Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 11 of 31

Husna tayi aure tana zaune a garin Abuja Mijinta ma'ikacin banki ne tana nan da ciki tsoho haihuwa ko yau ko gobe shirin dawowa gida take ta haihu kamar yadda mama ta buƙaci hakan, Husna ce babba acikin ƴaƴan mama A gidan su Anwar

Inkiya mama taiwa su Khairat akan suyi shuru gudun kada Hanan taji abin da ya sami Anwar ta ɗaga hankalinta bayan tarin wulaƙanci da take sha a wajan sa amman ita zuciyarta kamar kare ya cinye Komai zai mata bata ganin Laifin shi akan shi bata Kula kowa duk ta Kori maneman ta wannan dalilin ya ƙara hassasa ƙiyayyar mama da Anwar wadda bata yarda ta fito fili ta Nuna masa ba ta ƙaunar tashi.

Duk yadda mama a farko taso Taja hankalin Anwar akan Hanan tayi amman da yake kamar Dutse yake Ko gezau shi kuma Abba yaƙi ɗaukar mataki akan soyayyar Anwar da Hanan kasancewar Abba yace ba ze wa yaron shi Auren dole ba duk wadda yake so yana da ƴancin aura wannan kalamin na Abba ya tunzura mama dan taso yayi wa Anwar dole ya amshi auren Hanan ganin duk wata hanya tabi batai nasara ba yasa ta ƙara Jin wutar Ƙiyayyar Anwar acikin zuciyarta sedai Mama ƙarshen Makira ce bata yarda ko a fuska ta Nuna wa Anwar bata son shi wanda Tuni Khalid shi ya gama karantar wacece mama shima Anwar ɗin Ko ya karanceta Oho badai ya nuna mata yasan mai take ciki kasancewar shi Mutum marar son magana bare hayaniya.

Hanan tabi su Khairat da kallo tana Ƙoƙarin Yin magana ne Mai aikin su ta shigo da kayan Abinci a saman tray ta nufi dining maganar mai aikin ce tasa Hanan miƙewa da sauri inda mai aikin take tambayar mama ta gano Jikin Alhaji ƙaramin yaya Jikin nashi yake.

Zumbur Hanan ta Miƙe tana dafe Ƙirjinta.
"Mama Yaya ne babu lafiya amman baki gaya mini ba?"
Mama Yaƙe taiwa mai aikin tana cewa da sauƙi Mai aikin tana fita mama tace "To marar zuciya ubanki zaki masa yama Mutu mana wani nada asara ne" Hanan bata tsaya Jin ƙarashen maganar da mama take yiba ta fita daga Part Ɗin nasu Direct Hanyar part Ɗin Anwar ta nufa duk da yana yawan yi mata gargaɗin shigar masa part amman haka ta faɗa Cikin part Ɗin nashi direct Kuma bedroom ɗin sa ta shiga Duk Fuskarta ta Jiƙe da ruwan hawaye.............
*YANKAN ƘAUNA…I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *009*

Kwance yake samɓal a saman gadon Numfashin sa yana sauka a hankali, Idanunshi a rufe ruf duk Zara zaran gashin idanun shi sun rufe masa Idanu ruf, Ƙarasawa tai wajan Ac control ta ƙara mai ƙarfin AC'n kafin ta nufi gadon jikinta duk a sanyaye wani Irin tausayi rayuwar shi take bata wadda take Jin Ninkin soyayyar shi acikin Zuciyarta fiye da ƙima Fiye da zaton mai zato.
Guntun hawayen dake Zubo mata take sharewa a fili ta furta "Wai kai baka jin Yadda nake jine wai kai wace Irin zuciya gare ka ban taɓa Jin ka furta kalmar kana soba sedai naji kalmar ana son ka a bakin mata da yawa daga Ciki harda ƙawaye na Dan Allah ka cire tsanar soyayya a zuciyarka kazo ka tallafi wadda take maitar son ka" Hanan ta furta kalmar tana tsira masa ido shima kuma adaidai nan ya buɗe idanun shi da suka ɗan Kumbura kaɗan suka ƙara Girma Yawun tsoro ta haɗiye ga kuma wani irin fitsari daya ke Ƙoƙarin zubo mata a hankali take ja da baya tana Ƙoƙarin sauka daga saman gadon sedai hakan bai samu ba sakamakon hannunta da Anwar ya cafke yayi wa Riƙon tsauri wanda har ƴar ƙara ta saki sabida zafi.

Rintse idanu tayi ta buɗe su har lokacin kallonta yake ba ko Ƙiftawa yana so yasan yaya son ta zai shiga zuciyar shi Kodan nacin ta gare shi amman ya kasa Gaba ɗaya zuciyar shi a bushe take kamar Dutse Bai taɓa furta kalmar soba hasalima in aka ce ana son shi haushi yake Ji shiyasa yake mamakin Yadda yake Jin Khalid na waya da ƴammata shikam yayi ƙoƙarin gwada Saka soyayya aran shi amman hakan ya gagara sabida kallon mata yake duka halin su ɗaya wani abune yake taso masa tina wani mikin da yajima a zuciyar shi da sauri ya saki hannunta ya Jingine kanshi da Pillow wani irin hawaye mai zafi ya soma gudu a saman Fuskar Jarumin namiji kamar Anwar Da sauri Hanan ta Tashi har tana tuntuɓe garin saurin barin ɗakin dan tana hango Tashin hankaline a cikin Idanun shi wanda inta zauna kusa dashi Komai na iya samunta.

Karo aka ci tsakanin Khalid da Hanan wanda bata Kula shiba Inna tabi Hanan da kallo haka suka É—unguma zuwa É—akin Anwar wanda Jin alamun shigowar su yayi saurin share hawayen shi.

"Oh Ni Æ´asu bawa dai ba abakin Komai yake ba Ni Baraka Jibi yadda Muhammadu ya koma Lokaci É—aya sannu kaji Muhammad Anwar"

Inna ta faÉ—a tana zama a kusa da shi kansa ya É—auka ya É—ora a saman kafaÉ—un Innah a jikinta ne yake Jin ÆŠumi na uwa.

"Khalid bai gaya maka dalilin ciwon nashi ba ko?" cewar Inna Khalid daya ke ɓallo magani tare da ɗaukar Gorar ruwa ya nufo wajan su yace wa Inna "Wallahi innah ban sani ba Allah dai ya bashi lafiya kawai" daga haka ya ɗago kan Anwar ya damƙa masa maganin a tafin hannun shi.

Anwar ya ɓata Fuska kamar wani ƙaramin yaro sabida a rayuwa baya ƙaunar magani tun yana yaro haka yake kuma gashi har an girma bai daina ƙin maganin ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.