gefen shi ta wuce ta fita daga falon Ba tare data bari wata maganar ta Kuma haÉ—a suba.

Tana Ƙoƙarin Fita daga part Ɗinshi suka ci karo da Mama wadda ita kuma lokacin ta fito ne daga wajan Abba wani irin kallo mama take aikawa da Saadah wanda kallon yasa saadatu ta saki Flask ɗin shayin dake hannunta Nan da nan Jikinta ya soma wata irin rawa kamar zata saka Ihu sabida kallon da mama take mata kallo ne mai kama da na Zargin wani abu
Murmushi mama tayi cikin ƙwarewa da barikanci.
"Saadah ko? kece mai aikin Husna da Hadiza ta kawo Mini jiya?"
Da sauri saadah tace.
"Ehh nice barka da rana"
Mama tayi Murmushi.
"Ɓatan kai kikai na ganki daga sashin Yaya?"
Zufa ce ta karyo mata da sauri tace.
"A,a Shine ya ce na dafo masa shayi dama jiya ne na dafa masa yau ma yace Mini na dafa masa"
Mama tai Ƙoƙari wajan Ɓoye mamakinta sai ta sauke ajiyar zuciya.
"Okay naga kamar Flask ɗin ma ya fashe zo Muje na baki ragowar na Babansa ki Miƙa masa Duk abin da yace Ki masa kiyi masa Kinji Shima yarona ne"
Kalmar ta bawa Saadatu mamaki ƙwarai na cewa duk abin da yace tai masa tayi masa wannan kalmar kamar akwai gyara a cikinta.
Bin bayan mama tayi zuwa Ɓangaren ɗakunanta wanda ta zaunar da Saadatu a falo, ita kuma ta shiga cikin ɗakin,Jim kaɗan ta fito tana Murmushi tare da Miƙawa Saadatu Sabon Flask.
"Karki ce masa nina baki Kice tsautsayi ne ya samu wancan ya fashe a hannunki Shine Kika zubo masa a wannan Ki tabbatar yasha Kinji Saadatu sa'ar mata duk abin da ya buƙaci yana son ci Ki zo ki faɗamin Ni zan baki Ki bashi a zummar Ke kika sarrafa masa Kinji"
Mama ta faÉ—a tana Murmushi Saadatu ma Murmushin tayi tare da cewa.
"To mama bari na kai masa"
Da farin ciki maɗaukaki a fuskar mama ta bi saadatu da kallo tana ayyana yau haƙona zai Cimma ruwa cikin sauƙi ashe wannan yarinyar Ni alkairi ta zame Mini.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.