Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 6 of 26

_*page*_ *11-12*

Bayan Su'ada ta shiga gida ta d'auki ledar da Ibrahim ya kawo mata ta kaiwa Mama.kayan kwalliya ne da turaruka na mata masu kyau da k'amshi. Mama tace "To an gode mai Allah ya bar zumunci."

D'aukan ledar tai ta wuce da ita d'akin su tana k'ara duba kayan fuskarta d'auke da mirmishi.

Bayan Sallar magrib ta d'auki wayarta ta kunna data,Sakon ban gajiya ta turawa mai da karin godiya,duk da bai online,itama kashe datan tai ta fito falo don cin abincin dare da dukkan y'an gidan kamar yanda al'adar gidan take.

Wajan k'arfe tara bayan sun gama hira ta dawo d'aki ta cire wayarta jikin charge, bayan ta hau WhatsApp sak'on Ibrahim ne ya fad'o cikin zak'uwa ta bud'e,shima dai godiyar ya mata da karamcin da su kai mai,mirmishi tai ta na bashi amsa.

" _Ka canci fiye da haka a gareni Khaleelee, ina jinka tamkar d'an uwana na jini, fatana zumuncin mu ya dore fiye da haka_"

Ibrahim da ke zaune k'ofar gida kan dakali yana shan iska kasancewar ba wuta yai mirmishi bayan karanta sakon nata,sannan shima ya maida mata amsa.

" _Insha Allah zumuncin mu me d'orewa ne,ni ma matsayin k'anwa na d'auke ki Su'ada, kuma insha Allah nan gaba ma matsayin ki zai zarce hakan_"

Maimaita rubutun tai ta yi,tana tunanin in matsayin ta ya zarce na k'anwa a gun Ibrahim to me zai koma? Bata da amsar tambayar don haka ta maida mai amsar

" _Haka na ke fata insha Allah_"

" _ki cewa takwara ina mai bangajiyar surutu fa_"

😂" _zan fad'a mai da safe yanzu ya yi bacci_"

Wata hirar suka shiga daga nan kuma. Su'ada na ta juyi kan gado cike da farin ciki,don yau Ibrahim ya bata lokaci sosai sun sha hira duk da rabi duk kan matsaltsalun karatu ne da rayuwar makaranta amma sun d'au lokaci suna tattaunawa sannan su kai sallama.

*****************
Tun daga wannan ranar sai wata shak'uwa sosai ta k'ara shiga tsakanin Ibrahim da Su'ada, kasancewar yanzu ba school tana samun lokacin chart sosai,shi kuma in bai da aiki kawai sai yaji yana zamu d'in bud'e data ko zai ganta online su yi hira.

A haka wata guda cif da Mama ta d'ibawa Su'ada ta fidda miji cikin samarinta ya cika,kuma a lokacin ne Jameel ya bud'e mata wuta kan ta bashi dama ya aiko, kullum sai dai tace ya bata lokaci, ba ma shi kad'ai ba ke damunta kan suna son fitowa.duk ta rasa sukuni, Allah ya taimake ta Mama batai mata maganar ba,har Abbansu ya dawo gari,hankalin Mama ya koma ga kula da mijinta.

Yau da dare suna chart da Ibrahim take bashi labarin halin da take ciki.
Ji yai wani gumi ya yanko mai ya ji gabansa na fad'uwa, cikin ransa ya ke tunanin anya bai son yin sake kuwa,anya wankin hula bai shirin kaishi dare kuwa? Lalle in ya ci gaba da wannan zurfin cikin zai kwana ciki.

Tattaro nutsuwa ya yi ya sawa kansa,sannan ya fara typing

" _Su'ada ashe y'an takarar taki da yawa haka? An yi masu k'ananun jam'iyu zasu iya tsayawa takarar neman wannan kujera kuwa_?"

Bata gane zancan nashi ba,sai taga ma kamar wata yake son bawa amsa ba ita ba,don haka tace mai

" _Ban gane ba Khaleelee ko baka fahimci maganata ba_"

Mirmishin yak'e yai daga kwancan da yake don cikin damuwa ya ke jinsa sosai.

" _Na gane mana Su'ada, na san me kike nufi nine dai biki fahimci maganata ba_"

Amsa ta maida mai da
" _Eh gaskiya hakan ne ban fahimci zancan naka ba_"

" _Su'ada yanda tarin maneman auran ki su ke,kuma su ka shirya aure a yanzu, shin yanzu in me k'aramin k'arfi kuma wanda zai iya yin aure amma nan da shekara guda ya zo neman soyayyarki a yanzu zaki bashi dama kuma ki soshi_?"

Ji tai kanta ya wani yi gim ta fara gane me Ibrahim ke son cewa,in har kuwa hakan ya kasance za tayi farin cikin cikar burinta.

" _Abunda ba ka sani ba Khaleelee duk cikin masu neman auran nawa ba wanda hankalina ya kwanta da shi,wlh duk wanda na zab'a cikin su na cuci kaina,don duk basu cika sharud'an da nake so mijin da zan aura ya cika ba,basu da wasu quality's da nake buk'ata ga mijina_."

" _Su'ada shin namiji irina me irin halayena zai iya zama cikin zuciyarki_?"

Hannayenta har rawa su ke wajan maida mai amsa

" _Mai zai hana Khaleelee? Ban Neman komai tare da mijin aure na irin kyawawan halaye, sam abun duniya bai birgeni ga namiji matuk'ar halayensa muyagu ne,abu na gama cikar halitta wannan itama ina fatan samu,ba kuma wai kyawun fuska ba,Aa kawai dai in namiji ya kasance kalar sadauki shima yana birgeni_"🙈

"Alhamdulillah."
Ya furta a fili tare da d'ora wayar kan k'irjinsa, lalle ya san ba zai sha wahala ba wajan Su'ada ya fuskanci samun soyayyar ta cikin ruwan sanyi.

" _Su'ada_! "
" _Na'am Khaleelee_"

" _Shin Ibrahim zai iya bayyana miki ya na cikin y'an takarar neman soyayyar ki_"

"Wayyo Allah na,Allah Allah wai gaske ne wannan rubutun da Khaleelee ke yi ko tsokana ya ke?"

Su'ada ta fad'i bayan ta mik'e tsaye tana k'ara kallon screen d'in wayarta.

Rasa me zata maida mai amsa tai sai yarfe hannu take kamar me jin fitsari, minti goma cif yaga bata maida mishi amsa ba don haka yace

" _Su'ada biki ce komai ba,ko dai ban kai in shiga cikin y'an takarar ba_?"

Saita kanta tai wajan bashi amsa " _Khaleelee_🙈"

" _Hhhmmmm bud'e idon kiyi magana mana_"

"🙈 _kunya na ke ji,ban San me zance ma ba_"

Wadataccan mirmishi yai yana jin wani sukuni na ratsashi.

" _Karki damu fad'a min duk abunda ke ranki_"

" _Ba komai a ran Su'ada sai Khaleelee_🙈🙈🙈

Tana tura mai tai saurin kashe datar da wayar ma gaba d'aya.

Shi kam rubutun yai ta maimaita karantawa yana sakin wani mirmishi me cike da zallar shaukin so.

*********
Su'ada kwana tai mafarkin Khaleelee. Da safe kowa ya ga tsananin fara'a tare da ita,duk da ita d'in me fara'ar ce amma ta yau ta banbata, Jiddah ta gaji dai bayan sun zauna break take cewa "Aunty Su'ada wai meye labari naga kinata fara'a tun asuba?"

"Kai Jidda gulma ko,daman can ni me fara'a ce."

Abbansu ne ya d'ago yana kallonsu cikin mirmishi yace "Su'ada daman me fara'a ce Amma nima naga yau tai yawa."

Duk dariya suka sa,ita kam abincinta taci gaba da ci tana k'ok'arin rage farin cikin da ke kan fuskarta,duk da yak'i b'oyuwa.

Bata bud'e wayarta ba sai bayan sha d'aya a k'ok'arin ta na danne zumudinta ga Khaleelee.

Tana bud'ewa sak'on sa na fad'owa ta message.

_Amincin Allah da rahamarsa su tabbata gare ki,Ina fatan gimbiyar mata ta tashi cikin k'oshin lfy, kin d'arsa min Zuma a baki kin gudu,tun daran jiya har zuwa yanzu nake ta kiranki wayar a kashe,ki barni ko Kalma d'aya in fad'a miki kin k'i,kin sa na kwana cikin maraici da zumudin kasancewa da ke,don Allah da kin bud'e wayar ki sanar dani_"
"Wash Allah Khaleelee na."

Ta fad'a tana dafe k'irji, yanzu ta ya zata iya sanar mai ta kunna waya,message zata mai ko kiran sa zatai? Kai duka ba zata iya ba,kunna Data tai tana son duba sak'onninta na WhatsApp, nan ma da sak'onsa,ta karanta ta k'ara karantawa,tana jin wani sukuni na ratsata.

K'arar wayarta ce ta dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, sunan Khaleelee ta ga na yawo kan wayar ji tai gabanta ya fad'i, Karo na farko da zata fara waya dashi matsayin saurayi ba telanta ba.

Har ta katse tana taraddadin d'auka,wani kiran ya kuma shigowa cikin sanyin jiki ta d'aga da kara wayar a kunnanta, shiru ne ya biyo baya na y'an sakanni.

" *Su'ada*"

Can k'asan ta amsa kamar tana tsoron ajita, " "Na'am,ka tashi lafiya"

"Um um,kin sa ciwo ya kamani tun jiya."

Kamar yana kallonta ta zaro ido da fad'in "ciwon me kuma?"

"Hhhmmmm ciwon sonki mana."

Shiru tai tana jin kunyar zancan nasa, shi kuma jin tai shiru yasa ya d'ora, "Me yasa kika kashe wayar ki jiya,kuma yau kika k'i kunnawa da wuri,kin san abunda hakan ya haifar min kuwa?"

Cikin shagwab'ar da bata san ta yi ba tace"Um to ni ban San me zance ma ba shi yasa na kashe."

"In ke biki San me zaki fad'a min ba ai ni Ina da abun fad'a, kinsa jiya na kwana ina juyi da kiran sunanki,sai da Jabir yai tamin addu'a yai zaton ko gamo na yi."

Bata San lokacin da dariya ta sub'uce mata ba tace"Khaleelee, wai gamo."

"Eh mana gamo nai ammifa a so da kyakykyawar yarinya me d'abiun mutanan kirki, duk ta mamaye zuciyata."

"Hhhhm" kawai tace,shi kam kalamai kawai ya rink'a sakar mata wani tayi mirmishi wani tai dariya wani ko shiru ta ke kamar ruwa ya cita, minti ashirin sukai sallama,ya barta da waya a hannu tana tunanin daman haka Khaleelee yake,tana mai kallon shiru shiru ashe fallallene shima.

******* cikin d'an lokaci soyayya me k'arfi ta shige tsakaninsu, ko yaushe kaga Su'ada mak'ale da waya a kunne,in har ka samu basa waya to aiki ya sha kansa a shago, da rana waya da dare charting ko yaushe cikin sakarwa junan su kalamai suke,kuma yace duk lokacin da Mama ta k'ara mata zancan fidda miji a shirye yake ya turo manyan sa.

Wannan ya k'ara sawa Su'ada nutsuwa da shi ta kuma sakankancewa da soyayyar sa.

*Taku ce*
*Y'ar mutanan Ja'oji*🙋

[2/23, 11:52 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.