Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 21 of 26
_*page*_*41-42*
A sannu kwanaki suke ja,yau ya rage kwana uku Su'ada tai arba'in,suna ta shirye shiryen zuwa gida suyi kwana biyu sannan su zagaya dangi,zuwa Yanzu kam Nusrat kamarta da mamanta k'ara fitowa take sosai,har rashin k'iba na Su'ada ne,sai tsayi fa Masha Allah ta d'auko Khaleelee don kana d'aukanta zaka tabbatar da doguwar yarinya ce ita,sab'anin Su'ada da bata da tsayi bata da k'iba.
A iya tsakankanin Khaleelee ya bud'ewa Su'ada wuta ko yaushe fad'a mata yake hak'urinsa ya k'are amma ita kam ta kafe mai sai Innaro ta bar gidan zata iya kula dashi,don tasan yanda kullum Innaro ke fad'a Mata tayi taka tsantsan da shigewa namiji a Lokacin da take jego dukda ta sami tsarki amma taki yarda dashi.
Ranar da sukai arba'in ta zaga dangin Khaleelee duk da suke kusa tai musu yawon arba'in, washe gari kuwa suka wuce gidansu Wanda a ranar Innaro tai sallama dasu gaba d'aya.
Sun sami kwana biyu a gida suna zaga dangi, ranar da suka kwana biyun da dare yazo ya dauketa.
Ta shirya mai tsaf don itama tai kewarsa,don haka batai sanya ba wajan sa hannu bibbiyu ta amshi mijinta.
************
Lokacin da Nusrat ta shiga wata biyu dai dai Su'ada ta koma bakin aikinta,a Lokacin kuma hidima tai mata yawa,amma haka take tsara komai cikin lokutanta.bata shiga hakkin mijinta dana yarta sabida aiki.wannan yasa kullum Khaleelee ke k'ara bata kwarin gwiwa kuma yake taimaka mata da dukka ayyukan gida.
To tsakanin Sakeena da Su'ada ba yabo ba fallasa, zaman ya dawo irin na farko,don lokuta da
dama Su'ada tana ganin Abu sai dai ta kauda kai,musamman kan yanda Baby Ke kulafacin d'aukan Nusrat, wani lokaci tana ji za taita mata fad'a kan yawon goyon da takewa Nusrat d'in wai k'irjinta zai bud'e, sosai ran Su'ada ke soyuwa amma sai ta danne,wani lokaci har sai tayi kamar zata hana yarinyar d'aukan ta amma sai ta fasa,don yanda baby ke nacin Nusrat d'in ba magana.
Wata ranar Asabar da safe Sakeena na tsakar gida tana aiki, tacewa Baby ta kawo mata robar magi a falo,Baby ta amsa amma bata kawo ba har wajan mintina biyu,Sakeena ta k'ara magana,sannan ta fito tana gyara goyon Nusrat da ke bayanta, cikin fishi Sakeena ta kawo mata duka da fad'in "Kina goyon k'anwar uwarki dole nayi magana ki share ai, ta bud'e baki zatai magana ta k'ara kai mata bugu,tai baya da sauri hakan yasa kan Nusrat buguwa a bango,karar data tsanyara yasa Su'ada dake tsakar gidanta tana aiki sannan tana jin duk abunda su keyi ta fito da sauri,da azama ta k'arasa ga Baby wadda duk ta gigice tana ta jijjiga yarinya tace " Aunty Wallahi ban sani ba,mama ce za ta dakeni nai baya shine na bugeta."
D'an mirmishi Su'ada tai bayan ta kwance ta a bayanta tace "Karki damu,ai nasan da ganganci ba zaki bigeta ba Baby."
Wajanta ta shige zuciyarta na mata k'una,bayan ta rarrashi yarinyar tai shiru sannan ta sauke ajiyar zuciya tana shafa mata kai,a ranta take mamakin wai meye dalilin da yasa Sakeena tsangwamar Baby don tana d'awainiya da Nusrat,tabbas tasan sarai da Sakeena nada iko da tuni ta hana Baby jigilar d'aukan yarinyar. Amma ya zama dole ta d'au mataki,duk nacin Baby zata daina bata Nusrat tunda uwarta bata son hakan. "
******
Da Rana Khaleelee ya dawo cin abinci ya kula sam Su'ada bata da walwala, don haka ya ajiye cokalin da ya d'ebo abincin ya zuba mata ido,kanta da ke k'asa ta d'ago don taji alamun kallona ta yake,d'an mirmishi tai tana kauda kai gefe,bai d'auke idonsa a kanta ba haka bai ce mata uffan ba,gajiya tai don kanta tace "Wai wannan kallonfa?"
Janye plat d'in abincin yai daga tsakiyarsu tare da rik'o hannunta ya d'an matsa cikin nashi.
Sanyaya murya yai sosai ya fara magana"meye matsalarki? Na hango damuwa tare dake."
Sosai tai k'ok'arin wadata fuskarta da fara'a kafin tace"Ba abunda kW damuna, kawai ban jin dad'in yanayin ne Yau. "
Cikin kallon ban yarda dake ba ya k'ara fad'in "Damuwar dake kan fuskar ki tafi k'arfin ace rashin jin dad'in jiki ne ya saki haka,ki fad'a matsalar ki Su'ada, ko akwai wanda yafi cancanta da jin matsalar ki sama da mijinki?*
Girgiza kai tai cikin sanyi tace " Kasan me? Wallahi Nusrat ce ta buge d'azu,kukan da tai da yawa shi yasa duk zuciyata tamin rashin dad'i. "
Zaro ido yai da fad'in "Wane irin bigewa?garin yaya hakan ta faru?"
D'an motsa hannunta dake cikin nasa tayi kafin tace "tsautsayi,a bayana take nazo shiga kitchen na bugeta,ta bugu sosai ,tai kuka da yawa,shi Yasa duk jikina ya mutu ."
Tashi yai a hankali zuwa kujerar da yarinyar ke kwance tana bacci ya d'aukota tare da zama yana dudduba fuskarta zuwa jikinta.d'agowa yai yana kallon Su'ada da d'an mirmishi yace "Da sauk'i ai,ki kwantar da hankalinki kinji."
Gyad'a kai nai nima ina d'an mirmishin.
Daga haka bai k'ara bi takan abincin ba ya kwanta tare dasa yarinyar a k'irjinsa yana d'an shafa bayanta.
___________
To tun daga ranar sai Su'ada ta rage bawa Baby Nusrat, in ta shiga wajanta dai zata bata ita tai ta mata wasa amma bata bari ta fito da ita tsakar gidansu.
Ganin haka yasa duk jikin Sakeena sanyi.duk da Su'ada bata wani canja mata a fuskaba amma tasan sarai abun na ranta,yo in maye yaci ya manta uwar d'a ai bazata manta ba.
**********
Rayuwa na ja,abu da yawa na faruwa, a haka har Nusrat ta sami watanni bakwai, kuma alokacin ne wani cikin ya b'ullo a jikin Su'ada, na watanni biyu,Su'ada bata da zab'i sai zab'in mijinta,don taso tun da wuri ta fara tsarin iyali amma Sam Khaleelee ya zubawa idonsa toka yace bai san batun ba, bata ja cancan ba ta bari,to haka yanzuma da cikin ya bayyana taji fargaba sabida duka Nusrat watanninta bakwai,akwai d'awainiya sosai a kanta.ga aiki ga hidimar gida,amma tasan tunda Allah ya tsara mata hakan to bazai kasa basa hanyar da zata sami sauk'i ba.
A b'angaran Sakeena ma tana nan tana ja,haihuwa yau ko gobe don tsohon ciki gareta.
Su'ada bata da mugunta kk rowa,ita komai nata bai rufe mata ido ba a rayuwa, hakan yasa ake samun sauk'i cikin zamanta da Sakeena, tabbas da yanda d'abiun Sakeena suke haka nata suke to lalle da abun bazai kyau ba. Amma dake ita komai nata cikin nutsuwa da ilimi take sai wani d'abiun shirme na facaloli bata yi,don ita har ko yaushe d'aukan FACALA take matsayin Y'ar uwa.
Wannan karon cikin bai bata wahla sosai,don haka bayan ita da mijinta bama Wanda ya san tana da shi.
************
Cikin ikon Allah Sakeena ta haihu lafiya,y'arta mace.ba kyashi ko hassada Su'ada ta harhada kayan Nusrat na jinjirantaka kaf, ta baiwa Sakeena, duk da tasan anan gaba kad'an duk abunda ta bayar d'in sai ta k'ara siya,amma hakan ba damuwarta bace,tunda tasan Allah ya hore Mata abunda zatai hidima dashi.
Sosai Sakeena taji dad'in wannan tulin kaya da Su'ada ta bata don daman abubuwa da yawa bata dasu sabida ta kwana biyu bata haihunba,duk da taci burin yin hidima sosai a Wannan haihuwar sabida yanda taga Su'ada tai abubuwa tamkar biki abun ya birgeta,kuma ta K'ara jin kishi a ranta na itama sai tayi kwatankwacin haka.Lokacin da tajewa yaya Muktar da abubuwan da take so yai mata,ya kalleta cikin mamaki da fad'in"Sakeena shin kin manta yanda rayuwar nan ta canja ne,kina kallon wannan term d'in duka sati d'aya da komawa na kashewa yara kud'in makaranta da sabon uniform da littattafai,a gabanki na buga lissafi uban kud'in dana kashe,account d'ina gaskiya yanzu ba wani kud'in kirki a ciki,kud'in dana ware zan sai rago ne kawai dana abincin suna,don haka kiyi hakuri yanzu kam gaskiya bazan iya miki way'annan uban abubuwan ba sabida bani da Wallahi. "
Tumzuro baki gaba tai cikin b'acin rai tace"Amma ai haihuwa ba mutuwa bace,tun ciki ba wata guda ake mai tanadi,mutuwa ce ke zuwa bagatatan,don haka gaskiya ba zai yuyu ace duk haihuwa sai dai inyi malejin komai ba,yanzu shekara biyar rabona da haihuwa, ya kamata ace an min komai na bajinta,fisabilillahi fa."
Shi duk mamaki ma ya gama cikashi, bai tab'a zaton rashin lissafin na sakeena ya Kai har haka ba.
"Wai Sakeena yanzu haihuwa ta nawa kikai don Allah?"
Wani kallon rainin wayo tai mai kafin tace " kai za'a tambaya wannan ai,dalili kuwa kai kake yin cikin don haka zakafi gane lissafin yawon haihuwar. "
"To Yanzu Sakeena in kina da lissafi ko a haihuwar fari ne kika ce nai miki Abu nace miki bani dashi kya yimi uziri,balle haihuwa ta biyar, meye ban yi miki ba lokacin da babu hidima sosai a kaina? Kafin kice nake miki, amma yanzu in kika ce nai miki abu nace bani dashi sai abun ya zama tashin hankali? Ki ci gaba in kina kallon wannan hanyar ce me b'ullewa a rayuwar ki.Amma bazan gaji da fad'a miki ba cewa na kusa gajiya da halinki.kuma kin sani randa duk hak'urina ya k'ure a kanki abun ba zai mana kyau ba."
Jin ya hau sama ya sa tai tsit da bakinta sai kumbure kumbure take kamar fanken da ya sha yis.
*********To iya dai abunda Allah ya horewa Yaya Muktar yayi iya yinsa na abincin suna,haka nan kayan barka yayi abunda zai iya.
Khaleelee ma ya bashi gudunmawar dubu biyar sannan ya siyawa Babyn riguna masu kyau guda uku.
Su'ada kam tai mata kunun aya da yawa sabida taji tana fad'awa wata k'anwarta tana son yin kunun aya da alale na suna kuma bata sa kud'i, to daman tana ta tunanin me zata mata na sunan don haka tai mata kunun ayan da alale da yawa.
Y'an gidansu Su'ada sun zo suna harda maman su,da atamfa turmi d'aya da riguna biyu masu tsada maman ta bawa Sakeena.
Sakeena a zahiri taji dad'in abunda Su'ada tai mata da wanda mamanta tai mata,amma kasan ranta take kishin inama itama tana da dama kalar ta Su'ada, ace komai zaka fidda kud'in ka kayi shi yanda kowa zai gane kayi bajinta, Amma ba wannan damar,k'arshe ma wadda kake kishin akanta wai ita zata taimaka maka,kaicon wannan rashin kud'i.
***********
Lokacin da cikin Su'ada ya kai wata bakwai lokacin Nusrat ta cika shekara guda,don haka ta yayeta ta kaita gidansu kamar yanda mama ta buk'ata.
*******
Tashin hankali Wanda ba'a sa masa rana,ranar wata Alhamis ne cikin dare Khaleelee yaji Jabeer na bugun k'ofar su cikin tashin hankali ,jiki na rawa Khaleelee yazo ya bud'e mai daga shi sai gajeran wando. kafin ya tambayeshi meye Jabeer ya fara fad'a mishi"Yaya Khaleelee wuta ta kama a shago,yanzu su hamza ke kirana a waya wai wuta nata ci cikin shagonmu. Kan Khaleelee rik'ewa yayi,hankalinsa yai bala'in tashi, da gudu ya koma d'aki yana neman riga yasa,Su'ada data biyo bayansa jikinta na rawa take fad'in "me ya faru ne Abban Nusrat? Don Allah fad'a min abunda ya faru."
Tana saka jallabiyarsa yake fad'in "Su'ada wuta ce ta kama a shagonmu."
Daga haka ya fito da sauri, a waje yaya Muktar har ya rigashi fita shi da Jabeer.
Lokacin da suka je shagon waje ta turnuk'e fa wuta ce ke ci bilhakki,don kusan shaguna hud'u ne su ke ci a wajan.
Jama'a duk sun fito duba shagunansu.
Lokacin da y'an fire services suka zo wutar taci abunda taci don tai b'arna matuk'a,sabida shagon dake kusa da su na saida katifu ne,na hannun hagun kuma na saida yadika ne.
Sai wajan sallar asuba akayi nasarar kashe wutar,a lokacin ne kowa ya fara duba shagon sa, babu wani abun mora komai ya k'one murus sai k'arafuna,
'Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun'
Shine kalmar da Khaleelee keta maimaitawa lokacin da yaci karo da sif d'in da yake zuba kayan da bai d'inka ba,ta k'one k'urmus ita da abunda ke cikinta.
*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 12:04 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.