Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 6 of 31

"Ƴammata Dafatan dai lafiya kike wannan kuka?"
Cewar wata mace baƙa tana tsaye a saman kan Sa'ada Ɗago idanu tayi tana kallon Matar fuskarta tai dumu dumu da hawaye da majina.
"Babarmu aka rubuto wa magani Mu Kuma bamu da KuÉ—in maganin gashi Kuma Likita yace lallai se Mun bata in ba haka ba komai na iya faruwa"
Matar ta ƙarewa sa'adatu kallo a fili tace.
"Madallah da Ubangijin daya halicci wannan sura mai kyau Ina fatan Allah ya kare Miki Mutunci ki dama Ƴammata zasu yi koyi da Halin ki gaki dai babu Namijin da baze ganki ya ƙyasa ba amman Kin kare martabar ki dan Kina da surar da waje ma za'a iya fitar da mahaifiyarki amman Baki banzatar da kanki ba Muje naga Babar taku"
Sa'adatu ta share hawaye tayi gaba matar na binta a baya Suka je wajan su Ummi wadda Hajiya ke Jikinta duk Yawu ma ya ɓatawa Ummi Kayanta wanda Hajiya ke zubar dashi.

Suka gaisa da Ummi da matar.
"Allah sarki Ni zan taimaka Muku Yanzu dai Kuzo Muje Ku kai mahaifiyarku Gida ke Kuma seki Biyoni a Janguza Gidana yake Sana'ata kai yara gidan aiki to akwai Gidan da suke son Masu aiki a rijiyar zaki sena kaiki"
Godiya sukai wa matar Suka kama Hajiya suka fita suka shiga napep har Gida matar ta rakasu wadda tace Sunanta Hadiza Gudun magana yasa Sa'adah ta dakatar da Hadiza a waje Bayan sun kai Hajiya Gida Ta fito tabar Ummi tare da Hajiya.

Tafiya sukai Hadiza tana cewa sa'ada ashema basu da Nisa Har Suka tsallaka Titi wani katafaran Gida suka Shiga mai gadi ya buɗe Musu Ƙofa Yana tsokanar Hadiza A wani ƙaton falo suka zauna seda Suka jima a zaune sannan matar Gidan ta fito Sa'ada tabi matar da kallo wadda take ma sha Allah ƙatuwa da ƙyar take tafiya sabida Jikin da Allah ya bata gata baƙa Ƙirin se Uban ƙaton Hanci a ɗage take kallon su Kafin ta zauna da ƙyar aikuwa seda Kujerar ta Loɓa sabida Ƙibarta.

"Hadiza se yau kika ga damar kawo Mini mai aikin gashi jibi zan bar ƙasar?" Hadiza ta fara fadanci tana ƙasa da kai tana cewa.
"Tuba nake uwar ɗakina Ƴammatan ne sunyi wahala"
Se Lokacin Sa'ada ta gaishe da matar wadda ta zuba mata idanu na wasu Lokuta kafin ta kalli Hadiza tana ce mata "Badai wannan yarinyar kika kawon na É—auka aiki ba?" Hadiza ta sosa kanta.
"Eh ita ce Hajiya anan ma Kusan ku take"
Dariyar yaƙe matar tayi tare da cewa "Ina Hadiza bazan iya ɗaukar wannan yarinya ba ai seta ƙwacen Mijina Gaskiya kuma fita dan Lokacin dawowar shi ya kusa"

Sa'ada ta matsa Jikin Matar ta kama ƙafafunta "Dan Allah Kimin alfarma Nai kona wata ne Mamana zan samawa Kuɗin magani"
Cikin rashin Imani irin na wasu masu haunu da shunin matar taja tsaki tana cewa "Dallah Ku fita bazan ɗauki jaraba da kuɗina ba wannan kyan naki na halaka ai sena Halaka kaina na ɗaukeki" Daga haka ta tashi tabar su a falon Hadiza ta kama Hannun Sa'a suka bar Falon Har suka Fita titi Sa'ada na kuka Hadiza tayi Matiƙar tausayawa Sa'ada sabida haka rarrashinta tayi tare da bata tabbacin zata cigita mata wani Gidan aikin In sha Allahu har naira ɗari Biyu ta bawa sa'ada wadda ta damƙe Kuɗin tayi Gida Koda taje babu yadda Hajiya take Sabida haka hankalinta ƙara tashi yayi Fiye dana farko Saka Hajiya tai a gaba tana Kuka wajan La'asar Aunty Murja ta kawo Musu abinci da Kuɗi tace Inji Mijinta Da murna sa'ada ta Ɗauki naira dubu Biyun Da Mijin Aunty Murjar ya aiko Musu dashi ta fita wajan siyo wa Hajiya magani wani ƙaton Chemist ta je a bakin Titi ta bashi katin tare da Kuɗin ya zuba mata ido kamar maye mai chemist Ɗin kenan, Bayan ya karanta.

"Baby ai kuÉ—in ki Dubu ashiri ne ba Biyu ba"
Sa'adatu taji wani iri da sunan daya gaya mata amman seta danne tace "I in kana bada bashi ka bani In sha Allahu wannan watan In yazo ƙarshe sena baka kuɗin"
Yayi wata Æ´ar iskar dariya tare da cewa.
"Haba Baby kina da kaddarar da bama sekin Biya kuɗi ba kawai Ki zo na Rungumeki na taɓa Miki Ƙirjinnan naki da yake shaƙe da dukiya sena baki maganin kyauta kefa mai kyau ce Nai mamakin ma da kuɗin magani ya gagare ki bayan Kina da Dukiya a jikinki"
Sa'ada ta maka mai wata banzar harara ta warci Katin taja tsaki tabar Chemist Ɗin tana ala wadai da halin wasu mazan, Rasa ina zata sa kanta tayi tana jin Allah kada yasa tai saɓon sa akan samarwa Hajiya lafiya Gungun wasu mata ta gani suna doso Hanyar data tsaya da alamun almajirai ne Dab da ita suka zo suna tafiya suna faɗin Irin Kuɗin sadakar da suka samu a wani Gida se maganar ta fisgi hankalinta har sun ƙulewa ganinta seta Bisu tana kiran "Bayin Allah ku tsaya" mace ɗaya ce tsaya sauran ko sukai tafiyar su sa'ada tana Ƙifta ido tana haki tace wa matar "Naji kuna maganar Gidan sadaka dan Allah ina ne nima naje Ko zan samu?" matar badan ta yarda da sa'adah na Buƙatar taimako ba sabida Yanayin Jikinta amman haka tai mata kwatancen Gidan anan kankare Sa'ada tai mata Godiya aiko da sauri ta Koma Gida suka gyara Hajiya Lokacin Magariba ta kawo kai abincin da Aunty Murja ta aiko musu dashi suka ci wanda Ummi ke sheda mata Saƙon Aunty murja na cewa kullum zata ke aiko Musu da abinci dafaffe Inji Mijinta Godiya tai Duk hankalinta yana ga zuwa Gidan sadakar Bayani taiwa Ummi lokacin data ke Mayar da Hijabinta.
"Wai kina nufin sake fita zaki Sa'adah ki huta mana tunda Hajiyar ma ta samu bacci" cewar Ummi a galabaice tace wa Ummi "Bani da Nutsuwa Ummi barni naje ina da tabbacin nasara da yardar Allah" Ummi tashi tsaye itama tayi "Gaskiya bazan bari ki fita ke ɗaya ba Yadda duniya ta lalace" Se Lokacin Maganar mai chemist Ɗinnan ta faɗowa sa'ada ta soma gayawa Ummi tana dariya Rufo ƙofar sukai kamar yadda suka saba suka fita daga Gidan Suna Jin Umma na shewa tana aibata su titi suka Nufa suka sami abin hawa aiko tiryan tiryan sa'adah ta gane kwatancen Gidan ƙato ne ga mata nan Birjik Sunbi layi suma layin suka bi Ana kiran sallar magariba layin yazo kansu Sedai abin mamaki Mai gadin seya Nuna sa'ada yace Ita zata shiga Ciki Ummi Kuma ta tsaya a waje Da ummi zatai magana ganin babu wanda akai wa haka sesu sa'adatu ta dakatar da ita ta shiga Gidan Mai gadin yay mata jagoranci har zuwa babban falon gidan daga nan yayi Mata sallama ya fita a ƙasan carpet ta zauna ta tsure tana raba ido ƙaton Mutum ne baƙi mai ƙaton Tumbi ya fito da jallabiya ajikin sa Ya zauna sa'adah tana gaishe dashi.
"Ƴammata meke tafe dake?"
Tiryan tiryan ta gaya masa matsalar ta Yayi Murmushi tare da Miƙewa tsaye "Biyoni ki amsa Allah ya bata lafiya" Jikin sa'adah na mugun rawa tabi bayan shi Ƙofar wani ɗaki ne a buɗe Kamar an jata haka ta faɗa Cikin Ɗakin aiko tana shiga Mutumin ya kashe hasken ɗakin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.