Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 8 of 26
*page 15-16*
An kasafta gidan su Ibrahim an fidda mai b'angaran sa, d'akuna takwas da ke cikin gidan ya zama guda hud'u nashi guda hud'u na Muktar amma kasancewar Baba na zaune a d'aya, Jabir d'aya, kuma cikin rabon Muktar na sun ya ke ya sa ya zama biyu ya ragewa Muktar duk su ka kwashe kayansu su ka had'e a d'akuna biyu,Wannan dalilin ya sa Sakeena ta fara magantuwa da k'unci ta ke k'orafin tunda dai Amarya za'a kawo ai ita d'aki biyu ma ko uki sun ishe ta,ita dai gaskiya an shiga hakkinta,duk surutun da ta ke yaya Muktar bai kulata ba.
Kud'in da ke hannun Ibrahim da kud'in filinsa da ya siyar ya bashi damar sauke duk d'akunan na sa da yankin tsakar gidan da aka fitar masa ya shaci gini lafiyayye, a kai mai tsarin gini na zamani,falo babba da d'akuna biyu sai kitchen da band'aki duk cikin falon sannan d'an k'aramin tsakar gida a ka fitar da k'ofa zuwa tsakar gidansu yaya Muktar. Wata biyu a ka d'auka wajan ginin don a sannu ake yin komai,kafin me lafiyayyan waje ya fito ya yi fes da shi, har tsakar gidan su Sakeena a ka gyara zuwa k'ofar gida.
A b'angare guda kuwa Hajiya Uwa wata uwar d'akin Ibrahim ce kuma y'ar uwar mahaifiyarsa ce,harkar saida kayan sawa ta ke,su na shiri sosai da shi don shi ke d'inka ma ta kayan saidawar ta,Ita ya d'ora kan had'a lefe,komai ita ya ke bawa ta na siyo mai,kasancewar ta wayayyiyar mace kuma tsohuwar y'ar kasuwa ya sa ta ke siyo mai kaya na d'aukan magana.
**************
Wata k'awar Maman su Su'ada principal a makarantar emmata ta karb'i takardun Su'ada ta samo mata teaching,kai tsaye Ibrahim ya amince mata a lokacin da ta sanar dashi,kuma ya bita da addu'ar alkairi, cikin d'an lokaci ta fara koyarwa a secondary d'in.
A bangare guda kuwa lokacin bikin su sai k'ara k'aratowa ya ke an cinye watanni yanzu har ya rage sati biyar.
Dukkan abunda a ke buk'ata a lefe an gama had'awa, Hajiya Uwa tai wa Ibrahim namijin k'ok'ari don ta had'a mishi komai ba raini.Yaya Muktar shi ya siya mai akwatina set guda 6 peaces kamar yanda yai alk'awari.
Ranar a ka kawo kayan gidan su Ibrahim don y'an uwa su gani kafin a kai.
Ranar Hassada ta biyu ta fara kama Sakeena a kan Su'ada, ta gama hassadar ginin da a kai mata sannan ta zo hassadar ganin irin kayan da a ka had'a mata. Cikin mutane ta na ta murna kamar me,amma da ta shiga d'aki ji tai kamar ta zubda hawaye don takaici.
Da dare bayan Ibrahim ya dawo ta ke tsokanar sa cikin barkwanci da ga nan ta soko mai a bunda ke ranta "Ibrahim wannan kaya haka na ce anya kuwa ba a yi k'arya ba wajan had'a su,ina ganin kamar ka k'are k'arfin ka a lefan nan,Allah ya sa ma dai Hajiya Uwa ba ta had'a ma harda bashi ba duk da na ji Zakiyya ta na cewa komai kud'i ka ke badawa a siyo ma."
Cikin mamaki ya ke kallon ta,can ya ce" Maman Abba me ye abun k'arya cikin wannan kayan? Akwati shida shi ne k'aryar?lalle don bi ki san wace Su'ada ba shi yasa har ki ke zaton an yi k'arya wajan had'a mata wannan kayan. To kin san me?cikin kayan nan babu a bunda ya ke bak'on ta,duk ta saba amfani da irin su har ma na sama da su.wannan kayan ba komai bane wlh don da ina da kud'i Su'ada ta fi k'arfin wannan kayan zan ninninka mata su."
Cikin takaici da mutuwar jiki Sakeena ta ce" A'a wai daman ba haka na ke nufi ba,ina ganin wai kamar rayuwar ka San canji canji ce, da ka tattala kud'in hannun ka kwa siyi kayan abinci,ka ga kar da ga zuwan amarya a fara k'a k'a k'ara k'ak'a."
Zuwa yanzu kuma Sakeena ta k'ular da Ibrahim don haka a d'an fusace ya ce "Allah ba zai hanani a bunda zan yi wa Su'ada hidima da shi ba, da ga zuwan ta ba zan rasa a bunda zan bata ta ci ba."
Mik'ewa yai ya na shigewa d'akin su.
Ita kam Sakeena tagumi tai ta na nazarin wai wace ce wannan Su'ada haka da aka cikawa mutane kunne da ita,y'ar uban waye da za'a ce ta fi k'arfin ma Wannan uban kayan in dai ba rainin wayo ba.

Washe gari a ka kai lefe gidansu Su'ada, koya ya yaba da kaya kuma ya yi ala san barka.
Su'ada kanta ba tai zaton wannan kayan haka ba,dalili ta san Ibrahim ba shi k'arfi ga hidimar ginin wajan zama da ya yi don ya mata hoton wajan ta gani an kashe kud'i sosai.
Ai kuwa da dare ta kirashi ta na mai Addu'a Allah ya k'ara bud'i da arzik'i,shima cikin jin dad'in addu'ar ta ya shiga jera mata sa albarka da fatan ta zama uwar gidansa har aljanna.
**********
Saura kwana uku a fara Biki a ka je jere, Mata da ba'a raba su da abun fad'a tun da ga k'ofar gida wasu su ka fara gunagunin wajan zaman Su'ada, wai an kawota gidan gargajiya gidan dangin miji,yarinya ta taso cikin gata amma ammata aure da telan mata,daman ai sai dai zaman hak'uri ba wai na nishad'i ba.
Wasu da suka ga yanda aka tsara gini a part d'in na ta sai su kai shiru,don ko tayil bango da bango ne,ko ina na wajan layil ne,falonta k'ato da d'akunan ta biyu manya ba inda ba'a cika mata da kaya ba, kayan d'aki set biyu a kai mata ga Rolay chair's d'in ta manya manya, sun cika falon, kayan wuta babu abun buk'atar da babu,kama da ga kayan kallo na zamani firji zuwa kayan amfanin wuta na kitchen, ko ina na kitchen d'in ta an cika shi da kaya,sauran ma d'aki aka sa mata cikin sif don sun yi yawa.
Sakeena fa tun da ta ga an fara shigo da wannan uban kaya zuciyar ta ta fara bugawa,ciwon da bai da magani ya taso mata wato ciwon hassada.kyashi da bak'in ciki su ka turnik'e ta,yak'e wanda ya fi kuka ciwo ta fara yi,tun bayan da su ka gaisa da y'an kafin ta shige d'aki ta na ta k'unci,tana tunanin yanzu haka zata zauna da FACALA wadda ta fita komai?.
_____________
An kama biki ganga ganga, Ranar Alhamis a kai kamu da traditional day,Ranar Juma'a a kai party cikin gidan zoo don nan k'arfin sa ya ke,Ranar Asabar Maman su tai yinin ta,Sai Ranar lahadi a ka d'aura aure da misalin k'arfe sha d'aya na safe.
Tun da a ka d'aura auren nan Su'ada ta fara kuka don yanzu kam ta tabbatar barin gida ya zo,duk yanda k'awayen ta ke tsokanarta ta zama ta Khaleelee ba ta saurare su ba.ganin kukan ya yi yawa ya sa wata k'anwar mahaifinta ta jata d'aki tai ta rarrashin ta da mata nasiha,Sai a sannan ta samu kukan ya tsagaita, ta ce ta k'ara gyara fuskarta don angwaye za su shigo a yi hotuna.
K'awarta Khairi ce ta k'ara gyara mata kwalliyar ta sannan ta sake mata d'aurin da d'an kwalin Shaddar da ke jikin ta.
Dummmm ta ji gabanta ya fad'i lokacin da a ka ce ga su Ibrahim sun shigo gaida iyaye,ba ta san dalili ba duk yanda ta kai ga d'okin son ganin wannan ranar amma sai ta ke ta jin fad'uwar gaba tun safe. Cikin kunnanta ta ji muryar Jiddah ba fad'in angwaye sun ce me hoto ba jira su fito a yi.jikin ta ba k'wari ta mik'e rik'e da hannun Khairi da sauran k'awayen su su ka fita cikin gate inda tarin cincirundon abokan Angon su ke.
A hankali ta ji hannunsa cikin nata lokacin da a ka fara sakar musu camera a ka.duk ilahirin jikinta rawa ya ke,mamaki ya kama Ibrahim yanda ya ga ko ido ta kasa d'agawa ta kalleshi.
Rage tsayinsa yai ya na mata magana cikin kunne "Su'ada me ke faruwa ne?wannan fa ranar farin cikin mu ce, nai tunanin ganin ki cikin farin ciki da nishad'i amma sai na ga duk jikin ki ya yi sanyi, ko a kwai matsala ne?"
Ya k'arasa maganar da tambaya, a hankali ta girgiza kai alamar ba wata matsala. "To me ne ne ki kai sanyi da yawa,ko ba ki son a kawo ki gareni yau?"
D'aga kai tai alamar Eh,ai kuwa bai san lokacin da dariyar sa ta bayyana ba,ya k'ara matse hannayen ta cikin na sa,
kallon da ya ga kowa na musu ya sa ya basar kawai.
Haka a ka gama hotunan har su ka tafi Su'ada ba ta bari sun had'a ido da Ibrahim ba duk kuwa da k'ok'arin sa na yin hakan.
Bayan tafiyar su da kamar a wa guda ya yo mata message Wanda ya k'ara kashe mata jiki.
_Matata farin cikina,wannan ranar mu ka dad'e mu na fatan Allah ya nuna mana,yau ga ta ta zo an d'aura mana aure Su'ada ta zama matar Ibrahim amma kuma na kasa ganin farin ciki a idon Su'ada sai Tsoro da fargaba kawai na gani,me ya sa? me ya sa Su'ada fargaba haka?In har a bunda na ke hasashe ne to ki kwantar da hankalin ki,za ki samu mijinki me hak'uri da kauda kai ki shigo gidan auranki cikin farin ciki kinji Matata._
Lumshe ido tai bayan gama karantawar ta na wani tunani cikin ranta. A hankali kuma ta saki k'aramin murmishi.
A gidan su Ibrahim ma yinin biki su ke sha abunsu,don har da y'an DJ su ka d'auko,y'an uwa da abokan arziki su ka rak'ashe.wajan k'arfe biyar su ka taho d'aukan Amarya,in da aka ware mata uku masu karb'ar Amaryar, Hajiya Uwa sai wata Goggo k'anwar Mahaifinsu,da wata yayar mahaifiyar su, Sakeena ta dage itama da ita fa za'a yaya Muktar ya ce mata ta zauna,fit tak'i don ita burinta ta je ta gano gidan su Su'ada.cikin b'acin rai yaya Muktar ya ce "ke wai me ke damunki ne yanzu,nema ki ke ki canja hali,kawai a bunda ki ke so shi za ki yi? In kin zauna har d'akin ki za'a shigo miki da Amaryar."
Ganin abun na neman zama rigima tsakanin ta mijinta ya sa Goggo ta ce "Sakeena ai ke me karb'ar bak'i ce kuma Amaryar ma in ta zo ke zaki tare ta bai kamata ki fita ko ina ba."
Da haka dai ta koma ciki ranta bai so ba,don ta so ganin k'wak'waf.
******
Zuwan dangin Ango ba b'ata lokaci a ka basu amarya,Su'ada kuka y'an uwanta kuka duk sun bawa jama'ar wajan tausayi. Su kuwa abokan Ango da shak'iyanci sai vedio su ke wai za su Nunawa Ango.
*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*
[2/23, 11:53 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.