Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 23 of 26

_*page*_*45-46*

Bayan tafiyar Khaleelee Su'ada taje d'akin mama ta sameta tanaiwa Nusrat shirin bacci. Zama tai gefen gadon tana duban mama.
Bayan ta k'arasa sa mata riga ta kwantar da ita gefe sannan ta dawo da hankalinta ga Su'adan "ya akayi ne Su'ada?"

Gyara zama tai tana kallon maman cikin serious voice ta fara magana"Mama daman wata magana mukai da Abban Nusrat yanzu da yazo,kan batun taron suna ne,hidima ta mai yawa,kuma kinsan har yanzu ba wai gama had'a shagon su kai ba,to shine nace mai kawai ba sai anyi taron suna ba."

Cikin girma da nutsuwa mama tace "Na sani Su'ada, na san halin da mijinki yake ciki don haka nace ki dawo gida,ai bazan rasa me zauna miki ba,kawai dai ban son a k'ara mishi nauyi kan wanda yake kansa yanzu,don haka ki kwantar da hankalinki kinji,komai na taron suna za'a yi,kuma zan fad'a mishi karya kashe naira biyar d'insa,yaji ma da gyaran wajan Neman kud'insa, ni da mahaifinki muna dashi Su'ada to in bamu taimaka muku ba meye amfanin samun namu,kuma kema kullum ina k'ara Jan hankalinki,duk abunda zaki samu ki d'auka keda abun karkashin igiyar aure kuke,don haka karki zauna tara kud'i cikin account mijinki yana cikin matsalar kud'i, ki fiddasu ki bashi ya rink'a hidima dasu,basu da wani amfani bayan wannan."

Gyad'a kai Su'ada tai da fad'in "Mama ba kud'i cikin account d'ina duk na fitar dasu na bashi,dasu ne kuma aka bada kud'in ragunan a darki, sannan mukai siyayyar haihuwa,sauran abunda ke hannuna yanzu dubu goma ne,sune daman zan baki ki Siyo ma yaron rigunan fitar suna."

Cikin jin dad'i mama tace "Masha Allah, haka nake sonki dashi Su'ada, ki zama me tausayin mijinki ako wane lokaci, shima zai zama me tausayinki komai runtsi.

****Bayan fitar Su'ada a d'akin, mama ta tashi zuwa d'akin Abba,anan ta zayyane mai duk yanda sukai da Su'ada, jinjina kai yayi,yana fad'in "To yanzu yanda za'ayi kiyi list na duk abunda kike ganin zaku buk'ata sai ki lissafa kud'in ki fad'a min in baku,kuma insha Allah in na koma zan k'ara turo da kud'i ki bawa Ibrahim d'in ya k'arasa gyaran shagon.
Godiya sosai Mama tai mai,shi yasa a duniya take jin tsananin son mijinta,don Abban su Su'ada yana iya juyewa iyalansa duk abunda ke aljihunsa ya tashi ba ko sisi a jikinsa,shi yasa kuwa Allah yake k'ara bud'a mishi harkar samunsa.ko Wannan dawowar da yayi sai da ya k'ara gyara musu gidan,har sabon fenti akai.

Sai da safe Mama take fad'awa Su'ada yanda sukai da Abba,inda sabo Su'ada ta saba da hidima da kyautatawar mahaifinsu garesu,amma wannan karon tana jin nauyi da wata irin ninki k'aunar mahaifan nata a zuciyarta.
Zuwa tai d'aki ta sami Abban yana zaune Nusrat na kan cinyarsa,tanata gwalangwalan d'inta,bayan ta zauna ta gaida Abban,ya amsa cikin kulawa yana tambayarta ya Jinjirin,cikin yanayin da ta saba yiwa Abban nasu magana cikin shagwab'a tace" Abba wannan yaron kuka gareshi, sam bai barinmu barcin dare, Nusrat ta fishi hakuri, ni duk ji ma nake kamar na dakeshi."

"To ai da kin dake shin zai yi shiru da wuri,kinga muma kunnuwanmu sai su huta sa kukan nashi."
Mama dake shigowa d'akin d'auke da jinjirin ta fad'a.

Dariya Su'ada da Abba su kai a tare,sannan Su'ada ta tsaida hankakinta waje guda tana yiwa Abban godiya.

Shi dariya ma abun ya bashi,yace "Su'ada don na muku hidima shikenan kike ta wannan godiyar? Shin kina da wani me yi miki bayan mu iyayenki da kuma mijinki? hakkinki duka yana kanmu da mijinki,kuma Ibrahim yaron kirki ne,kullum k'ara yaba hankalinsa nake,bayan wannan jarabtar data sameshi na san zuwa yanzu da tuni ya gama komai daya rataya a wuyansa,kamar yanda Mamanku ta sanar dani irin namijin k'ok'arin da yayi a wancan karon,to a wannan karon ma tunda munsan babu ne mu iyaye sai mu tallafa ai."

Tsawon lokaci Abba ya d'auka da Su'ada yana mata nasiha da k'ara sanar da ita girman mijinta gareta, har kwalla sai da tai.tana k'ara yiwa iyayenta addu'ar fatan dacewa duniya da lahira.

*********
Yau ma da dare Khaleelee yazo gidan,a waje suka had'u da Abba, bayan sun gaisa cikin girmamawa,Khaleelee ya k'ara k'asa da kansa sannan yace "Abba daman ina son maka maganar sa suna,nai mai hud'uba da sunanka."

Sosai fara'ar Abba ta k'aru,yace "To madalla Allah ya raya mana shi cikin aminci yayi musu albarka."

Cikin jin kunya Yake amsawa sannan ta tashi ya k'asara ciki.

Abba yaji dad'in takwarancin da Khaleelee yai mai,don haka yana shiga d'aki yake sanar da Mama zancen,itama taji dad'i sosai.

****Lokacin da ya shiga d'akin duk su Jidda na ciki,bayan sun gaisa su ka fita su ka basu waje,a kujerar gefen gadon ya zauna yana fad'in "Washhh yau d'inkin ki ya gajiyar dani fa matar tela."

Y'ar dariya tai tana gaidashi tare da tambayarsa gida dasu Baba,yace "To Baba yana can yana fama da jiki sai godiyar Allah."

Cikin tausayawa tace "Allah sarki Baba,don Allah kai mishi sannu in ka koma."

Jinjina Kai yai yana fad'in "mik'o min Abban.ko yau rowarsa ake min."

Kallonsa tai cikin rashin fahimta tace "Abba kuma? Ya za'ai ma rowar abunka."

Bayan ta mik'a mai shi tace "Naji kace Abba."

Gyad'a kai yai yana mirmishi yace "Sunan Abba nasa mai,da fatan yayi miki."

Da fara'a sosai tace "Wayyo, amma naji dad'i fa,Allah ya raya mana shi cikin aminci."

"Amin ya Allah, kin san Yanzu naga Nusrat hannun Khaleelee wai nace tazo ta mak'ale kafad'a,ina ganin fa ta manta ni."

"Ah haba ya za'ai ta mantaka, kawai yanzu ta saba dasu ne,ko nifa bata yarda dani."

Cikin tsokana yace "To ko mu barmusu ita ne?"

Itama cikin tsokanar tace "In zaka iya ba."

"Kiji wai in zan iya,meye don na barwa Mama ita."

D'age gira tai tana y'ar dariya tace "Kasan Abba ma jiya sai da yace wai wannan y'ar ai tasu ce,mu ga namu mun Haifa."

Dariya yai sosai yace " Damu da su duk muna karkashin Su Abba muke."

D'an gyara zama tai kafin ta fara bashi Labarin Abunda Abba yace kan suna da duk abunda suke buk'ata ."

Sadda kai yai kafin ya d'ago yace "Su'ada ni kam a wannan rayuwar akwai namijin da ya kaini Sa'ar surukai? Ina tabbatar miki ni d'in na daban ne a Wannan rayuwar,ana dad'ewa ba'a sami surukai irin nawa ba.bazan gajiya dayi musu addu'a ba,Allah ya bani ikon k'ara rik'e musu ke da amana."

"Ameen Ameen" Su'ada ke amsawa a lokacin da yake ta yiwa su Abba da mama addu'a.

Tashi yai zuwa gun Abba yayi godiya sosai.

*****Sakeena dai tun Randa Khaleelee yaje sukai magana da Su'ada kan cewa ba taron suna daya dawo gida yake fad'a mata ba suna,to tana kan hakan cewa ba suna,amma kwana hud'u da haihuwa da haihuwa Su'ada ta kitara a waya tace don Allah ta fad'awa mak'otansu zancen suna, bata ce mata Khaleelee yace ba suna ba ta bita da to.bayan ta kashe wayar ta jijjiga kai da fad'in "Wato mijinki yace ba suna,shine ke don son iyawa zaki ce in fad'awa mak'ota ko,to wannan karon zaki sha kunya, don zan miki gayyar da zaki rasa abun basu,tunda ke kin iya k'i fad'i."

Tun a lokacin ta tashi yara ta rink'a aikasu gida gida wai suce Su'ada tace a fad'a musu zancen suna a can gidan iyayenta medile,har bayan layinsu da kewaye ta ai aika. Ai kuwa mutane da son abun duniya sunga wancan karon yanda akai wadak'a da abinci da nama,ga take away in mutum zai tafi, wannan yasa kowa d'ora aniyar zuwa suna medile,ca suke don dai kud'in mota naita d'ari ta kaika ta dawo da Kai. Hhhhhhhhh kaji son banza fa.

*********Mama ta shiga kasuwa ta siyowa Su'ada tsadaddan less da dank'ararriyar shadda, ga takalma da mayafai,sannan yaro ma aka siyo mai kayansa rankacakaf.

Abunka da matar tela, tuni ya kawo mata wancan kala biyar din data bashi sannan ya k'arb'i less da shaddar suma yace zuwa fan suna da safe zai gama.

********
Ranar suna yaro ya amsa sunan Muhammad Mustapha,za'a rink'a kiransa da Fudail.

Hidimar suna sosai ake a gidan,dangin Khaleelee da suka zo Waje daban aka saukesu tare da kayan abunci ci iya cinka, ga lemukan jarka kala kala.

Da azahar kam sai ga gayyar y'an unguwar su Su'ada inda kasan an kunna famfo haka suka rink'a shigowa.sosai Su'ada tai mamakin yawonsu,amma taji dad'i sosai,suma tarya akai musu ta girma.
Aka wadatasu da abinci kala kala da lemuka,ai kuwa nan suka shiga zance da watsa shinkafa,wata cikinsu da bakinta bai iya shiru tace "Kai masha Allah, Ashe dai da gaske da ake fad'a yarinyar man y'ar masu dashi ce, ji gida don Allah, dasss ko ina fees. gashi dad'i na da hidimarau abunci ba k'auro,kinga wannan haihuwar ma da take ta biyu komai rabajau."

Wani kululu ne ya tasowa Sakeena, a duniya in kana son ganin bak'in cikinta to ka rink'a fad'ar arzikin su Su'ada a gaban ta.tabbas da tasan wannan hidimar aka shirya da bata gayyaci kowa ba,ita da tai gayya don aji kunya amma sai akasin hakan.

Dangin Khaleelee sun San wannan hidimar bashi yayi ba,tunda sun san yanzu halin da yake ciki,don haka su kaita sawa iyayen Su'ada albarka.

Khaleelee ma lokacin da yake shago yaga almajirun au Su'ada da kayan abinci nik'i nik'i, yayi mirmishi yayi cikin ransa yana fad'in "Allah ka sakawa iyayen matata da gidan aljanna, itama kai mata sakayya da alkairi ya bani ikon kula da ita.

Bayan sun yi walimarsu a shago, da la'asar ya d'and'asa wankansa cikin sabuwar shadda ya nufi gidan suna don Su'ada nata kiransa da wai yazo me hoto yazo,shi da Jabeer suka je,suma aka k'arasa hidimar Sunan dasu.

***Tunda Sakeena ta dawo gida take bak'in cikin hidimar da akai a gidansu Su'ada da yanda taga an k'ara gyara musu gidan,wani kishin data kwana biyu ba tai akan Su'ada yau taje ji,haka ta kwana rai ba dad'i.
(Ya Allah! Wai don Allah me had'a facala kishi da facalarta,ke baku had'a miji ba baku,had'a tukunya ba,Baku had'a komai ba Sai y'an uwar takar mazaje amma Ku zauna kishin juna."

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋

[2/24, 9:17 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.