Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 5 of 31
Almajirin Aunty murja yayi sallama Cikin Gidan Mijinta yana tsakar Gida yana Alwala Almajirin yace ana sallama Gaban Aunty Murja ya faÉ—i sanin halin Mijinta mafaÉ—aci ne sedai Kuma In ka fahimtar dashi abu yana da saurin fahimtar ka.
Ta shiga damuwa Na yadda bata gaya masa Abin da ya danganci su sa'adah ba kuma tasan ta yuwu wannan Baffan nasu ne yazo wajan Mijin nata Har almajirinta yayi mata sallama tana tsaye Ganin dai Wannan tsaiwar ba zata fusheta ba yasa ta koma falon ta tana addu'ar Allah yasa kada Baffan su Sa'adatu yay nasara akan Mijinta.
Mijin Aunty Murja ya ƙarasa wajan Baffa dake tsaye Suka gaisa kamar abin arziƙi.
"Dama na kawo maka ƙarar matarka ne"
Mijin Aunty Murja ya cika da mamaki sanin matar shi bata ma shige shigen maƙota kuma ba'a taɓa kawo masa ƙararta ba suna zaune lafiya kusan Shekara Biyar Haihuwa ce kaɗai Allah bai basu ba.
"Ina jinka wani abun tayi maka Allah ya baka haƙuri amman nayi mamaki da kace ƙarar matata ka kawo Mini"
Baffa ya ce.
"Ƙwarai matarka data ke shiga Gidana wajan Ƴammatan data gani aciki to ba ƴaƴana bane, Yara ne ƴan iska Ni kaina sun isheni ga baƙin Jini kwanaki a masallacin Juma'a har sadakar su na cigiya ba'a samu wanda ya taya ba to babu matarka babu su yau naga har abinci takai Masu ƴaƴa ne Marasa kunya sun isheni sun ishi rayuwata duk yadda zan kwatanta maka halin yarannan ba zaka fahimta ba amman dai nina san ba ƴaƴan arziƙi bane ba"
Mijin Aunty Murja yaji ransa ya ɓaci Amman bai nuna wa baffa ba yace.
"To in sha Allahu zanyi Mata magana kayi haƙuri ba zata kuma shiga ba In banda abin Murja babu mai son hurlɗa da ɗan iska"
Baffa yayi masa sallama ya tafi dama da ire iren waɗannan zantukan Baffa yabi ya ɓata su Sa'adah a layin Shiyasa kowa yake Musu kallon baibai se wanda Allah yasa yasan halin da suke ciki ne yake Musu Uziri.
Mijin Aunty Murja ya shiga gidan kallo É—aya tai masa tasha Jinin Jikinta.
Seda suka Nutsu a falo Sannan ya dube ta.
"Mai ya haÉ—aki da Æ´ammatan can Gidan Kina kallon Baffan suma yana kuka da halin su bare ke ina ruwan ki dasu har Kike basu abinci ba tare da sanina ba to ni ina rayuwata Cikin Rufin asiri ba zaki ja min surutun layi ba"
Murmushi Aunty Murja tayi tare da tsira masa idanu har ya gama maganganun sa cikin faÉ—a.
"Wallahi Allah Bai gaya maka gaskiya ba Nima ada yadda ya gaya maka haka nake Musu kallo sabida Ina jin yadda ake yi dasu Inna je Kitso can Gidan se yau da Babbar ta fito tana Kukan neman agaji akan Yayanta yana Dukan ƙanwarta shine na shiga Abun babu daɗin faɗi rayuwar yaran abin tausayi ce nai kuka ba ɗan kaɗan ba dama jira nake kazo mu san abin yi"
Ya fuskanci matar tashi tiryan tiryan ta shiga gaya masa halin data ga su sa'ada aciki sanin wacece matar shi yasa bai musalta mata ba amman seya Kalleta da kulawa yace.
"To ta yaya kike ganin zamu tallafa Musu sabida Mutum mai sharri abin tsoro ne na fahimci kamar da baki suke aibata yaran"
Aunty Murja ta jinjina kai tare da cewa.
"Dama shine matsalar Amman kayi shawara se Muga wani taimako zamu basu wanda zai Riƙe su dan ina gudun kada babu tasa su fara harkar banza Tunda babu laifi yaran suna da kamun kansu daidai misali"
Ce mata yayi zeyi shawara abin da ya yanke ze sanar da ita da haka suka shiga wata Hirar ta daban.
Jikin Hajiya ne ya rikice ta dinga wasu irin surutai tana zubar da Miyau abin daya ɗaga wa su Sa'adatu hankali kenan ga maganin Hajiya ya ƙare dama wani bin Ciwon nata kamar shigar Jinnu yake amman dai Likitan ta ya shaida masu wani bin masu lalurar suna haka, ga Hajiya babu baki bare tace ga inda ke mata ciwo yadda suka ga dare haka suka ga rana da sassafe Sa'adatu taje shagon kamalu babban yayan su don ta sheda masa ga halin da Hajiya take ciki dan yazo Ko zasu kaita asibiti Abin mamaki dubu ya cillo mata yace suyi kuɗin Mota shi bashi da kuɗi ta sunkuya ta ɗauka bata koma gida ba titi taje ta kira mai napep Ita da Ummi suka tallafo Hajiya zuwa napep Ɗin Direct asibitin Murtala suka wuce da ita Koda mai napep ɗin ya sauke su bai karɓi kuɗin suba yace su barshi sukai yi masa Godiya suka kama Hajiya zuwa CIkin asibitin in da suka zauna Zaman Jiran yankar katin ganin Likita Koda layi yazo kansu Sun sami nasarar Ganin Likitan masifa yahau yi Musu akan sakacin da sukai Har Jinin Hajiyar tasu yakai Maƙurar hawa Ita dai Sa'adatu Haƙuri take bawa Likitan magani ya rubuta Musu Tare dayi Musu Gargaɗin lallai su Nemo shi su bata sabida Komai yana iya faruwa Jikin sa'adah har rawa yake bayan sun fito tana tafe tana haɗawa da Gudu zuwa pharmacy dan ta siyo maganin Da dubu ɗayan hannunta gani take In bata sai maganin ba Hajiya ƙila ma ta Mutu...........Autar manya 09022260850
*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*
*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*
*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*
_A WANI ÆANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAÆŠANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ÆANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ÆŠANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAÆŠIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*
*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*
*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAÆŠANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ÆŠAIÆŠAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAÆŠANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO
*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
    Â
     *NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
           *005*
Sedai ƙafafun ta sun sage ne Lokacin data ji Zunzurutun Kuɗin maganin Yawu ta haɗiya muƙut tana share Gumin Fuskarta duk da akwai sanyin Safiya iska tana kaɗawa Amman Hakan bai hana Gumi ya wanke sa'ada ba Ta ina zasu sami Kuɗin maganin Hajiya wanda ayau jikin nata yakai maƙurar wajan rikicewa Zaman dirshan sa'adah tayi tana Rusa kuka hannunta riƙe da Katin maganin Idanunta yayi jajir Fuskarta ta kumbura sabida Kuka.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.