Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 22 of 26

_*page*_*43-44*

To kamar yanda kowa ya sani wuta na da cin rai,amma kuma k'addara ce da jarrabawa,in ka mik'a lamuranka ga Allah sai ja sami nutsuwa kuma ya maida maka mafi alkairi.

Khaleelee yayi ta maimaita kiran 'Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun' hakan yasa yake samun nutsuwa.
Yau kwana biyu da yin gabarar,duka kostomomin sa da yasan da kayansu gurinshi ya sanar dasu halin da ake ciki.kuma fad'a musu duk wanda yake ganin a biya shi kayansa to yayi mishi magana,wanda ya yafe kuma ya gode.

To dake lokacin kusan azimi ne akwai bala'in kaya a shagon nasu jama'a nata kawo d'inki,kuma mafi yawon kayan shagon masu tsada ne kasancewar yana hurd'a ne da masu hannu da shuni.
To ba'a raba su da sabbin customers ko yaushe, don haka duk wa'yanda basu wani saba ba suka nuna kin amincewarsu,wasu suce a raba asara ya biyasu rabi wasu suce a biyasu duka.

List yayi na wa'yanda suka nemi hakkinsu,da kud'in kayan nasu.

Tofa! Abun da yawa,lissafin da yayi kusan kayan dubu d'ari uku ake nema ya biya,dukda masu Neman basu fi mutum goma ba amma adadin kayan nasu yakai wannan kud'in.

Da farko Jabeer ca yai babu wanda zasu biya komai,don suma asarar da sukai bata misaltuwa,kekunansu babu Wanda zai moru,daga na d'inki har zuwa na surfani.k'arshe ma sa suka had'a karafunan y'an gwangwan ne suka siya.

Damuwar da Khaleelee ke ciki ta bayyana jikinsa, dukda k'ok'arin sa na boyeta.
Sosai Su'ada take kwantar mai da hankali,tana nuna mishi jarrabawa ce, yayi hak'uri, Allah zai maida mishi mafi alkairi.

Da kalamanta yake samun nutsuwa,haka Baba duk da yana cikin rashin lafiya amma zai kirashi d'aki yayi tamai nasiha da kalamai masu dad'i.

*******
Khaleelee ya had'a kud'in da suke cikin account d'insa duka budu d'ari da hamsin ne,kuma dubu saba'in ta mutanan da sukai mai transfer kud'in d'inkinsu ne,to tunda d'inki bai samu ba sun yafe mai kaya ai dole ya maida musu kud'in su. Bayan ya maidawa kowa ya rage dubu tamanin,tanan ya fara ragewa sabbin kostoman nasa.

Ranar litinin da Su'ada taje aiki, ta tsaya banki ta fito da kud'in cikin account d'inta duka,daman ita ba amfani take da kud'in albashinta ba,ko ya shigo barshi take ciki,in kaga ta cire kud'i to biki ko suna ne zatai gudunmawa ko anko,sai kuma alheri da takewa mutane.

A ranar ta bashi kud'in yaje ya bibbiya sauran kud'in su, duk da sunsha fama kafin ya k'arb'a, ca yai ba zai amsar mata kudinta ba,sai dai in rance ta bashi,sai da yaga da gaske tana mai kuka sannan ya amsa.

Bayan ya biya su duk kud'insu,sauran ya dawo Mata dasu,ta ajiye.sabida so take ta bashi ya sai keke ko guda biyu ne.

**********
Yau wata guda da yin gobarar su Khaleelee gashi har an shiga azumi.

Sun yi tsammanin hukumar dake kula da shagunan kasancewar shagunan gwamnati ne zata gyara musu shagunan da wuri amma har azumin ya kama ba'a gyara ba.
Kud'in da Su'ada ta bashi ya sai keke,guda daya siya ya ajiye a gida, wa'yanda suka sami labarin yana d'inki a gida ne suka d'an kawo mai ba wani me yawa ba.

To Alhamdulillah Abban Su'ada yayi rawar gani wajan basu gudunmawa a azumin nan tunda yasan halin da Khaleelee ke ciki,don haka kayan abincin da zasu buk'ata har na tsawon watanni ma ya had'a musu,dai dai da gishi sai da aka had'awa Su'ada cikin kayan abincin,tamkar da gara haka aka had'a musu.

Ba magana fa wajan nuna jin dad'in da Khaleelee yayi,yaje gida yayiwa Abba godiya sosai. Abba yace ba komai ai dole ne ya kula dasu.

Har kayan salla ma sai sa Abba tayiwa Su'ada kala uku, duk da yasan Su'ada ba rasa kaya tai ba,amma shi kayan salla in ka saba duk sanda rashi yasa ba kayi ba sai kaji ba dad'i, don haka ta had'a da y'an uwanta yayi mata.
Ita kuwa Nusrat daman tana can gidan tun yaye basu dawo da ita ba.don shi Abba ma so yake wai su bar musu ita,don yanda take kama da yaran gidan ya b'aci, hakan yasa Abban ke bala'in ji da yarinyar.

Alherin da Su'ada ta saba bata canja ba,satin salla taje kasuwa taiwa su Baby da y'ay'an Zakiyya siyayyar d'an kunne da sarka da dai y'an tarkacen yara mata.

*******
Ba wani d'inkin kirki Khaleelee ya samu ba amma dai yafi babu,da kud'in su kai girkin salla da y'an sauran hidima,babu yanda za'ai dai mutum yace yaga wani rashi a tare dasu,duk kuwa da babu wani kud'i a hannun Khaleeleen.

*******
Sannu sannu cikin Su'ada ya shiga wata tara, kamar yanda edd d'inta ya nuna tsakiyar wayan zata haihu,wannan karon Khaleelee bai mata wata siyayya ba,sabida har zuwa lokacin bai zauna daram a shago ba,duk da an gama musu gyara komai da komai,harma sun koma,to duka keke biyu ne a shagon Wanda Su'ada ta bashi kud'i ya siya sai kuma d'aya da Abbanta ya aiko masa dal a cikin kwalinsa.to ana dai samun abunda ake samu,dashi suke d'an cefane.

Don haka kudinta na watanni biyu na albashi da ta amsa bayan gobar nan shi ta had'a ta bada dubu sittin aka siyo mata rago da tunkiya a k'auyensu dake,Wanda tace a barshi sai ta haihu a kawo.
Sauran kud'in hannunta taje kasuwa tai siyayyar Haihuwa,sabida bata da komai duk ta baiwa Sakeena.

Don haka yanzu haihuwa kawai take jira da fatan sauka lafiya.

*********
Da ikon Allah kuwa tsakiyar wata ta haihu,d'anta namiji, cikin koshin lafiya.

Bayan sun dawo gida daga asibiti mama ta buk'aci Khaleelee daya taimaka ya bar Su'ada ta dawo tai wanka ko na sati uku ne a gida, sabida wannan karon babu me zama da ita Innaro bata da lafiya, sannan k'annanta duk suna makaranta ba cikin hutu ake ba

Babu yanda Khaleelee zai iya don haka ya amince,mama tazo da motarta ta d'auke su.

Sakeena dai tunda akai gobarar nan taji a jikinta, don ta tausayaa Khaleelee matuk'a, to amma a wani sashi na ranta take fad'in 'yanzu dai ba wani rawar kai tunda ba'a da komai,amma bayan d'an lokaci tana ta sa ido taga ta inda Su'ada zata gaza amma babu,komai yanda take a wadace haka take abunta.

Washe garin da akai haihuwar Khaleelee yaje gidan su Su'ada, bayan sun gaisa da Mama ya shiga d'akin da Su'ada take,tana zaune tana cin abinci ya shigo,da mirmishi ta tareshi,amma sai ta hango damuwa kan fuskarta, tsam tai da ranta har ya k'araso kusa da ita ya zauna yana d'aukar jinjirin.

Ji tai abincin ya fita a kanta,don haka ta tureshi gefe tare da maido duka hankakinta ga Khaleeleen.
A sanyaye ta gaisheshi ya amsa yana kirkiro mirmishin da bai kai zuci ba.
Kafeshi tai da ido cikin kallon tuhuma,abunda yasashi sakkowa kusa da ita ya zauna tare da damk'e hannunta cikin nasa,kallon juna suke na d'an lokaci kafin ta d'ora kanta a kafad'arsa.cikin k'aramar murya take mai magana. . . .
[2/24, 12:04 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.