Yankan Kauna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yankan Kauna By Autar Manya.txt
Chapter 10 of 31
*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
​*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
    Â
     *NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
           *008*
ƙirjinsa ne ya soma ciwo ga wani irin zafi da yake yi masa tun yana iya Numfashi har fitar Numfashin Nasa ma tazo ta gagara a hankali Numfashin sa yake ɗauke wa kafin ya faɗo daga saman gadon tim baya Numfashi A wannan Lokacin bashi da Bambanci da gawa dama haka Yake yi Duk Lokacin da Ciwon zuciyar sa ya tayar masa wani irin baƙin Gudan Jinine ke fitowa daga cikin Hancin sa Adaidai wannan Lokacin Khalid ya shigo Gidan dawowar shi daga Office kenan kasancewar yana ɗaya daga cikin masu kula da Branch ɗin Alhaji dake kasuwar sabon gari Har Khalid zai shiga Part Ɗinsu wajan Innah domin yace tayi Musu Dambu kafin su dawo sanin Anwar Yana masifar son Dambun Shinkafa seya fasa ya tsaya a compound ɗin gidan tare da Fito da wayar shi yana kiran Number Ɗin Anwar wanda seda Khalid yayi masa Five Misscalls amman Anwar bai ɗauka ba A fili Khalid yaja tsaki tare da shafa sumar kanshi yana cewa.
"Wannan Bahagon Mutumin ina ya saka wayar shi Oho! Jin ana kiran sallah Khalid ya Nufi Bakin Jerin famfunan dake Compound yayi alwala ya shiga masallaci Bayan sun idar da sallar ya Nufi Part Ɗin su har ya ƙarasa Falon Innah yana Kiran Numbers ɗin Anwar Amman baki ɗayan su ba'a ɗauka ba zama Khalid yayi Rahma Autar Innah tana Kunna kallo ganin shi ta dakata tana masa sannu da zuwa.
"Ina innah Anwar ya shigo nan kuwa?" Rahma tace "A,a bai zoba Inna kuma tana É—aki tana sallah" Daga haka tabar wajan sanin idan Manyan yayin nasu suna Falon basa zama su aciki.
Khalid se kiran Numbers Ɗin Anwar yake suna shiga amman har Lokacin bai ɗauka ba se duk yaji babu daɗi sabida da zarar sun dawo daga Office to suna tare Muddin ba Ƙasar Anwar ya bari ba, Ko shi in yaje Lagos ko wata jahar kai kaya.
A haka Innah ta fito tana Murmushi "A,a naga Hassan ban ga Hussainin ba ina Muhammad ÆŠin?" Inna ta faÉ—a tana zama a saman Kujera Khalid cikin rashin walwala yace mata "Tunda nazo nake Neman Layi kanshi amman bai É—auka ba Duk hankalina ya tashi Innah Ina Malam?" Innah ta ÆŠan sauya fuska cikin halin damuwa tace "Malam yana É—akin sa yana karatun alkur'ani wai nan Saifullahi ko Fatihu yake Jira su dawo daga shago su kaishi Aski amman ya kamata ka binciki halin da Anwar yake ciki sabida kasan yana da matsala wadda bama fatan tashin ta"
Khalid tashi yayi tsaye tare da cewa inna bara ya leƙa part Ɗin Anwar ɗin Ko yana ciki Cikin sanyin Jiki Innah tace "To Allah yasa dai lafiya Kona Biyoka?" Khalid ya ɗan kalleta sanin matsayin Anwar a wajanta Ko shi data Haifa bata Nuna masa Soyayya kamar wadda take nuna wa Anwar "Inna ta Anwar Ki kwantar da hankalin ki Innah bari naje yanzu zan dawo" Inna har bakin Ƙofa ta bi Khalid wanda seda taga ya nufi part Ɗin Anwar Sannan ta koma ciki Khalid yana Jan Handle ɗin Ƙofar Bedroom ɗin Anwar yaji ta buɗe ya shiga ciki ɗakin akwai Duhu sosai wayar shi yasan ya ya lalubi swich ɗin ɗakin haske ya bayyana tarwai wanda Idanun Khalid suka ci karo da Anwar a ƙasa wanwar kamar gawa da gudu Khalid ya saki wayar ya nufi wajan shi gaba ɗaya ya tattaro Shi Jikinsa yana Jijjigashi "Anwar! Anwar tashi mana yaushe Ka faɗi ciwon kane ya tashi garin yaya?" Duk Khalid ya shiga jera tambayar kamar Anwar yana Jinsa bayan shi tuni yayi nisa acikin suman da yayi.
Da sauri Kuma Khalid ya ɗauki wayar shi Allah yasa bata tarwatse ba ya shiga Kiran Doctor wanda shike Duba Anwar Idan ciwon shi ya tashi Doctor ya tabbatar wa da Khalid ya bashi Minti Goma sabida yana kusa dasu ne Gidan shi Khalid ya kashe wayar ya janyo Anwar saman Jikinshi gaba ɗaya Hankalin Khalid a tashe yake A haka Doctor Yazo ya same su wanda Shigowar Doctor ce ta fargar da Ma'aikatan Gidan Sanin Halin da Anwar yake ciki sabida Kowa yasan in kaga Doctor yazo Gidan to ciwon Anwar ne ya tashi Ma'aikatan gidan Sune Suka sanar da Mama abin da yake faruwa da sauri ta zari mayafi Jikinta har rawa yake ta nufi Part Ɗin Anwar Sedai koda ta ƙarasa Khalid ne a bakin Ƙofar gadan gadan ta nufi Buɗe Ƙofar Khalid ya hanata ta hanyar zira key.
"Marar kunya tsohon munafuki ka barni na wuce naga halin da yake ciki kodan bani ce na haife shiba in uwar shice Ni zaka Hanani shiga ne?"
Khalid ya kawar da kanshi bai tanka wa Mama ba wadda hakan ya ƙara fusata ta seta hau masifa Khalid yayi mata banza har Doctor ya fito yana yarfe zufa hannun shi da kayan aikin shi mama bata daina masifar da take yiba seda Doctor yayi gyaran murya kafin ya kalleta "Hajiya kamata yayi Ki fita sabida Maganar ki zata iya Janyo masa matsala" mama tahau Sosa kai tana cewa Doctor "To ai abinne da ciwo Ƙiri ƙiri nazo zanga halin da yake ciki wannan Munafukin ya hanani sabida Ni ba uwar shi bace ba to duk dai tsiya ba ku isa kun raɓa alaƙar ƴaƴana dashi ba" Likita ya mayar da hankali wajan Khalid yana bashi takardar magani tare da yi masa gargaɗin kula da lafiya Anwar sabida zuciyar shi tana cikin hatsari.
Khalid ya amsa Still Rufe ƙofar ya kuma yi yabi bayan doctor yabar Mama a tsaye cike da mamaki Haka halin Khalid yake Shi baya son Ƙunbiya Ƙunbiya yadda Halin Anwar yake haka halin shi yake shine ma yasa zaman su yazo daidai bambancin su kaɗai Anwar baya da yawan Magana Kuma yana da Miskilanci saɓanin Khalid mai Yawan magana da son shiga hurɗar Jama'a.
Khalid bai gigin shedawa innah ba ya shiga Mota ya nufi pharmacy ya siyo maganin da Doctor ya rubuta tare da yi masa takeaway ya dawo Gida har Lokacin Anwar yana bacci sabida alluran da Doctor yayi mishi A gefen shi Khalid ya zauna yana jiran ya tashi Har bayan Isha a lokacin Kiran Innah ya shigo wayar shi tashi yayi ya fita a wannan Lokacin bai Rufe Ƙofar ba yabar ta a buɗe ya nufi part Ɗin su.
Tun daga Ƙofar falo Mama take bambamin bala'i "Sabida bani na haifi Anwar ba yasa ake nunan fifiko akan shi fisabilillahi mai nake wa Anwar da har Khalid zai hanani ganin shi?"
Khairat ce ta tintsire da dariya har tana bugewa da Kujera "Kema mama mai ya kaiki Ni wallahi ban ga amfanin baka son Mutum ba kuma ka dinga Nuna wa kana son shi a gaban idanun shi Tunda bakya Son Ya Anwar why note ba zaki Nuna masa zahirin Ƙiyayyar da kike masa ba seki dinga pretending Kina son shi a gaban idanun shi To ina zaton Sun gane ki"
Ihsan ma dariya take Yi jin maganar da Khairat tayi a daidai wannan Lokacin kuma Hanan ta fito daga Bedroom Ɗinta Babbar Yarinyar Mama ce tuni ta kammala degree ɗinta Hanan tana masifar Son Anwar duk da Mama bata son Anwar ko kaɗan Hanan agolar mama ce data zo da ita gidan su Anwar saɓanin Husna da Khairat da Ihsan da suke Ƴaƴan Mama acikin Gidan su Anwar dan mama bata da ɗa namiji matanta Uku a gidan har Hanan Huɗu kenan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.