Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 26

_*page*_*9-10*

Typing ta fara yi tana bashi amsa.

" _Da farko dai kaga Jameel soja ne,ni kuma banda ra'ayin auran soja,sannan kaga kalarsa fari ne sosai,ni kuma namiji fari baya min kwarjini ko kad'an wlh,sannan dai cikin halayensa da yawa basu min ba,don yana da zafin rai da nuna gadara duka banson namiji irin haka,wannan dalilin ne yasa sam bazan iya auran saba_."

Kallon rubutun Ibrahim yai tayi yana k'ara maimaitawa mamaki yake ganin yanda tace farin namiji bai mata kwarjini,sannan shi dai kallo d'aya yaiwa Jameel yasan ya ajiye yayan bankin, yanzu ko dan kud'in sa Su'ada bazata soshi ba kenan.ya dad'e kafin ya bata amsa yana nazarin maganganunta.

" _To wane Namiji ne kalar zabinki_?"

" _Da farko kaga ni ina son Namiji dogo, sannan ina son namijin da yasan darajar mutum,ba mai d'aga kai da gadara ba,sannan_. . . _ko dake sauran sirrina ne kawai_"

" _hhhmmmm Su'ada manya,to shawara ta kiyi ta addu'a kina neman zabin Allah, karki nemi zabin ranki kinji_."

" _Na gode Khaleelee, ko yaushe cikin addu'a nake wlh musamman yanzu da mama tasa min lokaci in fidda miji cikin samari na_."

Ji yai gabansa ya fad'i da cin furucinta, shin me ke damunsa ne kan Su'ada, me yasa yake shayin fad'a mata sirrin ransa.tabbas yasan babban abunda ya tokareshi daga gareta to rik'e mutuncinsa ne,bai son cusa kansa in da za'a ga k'ask'ancin sa,ko yaushe yana tsayawa ne iya huruminsa da inda za'a ga mutuncin sa,amma tabbas ya san zuciyarsa na kwad'aita mai soyayya da Su'ada sabida kyawun halayenta da nagartarta.

Jin shiru bai maida mata amsa ba yasa tai zaton ko ya shiga wani uzirin ne,amma bayan mintina sai taga amsa ta dawo.

" _To Allah yai miki zabin mafi alkairi cikin rayuwar ki_."

Daga haka ya sauka ya kashe datar ya shiga tunani da nemon mafita.

*********Kwana biyu tsakani Su'ada ta matsawa Ibrahim da maganar zuwan da yace zai yi,don haka a ranar yace mata zai zo. ta sanar da mamansu cewa kana Ibrahim tela yace zai zo har gida yai mata murnar kammala karatu,cikin kawa maman tace a shirya mai abun motsa baki kafin yazo.

Danbun naman kaza da cake Su'ada ta shirya tare da lemon kwakwa me d'an karan dad'i. Zuwa k'arfe hud'u ta gama komai tai wanka,bata wani yi kwalliya ba sai powder kawai tasa tare da lipstick, ta zira doguwar rigar material tare da yafa k'aramin bakin mayafi.

Lokacin da Ibrahim ya tsaya k'ofar gate d'in su Su'ada kawai sai yaji gabansa na fad'uwa, k'ok'ari yai ya tattaro mazantaka,kiranta yai a waya ya sanar da ita ta k'araso.

Cikin y'an mintina ta fito fuskarta d'auke da mirmishi sosai tace "Khaleelee a gidan mu,lalle yau mun ja babbar sa'a."

Y'ar dariya yai yana shafa kai yace "Ai komai kamawa ta ke Su'ada gashi yau nazo kuma ina fata daga yau nai ta zuwa har sai an gaji dani."

D'an zaro ido tai da fad'in "Waye zai gaji da kai d'in Khaleelee? Ai kai baka cikin mutanan da za'a gaji da su, zo mu k'arasa ciki na tsaida ka da magana."

Bin bayan ta yai zuwa cikin gidan,a sitting room tai mai masauki bayan sun gaisa ta mik'e tana fad'a mai " Ina zuwa Khaleelee minti biyu."

Kallonta yai ido cikin ido sannan fuskarsa na bayyana wani k'ayataccen mirmishi yace "Na baki minti biyar ma Su'ada."

Farrr tai da wadatattun idanuwanta tace " Tom na gode."

Cikin gidan ta shiga cikin farin ciki take sanar da Mama Khaleelee ya na sitting room. Mama tai mirmishi tace "To ina masa barka da zuwa,ki karramashi yanda ya kamata kinji ko?"

Gyad'a kai tai alamun amsawa sannan ta fita zuwa kitchen tana k'walawa Jidda kira,cikin k'osawa Jidda ta k'araso kitchen d'in "Oh Aunty Su'ada kamar zaki tsaga min kai da wannan kiran naki. Ya k'araso ne?"

"Eh ya k'araso don Allah sa mayafinki ki kai mishi ruwa da lemo ina zuwa yanzu."

"Ok ba damuwa Jidda tace tare da juya zuwa d'aki ta d'auko mayafi. ruwan roba da lemo tasa kan farantin tangaran da glass cup ta tafi kai mai,ita kam Su'ada tsara plate tai sosai yanda zasu ja hankalinsa ya ji yana son cin abunda ke ciki. Sannan ta samu glass juck ta zuba Lemon kwakwa d'in,a babban faranti ta jera ta d'auka zuwa sitting room d'in,da sallama a bakinta ta shiga,su na ta hira da Jidda ya amsa mata kallon agogon hannunsa.ta San me ya ke nufi don haka bayan ta ajiye kayan ta d'ago tana kallon sa da dariya tace" Amin Afuwa Khaleelee na wuce lokacin da aka bani ko?"

Gyad'a kai yai ya ce "Don ma ga Jidda ta zauna tayani hira da an bar bak'o shi kad'ai."

"Sorry don Allah, yanzu dai ga abu ka ci sai mu yi hira."

"A'a ni ba abunda zan ci na koshi sosai gashi nasha lemo ma."

Had'e rai tai tare da kauda kai fuska alamar fishi.

Jiddah dariya tai tana mik'ewa tace "Bari na koma ciki maybe don ni ne baza kaci ba."

"Kinji ki cikin Ku waye bak'ona,kawai dai a koshe nake ne,ni da cin wani abu kuma sai dare."

"Tab' d'in ni dai ba ruwana kai da mutuniyar don naga ta ci murrr."

Dariya yasa shima yayin da Jiddah ta fice tana tayashi.

Ganin tai shiru bata k'ara Magana ba yasa ya shima yai shiru na wasu y'an dak'ik'u,yanayin zaman nasu sai ya ke hararo mai abubuwa da yawa cikin ransa bai aune ba ya ji mirmishi ta kufce mai wanda har yasa hak'oransa bayyana.gyaran murya yai cikin kwantar da harshe yace "Su'ada irin karb'ar da a kaiwa bak'unci na kuma kenan?"

Turo baki tai cikin kalar shagwab'a ta ce" To ba kai ne ba na b'ata lokaci na wajan had'a ma abu kace wai ka k'oshi."

"To in dai don wannan ne ki yi hak'uri zan ci kinji."

D'an mirmishi tai da fad'in "Yawwa ko kai fa Khaleelee."

Yanda tai maganar sai abun ya bashi dariya ya girgiza kai ya na d'aukan cake guda d'aya ta kai bakinsa.

Mik'ewa tai da ta na cewa "Bari na baka waje ka gama ko."

"A'a ki yi zamanki ba damuwa."

Duk ji tai kunya ta kamata bazata iya sashi gaba yana cin abinci ba. Dabara ta fad'o mata tace "OK to bari na d'auko wayata."
ya gane take son mai kawai don ta fita d'in ne don haka yace "To na baki minti biyu in kika wuce kuma kisha bulala."

Dariya tai tare da fita.

Shi kam Ibrahim duk yau sai ya ke jin sa wani iri,kamar ba shiba,ga wani nishad'i da yake ji ma ratsashi.

Cake d'aya kawai ya ci da danbun nama kad'an ya d'an sha lemon kwakwar rabin kofi.

Har minti biyar yaga bata dawo ba don haka ya d'auki wayarsa ya mata flashing. Can sai gata idonta kan kayan tace "Hhhmmmm Khaleelee k'afarka k'afar kayan nan fa,don bazaka barni dasu ba,in ka je gida da dare kaci."

"Su'ada Allah don ke ce ma fa kawai na d'an tab'a, ni ban son cin komai in ba irin lokacin cin abinci ba,cikina bashi da zurfi sam,ko abinci ba wani me yawa na ke ci ba."

"Tab d'in matarka zata sha fama kenan."

"Haba? Faman me zata sha?"

"Sabida ba ka son abinci,ko yaushe sai tai rarrashi zaka ci."

Y'ar dariya yai tare da shafa gemu yace "Ba ko wace mace bace ke damuwa da cikin mijinta,wata in dai ta dafa ta yi me wuyar ko kaci ko ka barshi bata da matsala."

Cikin mamaki ta ke kallon sa" Lalle wannan wace irin mata ce haka,ni wlh in nai abinci naga ba'a ci da yawa ba duk sai in shiga damuwa,in yi ta tunanin ko dad'i ne bai yi ba aka k'i ci."

"Hhhhhmmm ke kenan Su'ada amma matan da yawa muna tare da su muna kallon d'abi'unsu sai hamdala kawai."

"To Allah ya shirya su."

Cikin dariya yace "Amin dai ."

Khaleelee ne ya yi sallama k'ofar d'akin, A tare suka amsa mai,sannan ya shigo fuskarsa cike da fara'a yace "Aunty sannu da gida."

"Yawwa my Khaleelee, ga takwaranka ya zo."

K'arasawa yai wajan Ibrahim ya gaida shi, shi kam rik'o hannunsa yai yana tsokanar sa "Kwana biyu Khaleelee an daina zuwa da kai wajanmu,gashi ka zama k'ato ko hanya na ganka ban iya shaidaka."

Cikin yarinta Khaleelee yai dariya da fad'in "Haba dai Kana ganin pic's d'ina fa a wayan Aunty Rannan ma tace kace wai kana gaida ni."

Dariya Su'ada da Ibrahim su ka sa,Ibrahim na ta jan sa da hira da tambayarsa school.To Khaleelee Radio nan ya kunce da surutu,Ita kam Su'ada jefi jefi ta ke s musu baki cikin hirar sai dai mirmishi kawai ta ke. biyar da rabi ya dubi agogonsa ya na jawo ledar da yazo da ita,mik'o mata gaban ta yayi yana cewa "Ayi hak'uri ga kyauta ba yawa,ina tayaki murnar kammala karatu lafiya,Allah ubangiji ya sa ki amfani karatun ki."

Cikin jin dad'in addu'ar sa tace "Ameen Ameen Khaleelee na gode sosai,ga shi har da wahala haka,wlh zuwan naka yafi min komai dad'i fa."

"Nima na gode sosai da irin taryar da akamin, yanzu in ba damuwa zan gaishe da Mama."

"Lah ba damuwa bari nai mata magana."

Bayan ta shiga ta sanar da Mama tace yazo su shiga.

A falo take zaune ya shiga su ka gaisa cikin girmamawa tana tambayar sa Sana'a don daman shine telanta itama. Amsa mata yai da Alhamdulillah.sannan tai mai fatan alkairi ya taso suka fito tare da Su'ada da Khaleelee d'an rakiya.

A bakin gate su ka tsaya hannayenta d'auke da ledar da ta juyo mai cake da danbun naman da bai ci ba.

"Su'ada kin rantse dai sai na tafi da kayan nan ko?"

"Eh ka ci ka bawa Jabir.ka san gauraye da kwad'ayin cikin dare."

"Inye lalle kin ci bashi zan rama kuwa da."

"A'a yi hakuri Khaleelee wasa na ke ma ."

Kafin yai magana wani me napep da ya ajiye wasu ya fito cikin layin.tsaidashi yai ya fad'a mai in da zaije, bayan ya shiga ta mik'a mai ledar ta na ta mai godiya .

*25/10/2019*

*Taku ce*
*mutan Ja'oji*🙋
[2/23, 11:51 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.