Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 16 of 31

Rufo ƙofar sukai suka baro Hajiya dan Ummi zata raka sa'adah dan taga muhallin da za'a kai ƴar uwar tata Ɗakin Baffa suka shiga sabida yau bai fita ba wai baya jin daɗi yana fama da Mura sukai sallama ya amsa musu Ummi ce ta faɗi maganar.
"Baffa sa'adatu zata tafi Gidan aiki shine tazo yi maka sallama"
Sai Lokacin ya É—ago yana binsu da kallo.
"Ita bata da bakin magana sai ke tsagera to Allah raka taki Gona in kuma ta kwaso abin Kunya ta nemi wani Gidan ba nawa ba"
Ummi tai saurin cewa.
"Tunda tsanani da rashi da Buƙatar taimako bai saka ta zubda Ƙimarta ba In sha Allahu rabbi Neman halak alkairi ne a gareta"
Tana faÉ—a masa hakan taja hannun sa'adah suka bar É—akin suna ji yana zagin Ummi harda cewa sai tazama karuwa In sha Allahu su dai fita sukai dan Ko Umma ba suyi wa sallama ba domin Itama babu alkairi a harshenta.

Suna tafe suna Ƙus ƙus daga gani sirri suke ita da ummi Hadiza ta Juyo tana cewa.
"Dan hankalin ku ya kwanta Zan ranta wa sa'adatu dubu takwas Muje wancan shagon Ku sai wayoyin hannu Kona dubu uku da É—ari biyar biyar ne sai Ku sai layuka sai ku dinga waya ina ga hakan zaku fi samun kwanciyar hankali In yaso duk sanda Allah ya hore mata sai ta bani KuÉ—ina"
Godiya sukai mata aikuwa suka je shagon Sukai sai wayoyin waɗanda suke clean Tare da sim card suka saka harda katin naira ɗari ɗari bayan sun gama suka tafi aikuwa bakin su yaƙi Rufuwa sabida farin Ciki Da ƙafa suka je har Layin Muhallin wanda tsiran su babu Nisa Tundaga farkon layin Suka sha Jinin Jikinsu sabida yadda manyan Gidaje suka cika layin a gaban wani ƙaton Gida Hadiza ta tsai dasu Gidan da fasalta kyan sa da tsarin sama ƙauyanci ne sai da Suka sha tambayoyi kafin abari su Shiga farkon Gate Ɗin wanda kafin sukai Cikin Gidanma sai da aka Kuma tsaida Hadiza har waya akai Cikin Gidan kafin a bari su Shiga daga Ummi har sa'adah bakin su ya rufe hadiza Kuwa Mita take tana sababin Kamar masu tsaron Gidan basa gane Mutane Koda yaushe kazo sai an maka tambayar tsiya Sukam su Ummi baki ya ɗinke dama akwai irin Gidajen nan a ƙasar nan ama cikin Unguwar su lallai mai Kuɗi ya Huta.

Numfashin sa'adatu ya tsaya na wucin gadi sanda suka je bakin part Ɗin Mama dan wani azababban Kyau da tsari part Ɗin yake dashi wanda kwatan tashi ma ɓata Lokaci ne Da ƙyar suka iya buɗe Ƙofar Babban Falon da girman sa ya kusan zautar da tunanin su sa'adah tsarin sa da dukiyar da aka narka masa ce ta Firgitasu wannan rayuwa kamar ba za'a mutu ba zama sukai Mai aikin dake kaiwa da Komowa a falon ce ta kawo Musu ruwa da abinci Shinkafa da Miyar kaji da lemo Hadiza ta zage tana ci Ita kuwa Sa'adah Ledar Kayanta ta zazzage ta Ƙulle kayan a ɗankwali Nasu abincin ta Juye a ledar tana cewa Ummi idan taje Gida suci da Hajiya ta bawa Hajiya naman sosai taci Yadda Sa'adah tayi ɗinne ya ƙara Birge Hadiza lallai yarinyar akwai tausayi da Jin ƙai sai da suka kammala ko ace Hadiza ta kammala kafin Mama ta fito daga ɓangaren Bedroom Ɗinta Sa'adatu da Ummi suka gaishe da Mama cikin ladabi ta amsa a sake tana cewa.
"Hadiza ki mini afuwa ina tare da baƙi ne ƴan barka ina yarinyar take?"
Sa'adatu ta É—ago idanunta wanda suka haÉ—a ido da mama Sa'adatu ta saki Murmushi yayin da Mama kuma taji gabanta ya faÉ—i kaÉ—an.

"Wannan ce Sa'adatu sunanta marayu ne dan Allah Hajiya A dinga taimakonta mahaifiyarta tana fama da shanyewar ɓarin Jiki dole ce ta fito da ita ma aikin"

Mama ta É—an yamutsa fuska.
"Idan ban da abinki Hadiza meye na wannan jawaban zatai aiki zan biya ta babu rashin ci babu rashin sha a gidannan ga part É—in mai aikina can Kande su zauna tare Sabida Kin san duk na kori ma'aikatana mata sai kande kaÉ—ai na bari tana Mini Girki da gyara mana É—akunan barcin mu yanzu maza nake dasu suke mini komai domin matan da kika kawo Min ban yi dace ba gaskiya basu da tsafta shiyasa duk na sallame su, To idan ita É—in naga bata da matsala zan iya É—aukar tama gaba É—aya sabida Alhaji yana faÉ—an yadda maza ke mana share sharen Gidannan gaskiya"

Hadiza ta kuma yin ƙasa dakai tana wa Mama godiya kafin maman tace.
"Ba damuwa Zaku iya tafiya hadiza zaki ga saƙo ta bankin ki anjima"

Sannan ta É—aga Murya tana Kiran.
"Kande! kande!"
Da sauri wannan mai aikin data kawo Musu abinci tazo ta zube a gaban mama Dattijuwa ce sai dai da ƙwarinta sosai, mama ta kalleta "Kande ga mai aikin Husna nan ki kaita ɓangaren ku kin sami ƴa" kanden da far'a ta ɗauki Ƙullin kayan Sa'adatu tana cewa "aikuwa dai na huta zaman kaɗai ci damma da kayan kallo"
Mama ta tashi ta koma inda ta fito Hadiza ta kalli kande tana cewa.
"Dan Allah ga amanar tanan Kande Ƴata ce ta zumunci" kande tayi Dariya "Wallahi Hadiza karki damu waɗanda kika kawo ma da Hajiya mama ta kora ni bamu taɓa samun saɓani da suba sabida tace Mini kece kike kawo mata masu aiki Nice kaɗai ta samu a wajan wata ai ɗa na kowa ne Nima ina da su a ƙauye"
Tashi sukai Hadiza da Ummi suka fita kande Kuma ta Nufi ɓangaren su da kayan sa'adatu wadda tabi su Ummi don yi Musu rakiya kamar ba zasu rabu da ummi ba sun Rungume Juna suna Ta kuka sai da Hadiza ta ɓanɓare Ummi Sannan Suka rabu da Junansu.

Sa'adatu kuka take sosai haka ta juyo idanunta ko gani bayayi sosai a maimakon tayi part ɗin da aka kaita sai kanta ya juye ta nufi wani part ɗin na daban wanda ita sam bata tantance wanda aka kaita da shi ba Sai da ta shiga falon taga bambancin Girma da kuma tsari dan wannan bai da girman wancan kuma bai da wasu tarkace acikin sa daga Saitin Kujeru sai kayan kallo sai shinfiɗaɗɗan carpet sai Manyan haɗaɗɗun labulaye sai azababban ƙamshi mai kama Hanci data ke shaƙa Ƙoƙarin juyawa take don ta koma sai dai ƙafafun ta sun sage ne Lokacin data ɗaga idanunta dan ta kalli Motsin data ji ajikin Ƙofar dake kallonta idanunta ne suka Shiga cikin nashi.......
*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.