Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 22 of 31

Adaidai nan sa'adah ta juya da sauri tabar falon mama sabida tazo ne ta shaida mata ta kai masa shayin amman an samu akasi ya ƙone dan duk azatonta yaron Mama ne sai dai koda ta kawo kanta taji abin da yafi ƙarfin kanta.

Dariya Hajiya turai tayi.
"Tabbas Shafa kinyi kyan kai Duk magungunan da muka amso muka rasa yadda zamuyi dasu kinga ga hanya nan duk abin da yace yana so saiki bata takai masa a zummar ita tayi Koda wasa kada ki Kuskura Ki nuna da wata manufa a ranki Ko ita yarinyar karki Nuna mata cewar ga abin da yake zuciyarki"
Dariya mama tayi.
"Aini hadari ce sa gabanka inda kake so! ƙaryar Mutum ya gane abin da yake rai da zuciyata, Ni yanzu ta rai nake bata so ba Burina naga bayan anwar so nake ya mutu kamar yadda Bokan daya bamu maganin nan ya tabbatar mana da in yaci zai Mutu Mutuwar da babu wanda zai zargi komai to Burina kenan dan ni yanzu bata soyayyar da Hanan take masa nake yiba sabida nasan ba ze taɓa auranta ba yadda zuciyarshi Ɗinnan take kamar dutse, To na fison ya sheƙa naci kare na babu babbaka ko ma Huta da Ƙulla Tuggu nida yaya Mutuwar sa ita ce mafita kaɗai, Don inna barshi a raye tabbas zai aure Kuma zai haihu"
Dariya Turai take kafin tace.
"Tabbas in ya rasu zamu huta ne da Ƙulla masa sharri wajan Ubansa Kinga daga nan kowa ya huta, Amman Kina ganin maganin zai aiki dan Mun kai wata Shidda fa da amso shi"
Mama tai Murmushi.
"Ko jiya nai waya da shi ya tabbatar da inna sami hanya nai ta zuba masa yana ci a hankali zai ratsa Jikinshi rana ɗaya za'a wayi gari aga baya duniyar Kinga ko yanzu Tunda har yana cin abincin wannan yarinyar ai shikenan Magana ta ƙare, Haba ni ai ban taɓa ganin Dutse irin Anwar ba baya cin Komai fa namu sai ruwan zafi kaɗai zaizo Dining ya ɗiba ya zuba sugar da Lipton tea ko ya haɗa coffee yasha amman bayan su duk Irin Girki daze gani baya ci, Sai dai Baraka ta girka masa, To kinga shi ruwan zafi ta ina zan zuba magani aciki bayan fari ne tas wannan jaraba damai tai kama Har yanzu Burina yaƙi cika"
Da haka sukai ta tattauna maganganunsu na Mugun Nufi akan Anwar.

Sa'adah jikinta rawa kawai yake É—akinsu ta faÉ—a ta shiga Toilet tai zaman Dirshan aciki sai Kuka take Dama har yanzu akwai Mugaye irin haka tabbas Umma Muguwace ajin farko amman tana zaton wannan matar Babar Umma ce tunda gashi nan tana ji da Kunnenta zata ga bayan Wanda take zaton É—an Mijin tane.

Tarin tambayoyine a zuciyar sa'adah sai dai wa zata tara dasu ta yaya zata kare rayuwar Bawan Allah wanda ake farautar ranshi.
Jikinta gaba ɗaya yayi sanyi domin bata san ta  inda zata fara ba ajiyar zuciya ta saki kafin ta tari ruwa ta wanke Fuskarta ta fita waje ta zauna tare da rafka tagumi.

Har wajan bayan sallar azahar tana takure sai da baba kande ta shigo sannan ta ɗan saki Jikinta tana son sanar da Baba kande zuciyarta Kuma tana kwaɓarta akan bata san halin Baba kanden ba kar ta gaya mata maganar ta zamo mata matsala.

Sai da rana ta ɗanyi sanyi wajan ƙarfe Uku sannan ta sanya Hijabinta tabar ɗakin kai tsaye Wajan Husna taje ko tana da aiki samu tai suna bacci sai ta rufe musu Ƙofar tabar wajan...

"Saadatu sa'ar mata"
Muryar mama a bayanta.
Jikinta ne ya soma rawa Nan da nan gabanta ya yanke ya faÉ—i kafin tayi ta maza ta juyo tana Murmushi.
"Sannu da fitowa Hajiya"
Ta faɗa tana zubewa a ƙasa.
"Tashi mana Sa'ar mata ya kuwa sha shayin nashi Kinsan yayan nasu ne da Jin ƙyanƙyami"
Sa'adah tai murmushi kaÉ—an.
"Eh sai da naga ma yakai Cup É—in bakin sa sannan na baro Wajan"
Mama ta wani zaro ido.
"Da gaske?"
Sai kuma ta gyara Nutsuwarta.
"To shikenan duk abin da yace yana so ki fara sanar dani kafin ki kai masa karki yarda na sami labarin Kin kai masa abu ba tare da sanina ba"
Da sauri ta girgiza kai tana cewa.
"In sha Allahu Hajiya"
Mama tabar wajan saadatu tabi ta da kallo.
Tsaki Hanan taja wadda take kwance saman doguwar Kujera tana hararar saadah wadda ta miƙe zuciyarta tana Ingizata akan taje taga a wani hali Bawan Allah nan yake.
Fita tayi daga falon kai tsaye ta Nufi sashin Anwar.*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *17*

Rasa yadda zatayi ta shiga cikin falon nashi tayi, ga zuciyarta ta ɗokanta da taga a cikin wani irin hali yake, Daga tai nufin buɗe ƙofar falon sai ta dawo da baya ta wani dafe ƙirjinta da hannunta wanda Ƙirjin nata ke faman Lugudan duka dum!dum!
Sau wajan uku tana yin hakan a karo na huɗu ne taji zuciyarta ba zata jure ba sai kawai ta Buɗe Ƙofar ta shiga Duk da rana ce amman sai yanayin falon ya koma kamar Duhun dare sabida Manyan labulayen dake zagaye da falon ga hasken shima a kashe yake tsaye tayi tana murza hannunta sabida bata kawo yana ciki ba tana Ƙoƙarin saka ƙafafunta don ta Juya taji sassanyar Muryarshi wadda tai kama data marar lafiya.
"Mami zonan"
Sai tayi duru duru ta rasa da wa yake wa kuma yake Kira sai ta kuma Ƙoƙarin tafiya.
"Please mami zonan ki Miƙo min wayata"
Cak ta tsaya tana jan numfashi Ita ce Mamin kenan meye dalilin shi na Ɓoye mata suna alhalin tana ƴar aiki a gidansu kuma duka duka Jiya tazo Gidan nasu Amman har ya sauya sunanta, Tunanin datai na sunan nata ko Wani suna ne gare shi mai Daraja yasa taja ƙafafunta da suka mata sanyi Ta ƙarasa Wajan shi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.