Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 28 of 31

Yau kimanin sati rabon shi da ita dafe yake da ƙirjinshi dake yi masa zafi Yana kwance a saman Doguwar Kujera a falon shi.
Khalid ya shigo cikin shirin fita.
"Lafiya na ganka a kwance ba zaka fita Office bane?"
Khalid ya faÉ—a masa yana zama a gefen shi.
Tashi yayi tare da yamutsa fuskar shi kaÉ—an.
"Bana jin daÉ—i yau ba zan fita ba"
Khalid yaÉ—an tsira masa ido.
"Innah ma tai min Complain na yadda ka sauya kwana biyu Zamu iya shearing Matsalar ka?"
Anwar ya jingine kai da Jikin Kujerar yana sakin numfashi.
Khalid ya miƙe a zuciye.
"Ka mayar dani soko Ni ko meye ina sanar dakai Anwar akwai abin da ke damunka Ko wannan yarinyar ce?"
Da sauri ya É—ago yace.
"Wa kenan?"
Khalid yayi Murmushi tare da cewa.
"Ban sani ba kafini sanin ta ay wadda na zo na tarar dakai da ita ban san dai alaƙarku ba amman nasan matsalar baze wuce daga wajan taba"
Anwar yayi Murmushi.
"Yes ita ce kasan Ni bana yaudara ban taɓa yin soyayya ba bare na yaudari ƴammata wallahi Auren ta zanyi sabuwar mai aikin gidan ce..........
A takaice ya gayawa Khalid Komai dake faruwa.
Khalid yay dariyar shaƙiyanci.
"lallai ka shiga da yawa akanta zaka fasa zuwa Office daÉ—i na da Gobe saurin zuwa da kana ganin kamar bani da abinyi Ko kadai Ji yadda soyayyar take Ko?"
Anwar ya harari Khalid cikin wasa tare da cewa.
"Ni dai ka bani shawara raini ne bana so gaskiya Kuma ban iya rarrashin mace ba bare na lallaɓata"
Khalid dan dariya har da ƙwarewa.
"Aifa shiyasa naga kana kwance ka dafe Ƙirji kaga tashi Muje Office daga nan sai Muje wajanta Ko?"
Tashi yayi ya shirya suka fita har suka kai Office labarin saadah yake bawa Khalid yana jaddawa Khalid yadda yake Jin tausayin ta.
Khalid ya dire Anwar a office ya wuce shima wajan la'asar suka tashi ya Kuma Biyowa suka tafi tare don Anwar bai fita da Mota ba.

A ƙofar Gidan su saadah sukai Parking Khalid ne ya fita ya sami yaro yace yaje ya kira Musu saadah acikin wancan Gidan Sanda yaron yaje saadah tana bacci Ummi ta tasheta Fuskarta duk ta Kumbura idanunta ya ƙara Girma ta sa Hijabi ta fita Ido Huɗu sukai da Khalid wanda ta ɗan shaida shi sabida haka sai ta ƙarasa wajansu ta ɗan tsaya daga Nesa batare data yi magana ba...........*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
​

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*20*

Idanunta ya zubawa ido yaga yadda suka kumbura sukai wani irin Girma Fuskarta tayi jajir gaban shi ne yaɗan faɗi kaɗan cikin wani irin yanayi yake Ƙureta da kallon shi, Kafin yaja ajiyar zuciya Tunda ta fito ta Tsaya a wajan bata ƙaraso wajan suba sai Khalid ne yayi masa Inkiya wadda tasa Dole shi ɗin ne ya fito daga Mota yazo Inda take.

"Mata masu Mulki, Nayi Laifi ne?" ya faÉ—a yana É—age mata Girarshi Guda É—aya.

Hararar shi tayi tana Juya masa baya da sauri yakai hannu zai Juyo da ita sai Kuma ya fasa ta hanyar mayar da hannunshi yana yarfewa.
"Kinga É—an juyo kalle ni kaÉ—an"
Ya faÉ—a a rarrabe.

Ƙin juyowar tayi sabida gaba ɗaya ganin shi da tayi sai take Jin wani irin yanayi kamar taita masa Kuka ko ta sami salama a zuciyarta.

"Nine ko mami ayyah ki haƙuri dan Allah" ya faɗa a hankali.

Maganar tashi ce ta kashe mata Jikinta da wani irin yanayi a tare da ita ta juyo sai dai tayi ƙasa da ƙwayar idanunta.

"Tunda ka tafi baka dawo ba sai yanzu?" ta faÉ—a batare da shirin maganar zata fito mata ba.
Murmushi yayi mai sauti.

"Nayi laifi ki min uziri yanzu dai nazo da Khalid zamu gaisa sai mu wuce anjima zanzo"
Daga haka ya ciri wayar shi ya Kira Khalid dake Cikin Mota wanda ya fito ya ƙaraso wajan Sun gaisa da saadah Sama sama ya koma Mota babu wata Doguwar magana a tsakanin ta da Anwar yayi mata sallama suka wuce da wani Irin Farin ciki ta shiga Gida tana bawa Ummi labari.

Anwar Gaba É—aya ya ishi Khalid da maganar saadah a mota Suna zuwa Gida bayan sallar magariba Ya shiga wajan Malam Har É—aki bayan sun gaisa da malam a nutse Anwar yace.

"Dama abin da yasa nazo wajan ka"

Sai yayi shuru, Innah ce ta shigo tana Dariya.
"Ka gaya masa mana kona gaya masa Yanzu Khalid yake min albishir"
Da sauri Anwar yabar É—akin Innah ce take shaidawa Malam wanda yay hamdala ga Allah.

Lokacin da Innah ta gama gayawa malam maganar da Khalid ya gaya mata akan yarinyar da Anwar ÆŠin ya ke so Malam ya kalleta.
"Allahu akbar Amman naji daÉ—in wannan lamari, Mu babu ruwanmu da KuÉ—i tarbiya Muke wa In sha Allah zansa ai min binciken halin yarinyar In ta gari ce Alhamdulillah sai nai wa Sulaiman magana"
Da Farin ciki Innah ta Bar wajan malam taje ta sami Khalid a falo yana cin abinci ta sanar dashi yadda sukai da Malam wanda shi Kuma ya sanar da Anwar sabida Shi kam Anwar su Innah sun zama surukan shi.

Bayan sallar isha'i yayi kwalliya cikin brown shadda Ɗinki half body batare daya sanya Hula ba sai baza ƙamshi yake ya ɗauki Mota zuwa Gidansu saadah wadda itama Tun magariba datai sallah ta zauna ta tsara kwalliya Cikin wani Yellow Boyal da sukai da sallah yau saadah harda su Jambaki da kwalli Ummi sai dariya take mata bayan ta idar da sallar Isha'i yaro ya shigo yace ana sallama da Saadatu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.