Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 26

_*page*_ *3-4*

Misalin sha d'aya da rabi na dare tana kwance kan gadonta d'auke da wayarta kallo d'aya zakai mata kasan chart take don yanda take sakin mirmishi lokaci zuwa lokaci.

Pic's d'in dinner d'in da suka dawo ne yau ta d'ora kan status d'in ta,comments da ake tayi kan pic's ne yake sata yin mirmishi don duk wanda ya bud'e zai ce kamar kece amaryar kinsha kyau.
A nan Sak'on Telanta ya shigo a
"Assalamu Alaiki,biki yi bacci ba kenan?"

Cikin zak'uwa da d'oki ta bashi amsa da "Um ban yi ba tukun,ina dai niyar yi."

Bayan y'an sekonni amsar shi ta dawo " Ansha dinner ko? Ina fatan dai d'inki yayi kyau? "

Mirmishi ta saki tana rubuta mai amsa "Hhhmmmm bari Khaleelee d'inki ya d'au magana fa wallahi, har na samo mana wata costumer wai zata min pic tana son a mata irin gown d'in,nace a'a bana bari a d'aumin d'inki sai dai in had'a ta da tela na zai Mata irinta sak. To yanzu dai na bata number d'inka zaka jita."

Cikin jin dad'i ya maida mata amsa" 👍👍👍 ina godiya fa Regular costumer da k'ok'arin kullum shago ke k'ara tsaiwa ."

Sosai taji dad'in yabon da ya Mata "Hhhhhmmm kullum ina cema ka daina min wannan godiyar ya kamata ace ka daina tun tuni, naji dad'i ai shine gari,kai dai kawai ka ci gaba da tsatsubo min d'inki ina d'aukan magana 😄."

"😂😂😂 karki damu Su'ada ai ke ko da d'inki ko babu kina d'aukan magana fa."

"A'a fad'a kawai kake yi Khaleelee🙄 ."

"Da gaske na ke Su'ada kinga fa yanda kika dakushe duk emmatan gun dinner d'in nan,ina ta kallon status kyau yasa ma na kasa magana😂 ."

"Hmnmm Khaleelee baka rabo da tsokana wlh,amma ni dai na San duk kyan kwalliya in ba'a d'ora Mata had'ad'd'an d'inki ba dakushewa take."

Juyi yai kan katifarsa yana y'ar dariya sannan ya bata amsa, " Hhhmmmm to insha Allah zan ta k'ara dagewa da k'aro fikra don in ta fito da Su'ada😂😂😂😂 ."

"Yawwa haka na ke son ji daga gareka, zan kwanta sai da safe ko."

"OK Allah ya tashemu lafiya."

"Amin na gode."

Juyi kawai ya ke kan katifar ya na tunani cikin ransa, mintina arba'in yaga bai samo mafita ba kamar kullum don haka ya kashe wayar tare da yin addu'a ya lumshe ido yana fatan bacci ya d'auke shi da wuri.

**********
Yau tsahon sati guda kenan da Su'ada ta fara sak'a da warwara kan neman mafita.tabbas da gaske duk abunda take ji game da Telanta ta fara gasgata so ne.to amma ta yaya don mutum na birgeka kuma kuna zumunci sai kawai so ya kunno kai tsakaninku, a zahiri ta tabbata in so ya mata haka bai mata adalci ba,don bata cikin matan da zasu iya tunkarar namiji da tayin so ko da kuwa son ne silar ajalinta,ta dad'e da gano halin maza na wulakanci ga duk macan da suka fahimci tana mutuwar sonsu koda kuwa suma su na son nata, to balle ita da kullum zumunci da shak'uwa take gani cikin idanuwan Khaleelee tare da ita, bata tab'a ganin wata alama ta so ga Khaleelee ba, hasali ma shi in dai ya ga mace ta fiye rawar kai da shishshigi tsakanin sa da ita had'e gira ne,don ya ce duk mu'amalar sa da mace bazai bari son gaske ko na wasa ya had'a su ba matuk'ar harkar d'inki ce ta had'a su,domin kuwa duk telan matan da ya sa soyayyar costumer cikin sabgarsa bazai wani tsinana abun arzik'i ba,daga ya fara soyayya da wannan costumer in wadda tafi ta ta zo zai koma kanta.tasha jin yanawa yaran shagonsa wannan maganar kan su tsaya iya bakin sana'ar su akan ko wace costumer kawai,in yaso in sun bar shago suje su yi soyayyar su.

To mutumin da ke jawa yaransa kunne kan haka ta ina shi zai fara hakan.
A zahiri maza da yawa ke sonta cikin danginta da jama'ar gari,so na aure kuwa,amma bata tab'a ganin abun birgewa tare da su,ga namiji har namiji dai abun birgewa amma ita in ya zo mata da batun so sai taji duk bai birgeta. Tun tuni tsarin halittar Khaleelee ke birgeta,halayensa da tsaftarsa ke k'ara fizgarta gareshi,da tai tunanin kawai iya birgeta ya ke yi,amma yanzu ta tabbatar mugun sonsa ya hudata ya kama zuciyarta,yanzu dole ta nemawa kanta mafita, d'ayan biyu dole a yi d'aya ko dai ta nisanci Khaleelee ta jawa kanta mutunci da girma,in kuma ba haka ba taci gaba da zuwa shagon Khaleelee tabbas asirin zuciyarta zai bayyana.daga nan kuma girmanta da k'imarta da yake gani kuma su shek'e. Wanne kenan za tayi? Ta tambayi kanta cikin tsananin damuwa, wannan take ta sak'awa da kuncewa har bacci yai gaba da ita.

Amma farka warta da wannan batun ta farka,bayan tai sallar asuba ta shiga kaiwa Allah kukanta kan yai Mata maganin wannan ciwo daya kamata, nan wajan bacci ya k'ara gaba da ita.

Jidda k'anwarta da suke kwana d'aki d'aya ce ta ga har wajan k'arfe bakwai bata tashi ba kuma tace musu tana da exam k'arfe takwas don haka ta fara tashin ta "Aunty Su'ada ki tashi kin makara fa."
Da sauri ta mik'e tana salati tare da kallon ogogo,a hanzarce ta tashi ta wuce band'aki.

Duka a gurguje tai shirin nata data fito ko break bata tsaya tayi ba ta amsa kud'i wajan mamansu ta fice.

Tana tafiya cikin adai daita ji take kamar tai iska ta kai kanta school don duka mintina kad'an suka rage takwas ta cika.

Allah ya taimaketa lokacin data isa ga d'akin jarrabawar a sannan malaman da zasu jiresu suka k'araso don haka kusan a tare suka shiga, babu wata ishshshiyar nutsuwa tare da ita sai data ga ta zauna tsaf an bata question pepper a sannan ta saki ajiyar zuciya tasan ta tsira.

***********
Zaune yake kan dakalin k'ofar gidansu bayan ya gama sharar wajan,cikin ransa yake fad'in 'kwana biyu Su'ada shiru ko wucewarta ban gani ba yau tsahon sati biyu kenan, duk zasu fara exam amma ai in zata wuce ta bakin shaginsu tana d'aga musu hannu, ya dubata online ma bata hawa,duk daman in zata fara exam kashe wayanta take babbar sai dai tabar k'aramar a hannunta'

Ciro wayarsa yai cikin aljihu ya fara nemo number d'inta,ringing d'aya biyu ta d'auka yai mata sallama cikin cool voice d'insa,itama cikin fara'arta ta amsa duk da k'ok'arin ta na danne zakuwar ta na karya gane nishad'in da take ciki, "Malama Su'ada kin b'uya gaba d'aya."

"Hhhmmm bari kawai Khaleelee exam ta binne ni,ban gane komai in ba farar takarda in cikata da bulun Biro ba."

Dariya sosai maganar ta bashi bayan ya gama darawa yace "To Allah ya bada sa'a ya sa a fito da kyakykyawar sakamako."

"Ameen na gode Khaleelee, insha Allah yau zan kawo d'inkunan ankon graduation d'inmu,yanzu da mun fito exam zamu wuce kasuwa mu siyo zan kawo ma guda takwas har dana su K /Mata."

"OK sai kin kawo Regular costumer."

Dariya tai kawai ta kashe wayar.
Wani farin ciki taji ya lullub'eta na jin muryar tasa.

*********
Bayan awa guda su ka fito da ga exam d'in mutum uku suka wakilta zuwa kasuwa cikin su takwas da za suyi ankon kala d'aya, daman tuni sun fiddata a waya kowa ya san kalar da kud'in.

Mudatex suka shiga kai tsaye don a nan suka San zasu same ta bada wahala ba.

Bayan sun siyo sun fito a bakin titi sukai sallama kowa yai hanyar unguwarsu ita kuma ta taho da duk atamfofin kamar yanda su ka shirya Ibrahim zai musu d'inki duka iri d'aya.

_*da yuyuwar nan gaba kad'an ya koma na kud'i*_🥰

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋

👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

*18/10/2019*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.