Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 4 of 31
Ita dai sa'adah jin Aunty Murja take don tasan da kamar wuya Mijinta ya taimake su sanin duk wani wanda yay yunƙurin taimakon su tofa Baya kaiwa da yayi Musu taimakon yake fasawa In ma sunje se Mutum ya kore su ada kafin faruwar hakan suna sana'oin su na cikin gida amman takai ta kawo Komai suka kasa babu mai saya Hatta saurayin ma da Aunty Murja take faɗa ai ya taɓa biyo Ummi amman haka Umma ta fita ba'asan mai tace masa ba bai ƙara dawowa ba ita ko sa'adah dama babu wanda ya taɓa cewa yana sonta har zuwa wannan Lokacin.
"Ki dena tunani sa'adah sabida kada Ki kamu da wani ciwon sannan Ku dinga addu'a sabida sharrin maƙiya"
Shawarwari Aunty Murja ta bata sukai sallama Sa'adah ta koma gida É—aki ta shiga tana zama ana kawo wutar nepa Muryar Umma ce ke tashi a tsakar Gida inda take cewa.
"Babu shegiyar Munafukar matar da zata kuma shigowa gidannan a haÉ—u ana gulmarmu"
Sallamar Baffa daya dawo daga kasuwa da yake yana zuwa bakin asibiti yana siyar da kayan Miya ita ta katse maganganun da Umma take batai masa ko sannu da zuwa ba tahau Zuba masa ƙorafi.
"Dama inusa kai nake Jira ka shigo ka rabani da ƴaƴan muntari su fita daga harkata data ƴaƴana babu su babu mu bamu haɗa iri dasu ba se zaman waje ɗaya to tun wuri kai Musu kashedi a matsayin ka na ƙanin Uban su"
Baffa yay ƙasa da Murya cikin tsoron faɗan Umma yace.
"Haba talatu Me yasa zaki dinga ɗaga Muryarki akan waɗancan ƴaƴan hau ɗin ƴaƴan fata ki kwantar da hankalin Ki Kwanan nan ma zasu bar mana gidanmu Ki ɗan ƙara haƙuri Kuma zan ja musu Kunne"
Tana karkaɗa Ƙafa ta warci ledar hannunsa ta buɗe ta wani ƙyafe bakinta.
"Tsire fa nace ka kawo mini ba balangu ba" kafin tai wata maganar Zubaidah babbar ƴarta ta fito daga ɗakin su ta warce Ledar tayi ɗaki aguje Tun kafin takai ga zama ta soma cin naman tana dariya Zubaida kenan Ƴar madara ta raina uwar Kamar me Kuma gashi duk ƴaƴan ba wadda take so kamar zubaida bata cas bata as tana daga kwance zata ci zata sha ko waje seta kama take fitowa Kai sarki ubanka talaka sunan da matasan Unguwar ke Kiran zubaida dashi kenan sabida girman kanta.
Ga mamaki Umma batai magana ba sema É—akin ta data shige tabar Baffa a waje wanda ya nufi É—akin su Sa'adah dan ya kafa Musu sharaÉ—in Fita daga sabgar matarsa da Æ´aÆ´anta.
ÆŠaga labulan yayi Ba ko sallama ya zubawa Ummi idanu wadda ta Jingina da kanta kafin yayi gyaran Murya wanda yasa Ummi ta É—ago........
09022260850
Auta
*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*
*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*
*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*
_A WANI ÆANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ÆANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*
*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*
*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO
*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
    Â
     *NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
           *004*
Ɗago idanunta tayi ta zuba akan shi ya wani haɗe ranshi kamar bai taɓa dariya ba, Kuma kamar ba yanzu ya gama rawar Jiki a gaban Umma ba.
"Ke ina Æ´ar uwarki ku fito tsakar Gida ina son magana daku"
Ummi da take Jin hannunta kamar ze karye sakamakon dukan data sha a wajan Abbati a haka ta amsa wa Baffa da cewa.
"To Baffa"
Ya juya ita kuma Ummin ta Shiga uwar É—aki wajan Sa'adah wadda take Sauya kaya zuwa wata yagulalliyar Doguwar Riga ta bacci da baya Ummi ta koma tare da cewa sa'adah Idan ta kammala Shirin Baffa yana Kiransu Gaban sa'adah ya faÉ—i Nan da nan tsoro ya cika ta Ita dai Allah ya bata tsoro Har addu'a take Idan tai sallah akan Allah ya rage mata wannan yawan tsoro.
A gurguje ta sa rigar ta ɗora Hijabi akai suka fito yana tsakar Gida ya kama Ƙugun sa suka tsugunna a gabansa.
"Baffa gamu"
Ko kallonsu bai yiba.
"Na ganku mana Æ´aÆ´an banza to bari Kuji na gaji da ganin Æacin ran talatu In baku kama kanku ba zan tattare ku kuda Nakasashshiyar uwarku Ku bar min gidana"
Sa'ada bakin ta har yana rawa wajan Furta masa kalmar "Dan Girman Allah Baffa kai haƙuri In sha Allahu Ba zamu Kuma ba in ka kore mu ina zamu je bamu da kowa se kai Baffa"
Ya saki wata dariya tare da cewa "Ni meye naku Kuma ina ƙara jaddada Muku In kukai cikin shege babu wadda zata dangana kanta dani sabida Ina jin yadda maƙota suke faɗin yawon da kuke Fita Nidai babu ruwana"
Baƙin ciki yazo wa Ummi Wuya duk da tana jin jiki amman haka ta yunƙura zatai magana sa'adah ta Damƙe hannunta tana ƙifta mata ido da yake tsakar Gidan ya cika da hasken farin ƙwai yasa Ummin ta gane da ƙyar takai zuciyarta nesa wajan danne abin da ya taso matan.
"Baffa Kai haƙuri zamu Kiyaye"
Sa'adah ta faÉ—a Lokacin Almajirin Aunty murja yayi sallama yana cewa Ina ne É—akin su sa'adah Gaban Sa'adah ya faÉ—i tana kallon Almajirin da babbar Kular abinci a hannunshi Ummi se Lokacin tai magana tace.
"Gamu kawo nan"
Zata amsa Baffa ya amshe tare da cewa.
"Kai yaro daga ina?"
Almajirin yace.
"Daga Gidan Aunty Murja wannan Gidan mai kallon naku"
Da sauri Umma ta fito tana cewa.
"Kagani ko Inusa? wannan Murjar ita take zuga su Kullum seta zo sun haÉ—u a É—aki suna zagin mu sabida haka kaja mata Kunne ka fita ka sami Mijinta babu ita babu mu.
Ummi ta kalli Umma tana mamakin sharrinta wato idan Umma tai maka wani sharrin seka raina kanka Baffa ya kalli Almajirin yana cewa.
"Muje kamin sallama da Mijinta akan talatu senai shari'a da uban kowa agarin nan" zai fita da kular Umma ta warce tai ɗaki da ita suka bar su Sa'adah a wajan Da ƙyar Sa'adah taja Jiki tabar wajan sabida takaici tabbas zuciyarta ta kusan Bugawa da wannan Ƙuncin rayuwa da ƙasƙanci da suke fuskanta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.