Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 23 of 31
Jingine yake da Jikin Bangon ɗakin ya cusa kanshi a tsakanin Cinyoyinshi Hannun shi mai Ƙunar Kuma yana dafe da Ƙuncinsa.
"Sannu a ina wayar taka take?"
Ta faÉ—a bayan ta zube a gabanshi.
Da hannu ya nuna mata wayar dake yashe acan ƙasa tai saurin Miƙa masa tana jada baya Fuskarta ta sauya hankalinta a matiƙar tashe.
"Nice sanadi dan Allah kayi haƙuri tsautsayi ne"
Muryarshi ce ta katseta yana magana a hankali.
"Khalid kazo ka kiramin Doctor Please"
Daga haka ya katse wayar falon ne yayi tsit.
Daga shi har Saadatu babu wanda yayi magana Minti kusan Biyar sai ga Khalid É—in wanda ganin Mace a wajan Anwar ya bashi mamaki, amman bai nuna ba ya shiga Kiran Doctor É—in a hankali saadatu ta tashi zata bar falon Muryarshi ta katse ta.
"Mami kin iya shara, Dan Allah share Min Bedroom É—ina ki wanke Min Toilet"
Amsa mai tayi tana tashi Khalid ya bita da kallon Mamaki bakin Khalid fall tambayoyi amman ya gaza Furtawa sabida ba lokacin tambayar bane Minti kaÉ—an doctor yazo allura yayi ma Anwar tare da bashi magunguna.
Khalid ya tafi raka doctor Bayan ya dawo ya tarar Anwar na bacci Sabida haka sai ya fita.
Tsananin mamakin tsaruwar Bedroom ɗin ya sanya Saadatu sakin baki dan tasha ƙauyanci kafin ta gyara masa gado ta Share ɗakin ta goge tas bayan ta gama da nan ta shiga toilet nan ma wanke shi tayi duk da babu datti tazo ta haɗe kayan shi da suka zubo ta gyara ta Kunna turaren wuta sai la'asar ta gama Sabida bata da zafin nama.
Lokacin data fito falon Baccin yake har Lokacin bai farka ba, sabida haka sai ta wuce ta fita zuwa sashin su.
Lokacin data ƙarasa Husna ta tashi daga baccin Gyara mata ɗaki tayi a gurguje ta kammala mata komai sabida akwai baƙi sosai a babban falon Gidan bayan ta gama ta shiga wajan su tana shiga ɗaki zama tayi a bakin gado tare da rafka tagumi tana ganin kanta abin tausayi Amman Mutumin nan yafi bata tausayi fiye da kanta sabida kana kallon shi kasan yana da tarin damuwa.
Tsintar kanta tayi tana mai ɗaga hannu tana hawaye tana roƙar Allah daya yaye masa damuwar shi, Bayan ta shafa ta cigaba da mamakin dama masu Kuɗi suna da damuwa har haka.
KaÉ—aici kewa duk ya dami saadatu.
Haka ta zauna har akai magariba bayan ta idar da azkar sabida har Lokacin bata sami tsarki ba Fita tayi Kitchen wajan Baba kande ta taimaka mata wajan Haɗa Girkin dare baba kande se mita take na yadda yau taita sauke ɗora sabida baƙi ƴan barka.
Bayan sun kammala Saadatu tukunya ƙarama ta samu ta zuba ruwa da kayan haɗin shayi ta Ɗora tana tsaye ya tafasa ta juye ta haɗa komai cikin Dogon tray ta fita dashi zuwa ɗakin su sai da aka yi sallar Isha'i ta miƙe bayan ta watsa ruwa gami da sauya kaya ta ɗauki tray ɗin ta nufi wajan shi tana tunanin koya ci abinci Gaba ɗaya tausayi rayuwar shi take bata tana Jin ina ma zata ji labarin shi koda kaɗan ne domin daga gani akwai abubuwan dake tare dashi.
Raɓewa tayi ajikin ƙofar falon shi sabida jin sautin maganganun dake fita daga cikin falon nashi Allah ya gani ba laɓe tayi ba dalilin tsayawar tata gudu take in ta Koma da kayan shayin Wani zai iya ganinta acikin ahalin gidan shiyasa ta zaɓi ta dakata har baƙin nashi su Fito sai ta shiga takai masa.
"Anwar karfa kai wa rayuwarka Illah shekaran Jiya Likita ya gama faÉ—a akan ciwon ka yau gashi ka Kuma kwanciya Ni bana son wannan yawan damuwar taka tunda ba cikakkiyar lafiya gare kaba"
Muryar mace ke tashi acikin falon.
Shi kam ba'a jin abin da yake faɗa sabida ƙaramin sauti da yake amfani dashi maganganu suke waɗanda suka danganci ban haƙuri da Nasiha da matar ke masa kafin ta gama ta fito Ɗauke Numfashi Saadatu tayi Lokacin da matar ta gama maganar ta fito daga falon, Wuff saadatu ta faɗa cikin falon tana raba ido yana kwance a saman Sopa jikinsa sanye da Singlet da Dogon wando yana ganinta yaɗan sauya fuska yay kamar bai ji daɗi a yadda ta same shiba.
Ƙasa tayi da kanta bayan tai sallama ya amsa mata a taƙaice.
"Yaya jikin naka dan Allah kayi haƙuri"
Ta faɗa kanta ƙasa tana ajiye Tray ɗin hannunta.
"Ke ni wannan ban haƙurin naki ya isa tashi kije"
Jitai gwiwarta ta saki a ranta take ayyana Saadatu kin zaƙe da yawa tunda bai neme kiba meye zaki kawo kanki Gurin wanda yafi ƙarfin ki.
Tashi tayi zata tafi.
"Zoki É—auke wannan abun"
Ya nuna tray É—in da hannun shi mai lafiyar.
Hawaye ne ya wanke mata fuska ta sunkuya zata É—auka yabi fuskarta da kallo.
"Kukan na menene Tell me?"
Bata yi magana ba domin in da amsar da zata biyo bakinta kuka ne mai ƙarfi ta yaya ta Ƙona shi ya kwanta Ciwo ta kawo masa shayi dan ta duba shi ya gwaleta Ji take kamar ita ce silar Komai na ciwon shi shiyasa taji hankalinta ya gaza kwanciya.
"Mami Come here"
Ya faÉ—a yana kallonta.
Ta fahimci me yake nufi sabida haka zuwa tayi gabanshi ta zauna.
A hankali ya kalleta.
"Ke sunan mahaifiyata gareki, Aikin me kika zo gidannan sannan ke a ina kike?"
Da nutsuwa ta É—ago taÉ—an kalle shi.
"Ina layin É—orawa nazo ne ina wa Wadda ta haihu anan gidan aiki ne..........
TaÉ—an bashi labarin dalilin zuwanta gidan nasu.
"Ina baki kuÉ—in maganin mama zaki koma gida ina nufin ki koma ku cigaba da Jinyar mahaifiyarku sabida duk wata Æ´a mace Mutuncin ta gidan su ko gidan Mijinta yanzu haka kowa da irin kallon da zai Miki"
Tunda ya soma mata maganar taji girman shi yana ƙara ƙaruwa cikin idanunta shine Mutum Na farko a duniya daya soma taimakon ta a maza batare daya nemi komai daga wajanta ba.
Hawaye ya wanke mata fuska.
"Nagode Allah ya jiƙan mahaifa in sun mutu in suna raye Allah yaja kwana, amman na riga na amshi Kudin wannan watan"
Ya tsareta da girman idanunshi.
"Miye kikai da kuÉ—in?"
Ya faÉ—a cikin hausarshi wadda take Nuna Ainihin harshen shi wato na katsinanci.
"Dama zan kai wa Ummi ne sabida kula da Hajiya"
Shuru yayi Kamar baze yi mata magana ba can yace mata.
"I understand you, zaki iya tafiya Ki shirya kayan ki"
Daga haka ya Mayar da kanshi ya kwantar.
Tashi tayi Jikinta duk yayi sanyi harta kai Ƙofar fita ta kuma dawowa.
"Me zan ce wa Hajiya?"
Shuru yayi mata sai da ta kuma nanatawa.
Sannan yace mata.
"Kice mata Anwar yace zai mayar dake Gidan ku, Ki basu kuÉ—in da suka baki"
Jimm tayi tare da sakin Ajiyar zuciya kafin ta fita daga Falon nashi.
Daran ranar Saadatu bata rintsa ba, Ta rasa ina maganganun sa suka dosa amman ta bawa zuciyar ta amsa da Taimakonta yake so yayi.
Washe gari Sabgarta ta shiga ganin bai mata magana ba.
Shima a nasa ɓarin Ayyuka ne suka taru akan shi a office, Ga Binciken daya tsaurara akan Fitar da kuɗin da akai bawai Biyan Kuɗin ne yayi Mishi ciwo ba A,a zafin Zargin da Abba ke masa shine ya ƙara tunzura shi akan dole ma sai ya Gano yaya akai Kuɗin suka fita wannan dalilin yasa a wannan rana ya dakatar da Alhaji Jamilu ya kuma dakatar da Chief Information Officer lamarin daya Girgiza zuƙatan mutane Biyun wato Alhaji jamilu yayan Mama matar Mahaifin Anwar da Amininshi wanda suke haɗa ka wajan cuta da handama acikin Kamfanin.
Anwar bai shigo gidan ba sai yamma Lis part Ɗin Innah ya wuce yaci abinci sannan ya fito zuwa nashi part Ɗin Lokacin daya shiga ana kiran sallar magariba alwala yayi ya fita masallaci sai da yayi sallah sannan ya Watsa ruwa Cikin shiga Black Jeans da white shirt ya fito yana ta baza ƙamshin turaren shi na Tom ford Oud wood, Babban falon su ya Nufa Baba kande tana ta hidimar haɗa Girki da sauri ta russuna tana gaishe dashi ya dakatar da ita.
Dan baya so babba kamarta tana rissuna mai.
"Baba kiramin wannan yarinyar mana"
Bata fahimta ba.
Yanayin yadda take yine ya nuna masa hakan.
"Wadda aka kawo sabuwar nan"
Da sauri baba kande ta juya ta shiga ɓarin su ta kirawo saadatu data ke zaune ta idar da sallah dan Lokacin ta sami tsarki sabida dama bata wani Jimawa.
Gaban sa'adah ya faɗi sanda Baba kande ke sanar da ita Alhaji ƙarami na kiranta.
Tashi tayi ta biyo bayan Baba kande zuwa falon.
Baba kande ta wuce Kitchen ita kuma ta Nufi inda yake tsaye ya harɗe hannayen shi a saman Ƙirjin shi.......
*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.