Tsofaffin Hausa Novels

Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt

Chapter 29 of 31

Lokacin Umma tana Girki a tsakar Gida ta dubi yaron tana cewa.
"Kai koma dai ka ƙara tambaya zubaida ko zainura Ko jamila dai Ko?"
Yaron yace "A,a saadatu aka ce Inji wani mai Mota" saadah naji taja mayafinta ta fito hannunta riƙe da tabarma.

Ta gaban Umma ta wuce wadda tabi saadah da kallo bakinta a sake yaushe tai sake har aka fara sallama da su saadatu.

Cikin wata salon tafiya take ƙarasawa wajanshi da ike akwai hasken wutar Nepa yana kallonta shi kuma yana Jingine a jikin Motar shi Bakin shi cike da far'a wadda bai taɓa irin taba.

"Mamina kinyi kyau ma sha Allah"
Ya faɗa sanda ta ƙaraso wajan shi rufe Fuska tayi da hannayenta tana Murmushi.
Ya sa wayarshi yana haska fuskarta.
"Yanzu wannan adon duk Ni kaÉ—ai gaskiya sai na bada Tukwici"
Dariya tai kaɗan tana Nufar Ƙofar Gidan Aunty Murja ta shinfiɗa masa tabarmar a saman dakalin Gidan.

A hankali tazo gabanshi tace masa.
"Ka ƙaraso ka zauna"
Yabi bayanta suna tafe kamar ango da amarya.
Zama sukai a tare ta gaishe dashi daga nan shuru ne ya biyo baya sabida babu wanda ya taɓa Hira acikinsu Kowa wannan Ne karon shi na farko.

Shine ya katse shurun ta hanyar Cewa.
"Kamar yadda zan ce Miki Sunana ANWAR SULE KURFI mu Æ´an katsina ne zama ya kawo Mu nan Nine babba wajan babana Nike jan ragamar kamfaninshi Bani da mata shekarata arba'in da É—ori ina fatan zaki aure ni nan bada Jimawa ba nake son ki kasance matata"
Ya faɗa yana kallonta Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta.
"To Allah ya zaɓa mana mafi alkairi"
Da sauri yace.
"Amin kina sona?"
Ta Ɓoye Fuskarta a tafin hannunta kafin ta ɗaga kanta alamun Eh.
Kamar an Fisgi maganar daga bakinta tace.
"Ina mamanku?"
Shuru yayi kamar baze magana ba can yace mata.
"Tashi na rakaki gida amaryata"
Shikenan har angama Hirar ta faɗa a ranta har bakin Ƙofar Gida ya kaita ya damƙa mata Kuɗi masu yawa a hannunta yace suyi amfani dasu sallama sukai ya tafi.

A guje zubaida ta faɗa ɗakin Umma tana Kuka tare da cewa "Wallahi Umma shine yazo wajanta Umma ina sonshi Ki taimake ni Umma Irin kalar Mijin dana ke so ne" Umma ta tallafi Haɓarta Tun ranar da Zubaida taga wannan Mutumi wanda yazo wajan sa'a bata ƙara Nutsuwa ba yau Umma taga abin da yafi ƙarfinta dan zubaida haukace mata tai da Koke Koke Da ƙyar ta samu ta rarrasheta tai Shuru Umma ta faɗa nazarin ta ina zata fara.

Cikin satin wata irin shaƙuwa ta shiga tsakanin Anwar da Sa'adah Kullum sai yazo wajanta Baffa daya ga Anwar Da zai soma tijara Tunda Anwar yazo ya gaidashi ya bashi Kuɗi shikenan Baffa yay Muƙus Su Saadah rayuwa ta sauya sabida Anwar Ya tsaya Musu a satin dayay yana zuwa daidai da Suttura sai da ya ɗaukesu ita Ummi suka je suka Zaɓo kaya masu yawa Ya kaisu wajan Ɗinki yasai Musu kayan abinci Mai yawa Haka zalika yace wa Baffa yana son ai gyaran Gidan kafin Biki Baffa Ba shiri ya amince sabida a wannan Lokacin Umma ma ta kasa gano kan baffa sabida Kuɗi.

Satin daya kama na sama aka Gyare Gidansu saadah tas har kayan É—aki aka sauya Musu wanda Umma ma taci albarkaci dan hatta Solar mai 24 hours aka saka Musu Kuma cikin satin malam ya gama Binciken shi an tabbatar da saadah bata da wata Illah sabida haka Malam ya kira Abba wanda bai musu ba daya ji maganar yay fatan alkairi Tare da cewa malam ai shine Uban ango ba shiba sabida haka shi Gudun mawa ce tasa cikin satin da malam da wasu daga Cikin Æ´an uwa suka kai KuÉ—i da sa rana wata Guda Gidansu Saadah.

Hajiya tana daga kwance amman Kukan farin ciki take haka zalika Kamalu daya kasa zaune ya kasa tsaye tunda aka kawo Kuɗin Sa'adah ya ke fitar da kuɗi yana basu Suna shiga kasuwa sabida yanzu babu laifi kamalu yana Jin ƙansu sosai ba kamar da ba Anwar yace baya Buƙatar Komai daga garesu amman kamalu yace ba za'ai haka ba ko yaya gwara An kaita da abin da Sukai mata Shirye shiryen biki Kota ina Ya kankama daga gidansu Anwar Innah nata shirin Haɗa lefe ita dasu Safiya waɗanda Suke ta ɗaukin Bikin sabida rabon su da biki Tun na Ya Khalid wanda kusan shekara takwas da auren matar shice tazo haihuwa ta rasu tun daga sannan bai ƙara aure ba Ko zancen auren ma baya so shiyasa ba kowa ne ma yasan ya taɓa aure ba.

Aunty Murja ita ta tsaya wajan gyara saadah Kullum tana gidanta tana gyarata da magungunan sanyi masu Inganci wanda BINTU SPARE AND MORE +234 706 733 8694, ta ke saida wa,dan sai da suka gama dana sanyi sannan Aunty Murja ta kuma siyo mata na gyaran Ciki duk a wajan BINTU SPARE AND MORE ɗin dai dake garin kanon dabo mandawari titin na goda magungunan masu Inganci ne dan gaba ɗaya da saadah na amfani dasu saida ta sauya dan sai hanata ma Ƙebewa da Anwar Aunty Murja tayi sabida sai a samu matsala sai da yay ta naci Aunty Murja ta yarda yake zuwa da yamma.

Biki ya rage sati Guda aka kawo Lefe wanda Ya girgiza jama'ar Unguwa Umma kam ƙaramin hauka ta Dinga yi sabida ruɗewa Ƴaƴanta Kuwa babu wanda ya iya fitowa waje sabida baƙin ciki.

Saura Kwana Uku Biki saadah tai Ƙunshi tai gyaran gashi kana kallonta kaga amarya haka zalika Ummi itama tai Shirin biki ga gida ya soma haɗuwa da ƴan uwa dan danginsu na ƙauye ƴan uwan mahaifinsu sun zo Sun cika gida ana ta sabga.

Saura kwana Biyu É—aurin aure Lokacin katin É—aurin aure ya zaga ko ina daga cikin inda ya zaga harda kamfanin Su Anwar wanda ya sami Isa wajan Alhaji jamilu kuma a ranar ne Mama tasan da maganar auren Anwar itama ta hanyar ganin katinan É—aurin aure a Falon Abba.

Ta shiga damuwa sosai amman bata nuna ba sai ɓige da kukan abba ya nuna mata ba ita ta haifi Anwar ba tunda har zai Nemi aure a kasa gaya mata a fili ta faɗi hakan amman a zuci ba haka bane Kukan baƙin cikin Auren ne fal aranta.
"Nima ɗan gayyane Shafa'atu su baraka ne suke Biki ke kuma naga kin gama Hidimar Suna ai bazan takuraki ba" Cewar Abba tambayar shi ta shigayi a ina Yarinyar take yace shi ina ze sani tunda Ba shiga sabgar auren yake yiba Mama a Ƙufule ta tashi ta nufi part Ɗinta tana zama a falonta Alhaji Jamilu yayanta ya shigo a haukace da katin ɗaurin auren a hannunshi.

"Shafa ta yaya Mukai sake har wannan yaron zai aure nan da kwana Biyu bamu sani ba ya zama Dole Mu lalalata wannan aure"
Mama tai Murmushin takaici.
"Yaya ina son a yau ba se gobe ba Ka nemo mana gidansu wannan yarinya Ko ta yaya a fasa auren nan da ita a ɗaura da Hanan sabida In ƴata ce agidan Ko ta yayane dai Dukiyar tamu ce Koda Mutuwa yayi Muna da kaso mai yawa saɓanin wata can taci sabida nasan in muka raba auren nashi da ita yadda Mahaifin shi ya saɓa gayya cewa zeyi a ɗaura da Hanan tunda yasan tana son Anwar ɗin tunda ga yadda lamarin yazo Na aje makamin Rai na koma na son tabbatuwar aure sabida da arziƙi a garin wasu gwara a namu garin"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.