Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 25 of 26

_*page*_*49*

Duk Kansu ba wanda ya k'ara magana,don jikinsu ya mutu,su sun gama sakankancewa fa Nusrat ta zama tasu,amma ga mama na zuwa da wani batu.

*******
Satin da akai hutun makaranta Mama tasa Jidda ta had'awa Nusrat kayanta da y'an yawa tace ta kaita gida tai musu hutu tunda Su'ada na gida yanzu.

Dukkansu ba wanda baiji kewar tafiyar Nusrat ba,amma ba yarda su ka iya.

Har cikin ran Su'ada taji dad'in hakan,Khaleelee ma da ya dawo ya ganta har da kaya fara'a tak'i barin kan fuskarsa.

****** Sosai Nusrat ta sake a gidansu,musamman da Baby kullum suna tare,da an mata wanka Baby zata d'auketa,in islamiyya zasu je tare da ita take tafiya,wata rana a korosu wata rana a barsu.

*******
A y'an kwanakin ne jikin Baba ya matsa,dole aka basu gado a asibiti,ciwo kullum gaba ya ke,har ya zama bai gane kowa.

Ranar jumma'a da asuba Allah ya k'arb'i ran Baba,tashin hankali wanda ba'a sa masa rana,tabbas Khaleelee da y'an uwansa sun shiga rud'ani,haka su Su'ada ji take tamkar Abbanta ne ya rasu,kuka ta yi shi ta gode Allah.

K'arfe bakwai na safe aka kai Baba makwancinsa.

Da daddare bayan y'an zuwa gaisuwa sun tsagaita sai y'an uwa na jiki kawai, Khaleelee ya daddafa ya shigo wajansa,ko gani ba yayi sosai sabida yanda kansa ke bala'in ciwo.

Kallo d'aya Su'ada tai mishi tai k'asa da kanta don wani bala'in tausayinsa take ji.

Ruwan wanka ta had'a mishi ta shigo d'aki ta sameshi kwance kan gado ya dafe kansa da hannu biyu idanuwansa a lumshe sai d'an hawaye ke bin gefen fuskarsa,zama tai gefensa tana rik'o hannunsa cikin sanyin murya tace "Abban Nusrat,kayi hak'uri don Allah, a wannan lokaci baba addu'ar mu ya fi buk'ata sama da hawayenmu,ka daure ka bar kukan haka."

Tashi yai ya zauna dafe da kansa cikin dashashshiyar murya ya fara magana "Su'ada Baba ya tafi,shike nan ya bi umma,yanzu bani da wata majingina ta iyaye.Su'ada Baba ya sha wahala kafin rasuwarsa,tun daren jiyan nan numfashinsa ke zuwa da dawowa,sai asuba Allah ya k'arb'i ransa."
Ya k'arashe maganar yana tsiyayar da hawaye masu zafi.

Dafo shi tai jikinta tana d'an pitting bayansa, tare da share mai hawaye,kalamai ta rink'a masa masu kwantar da hankali,har taji yana ta sauke ajiyar zuciya,sannan ta d'ebo ruwan sanyi ta bashi yasha.

shayi ta had'a mai mai kauri,don tasan rabonshi da abinci tun jiya da dare.
Da k'yar ta lallab'ashi ya sha.
Sannan ta raka shi band'aki ta taya shi ya yi wanka.

Daren gaba d'aya bai wani samu bacci ba,haka ya ke ga sauran y'an uwansa,ko baccin ya d'auke su bai yin nisa,don duk Wanda a kaiwa irin Wannan mutuwar bacci na wahalar zama a idonsa.

Haka aka ci gaba da karb'ar gaisuwa,tsawon kwana bakwai, kullum da ga gidansu Su'ada sai an kawo abincin sadaka manyan kula.
Abban Su'ada tun ranar da akai rasuwar ya taho daga legos, da shi ake zaman kullum yana gidan.haka ma mama da y'an uwanta,sun yi kara sosai sa sosai, har aka share zaman makoki.

*****
Kwana goma da rasuwar Baba aka koma makaranta, ranar kuma Khairiyya tazo ta d'auki Nusrat.
Amma tun ranar duk Friday sai an kawota lahadi Khaleelee ya maidata.

*Bayan wata guda*

****** Shirin bikin Jidda ake ta yi,tunda aka fara shirin biki sosai Su'ada bata zama ko yaushe su na tafe siyayyar kayan biki.

Su'ada ta kawowa Sakeena atamfar yini kyauta,sannan taiwa Baby ankon duka kala uku,don tace da ita za ta tafi sabida kula mata da Muklees, wanda lokacin ya ke shekara guda,yana yawonsa ko ina, da ke shi yana da kuzari da kazar kazar sosai.

To fa! Sakeena dai ta fara saduda,don zuwa yanzu tasan Su'ada tafi k'arfin ta, ta k'ere mata matuk'a,tun randa aka fara bikin ta gano harkar arzik'in da ya d'aure mata kai,don yanzu take k'ara tabbatarwa su Su'ada manyan mutane ne,kawai dai don su ba masu nuna abun bane.

Hidima akai sosai ta auran Jiddah, Su'ada fa ta gyagyaje ta sha sha'aninta,daman ba ta da wata damuwa da Muklees don ko yaushe yana tare da Baby,to ita ma Nusrat ganin Baby ya sa ta daina yarda da kowa a gidan balle taga ana biki,duk jama'a sun cika ko ina.

Ranar yini Su Zakiyya duk sun wa Su'ada kara,don duk Wanda ta gayyata y'an uwan Khaleelee da mak'ota ba wanda bai zo mata ba.

Haka akai hidimar biki aka k'are lafiya.

Ranar da su Su'ada za su dawo gida fir Nusrat ta k'i zama,wai sai ta bisu,musamman yanzu da ta shak'u da Baby,don ko zuwan kwana biyun tai ko yaushe tana gun Babyn.

Su'ada tace ba zata tafi da ita ba,sabida ba week end bane,ita kullum bata gida ina zata rink'a barinta.
Tana fad'a Baby tai caraf tace"Aunty sai ki rink'a barinta a guna,tunda yanzu yamma nake,in kin dawo sai na tafi.
Abba na jin haka yace ta tafi da ita,kar a barta kanta ya yi ciwo.duk yanda yake nacin son zaman yarinyar tare da su.

Khaleelee na gida su ka dawo, yana ganinsu da Nusrat yace "A'a y'ar week end yau fa litinin me ya had'oku da ita?"

Su'ada bayan ta dire kayan hannunta ta sauke goyon Muklees tana fad'in "Kuka take ta yi wai sai ta biyo mu,Abba yace mu d'aukota bayan ya san ina fita ko yaushe."

Kallonta yai qur, zuwa can yace "Ni nai murna da zuwan ta."

Kallonsa tai kamar ba ta gane me yake cewa ba tace "Ban gane ba."

Gyad'a kai yai bayan ya d'aga yarinyar yace "Eh na ga ke kamar bi kiyi murnar biyoki da tai ba ."

D'an mirmishi kawai tai ta wuce cikin d'aki.

A can ya isketa ta na rage kayan jikinta,ya tsaya bakin k'ofa hard'e da hannayensa,jiyowa tai ta na d'an kallonsa tai mirmishi kafin tace " Ya gida? Ya zaman shiru?"

Gyad'a kai yai ya na fad'in "ga zaman kad'aici ya dameni,amma ai yanzu ya k'are tunda kin dawo."

Dariya tai kawai ba ya k'ara tankawa ba sai da ta canja kayan sannan ta k'araso gareshi tana sakar mishi wani lafiyayyan kiss,shi ma ya maida mata martani cikin zak'uwa da kewa.

Taimaka mata yai su ka shiga kitchen kafin a kira salla ta d'an dafa musu abinci me sauk'i.

Nusrat na can wajan Baby har ma tai bacci.sai da za su kwanta ne Khaleelee ya je ya amsota.

_________________
Washe gari Su'ada ta shirya tafiya zuwa makaranta, Nusrat ba ta tashi ba,don haka Khaleelee yace ta barta in ta tashi shi zai mata.

*********"
Tun daga ranar ko yaushe in Su'ada ta tafi wajan koyarwarta shi ke shirya Nusrat ya bata abinci sannan in zai fita shago wajan sha d'aya sai ya kaita gun Baby.

Shi kuwa Muklees daman akwai me renonsa
A cikin makarantar da ta ke,don haka da ta je take kai mata shi.

************
Rayuwa ta mik'a,yayin da zaman Nusrat ya dawo gida da gaske, don haka Khaleelee ya sanyata makaranta.duk da k'arancin shekarunta amma tana da surutu.tun daga lolacin in Khaleelee Su'ada ke fita da ita ta ajeta a school d'insu da ke gaban layin kad'an.

"""""''''''Wata ranar lahadi Sakeena ta tashi da ciwon nono,abu kamar wasa sau gashi zuwa washe gari ciwo ya tsananta,sunje asibiti aka had'o mata magunguna,amma kullum ba sauk'i sai gun Allah.

Kacokan Su'ada ta daukewa Sakeena duk ayyukanta, ita ce mata girki shirya yara,sannan ta kula da ita.haka Su'ada za ta yini a tsaye wajan hidima,ga tata ga ta Sakeena,dole ta d'auki hutu a makaranta.

Ciwon Sakeena ya tsananta hakan ya sa aka basu gado a asibiti,duka d'auniyar Yara ta k'ara ninkarwa Su'ada, sannan ga girki fa take dare da rana ta aika musu asibiti.kullum da dare kuma Khaleelee ya d'auketa su je dubata.

Satinta biyu a asibiti Allah ya bata lafiya su ka dawo gida, a nan ma Su'ada ba ta bar hidima ga Sakeena da y'ay'anta ba.don doctor yace ta nisanci zuwa kusa da wuta,hakan ya sa Su'ada bata bar mata girkinta ba.

Bayan wata guda,Sakeena ta warke ras,har ta fara cike ramar da tai.
Wata ranar jumma'a da dare,duk yaren na tsakar gida a zaune,Nusrat na kwance gefe ta fara bacci,Sakeena ta fito daga d'akin ta,kallon Nusrat da tai bacci tai,sannan ta kalli Baby tana mata fad'a "Baby ya ki ka bar Nusrat kwance cikin sauro, kin ga har ya fara hawa jikinta,maimakon da tai baccin ki shigo da ita d'aki."

Kafin Baby ta taso Sakeena ta tsugunna ta ciccib'i yarinyar ta na shiga da ita cikin d'akin ta, kan gado ta d'orata tare da sakar mata net,sannan ta fito tsakar gidan itama ta zauna,kasancewar ba wutar NEPA kum injinsu babu mai a ciki.

Su'ada da ke tsakar gidanta tana jiyo sanda Sakeena kewa Baby fad'a akan Nusrat,mirmishi tai k'asan ranta kuma da mamakin yanda yanzu gaba d'aya Sakeenan ta canja,duk halayenta na kyashi da hassada ta ajiye,wata irin kula ta ke bawa Nusrat da Muklees, sai tai musu abu ma ba taiwa y'ay'anta ba.tun farfad'owarta da ga ciwo duk tai sanyi.

Fitowa Su'ada tai tsakar gidan Sakeena sab'e da Muklees,da fara'a Sakeena tace "Wai har yanzu bai bacci ba wannan sojan?"

Y'ar dariya Su'ada tai ta ajiye shi kan tabarmar tana fad'in "Rigima ta hanashi kwanciya,ga Abbansa bai dawo ba da na jonasu nai aikin da ke gabana,na tara singing sosai na students."

Rik'o hannunsa Sakeena tai sannan tace "Ai da kin kawo shi nan kin yi aikinki,ga Nusrat har tai bacci shi ido biyu,barshi ki je ki aikin ."

Juyawa Su'ada tai tana fad'in "Yauwa ai kuwa kin kyauta,bari nai sauri sauri na gama."

Sakeena kuwa d'aukan Muklees d'in tai ta sashi a jikinta tana ta lallab'ashi har yai bacci sannan shima ta kaishi d'aki kusa da Nusrat ta kwantar da shi.

Wajan k'arfe tara Yaya Muktar ya dawo,yana shiga d'aki ya iske su Nusrat a shimfide kan gadon Sakeena, abunda ko y'ay'anta ba ta bari su kwanta mata a gado,abun ya mishi dad'i, shi kanshi yanzu canjin da yake gani tare da ita abun na birgeshi sosai.

D'an mirmishi yai yace "Bak'i ki kai a d'akin?"

Cikin yar dariya tace "Su Nusrat ne fa."

Kamar bai gane ba yace "Au,mamansu bata nan ne?"

"A'a aiki dai za tai ne,ta kawoshi nan,Nusrat kuwa daman ka san sai tai bacci take shiga d'akin su."

Zama yai gefen ta yana rik'o hannunta ya fara magana cikin k'asa da murya, "Sakeena! sosai nake jin dad'in yanda ki ka d'auki Su'ada yanzu tamkar k'anwarki,hakan na faranta raina,musamman da kike k'ara Jan yaran nan a jikin ki, hakan zai sa su k'ara shakuwa da y'an uwansu,na tabbata ko bayan ranmu y'ay'an mu zasu zarce da karfaffan zumunci.na gode sosai Sakeena, ki k'ara had'a mana kan zuri'armu matsayin ki na babba kin ji."

Gyad'a kai tai jikinta a sanyaye tace "Daman can shed'an ne ke sani kin Su'ada, don Su'ada ba ta tab'a yin abunda zai bata raina da gangan ba,tana ban girmana yanda ya kamata,sannan a wannan rashin lafiyar tawa na gasgata cewa FACALA y'ar uwa ce,kuma abokiyar hadin kai ce,yanda Su'ada ta tallafeni da yarana da duk hidimarmu ni na kasa mata hakan a lokacin da take laulayin ciki,na ji kunya matuk'a da yanda tai ta d'awainiya da ni,bata kyankyamina haka za ta zauna ta wanke min wajan ciwon nan tas ta samin magani,sannan ta shirya min yarana, tai musu girki.lalle FACALA ba abokiyar fad'a da gaba bace.kullum ina son bawa Su'ada hak'uri kan abubuwan da nai mata na rashin kyautawa a baya amma ina jin kunya wlh."

Fara'a sosai kan fuskarsa yace "Karki damu,kawai ki bata hak'uri ki cire jin nauyi ko wani abu a ranki,hakan zai sa ku k'ara kusanci da juna."

Gyad'a kai tai kafin tace "Insha Allah da safe zan mata maganar."

*Taku ce*
*Y'ar mutan Jaoji*🙋‍♀

👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

💔💔💔💔💔💔💔
*Na sadaukar da wannan page d'in kacokan ga k'awa kuma Aminyata. Amrah Auwal mashi,Allah ya tsareki a duk inda ki ke,ya sa kece amrya kuma uwar gida a gidan uncle Aliyu sadauki*😍🙏

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.