Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 13 of 31
Cikin Nutsuwa da nuna ƙasƙanta kai wajan Allah maɗaukakin sarki Anwar yake addu'a cikin Sujjadar shi Ya jima Yana addu'ar kafin ya ɗago ya yi sallama Bayan kammala dukkan sallolin daya tara sakamakon rashin lafiyar data ɗan kwantar dashi har ta hana shi yabi sallar a kan Lokacin ta Istigfari ya dinga yi kafin ya soma karanto azkar daka ya kammala ya tashi ya Naɗe abin sallar yana mai zama saman One seater yana serching Channel dan ya kamo Mayyar tashi wato tashar kallon ƙwallon Ƙafa Tsaki yaja ganin basu fara wasan ba Khalid ne ya fito daga Bedroom Ɗin Anwar har Lokacin wayar shi na hannun shi Kuma gaba ɗaya hankalin shi yana kan wayar.
"Allah ya baka lafiya amman ni dai ina baka shawara wannan duk ba daidai bane ka zauna kana ɓatawa ƴaƴan Mutane Lokaci Danna san ba Budurwa ɗaya kake kulawa ba, This is not right, stop it"
Anwar ya faÉ—a mashi hakan, Khalid yayi Murmushi tare da cewa Anwar.
No matter how much I tell you how love is, you will not understand it sabida kai har yanzu baka san rayuwa yadda take ba ai soyayya dar ce nake gaya ma in mace ta gaya maka wata maganar ji zakai kana yawo a cikin gajimare dama zaka samu kai wuf da Hanan yadda take mai tar son ka malam ai da ka huta"
Tsaki Anwar yaja yaɗan taɓe baki Kamar baze yi magana ba can Kuma sai ya ce.
"She is not at all the type of woman I love, Sabida bana son siririyar mace In ma zan yi auren kenan, zan auro mace mai Ƙiba yadda nake Bani da jiki ɗinnan ta dinga tare Mini faɗa"
Ya faÉ—a yana Murmushi.
Khalid ya bishi da kallo Anwar bai da magana amman idan ya yanko maka wata maganar se ka cika da mamakin shi.
"To Mijin Æ´ar lukuta Allah ya ba ka"
ÆŠage gira yayi bai cewa Khalid komai ba yabar wajan Direct part ÆŠinsu ya nufa Ya nemi Guri a saman dining ya zauna Yana Æ™oÆ™arin haÉ—a Coffee Wayar shi ta hau Ringing Innah Ce sanar dashi tayi ta masa faten dankali Da sauri ya tashi yabar Coffee É—in yana ƘoÆ™arin Fita Mama ta fito daga Æangaren Bedroom É—inta da alamun Part ÆŠin Abba zata shiga sanin Ya dawo É—azu da yamma kano.
"A,a Yaya ina zaka kuma baka shafa coffee ba naga kamar shi ka haɗa?" cewar mama, ba tare daya kalli direction na wajan da take ba yace "Ehh na haɗa kuma inna tamin tayin fate" daga haka ya Nufi fita daga part Ɗin ta bishi da wani Mugun kallo tama kasa magana tai ƙwafa! ta nufi Part Ɗin Abbah.
Zaune ta tarar da Abba yana kallon Sunna tv a hankali ta ƙarasa wajan shi ta zauna a kusa dashi.
"Barka da zuwa Ranka ya daÉ—e yaya hanya?" Abba ya kamo hannunta wanda ya sha jan lalle yana murzawa.
"Hajiya shafa'atu Mowar mata yaya hidima da yarana da fatan na same ku lafiya amman wannan Ƙunshi yayi wa Farar fatar ki kyau" Ya faɗa still yana matsa hannun ta wanda yake a cikin nasa.
"Dan kai nayi Alhaji Allah dai ya barmu tare" ta faɗa tana kwanciya a saman kafaɗun sa wanda in ka kalle su sai kace matasa ne ƴan shekaru ƙalilan Cikin kwanto da iya kirsa tace.
"Nayi maka maganar zuwan Husna har yanzu baka bani amsa ba Ya kamata kace wani abu mana sabida ta shiga watan haihuwa ko yanzu aka ce mana ta haihu ba zamu yi Musu ba ta yaya zata haihu a dawa babu kowa nata"
Mama ta faÉ—a cikin Nutsuwa.
"Shafa'atu ba komai yasa kika ji nayi shuru ba ya kamata abar wannan yarinyar ta haihu a ɗakin Mijinta duka duka yaushe akai mata auren ma amman Mijinta ya kawon ƙararta na ƙazanta yafi sau Goma sabida haka kawo ta gida ma wata sangartar ce gaskiya abarta a ɗakin ta kawai"
Mama ta ɓata fuska.
"A,a nida nasa aka gyara É—akin dake kusa da nawa hatta kayan baby na siyi komai Dan Allah Alhaji karka hana zuwan nan Please"
Ta wani haɗe hannu waje ɗaya tana roƙon shi.
Yayi murmushi"wato rigimarki tana da yawa Shafa tunda kina son hakan Allah ya kawo ta lafiya" Yana faÉ—ar haka kuma ya É—auki wayar shi.
"Kazo ina son ganin ka inda hali ma kazo mini da shaidar dawo mini da kuÉ—aÉ—e na daka Fitar"
Daga haka ya katse wayar.
Mama ta wani marairai ce tana kallon Abba "Haba Alhaji Abin da kake wa Anwar Baya dace wa kamar ba mahaifin shiba, Nifa karka jamini zargi ace nike shiga tsakanin ka da ɗanka dama naga take taken matar Gidan can dan ɗazu ma da bai da lafiya dana je wallahi Khalid hanani yayi na ganshi yanzu ma kamar abin arziƙi yazo nan zai ci abinci Baraka tai Kiran shi ya fasa ya tafi can" mama a siyasance ta kawowa Abba ƙarar su Innah Murmushi Abbah yayi.
"Rabu da Shi dasu Baraka Kinji Ya riga ya saba dasu ne Kinsan ita ta yaye shi"
Mama bata so Abba yace haka ba se tai dariyar yaƙe ta kuma lanƙwasa kanta.
"Ina nemar wa É—ana afuwar ka dan Allah karka tuhume shi akan wannan KuÉ—i'
Abba ya kalleta "Idan ban tuhumi Muhammad ba Jamilu zan tuhuma wanda shi nake tare da shi tun kafin Muhammad yayi ƙwari?"
Mama taÉ—an sosa kai.
"Ni ba nufi na haka ba sabida bawai Yaya Jamilu dan yaya na bane Nina san baze taÉ“a cin amanar kaba Allah ya huci zuciyarka ai yaranne se Addu'a damma shi Anwar Komai nasa yana Æoyewa wasu kuwa da zaka ga In suka Æ™i yin auren suna aje matan banza a waje ai yawanci KuÉ—in su a wajan mata yake tafiya" ta faÉ—a tana Murmushi wanda ta faÉ—i hakanne Don ta Æ™ara jefawa Abba zargin yaron nashi aran shi Amman ba zaka taÉ“a gane da wace siga ta faÉ—i maganar ba sabida tsantsar Kirsar ta.
Adaidai nan Kuma Anwar ya shigo falon sabida Lokacin Abinci ma zeci yaga wayar Abba ya rufe ya tawo.
Ko zama Anwar bai kai dayi ba yaji Muryar Abbah.
"Ka dawo Mini da kuɗina daga nan zuwa gobe, Sabida ni ban yarda dakai ba Ƙila ma matan banza Kake bi ace shekararka Kusan arba'in a duniya amman bakai aure ba Duk sanda nai maka maganar aure kamar na haɗaka da ajalinka To Ni kuɗina bada ga kwance na same suba seda na tashi nai gogayya da mutane kala kala na tara su ta hanyar halak wallahi seka dawo Mini dasu Mutumin banza daga kai har Khalid Ɗin kunƙi Aure saboda Kunsa shashanci acikin ranku"
Innalillahi wa'innah Ilaihirraju'un itace kalmar da Anwar yake ta nanatawa dan yaji sassauci a zuciyar shi na maganganun da Abban shi ya gaya masa a wannan Lokacin kafin a hankali ya.........*YANKAN ƘAUNA…i littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.