Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 2 of 31

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*002*

Idanun sa'adah yayi ƙwalƙwal duk ya ciko da ƙwallah sam ita bata son tashin hankali a rayuwarta bata ma iya shiba to ina ma taga ƙarfin Yin faɗan.
Tana tsaye a bakin ƙofar har ta daina Jiyo Masifar Umma a hankali ta ke sanɗa tana fita tsakar Gidan seda ta ɗauke Numfashin tama sannan ta Ƙarasa bakin Rijiya ta zuba ruwa a Bokitin su ta shiga banɗaki Tana tsaka da wanke Jikinta.

Jamila ta turo ƙofar banɗakin taji shi a rufe.
"Wai waye acikin bayi ana kiran sallah salon a ɓata mana Lokacin alwala"
Sa'adah ta shiga Ƙifta idanu bafa sallar Suke akan Lokaci ba wani bin ma ana kiran sallah suna Jin kiɗa amman yanzu ganin ta shiga banɗakin yasa jamilar Biyota ko ƙila taga sanda ta shiga bayin ne Oho!

A wannan karon sa'adatu tai ƙarfin halin furta.
"Ehem"!
A gurguje ta gyara jikinta ta fito waje tana fitowa jamila ta kifa mata mari dama in da sabo sun saba Yiwa sa'adah irin haka sa'adah ta dafe Kunci Batace wa jamila komai ba tai Nufin barin wajan.
"Dama sena rama wa Zainura akan ki sabida haka ubanki zanci"
Ta kwarfe sa'ada wadda sauran kaÉ—an ta faÉ—a Rijiya Allah ya taimaka Abbati wanda take Bi masa ya shigo Gidan da sauri ya kama sa'adah yana furta.

"wannan wani irin shashan cine zaki faɗa rijiya a banza?" Bata ce masa komai ba ta zare Jikinta daga nasa tabar wajan Duk jikinta rawa yake haka ta faɗa cikin ɗaki Amman Idanunta duk ya ɓaci da hawaye.

Abbati ya shigo É—akin a tsaye ya tsaya yaushe rabon da yashi go gidan bare ma ya taimaka musu da wani abun.

Ya tsaya akan Ummi yana muzurai.
"Dama wajanki nazo tsagera to ba zaku ɓata mana sunan Ahali ba Musamman ke" ya nuna ummi wadda bata ko kalli saitin saba ita ko sa'adah wajan Hajiya taje ta raɓe tana ƙifta ido cike da tsoron Abbati.

"Babu hauka ce da zaku dinga bin gidajen masu kuɗi kuna roƙon su salon ku sa a zage mu to Allah ya gani meye bama yi muku"
Ummi ta É—aga mai hannu alamar ya dakata.
Ya ko buge hannun nata da zafin nama ya cigaba da cewa.
"Ni sa'anki ne ina magana zaki dakatar dani?"

"To Abbati me kake so nayi in ban dakatar dakai ba dame zamuji naman jikin mu zamu yanka muci in bamu bi gidajen masu kuÉ—in ba, daÉ—in tama wankau da kitso muke bi muyi musu su bamu kuÉ—i ba iskanci muke yiba munafukin daya kai maka gulmar ya rage"
Jin wannan kalmar Abbati ya cire belt yayi kan ummi sabida dama gaba ɗaya mazan kamar abokan gaba aka mayar da su sam in kaga yadda Abbati da Kamalu kewa su Ummi ba zaka ce sun haɗa alaƙar Jini dasu ba.

Abbati yayi kan Ummi da duka ita ko ta miƙe ta riƙe belt ɗin.

"Ki saki kona illataki"

"Wallahi bazan saki ka daki banza ba haka kawai KuÉ—in magani ma da gindin sa yake zaune kai ko ajikinka"
HankaÉ—a ta yayi aiko suka hau kokawa kamar zasu kashe Juna Duk da bashi Ummi take biba amman sam bata ganin Girmansu sabida rashin imanin su ga mahaifiyar su ko wannen su yana samu kamalu Provision store gare shi, Abbati Kuma Bumburutun man fetur yake amman se suyi sati ma basu zo duba hajiya ba bare sukai ga Sun taimaki su Ummi da ko kuÉ—in Omo ne wannan tasa gaba É—aya Mutuncin su ya zube a idanun Ummi Ita ko sa'ada tsoro Baya bari ta tanka musu Bare har suyi faÉ—a.

Ƙarfin Namiji da mace ba ɗaya ba Abbati yay wa Ummi duka duk da yaga bata motsi hakan bai sa ya dena dukan taba Abin tausayi Hajiya tana kallonsu tana gwaranci hawaye yana zubo mata Sa'adah ta riƙo Abbati tana kuka tana cewa.
"Wannan wani irin masifa ne da bala'i ciki ɗaya kamar ana ganin hanjin Juna kashe Ummi zakai to ka sani in ka kashe min Ummi Nima sena kashe ka dan Ummi ita ce garkuwar Mu duk kan wani ƙarfi da ƙwarin gwiwar rayuwa Ummi ce take bamu"
Sa'a ta faɗi tana kuka amman Abbati idanunshi ya rufe ganin ze kisan kai Sa'adah ta fita tsakar gida tana Ihun a kawo Musu ɗauki amman Babu wanda ya leƙo Ƙofar Gida ta fita Kanta ko Lulluɓi babu tana ihun a kawo musu ɗauki Abbati ze kashe Ummi Jin Kukan sa'adah maƙociyar su Aunty Murja ta fito aguje sukai cikin Gidan Da ƙyar Aunty Murja ta cire Abbati daga Jikin Ummi gaba ɗaya kamannin sa sun jirkice se faman Huci yake komai ma ze iya faruwa bada ban Allah ya kawo Aunty Murjar ba wadda seda tai namijin ƙoƙari ta iya shigo wa gidan sabida Kaf maƙota babu mai iya shigowa gidan Muddin bada Umma zakai Hurɗa ba Inko ka kuskura kai Hurɗa dasu sa'adah tofa ka shiga Uku da cin Mutuncin Umma dan har kabar Gidan tana maka habaici ƴaƴanta suna taya ta Shima kuma Baffa da kansa ze tari Mijin ka ya kafa masa gargaɗin kada ya kuma barin matarsa shigo masa gida wannan ne dalilin daya sa su sa'adah basa hurɗa da kowa a layin yauce rana ta farko ma da sa'adah tai kuka har Wani yazo dan ya taimaka masu.

"Wallahi nine ajalinki idan baki wasa ba shegiya Æ´ar iska tsinanniya"
Abbati ya faÉ—a.

"Kinga ni ko Aunty Murja wallahi ki zama sheda kome ya sami Ummi ni sa'adah Nima sena kashe Abbati dan wallahi baze kashe Min ummi ba don tafiye Mini shi a duniya"
Yayo kan sa'adah da huci yana aika mata zagi kai baka ce sun fito ciki É—aya ba.
"Ke kuma a suwa Mai kalar Munafukai Kema akwai tawa dake ko ban kashe kiba sena Miki Illar da zaki kasa Moruwa wannan shuru shurun naki Illah ne"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.