Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 26
_*page*_*31-32*
Haka aka ci gaba da gudanar da ibadar azumin Ramadan cikin falala ta ubangiji, lokacin da azumi ya raba Su'ada ta shirya zuwa gida yi musu barka da shan ruwa,tun safe ta tafi,sai bayan sallar Isha'i Khaleelee yaje ya d'auko ta,da abinci ta taho don ba girki Zata yi ba,ai kuwa suna zuwa gida yace "Su'ada zuba min abincin nan in ci,na kasa yin bud'e baki gamsashshe duk abunda nasa a bakin sai naji ba d'and'ano,kin gama saba min da girkinki Su'ada, ban jin dad'in wani abinci bayan naki."
Cikin jin dad'in yabon da yake mata tai y'ar dariya tare da fad'in "To shi wannan d'in da za ka ci kasan wa ya dafa ne?"
Shima mirmishi yai da fad'in "Koma ya dafa in dai daga gidanku yake to d'and'anon iri d'aya ne,in Mama ce tai to zaifi ma naki dad'i,tunda gunta ki ka koya,in kuma su Jidda ne su kai to d'and'anon zai zamo d'aya tunda duk gu guda kuka koya."
Tana dariya ta zuba mai,Sannu ta dawo kusa dashi take bashi a baki,a hankali cikin kwantar da murya take mai hira "Khaleelee na,kasan me kuwa? Allah ko yau nima ban wani maida hankali wajan shan ruwa ba,sabida duk sai naji ni wani sakayau, na saba komai tare da kai,daurewa kawai nai fa,amma da kamar na kiraka nace kazo na kasa cin komai."
Kanne ido d'aya yai yana d'age mata gira sannan ya ce "Eh da kin kirani,don a dai dai lokacin nima hakanne tare dani,duk da na san ke fa harda kewan wani abu ya hanaki sakewan."
da sauri ta d'an zaro ido da fad'in
"Kai, kewan me kake so kace?"
Kauda kai yai cikin basarwa yace "Kewan wannan jikin mana,kin saba kina cin abinci ina miki abubuwa,kina mak'alemin a jiki kamar mage."
Turo baki tai tace "A'a ni dai, abunda na san zan dawo na sameshi,kuma yanzuma ka jangwalo kaci gaba da ci da kanka ni kuma in kwanta anan."
Ta fad'a tana zamewa a jikinsa.
Ci gaba yai da cin abincinsa yana k'ara tsokanarta da wai daman haka take so,ita dai bata tanka shi ba tai lamo a jikinsa.
Da k'yar Su'ada ta rok'i Khaleelee ya barta zuwa kasuwa a lokacin da salla ta rage sati guda,K'annanta taiwa siyayya duk da da taje gida ta tadda an gama sai musu komai to amma hakan ba zai hana ta kyautata musu ba,under wear's ta sai musu da kayan kwalliya,sannan ta siyawa k'aninta Khaleelee wasu takalmi masu kyau.
'Ya'yan Zakiyya kuwa da Baby ta sai musu y'an kunne da sark'a sa su Abun hannu,ta siya musu kayan kwalliya,sannan ta had'awa Baby harda jaka,sabida tana jin kullum yanda yarinyar ke nacin Sakeena ta siya Mata jaka duk 'kawayenta an sai musu,amma uwar tai mirsisi da rantsuwar ba zata siya ba,kuma fa badan bata da kud'in ba kawai siyan ne ba niyya kuma alhalin Ubansu ya bada kud'in ai musu siyayya.mutuniyarta Islam kuwa wata riga da wando masu kyau y'an kanti ta siya mata da kayan kitso dasu ribbons masu kyau kalar kayan.
Itama taiwa kanta siyayyar duk abunda take da buk'ata, sannan ta tsaya wajan y'an girki ta had'a duk wani abu da tasan za ta buk'ata da sallar nan.
Lokacin da ta dawo gida bata baiwa kowa abunsa ba,sai da dare data Nunawa mijinta sannan ta fito da na su Baby ta k'wala mata kira,da gudu yarinyar tazo da fad'in "Aunty gani."
Mik'a mata kayan tai tace "Sark'a dasu dan kunne da jaka naki ne,sauran kuma duk na Islam ne."
Ihun murna yarinyar tasa ta fita a guje ko damar godiya bata samu yi mata ba don murna.
Lokacin yaya Muktar na nan ta shiga falo da kayan tana ihun murna,ajiyewa tai a gabansa tana d'aukar jakar tace "Abba kaga Aunty Amarya ce ta siyo min jaka,Wallahi Abba kaga daman kullum sai nacewa Mamanmu ta siya min sai tak'i,gashi Aunty ta siya min,kai wallahi naji dad'i na godewa Allah na godewa Aunty Amarya,Abba sauran kayan na Islam ne."
Ganin yanda duk ta rud'e da murna yasa Abban nasu dariya yace "Kai gaskiya yau Aunty Amarya tasa Maman mamanta cikin farin ciki,To maza koma kice mata an gode don da ganin yanda kike a rude biki ma yi godiya ba."
Juyawa tai da sauri sak'ale da jakarta ta koma taiwa Su'ada godiya.
Islam ma tana murna da aka gwada mata kayan,yace kema je kicewa Aunty an gode.
Bayan fitarta ya kalli Sakeena da take d'an yak'e kadaran kadahan yace "Sakeena je kicewa Su'ada nace na gode ."
D'an tab'e baki tai tace "To godiyar me kaikuma za ka mata,ba ga yaran sun je sun yi ba,kuma nima in ta fito da safe zan mata."
Tsayawa kawai yai yana kallonta da takaici yace "Yanzu mutum yai wa 'ya'anki wannan hidimar amma ki zauna sai da safe zaki gode mata,alhalin kuna gida guda,Tashi don Allah ni ki je ki mata godiya."
Ba dan taso ba ta tashi ta fice.
A turb'une tai sallama hakan ya sa ba suji Sosai ba,ita kuma bata k'ara ba ta sako kai falon a dai dai lokacin da Su'ada ta haye kan ruwan cikin Khaleelee tana k'ok'arin k'wace wayarta da ya d'auka wai zai shiga wani group d'in ta na WathApp da yaga an sa SIRRINMU MATA, sosai su ke kokawa da juna,dariya taci k'arfin Khaleelee wanda yasa take k'ok'arin cin galaba ta k'wace wayar.
Sakeena da ke tsaye tana kallonsu wani k'ululun bak'in ciki ya turnik'eta,wato ma suna jinta su ka k'i amsawa,sabida su na wasan jakai😃🤭,juyawa tai ta bar falon,data koma tacewa Yaya Muktar ai tai mata godiyar.
Da safe da Su'ada ta fito gaida Baba,ta tsaya su na gaisawa anan take mata godiya.Su'ada tace ai ba komai duk yiwa kai ne.
Kiran number d'in Zakiyya tai tace ya turo Umma Salama ta amsa musu y'an kunnaye,Zakiyya tai ta godiya.
A haka aka cinye watan Ramadan a kai salla cikin k'oshin lafiya,Su'ada ta taka rawar gani sosai,don tai abincin Salla wadatacce duk gidajan danginta dana dangin miji ta aiaika musu.mijinta ma ta fiddashi kunya wajan aboka,domin kuwa taron cin abincin salla a kai a shagon d'inkinsa,wanda Su'ada ta shirya musu abinci iri iri da lemuka.
Daga gajiyar hidimar salla sai ciwo ya rafke Su'ada, ciwon kai yak'i sauka tsawon kwana uku,tun tana shan magani a gida har Khaleelee ya takura mata zuwa asibiti.
Da kansa ya kaita asibitin,gwajin farko su ka tabbatar musu yaron ciki gareta na wata guda,tofa murna farin ciki nishad'i su su ka had'u su ka lullub'e rayuwar Khaleelee a lokaci guda,ya rasa ina zai sanya ransa,godiya yai tayi ga mahaliccinsa,ita kam Su'ada ciwon kai mara misali ya sakota gaba ko ido bata iya bud'ewa, ji take kamar kanta zai tsage,tana dafe da kannata ya kamata ta tashi, su ka fito zuwa bakin titi don daman a a dai daita su ka zo.
Da farin cikinsa ya shiga gidan, tun da ga k'ofar d'akin Baba yake tambayarsu ya jikin nata, cikin fara'a sosai Khaleelee ya amsawa Baba da fad'in "Da sauk'i sosai Baba."
Yanayin da Baba ya ga Khaleelee na farin ciki ko bai tambaya ba ya bashi amsar dalilin ciwon nata.
Tun fa daga wannan ranar sai ciwo ya 'kara sako Su'ada gaba kamar an k'ara hankad'oshi, laulayi sosai ta keyi,amai,ciwon kai,zazzab'i, kwad'ayi ,tsirfa ci wannan k'in wannan, sai ya zamana ko 'kanshi ba ko wanne Su'ada ke so ba,dukka turarukanta taji ta tsanesu,sai na Khaleelee kawai ta ke so,babu abunda ya dami Khaleelee game da tsirfarta,duk abunda tace tana so shi zai mata,duk aikin gidan ya dawo kansa, kama daga girki, wanke wanke,shara da gyaran gado, dukka shi ya ke yi,ko wanka bai barinta tai da kanta, kulawa ta musamman ya ke bata,don tausayi ma take bashi sosai,yanda kullum jikinta bai rabo da zafin zazzab'i,in an samu ya sauka to rana ta take,a nan kuma ciwon kai zai tsananta tai ta tsiyayar hawaye.
Ranar da Mamanta ta zo dubata taga wahalar da take sha ga aiki Khaleelee nata fama dashi,tace Jidda ta zauna ta rink'a musu aikin gida shima Ibrahim ya rink'a fita neman kud'insa, don baya samun zama a shago ko yaushe hankalinsa na gida in ya fitanma.
To zuwan Jidda ya sa Khaleelee samun rangwamin aiki,don yanzu bai aikin komai sai na kula da ita in yana gida, yawon aman da take yi yasa likita ya rubuta musu drip yace a rink'a sa mata,to dake Jidda daman fanninta ne sai take d'aura mata drip d'in kullum d'aya ake k'ara mata,har zuwa lokacin da jikinta zai yi k'wari.
Sakeena kam kullum zata shigo sau d'aya tai mata sannu sai kuma washe gari,don da tai bak'i take basu labarin irin laulayin da Su'ada ke yi take fad'a musu wai tsabagen iskanci da tsirfa ne,da nuna ita wata ce,d'aya cikin k'awayen nata tace "Haba Sakeena kamar biki tab'a haihuwa ba,ai ke mace ce kin san ciki kowa da kalar nasa,sannan ita na fari ne dole zai bata wahla."
Tab'e baki Sakeena tai da fad'in "Ba wani fa,da iskanci ko da laulayin,kullum sai tace ga abunda zata ci kuma sai an dafa tak'i ko kallonsa sai ta canja wani abun,shi yasa take ban haushi, wai ita dole gata me ciki."
Haka taita surutanta na son dole sai ta kushe Su'ada a gun duk wani da ya santa.
To ga wata sabuwa,rana tsaka Su'ada ta tashi da fad'in wai bata son warin gass da an kunna sai tai ta 'ko'karin amai nan da nan kuwa za tai ta kwara shi,abunda duk aka samu taci sai ta fito dashi, Jidda ta d'ora girki haka ta sauke,sai ruwan zafi ta jona musu a kettle su ka sha Tea,da rana kam su ka rasa abunda zasu ci, dole Khaleelee yaje siyo musu abinci,sam Su'ada tak'i ci, tana kallon abincin ta kauda Kai,don ji tai har kanta ya fara juyawa.can tana ta kwance taji yo kamar 'kamshin girkin Sakeena, nan da nan taji shi take son ci,ta kalli Jidda cikin yanayin wahla da ciwo tace "Plss Jiddah ce Maman Abba don Allah ta zuba min girkin ta in ci."
Ba musu Jidda ta sanar da Sakeena sa'kon Su'ada, ba dan taso ba ta amsa da to.
Bayan ta gama girkin ta zubo mata a wani d'an kwano Wanda bai taka kara ya karya ba,ai kuwa Su'ada kamar ta kwana bata ci ba haka ta hau abincin nan da ci, kafin ta gama dashi,Jidda kallonta kawai cikin mamaki tace "Wai Aunty Su'ada dad'in wannan girkin kika ji haka? To in jalop d'in ki ke so a yi miki mana."
Girgiza kai Su'ada tai tana fad'in "Wannan d'in tamin dad'i, da zan sami 'kari ma zan 'kara, girkin yai dad'i sosai."
Shiru Jidda tai tana mamakin lamarin ciki irin haka,a ranta tace "Allah karka had'ani da wannan lalura ni kam ko da lokaci na ya zo."
To da dare ma haka Su'ada tace Sakeena ta sa mata abincinta, Kai tsaye Sakeena tace ita tuwo tai, da Jidda ta fad'a mata tuwo ne tace koma meye ta bata.
Nan ma ba wani me yawa ta zuba mata ba,hannu baka hannu 'kwarya Su'ada ta cinye ta na sud'e hannu.Khaleelee da mamaki shima ya ke kallonta,Jidda tace mai da rana ma haka tasa na amso mata ta cinye kamar ta samu nama.
Y'ar dariya yai yace "Ai Alhamdulillah ma tunda an samu in taci bata aman, bari zansa m Maman Abban magana ta rink'a sa sanwa da ita tunda abuncinta kad'ai take so,mune dai ban san ya zamuyi ba Jidda,Kinga bata son warin gass kuma ba zamu zauna da yunwa ba,meye Shawara?"
Shiru Jidda tai na d'an lokaci kafin tace "Yaya kawai ka siyo mana murhun gawayi,sai ka siyo mana gawayin mu rink'a amfani da shi."
"A'a ko dai risho Jiddah,kin iya amfani da gawayi ne?"
Cikin dariya tace "To ai ni risho d'in ne ban iya amfani dashi ba,sabida ban tab'a kunnawa ba,amma kaga a gida wani sa'in in aiki ya mana yawa ba waje a gass muna kunna kol d'in."
Mik'ewa yai yana fad'in "OK bari na duba naga me gawayin bakin titin nan bai tashi ba."
Daga haka ya fita.
**********
Tsawon sati kullum Su'ada ba ta iya Kai komai bakinta sai girkin Sakeena, ya zama shi kad'ai take jin dad'in sa,safe dare rana.ita dai Jidda zata dafa musu su hud'u ita da Khaleelee da Baba.
Tun Sakeena na yin Kara harta fara turb'unewa,wai a dole ita ta zama wata abar ana nema a wajanta.
Wata ranar litinin Sakeena tak'i d'ora girki har k'arfe d'aya saura ,yara su ka dawo makaranta ba abinci ga Su'ada can ms nata jin yunwa,kawai sai tacewa yaran bata jin dad'i itama,ba zata iya wani shiga rana ta d'ora girki ba,kowa yasha gari da suga da gyad'a. "
Haka yaran su ka jik'a garin su ka sha suna ta murna,don a marmarce suke shan abunsu,Baba kam tuni Jidda ta kai mishi abincin da ta girka,lallashin Su'ada tai tayi akan taci wanda ta girka,ganin yanda Jiddan ta damu ya sa tace ta d'ebo mata,ai kuwa lomarta uku ta fara amai,ita kam ba ta San dalilin da yass yanzu bata iya cin komai ba sai girkin Sakeena.
Ganin yanda ta ke ta amai ga ba komai a cikin yasa Jidda kiran Khaleelee a waya ta shaida mai halin da ake ciki, ba jimawa ya shigo gidan, lokacin ta gama aman tana kwance kan cafet tana ta juyi,Ya d'agota jikinsa ya na tambayarta me take so ya siyo mata.
Cikin muryar rashin lafiya tace "Shinkafa na ke so,amma ta maman Abba ga Jidda tace wai ba tai girki ba yau."
cikin tausayawa ya ke shafa kanta,a hankali yace "Kiyi hak'uri ki canja wani abun na siyo miki yanzu yanzu."
Girgiza kai tai idonta na cika da kwalla tace "Ban son komai wallahi, shinkafar kawai na ke so,kuma tunda babu zan jira in tai na dare sai naci."
"A'a Su'ada ya zaki zauna ba abinci ko kad'an a cikinki,tun safe fa sauran gyad'ar nan kawai ki ka ci,kuma ki zauna har dare."
Baccin da ya fara daukanta ya sa bata k'ara tankashi ba ta gyara kwanciya sosai a jikinsa.
Shi kam gashinta kawai ya shiga shafawa yana matsa jikinta da hannu guda sabida taji dad'in yin baccin. Ai kuwa ta saki jiki tana sakin minshari alamar baccin yayi nisa.
*TAKU CE*
*'YAR MUTAN JA'OJI*🙋
[2/23, 11:58 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.