Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 3 of 31

Aunty Murja tagumi tayi tabbas akwai gagarumar matsala acikin Wannan Ahali cikin su ɗaya amman kamar zasu ga hanjin Junan su don Ƙiyayya Abbati fita yayi yana bambamin faɗa Aunty Murja ta zame tai zaman dirshan ta zuba musu idanu gaba ɗaya tausayin ƴammatan ya kamata Dama haka suke rayuwa amman a maƙota a rasa mai taimakon su sabida Munafurcin tsiya Kullum in sun fita tun safe se azahar suke dawowa haka zata ji ana Gulmarsu ana cewa ba'a san ina suke zuwa ba kuma matar Gidannan ita ce kan gaba wajan aibata yaran ashe haka suke fama ashe fitar ta dole ce.

Aunty Murja kuka ta sanya itama tana cewa.
"Allah ya kawo Muku É—auki amman tabbas rayuwarku akwai Ayar tambaya Ciki É—aya kamar kuna ganin hanjin Junanku"

"Wallahi Aunty Murja mu kaɗai Muka san ƙalubalan da muke fuskanta Ummi ko in duka yana kisa da tuni ya kasheta ni kam gaba ɗaya ma duniyar ta isheni"

Sa'adatu ta faɗi tana kuka Ummi kam Numfashi take ja sama sama kafin a hankali ta soma Nishi Can kuma se Numafshin nata ya ɗauke Idanunta suka ƙafe kallon kallo aka soma tsakanin sa'adatu da Aunty Murja kafin sa'adah tai kan Ummi da sauri Kuma jikinta yana rawa tana Furta kalmar.......09022260850

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*003*

"Ummi kada kimin haka meye haka ummi zaki ƙafar da idanun ki" tana faɗi tana jijjiga ummi gaba ɗaya Kuka yaci ƙarfin ta Muryar tata ma bata fita sosai Ganin kamar Suma ne ummin tayi yasa Aunty Murja ta fita tsakar Gida ta Ɗebo ruwa ta shiga yayya fawa Ummi Lokacin sa'adah ta rungume Ummi kamar wani zai ƙwace mata ita tana faman Gursheƙen kuka! A lokacin ɗan kwalin sa'adah yabar saman kanta Duk da Yadda Aunty Murja bata Cikin Nutsuwa seda tai Tasbihi Ga Allah sabida yadda taga gashin sa'adah har Bayanta Kuma irin baƙin nan ne na Fulani wanda baya Kitsuwa Ta daɗi sabida santsi Aunty Murja tabi Sa'adah da kallo tabbas Allah yayi Kyakykyawar Halitta sedai Rashin dake damun Su ya Ɓoye musu kyan nasu Musamman Sa'adah wadda take Ƴar Duma duma duk da suna cikin Yunwa amman Jikinta Kurman Jiki ne dan baya nuna damuwa Tana da ƙiba Daidai Misali Kuma bata Cika tsayi ba sedai ba gajera bace saɓanin Ummi data ke Doguwa sosai Marar Jiki dan Sa'adah ta fita Ƙiba sedai Itama tana da kyau amman bata kama ƙafar Sa'adatu mai kalar larabawa Ba.

Ajiyar zuciya Ummi taja Mai ƙarfi kafin Kuka yabi yo baya Rungume Junansu sukai Aunty Murja taji duk itama idanun nata ya ciko a hankali ta soma yi musu magana.
"Tabbas wanda bai san halin da kuke Ciki ba komai ma zai iya jefar ku dashi amman ni yau idanuna ya gane Mini Komai Kuma in sha Allahu zan taimakeku iya ƙarfina Kuyi haƙuri Ku cigaba da taimakon mahaifiyar ku sannan Kuma ku kare kanku da Samari mayaudara dan wani da wannan Surar taku mai kyau zai shigo rayuwar ku domin ya cutar daku"

Ummi ta ɗora kanta saman kafaɗun Sa'adatu tana sauke ajiyar zuciya kana kallon su kasan akwai tarin ƙauna ta Jini a tsakanin su tare da shaƙuwa mai yawa.

Lokacin sa'adah ta sami Nutsuwa ganin Ummi ta dena kukan se taja ajiyar zuciya.

"Mungode Aunty Murja amman ki tashi kada Baffa yazo ya ganki ze haÉ—a ki da Mijin ki"

Aunty Murja tayi Murmushi.
"Karki damu Mijina ai ba jahili bane yasan daidai yanzu dai bari naje zan sa Almajiri na ya kawo Muku Abinci"
Sa'adah ta girgiza kanta da sauri.

"Muna da abincin rana Da ike bani da lafiya babu wanda yaci"

Aunty Murja tayi Murmushi tare da cewa.
"Babu kyau ƙarya Sa'adah Nidai zan kawo Muku"

Sa'adatu tai murmushi ta jingine Ummi tabi bayan Aunty Murja zuwa soron dan tayi mata rakiya Tana binta a baya tana mata godiya a soro Suka tsaya Aunty Murja ta kuma kallon Sa'adah.

"Dan Allah Sa'adah Ku yafe Mini domin ada nima irin kallon da matan layin nan ke Muku Nima shi nake yi muku"
Da mamaki a saman fuskar Sa'adah tace.
"Wani kallo kenan Aunty Murja?"
Aunty Murja ta gyara tsaiwa tace.
"Ganin kuna fita da sassafe bakwa dawowa gida se da rana watarana da yamma yasa kowa yake Muku kallon kamar yawan banza kuke ganin yadda yayin ku suke shiga da fice Cikin Manyan shaddodi to ana kallon kamar suna baku ne Kune baku da Godiyar Allah"

Gaban Sa'adah ya faɗi idanunta suka ƙara kawo ruwa taja hannun Aunty Murja suka fita daga soron.

Gudun ko an musu laɓe dan al'adar ƴaƴan Gidan ce haka.

Seda suka fita Sa'ada ta kunce É—an kwalinta ta rufe Jikinta dashi ta kalli Aunty Murja tare da cewa.
"Wallahi Aunty Murja rabon Dana ga ƙwandala ta wani acikin yayyan mu har na manta Aunty Murja basa mana komai hatta mahaifiyarmu yau shekara ta uku tana kwance babu abin da suke mata daidai da kuɗin magani basa bamu sedai Mu fita Mu shiga gidaje Mu yi musu wankau Da kitso tunda na iya Su bamu kuɗi Da har Ƙunshi da fulawa ma nake yi to Shi matsalar se kana da kayan yin shi Allah yasan halin da Muke ciki ai Aunty Murja yanzu Hajiya tana shekara ta Uku da faɗuwa Tun Shekarar dana yi candy kenan Ummi ko bata ma yi candyn ba sabida bamu da shi ta haƙura"

Kama Hannun sa'adah tayi cikin tsananin tausayi tace.
"Nima yau na tabbatar da mai É—aki shiyasan ina yake yi masa yoyo don na gani da idanuna kuma In sha Allahu Idan Mijina ya dawo zan masa maganar ku ai ya kamata kwamatin Unguwar nan su duba halin da kuke Ciki Æ´ammata kamar Kuna yawon Neman abin da zaku ci abin da Duba Musamman yanzu da duniyar ta lalace"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.