Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 12 of 26
_*page*_ *23-24*
Washe gari kam Su'ada da wuri ta had'a abincin karyawa, kunun tsamiya ta dama kasancewar ta san Baba ya na sonshi,sannan ta d'an nik'a wakenta a blander tai mai lafiyayyiyar alala wadda ta ji kifi da k'wai, da yawa ta zuba mishi kunun a flask,sannan alalan ma ta zuba mishi da yawa.
Bayan sun yi wanka kafin su zauna karyawa Ibrahim ya kai mishi.
Sakeena na tsakar gida ta ga ya wuce da abinci ya kaiwa Babah,tsaki ta ja tana fad'i cikin ranta '' Aikin banza sabon sanabe,za a gaji a bari tunda mu ma muka saki''
Bai kula da yanayin fuskarta ba,gaidata kawai yai ya wuce.
Ita kam zuciyarta fal k'unci taita k'ananun maganganunta.
Tun daga ranar sai ya zamana ko yaushe da wuri Su'ada ke tashi tai abin karyawa sabida Babah,ko da su ba lokacin zasu karya ba.
Sosai Babah ke sa mata albarka dare da rana,wanda hakan ke sa taji dad'i kuma yake k'ara mata karsashi wajan yi mai hidima.
************
Lokacin hutun da Su'ada ta d'auka na aure ya cika, don haka wannan satin tai shirin komawa bakin aikinta.
Sassafe ranar Monday tai shirinta,bayan ta gama abincin karyawa Khaleelee ya kaiwa Baba nashi,ita kam a tsatstsaye ma ta sha ruwan tea.
Kamar yanda ya tsara kullum shi zai rink'a kaita, don haka tare su ka fito,Ta tsaya k'ofar d'akin Sakeena ta gaisheta,sannan tai mata sallama.
Bata san ina zata ba,ta dai amsa mata da "To sai kin dawo".
D'akin Babah ta shiga su ka gaisa ta fad'a mai ta koma aiki,yai mata addu'a sosai,cikin jin dad'i take amsawa, fito su ka wuce.
Har cikin makarantar ya sauketa,su kai sallama.
Yini gudu yau a tsaye ta yi shi,duk ta jigata.
Bata dawo gida ba sai k'arfe d'aya da rabi,a gajiya take,don d'an hutun da ta samu yau duk sai take jin kamar yau ta fara teaching d'in.
Lokacin da ta shigo gidan Sakeena na sallar azahar,yaran duk basu dawo ba,Islam kad'ai na ta wasanta a tsakar gida,ta d'an tsokaneta ta wuce wajanta.
Kai tsaye alwala ta d'aura tai salla, bayan ta idar ta shiga kitchen don samarwa Khaleeleenta abincin rana,Jalof d'in taliya ta mai Wanda yaji kifi bushashshe.
Wajan k'arfe biyu da rabi ta shiga wanka, ta na fitowa ta kirashi a waya,ta sanar dashi ta gama girki fa kuma taji shiru bai dawo ba.
Cikin jin dad'i ya sanar da ita yana nan shigowa gida.
Sai uku ya shigo, lokacin har bacci ya fara d'aukanta, da mirmishinsa kamar ko yaushe ya zauna gefenta yana matsa mata k'afa yace " Madam sannu kinji,yau an taro gajiya ko?"
Cikin fara'a take amsa mai bayan ta mik'e zaune "Wlh yau ko,hhhmmmm duk jikina ciwo yake kamar kamar me".
Hannu ya sa ya fara mammatsa mata k'afafu,a hankali yake magana " Eyya sannu kinji Babyna,ni nai tunanin ma baza kiyi girkin ba shi ya sa ban dawo ba,sannu kinji bari a miki tausa sosai."
Sosai ya mammatsa mata jikin,ai kuwa taji dad'in jikin,da k'arfinta ta mik'e tana had'a musu abincin.
Bayan sun gama ci ya ke mata maganar in ta dawo ta daina wahalar girkin rana kawai ta rink'a yin girki d'aya in ta dawo su ci da rana su ci da dare.
Ita kam tace A'a aiki ba zai shafi kula da ayyukanta na gida ba,kowanne zata bashi hakkinsa.
Bayan sallar la'asar ya koma shagon d'inkin sa, nan ta sami damar fara had'a girkin dare.
Tana cikin gyaran gyad'ar miya Sakeena ta shigo mata,faran faran su ke d'an hira,can Sakeena tace "Lafiya wai Su'ada naga yau kin fita da sassafe haka?"
"Lafiya k'alau wallahi Maman Abba na koma aiki ne Yau."
Da azama ta kalleta harshenta har yana had'uwa waje guda take fad'in "Wane irin aiki kuma?daman kina aiki ne?"
Bata damu da yanayin ta ba take bata amsa" Eh ai ina koyarwa a makarantar secondary ta maza, to daman hutun aure na d'auka, yanzu kuma hutun ya k'are. "
Wani dummmmm Sakeena taji gabanta ya fad'i, amma sai ta dake ta ci gaba da jero tambayoyinta wanda daman su su ka shigo da ita, "Ah kice malamar makaranta ce,amma baki tab'a fad'an ba kusan watanninki biyu a gidan nan,kinga kuwa Allah in nice ba zan k'i fad'a miki ba."
D'an mirmishi Su'ada tai tace "Nima dai Allah ne bai kawo hirar ba amma da na sanar da ke,meye a ciki."
Jinjina kai kawai Sakeena ke yi,can tace "Kice a wata kina fin me gidanma samun kud'i, tunda kin San shi fa d'inki sai sanda ya samu,wani sa'in sai kiga an yi wata guda ba'a sami d'inkin dubu goma ba,shi yasa da yawan mata ba su fiye son auran tela ba in dai da Sana'a d'aya kawai ya dogara,don wata rana za'a tashi abinda ma za'a ci ya gagara."
Wani k'ululun bak'in ciki ne ya zo wuyan Su'ada ya tokare, bata son cin fuska a rayuwa,amma ta lura Sana'ar Sakeena kenan cin fuskar mutum a gabanshi,in ba ma wulakanci ba meye za ta rink'a kushe sana'ar mijinta a gabanta.
Basarwa tai kamar maganar bata b'ata mata rai ba tace " La ai duk Sana'a ta gaji haka Maman Abba, maybe dai ke ce biki San da hakan ba,amma ko wace Sana'a a kwai lokacin da ta fi ci sosai,kuma shi d'inki da ki ke gani ai sirri ne,ba kowane tela ne yake zama ba d'inki a hannu ba,balle tela irin Khaleelee, shi da ya kama manyan mutane,kuma ya rik'e gaskiya da amana, ni fa ko da can ban tab'a zuwa shagon su Khaleelee na ga ba d'inki ba,sai dai wani sa'in za'a samu sauk'in yawan sa, kuma daman haka rayuwa take,yau bud'i gobe rashi,don haka nake mamakin matan da su ke sawa ransu su kullum sai sun ji su cikin wadata,ai kawai in an samu a rak'ashe in babu ayi hak'uri.
Kuma kin san Allah Maman Abba? ni a duniya ba saurayin da ke birgeni kamar tela, ashe rabon tela zan aura,ni kam ina son tela na a haka a dad'i ba dad'i, shi nake so ba wani abu ba. "
Gyad'a kai Sakeena tai tana fad'in "Ah lalle Su'ada ke yarinya ce,ko dake yanzu ai ki ka fara rayuwar auran,bari zama yai nisa y'a'ya su fara samuwa,a lokacin za ki gane maganar da nake fad'a miki, kina ganin Abbansu Abba, Sana'a nawa ya ke yi? Amma wani lokacin in abun ya had'e sai ki ga kamar mun zagi sama."
Sosai maganar ta bawa Su'ada dariya, amma sai ta gintse tace "Mu dai addu'a za muyi taiwa Mazajanmu Allah ya hore musu ya bud'a musu k'ofofin samun su,Allah ya tsare su daga haram ya had'a su da halalinsu."
Murgud'e baki gefe Sakeena tai da fad'in "Wa???ni zan rink'aiwa Miji addu'ar bud'i? Allah ya sitiri bukwi,to wlh duk randa kika damu wajan yiwa miji adduar ya sami kud'i,bud'i yazo, to randa duk bud'in yazo ke zaki fara hawaye, don da kishiya zai fara nuna miki bud'i yazo. Ke ni fa kullum addu'ata Allah ya rufawa mijina asiri yanda zai d'auke duk buk'atunmu da na yaranmu, amna wani sarari ko waye waye a dai yi sha'ani kawai."
Tsantsar mamaki fal zuciyar Su'ada, ita kam bata tab'a ganin mace kalar Sakeena ba,komai nata kalar na jahilai take yi,in ba jahila ba wa zai ke fad'in wannan magana haka,tabbas bayan ta fad'a mata tayi makaranta kuma boarding school har tai candy Allah da tace ko hanyar aji Sakena bata tab'a bi ba,amma dai duk da haka wallahi ilimi yai gaddama.
Kawai sai taji hirar ta gundureta gaba d'aya, don haka ta fara amsa mata da eh ko a'a,ta maida hankalinta ga girkinta, ganin haka yasa Sakeena tashi tace bari ta koma d'akinta.
Bayan fitar ta,Su'ada tai ta bitar hirar tasu,ba abun d'auka duk cikin zancen Sakeena, tsantsar wauta da jahilci ne kawai.ganin bai da wani amfani tunanin zancan ya sa ta kauda zancan cikin ranta ta shiga hidimarta kawai.
Bayan sallar magriba duk yaran Sakeena su na Falon Su'ada don an kawo wuta,kallo su ke,su na ta hayaniyarsu,ita kam tana cikin d'aki ta na kwalliya,k'ananan kaya ne jikinta wanda su kai masifar kamata,dogon bak'in wandon jeans da farar riga me adon bak'i da gwaldin a gaba,kayan sun masifar yi mata kyau,ta tufke gashinta cikin bak'in k'aton ribom wanda ya dace da shigar da tai,ta gama rikita jikinta da turaruka masu d'aukar hankali.
Bak'ar doguwar riga after dress ta d'auko ta ajiye a gefen gado zata sa,don ba zata fita falo cikin yara haka ba da wannan shiga, tana tsaye gaban mirror ta na mak'ala barimar d'an kunne a kunnanta taji Islam ta tsanyara wani gigitaccen kuka wanda ya sa ta fita da sauri don ganin me ke faruwa ta manta ma da batun d'ora wani abu a kan kayan jikinta.
Samun y'an uwan tai duk sun yo kan yarinyar,itama da sauri ta k'arasa ta d'agata daga fad'uwar da tai,rarrashinta ta shiga yi,don sosai take kuka sabida bakinta ya d'an fashe,toilet ta shiga da ita ta wanke mata bakin.
Khaleelee ya shigo falon da Sallama,ganin yaran duk a tsaye duru duru ya sa yabi su da kallo,kafin ya tambaya Faruk yace "Uncle Islam ce ta fad'i ta fasa baki ta na band'aki Aunty na wanke mata jinin."
Da sauri ya k'arasa shigowa yana fad'in "Subhanallah garin ya ta fad'i, kuna was an banza ko?"
Bai saurari amsarsu ba ya sa kai toilet d'in, ta d'ago zata fito ya shigo, su ka had'e, da sauri tai baya ta na fad'in "Sannu da zuwa."
Binta yai da kallo kafin ya kai idonsa ga Islam yace "Yawwa sannu, garin yaya Islam tasha k'asa harda fashe baki?"
"Wlh ban sani ba,ina d'aki ina shiryawa naji kukanta."
Bin jikinta yai da kallo ya kafe idonsa a k'irjinta don yanda rigar ta kamata sosai abun ba magana,ganin kallon da ya ke mata ya sa tai d'an mirmishi rana fad'in " A bamu hanya mu fita a toilet mana yallab'ai."
Shima mirmishin ya yi tare da rik'o hannun Islam ya juya.
A falo ya zaunar da ita kan cinyarsa ya na rarrashinta yace "Abba garin yaya ta fad'i ne kuna falon a zaune."
Cikin in ina Abba yace "Wallahi Uncle ban sani ba,ni kallo ma nake kawai naji kukanta."
Cikin salon rarrashi Khaleelee yace " Duk kuna zaune kun zubawa T.V ido kun barmin yarinya ta fad'i, duk wanda ya k'ara bari Islam ta fad'i sai na Zane shi."
Duk amsawa su kai da to, Su'ada ta fito daga d'aki da Vaseline ta tsugunna ta na shafa mata a bakin.
Ba wata gamsashshiyar Sallama Sakeena ta fad'o d'akin tana fad'in "Islam meya faru wannan kuka haka,ina salla tamkar na yanke nazo naga kukan me kike."
A tare Su'ada da Khaleelee su ka d'ago ido,kafin ma su bata amsa yaran su ka ce "Umma fad'uwa tai ta fasa baki."
Cikin rashin kalami tace "To garin yaya ta fad'i kamar ba manya a wajan."
D'an mirmishi Su'ada tai tace "Ina d'aki,su kuma su na kallo,maybe zamewa tai ba su lura ba."
Bata wani gamsu da amsar da ta bata ba ta mik'owa yarinyar hannu fuskar nan a tamke tace "Taso muje ."
Ba musu Khaleelee ya sauketa a kan cinyarsa yana kallon sauran yaran ma yace "kuma Ku je Ku yi sallar isha."
Bayan duk sun fice ya kamo Su'ada jikinsa yana magana k'asa k'asa "Wannan wankan fa yabi jiki Baby na,komai ya bayyana yanda zan more kallonsa."
Tura kanta tai cikin k'irjinsa tana wani miskilin mirmishi, cikin muryar shagwab'a tace" Ni ba ruwana, ba wani abu daya bayyana fa."
Shafa kanta ya yi cikin y'ar dariya yace " Ni naga abunda ya bayyana d'in ai,amma kin san me? ban son ki na fitowa gaban yaran nan da English wear's, sabida kayan sun kamaki sosai."
"Wallahi harna d'auko after dress fa da zansa na fito falon naji kukan Islam shine na manta ma na fito a haka."
Shafo gefen fuskarta ya yi yana cewa "Ok ba damuwa.amma fa kayan sun miki kyau sosai."
Mirmishin jin dad'i tai,don a kullum burin Su'ada tai abu Khaleelee ya yaba to ta gama jin dad'i. "
Bata k'ara cewa komai ba ta mik'e daga jikinsa tana fad'in "Taso ka watsa ruwa muci abinci."
Hannunta ya kama ya mik'e tare da bin bayanta.
************
Sakeena tun da ta fita a gun nasu take ta mita, wai ana kallon yara baza'a kula dasu ba,don rashin sanin darajar haihuwa,ba komai ai a sannu mutum zai haihu ne zai san meye d'a da dad'in sa.
Bayan ta gama wannan mitar kuma ta d'ora wai Su'ada ta na sa kayan da basu dace ba gaban yara zata b'ata mata tarbiyar y'ay'anta.
Yaya Muktar na jinta yai mata banza, don sabbin d'abiun da Sakeena ta samo abun na b'ata ransa matuk'a.
*************
Wajan k'arfe goma na dare su na kwance kan gado tai matashi da k'irjinsa, shi kuma yana wasa gashinta,a hankali tace "My choice!"
"Um Zuciyata."
K'ara shigewa jikinsa tai sosai tace "D'azu fa naga kamar Maman Abba tai fishi kam fad'uwar da Islam tai,kuma ka k'ara laifi bayan wanda nima nai,ka kori sauran yaran."
D'an tsaki ya yi yana tab'e baki yace "Au ke abun ya dameki kenan,har kin kasa cireshi a ranki tun d'azu."
Gyara kwanciya tai a jikin nasa tana magana cikin nutsuwa tace "Ba haka bane, ka gane My Choice, duk uwa bata k'aunar jin kukan d'anta,kuma kaga ita za tai tunanin ko ina falon yarinyar ta fad'i, sannan da tace Islam tazo su tafi bai kamata kace sauran ma su tashi ba,za tai tunanin wani abu a ranta."
Cikin rashin damuwa yace "Rabu da ita,ina sane nace su je,kina ganin yanda tazo ta tsaya kan mutane ba wata gamsashshiyar sallama fa ta fad'o mana falo,kuma tazo tana ta wani ciccin magani,da gangan za'a bar yarinya ya fad'i ne,kuma ita fad'uwa in tazowa yaro ko a cinya yake ai zai fad'i har tana wani fad'in wai kamar ba babba a wajan,wallahi wannan abun da Sakeena na yi sam ta fara fice min a rai."
Jin da tai muryarsa ta fara canjawa alamar fishi yasa ta shiga shafa k'irjinsa a hankali take fad'in "Kayi hak'uri kaji,wata rana sai labari, amma don Allah karka k'ara cewa yaran su fita daga wajan nan kaji."
Gyad'a kai kawai yai yana juyar da ita,cikin tsokana yace "Kin daddaneni kin d'ora min nauyi,nima bari in rama gaskiya."
Bubbuga k'afa ta farayi a gadon tana fad'in "A'a ban yarda ba,kullum cikin danneni ka ke,don na d'an d'ana shine zaka min wayo."
Bai bari ta k'ara cewa komai ba yasa bakinsa cikin nata. 🤐
*Taku ce*
*y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 12:05 AM] LAYUZA KABIR: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
_*Congrat Xeryisher, ina tayaki murnar kammala littafinki na KUCAKAR KISHIYA,Abunda ki kai dai dai Allah ya baki ladan,abunda ki ka kuskure Allah ya yafe miki*_🙏
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.