Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 17 of 26

_*page*_ *33 34*

Sai la'asar Khaleelee ya koma shago,ita kam Su'ada har lokacin bacci take,to sanin yawan baccin da take yanzu yasa basu damu ba.
Wajan magriba ta farka,ai kuwa ta farka da mahaukaciyar yunwa,cikinta yai yamutsawa,har jikinta rawa ya ke,tace"Jidda yunwa nake ji sosai wallahi, ji nake kamar hanjina zai tsinke. "

Dafa kai Jidda tai da fad'in "Yanzu ya zamuyi? Kuma naga Maman Abba yanzuma ko girkin bata d'ora ba."

Su'ada ji tai wasu hawaye na zubo mata,dob ta gama sa rai a cin abincin gashi babu,daddafawa tai taje ta d'aura alwala tai salla daga zaune,ta idar tana addu'a Khaleelee ya shigo, Jidda ta mai sannu da zuwa, ya amsa cikin fara'a sannan yace "Yanzu ta tashi ko ta dad'e?"

"A'a bata dad'e ba,yanzu ma ta gama batun yunwa take ji ."

To je ki amso mata wajan Maman Abban mana, Jidda tace "To ai batai fa girkin ba."

Da sauri yace "Yanzun ma? Innalillahi, to me yasa ba tai ba?"

Gyad'a kai Jidda tai da fad'in "Wai tace bata jin dad'i."

Cikin damuwa ya dafe kai,can ya fita zuwa gun Sakeena a bak'in k'ofar d'akin ya tsaya yana sallama. Yaya Muktar ya amsa mai yana d'age labulan yace "Ibrahim ya dai?"

Cikin damuwa Khaleelee yace "Daman Maman Abba zan tambaya ko da abinci agunta ta bawa Su'ada, wlh tun safe bata ci komai ba,da rana batai girkinba shine tace in tai na dare taci,to yanzu ta farka daga bacci yunwa take ji sosai wallahi."

Shafa kai yaya Muktar yai yace "jeka ina zuwa,amma dai ka samar mata wani abu kafin abincin ya sauka, kaga ba'a son barin me juna biyu da yunwa irin haka."

D'aga kai Khaleelee yai alamar to,ya koma wajansu da sauri.

Yaya Muktar kuwa bayan ya zauna bakin gado ya zubawa Sakeena ido,wadda take ta cika tana batsewa,ita a lallai karya samu fuskar mata fad'a, shima had'e rai ya yi da kallon tsakar idonta yace"Sakeena wai me kika d'au rayuwa ne? Me yasa kika canja dukkan d'abiun ki, da dai ba haka kike ba,amma yanzu duk abunda akace min kinyi Wallahi ba zanyi musu ba, yanzu Sakeena meye dalilinki na 'kin yin girki da rana gashi da daran ma bikiyi ba."

Turo baki tai cikin had'e gira tace "Nifa na gaji da ciyar da 'katuwa,Wallahi ba zai yuyu sabida samun waje tace kullum sai girkina zata ci,ko kai da kake mijina baka cin abincina sau uku a rana,kullum sau biyu kake ci,to balle kuma FACALA, kullum ba fashi safe,dare,rana ai ko uwata ce sai haka,in banda kinibibi ai Jidda tana d'ora musu girkin amma tace wai bata cin nata sai nawa,to ban iyawa,bab d'auka wlh,na satin ma da nai Allah ya ban lada,don in har na sake har ta haihu nawa zata rink'. . . ."

Bai bata damar K'arasawa ba ya d'aga mata hannu,"dakata Sakeena me kike son cewa? Matar d'an uwana kike cewa ba zaki rink'a bawa abincin dana siyo da kud'ina ba? kuma ma Sakeena ke ba mace bace,biki san lalurar ciki ba,a cikin Baby biki tsinci kanki a wannan halin ba,kin manta yanda kullum sai an k'arb'o miki abincin makota,kuma kullum basu gajiyawa da ke ba har tsawon wata tara, sai ke zaki gajiya da bawa matar d'an uwana? To Wallahi Wallahi matuk'ar kina nemawa kanki zaman lafiya dani to ki canja wannan halin naki,kuma ki tashi ki d'ora mana girki yanzu,don ba zaki bar min yara su kwana yunwa ba."

Kallansa tai cikin mamaki tace "yanzun zan d'ora girki an kusa sallar isha'in?"

Had'e gira yai sosai yana kauda kai gefe yace "Eh haka nace,in kuma ba zakiyi ba in ji yanzu."

Mik'ewa tai tana zunb'uro baki ta fice, Allah ya taimaketa tana da miya don haka kawai farar shinkafa ta dafa tana yi tana 'kunci,sai wajan 'karfe tara ta gama ta zubawa yaran ta zubawa yaya Muktar amma bata zubawa Su'adan ba.

Yana kwance a d'aki ta shigo ta ajiye mai flasks d'in,ko kallanta bai ba ta fice ta koma falo.
Can ya mik'e ya bud'e abincin, jim yai yana d'an nazari,kira ya 'kwalawa Baby,da ta shigo yace "Mamanku ta zubawa Su'ada abinci?"

Gargiza kai tai da fad'in "A'a bata zuba mata ba,na tambayeta ina na Aunty tace bata sani ba."

Turo mata kulan yayi da cewa "Maza d'auki wannan ki kai mata."

D'aukan flask d'in shinkafar dana miyar tai ta wuce wajan Su'ada.

Su'ada na kwance cinyar Khaleelee yana ta shafa kanta don bacci ya fara d'aukanta,sai Jidda kuma na d'akin da take kwana,Baby tai sallama cikin falon tana fad'in "Uncle ga abincin Aunty."

Da sauri ya fara tashin Su'ada yana fad'in "Tashi kici ga abincin nan Pretty."

Ajiyewa Baby tai ta fice, Jiddah ta fito don taji maganar abincin, kitchen taje ta d'auko plat da cokali tazo ta d'ibar mata wanda take ganin zai isheta.
Khaleelee da kansa yake bata don jikinta duk ba k'arfi, tas ta cinye tace a k'ara mata,shima wanda aka k'ara ta cinye tas tasha ruwa,ai kuwa tuni wani daddad'an bacci ya k'ara gaba da ita.

Ajiyar zuciya Khaleelee ya sauke cikin ransa yake fad'in "Ashe haka iyaye mata ke shan wahala, lalle ba zai gushe ba yana mai yiwa mahaifiyarsa har ranar da zai bar duniya."

Jidda kam tana kwance a d'aki tana kwasar takaici,haka nan taji Sakeena ta bala'in fice mata a rai,jin wata muguwar tsanarta take.

Sakeena kam na falo kwance bacci ya fara d'aukanta ,don haka bata ji sanda Yaya Muktar ya kira Baby ya bata abinci ta kaiwa Su'ada ba,sosai tai nisa a baccin taji maganar Yaya Muktar d'in yanawa su Abba magana kan su tafi d'akinsu su kwanta dare yayi.cikin mayen bacci ta d'ago ta kalleshi,ganin ledaji a hannunsa ya tabbatar mata daga waje yake.shi kam ko ta kanta bai ba ya juya ya shige d'aki,ledar abincin da ya siyo ya bud'e ya fara ci.
Ba sallama ta daga labulen ta shige,ta gefen ido ta bi ledar da kallo,duk ji tai d'akin ya gauraye da kamshin abincin da ta san na nata ba,gabansa ta 'karaso tana duba ledar wani mak'uk'un bak'in ciki na taso mata,ta zuba mishi ido cikin rashin fahimta,dube dube ta fara yi bata ga flasks d'in data kawo mishi abincin ba,da sauri ta fita kitchen nan ma bata gansu ba,ta dawo falo basa nan,Baby ta kalla tana zare mata ido tace "Ke ina abincin Abbanku?"

A tsorace yarinyar tace "Ai ya ban na kaiwa Aunty."

Da sauri ta juya d'akin tana 'kare mai kallo tace "Ni zan dafa maka abinci ka d'auka ka kaiwa matar 'kaninka? Wai me kake nufi dani?Wallahi yau sai dai ayita ta 'kare a gidan nan,ai Su'ada ba uwata bace da zan yi girki a daran nan don ita,daman kasan ba ci zakai ba kasa dole na dafa."

Kan yaya Muktar na k'asa yana ta cin abincin sa bai ko d'ago ba,balle ya tanka mata.

Duk bala'in da take a kunnan Khaleelee da Jidda, ita ko Su'ada ma baccinta take.
Ganin yak'i tanka mata yasa ta k'ara k'arfin muryarta 'karshe ta fashe da kuka,wai ana cutarta a gidan ita barin gidan za tai.

Baba ne ya fito zuwa tsakar gidan yana fad'in "Muktar kana ina?"

Da sauri ya fito a d'akin yana cewa "Baba gani."

Juyawa Baba yai yana fad'in "Kuzo Ku biyun."

Bayan sun shiga d'akin sun zauna Sakeena nata goge 'kwalla ita a dole an cuceta,Baba ya gyara zama kafin ya fara magana"Muktar wato abunda ba halinku ba zaku fara yanzu,tsakaninka da matarka da can baku samin matsala amma yanzu nema ku ke Ku zama kamar kaji,cikin daran nan Sakeena zaki rink'a d'aga murya ma'kota najinki,kowa sai ya san kin sami sab'ani da mijinki kenan. Fad'a min meya had'aku kai Muktar? "

Yawun takaici yaya Muktar ga had'iya sannan ya fara zayyanewa Baba komai kan batun abincin.bayan ya kai aya Baba ya kalleta yana son jin ta bakinta"Shin Sakeena abunda Muktar ya fad'a duk haka ne?"

"Baba tunda Su'ada tace girkina take son ci kullum safe rana da dare ni ke bata abinci,tsawon kwana takwas yau,to nima yau na tashi ban jin dad'i ban yi girki ba ta aiko na bata nace ban yi ba,da dare ta aiko ban yi ba,shine ya sani gaba a masifa wai dole in tashi in d'ora, haka na tashi da daran nan na girka abincin,to sabida bacci ya d'auke ni sai ya kwashe nasa da na kai masa ya duka ya bata,shi kuma yaje ya siyo wani a waje,Baba yamin adalci kenan?"

Girgiza kai Baba yai cikin halin dattako yace "Muktar laifinka ne a nan, tunda kullum tana bata yau d'aya da uziri yasa bata bata ba bai kamata kai mata fad'a ba,kuma ma tunda tace bata jin dad'i sai ai mata uziri ai,ka tilastata ta girka kuma sannan ka'ki ci, in ma bata bawa Su'adan ba sai ka raba biyu ka bata rabi kai kaci rabi,baka san mace bata son mijinta ya'ki cin abincin ta ba? Karka 'kara irin haka, Su'ada 'kanwa ce gun Sakeena ai,ba'a shiga tsakanin yaya da 'kanwarta,wata rana zasu had'e kai su barka kaida d'an uwanka a gefe."

Juyowa yai cikin muryar rarrashi ya kalli Sakeena, "Sakeena kina jina ko? Ki 'kara hak'uri kici gaba da girkawa da ita,in ma kud'in cefanan bai isa sai ya 'kara miki,kinga lalurace ta kawo hakan,nan da d'an lokaci sai kiga ta koma cin nata girkin,ki daure ke babbace, Su'ada 'kanwa ce gareki,a wannan halin tallafinki take nema bata da wata me taumakonta yanzu bayan ke,ki nuna mata duk abunda bata sani ba game da lalurarta har Allah ya sauketa lafiya kinji.tashi kije Allah yayi muku albarka."

Mi'kewa Sakeena tai jiki a sanyaye ta fice,gaba d'aya Baba ya gama kashe mata jiki,dattijon nada kwarjini da haibar da bazaka iya mishi musu ba,balle yayi amfani da kalamai masu sanyi wajan yin sulhun,haka zata ha'kura taci gaba da ciyar da 'katuwa ya ta iya.

Bayan fitar ta Baba ya dubi Yaya Muktar yace "Muktar duk nasan halin Sakeena, na san gajiya tai da bawa Su'ada girkinta,amma bata haka ya dace ka fito mata ba,kullum ina fad'a muku mata y'an rarrashi ne,duk tsaurin mace in ana rarrashin ta akan a'kidarta ana samun ta sassauta,amma in mace ta kafe kaima ka kafe to ba'a samun biyan buk'ata, ko ta sauko don dole to Wallahi ba zatai abunda ake soba,amma in ka lallab'ata ka rarrasheta sai taji a ranta eh an bata girmanta da matsayin ta,sai kaga ta sauko tayi yanda ake so ko fiye ma da yanda ake tunanin za tai.ka 'kara ha'kuri da ita kaji,kuma ka daina nuna mata ka fifita d'an uwanka ko matarsa a kanta hakan zai sa mata wani 'kullinsu a ranta taji duk ta tsanesu,kai ta ha'kuri kaji ko?"

Gyad'a kai yai yana fad'in "To Baba insha Allah za aita hak'urin."

"Yawwa tashi kaje Allah yai muku albarka Ku da zuri'arku."

*TAKU CE*
*'YAR MUTAN JA'OJI*🙋
[2/24, 12:02 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_Allah kai ne masani kan dukkan damuwarmu,Allah kai zaka bamu maganin ta, Allah ga hannayen mu sama muna rok'onka🙏🙏🙏 Allah ka dafa mana kai maganin matsalar mu_😢

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.