Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 14 of 26

_*page*_*27-28*

Bayan sallar la'asar Baba ya tako har tsakar gidan ya samu Sakeena bakin murhu,cikin fara'a ya fara yiwa yaran wasa yana tsokanar su, daga nan ya kalleta ba wata damuwa tare dashi yace "Sakeena ki had'owa me sunana duk kayansa da Faruku ki dawo musu dashi wancan d'aki na Jabeer, shi ya koma dakina da zama har sanda Allah zai raba zaman, ga gado nan da yar durowar kaya nace ya bar musu asa musu kayansu ciki."

Ya juya yana duban Abba yace "Sulaimanu daga yau wancan d'akin ne naku kaji ko?"

Gyad'a kai Abba yayi kawai don yaji abun banbarakwai a kansa.

Daga haka Baba ya koma d'akinsa.

Tofa maimakon murna sai jikin Sakeena yai sanyi k'alau,sai ta fara tunanin Allah yasa dai ba wani abun aka fad'awa Baban ba,don ko bata d'akin za'ai bata hanyar Baba taso abun ya biyo ba,taso Muktar ne da kansa ya shiga maganar ya 'kwatar mata y'ancinta,ita yanzu ma bata san ya za tai dashi ba.

Jikinta a mace har dare, lokacin dawowar yaya Muktar yai nan cikinta ya k'ara d'urar ruwa.

Bayan ya gama cin abinci yai wanka ya fita sallar isha'i, anan Baba yace mai "muje dakina ina son magana da kai."
Bai bud'e mai abunda ke faruwa ba kawai ca yai mai "Muktar sabida lalura da yanayin rayuwa nace Jabeer ya dawo d'akin nan mu rink'a kwana tare,kaga da yawa ciwo cikin dare Ke kamani,kuma na samu abokin d'ebe kewa ma. d'akin sa kuma nace ya barwa me sunana da Faruk su rink'a kwana a ciki."

Tsam Yaya Muktar yai da ransa,ko ba'a fad'a mishi komai ba to yaji a jikinsa kamar a kwai wata a k'asa, don haka ya kalli Baba ya na tausasa murya yace "Baba Allah ya sa dai ba wani abu ne ya faru ba?"

Cikin kauda zancen Baba yace "A'a ba abunda ya faru,je ka abunka."

Kawai shi Yaya Muktar sai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, don haka ya na barin d'akin Baba sai ya fito k'ofar gida,wayar Ibrahim ya kira yace don Allah ya fito waje ya sameshi za suyi magana.

Shi kam Khaleelee har ya cire kayansa ma ya maida ya fito,a kan dakali ya samu yaya zaune,bayan ya zauna gefensa,Yaya Muktar ya zuba mishi ido na d'an lokaci, can yace "Ibrahim kaji hukuncin da Baba ya yanke kan Jabeer ya barwa su Abba d'akinsa ?"

Gyad'a kai yai yana fad'in "Eh haka yace, wai ko don ciwonsa wani sa'in in ya tayar mai cikin dare ga mutum kusa dashi."

Yanayin amsar da Ibrahim ya bawa shi Sam bata gamsar dashi ba,mik'ewa yai yana fad'in "Allah ya kyauta."

Daga haka ya bashi hannu su kai musabaha yace "mu koma ciki Allah ya tashemu lafiya."

Shi kam Ibrahim ba dan Baba ya kwab'eshi da kar ya sanar da Muktar fad'an da Sakeena tai da Jabeer akan d'akin ba tabbas da ya sanar dashi komai,amma ya san bai da wannan damar,haka ya koma wajan sa yana cire zancen a ransa.

Yaya Muktar baiwa Sakeena maganar ba har sai da su ka zo bacci,har ta kwanta ya bubbuga k'afarta ta tashi zaune,zuba mata ido yai yana nazartarta don ya ga kamar a tsorace ta tashi.mutstsika ido ta fara yi ganin ya kafeta da ido, can dai da taga yak'i magana sai tai fuaka tace "Me ya faru wai?"

Cikin d'aure fuska yace mata "Ke zan tambaya me ya faru? maza ke nake jira fad'a min me ya faru kan batun d'akin Jabeer da ki ka 'kwallafa rai a kansa,shin wane rashin albarka ki kai har d'akin ya zama mallakar y'ay'anki?"

Cikin tsoro da kuma rashin kunya a sashi d'aya tace "Me kuwa ya faru,ni ba ruwana, Me d'akin ne ya min rashin kunya ni kuma na taka masa burki,na nuna masa ni ba Sa'arsa bace, to ni daga haka ban san me kuma ya faru ba."

Eh lalle zarginsa ya zama gaskiya, nan fa Ya Muktar ya sata gaba da masifa in da yake shiga ba nan yake fita ba,yaci mutuncinta tas kuma ya ja mata kunne kan sanin me take yi don wata rana za tai abunda za tai danasani.
To Sakeena dai baki ya mutu, sai muzuran k'arya take tana turo baki,shi kam ya juya mata baya ya kwanta.

Tsawon kwanaki uku duk Sakeena ta rasa me ke mata dad'i, ga d'aki dai an bar mata yara suna kwana a ciki,to amma miji yak'i sakar mata fuska sam,ga Jabeer da kullum ya shigo gidan zai tai mata muzurai,don k'ala bata had'a shi da ita yanzu,abincinta ma ya bar ci,duk wani kayan ta da ya ke amfani dasu ya daina,a gabanta zai wuce wajan Su'ada yace "Auntyna don Allah ban aran abu kaza."

To ita Sakeena hakan ne bata so,tab'a ana fifita Su'ada ko ana huld'a da ita.

Ita kam Su'ada ba ruwanta,yanda ta saba mu'amala da ita haka take,sai tab'a ma kwana biyun ta canja duk wannan d'aukan kan ta ajiye komai a sanyaye take yinsa.

********

A lokacin kuma watan azumi ya fara tunkarowa,duk musulmi nata shirye shiryen tararsa.

Ana jibi za'a d'au azimi Zakiyya k'anwarsu Khaleelee tazo gida gaida Baba,duk suna zaune a tsakar gida har Su'ada ana ta hira,a yanayin hirar rayuwa da su ke Su'ada ta fahimci Zakiyya mijinta bashi da k'arfi kuma su na buk'atar taimako a halin yanzu,don magini ne kuma harkar ta tsaya musu ba kasuwa.duk sai Su'ada taji jikinta ya mutu ta bata tausayi.
bayan ta gama abincin rana ta kawo mata falon Sakeena tace "Zakiyya bari in d'an kwanta,ai sai yamma zaki tafi ko?"

Amsa mata tai da "Eh sai bayan la'asar insha Allah."

"OK yo bari na d'an huta ."

Cikin dariya Zakiyya tace "To a huta da kyau Amaryarmu,ko har Babyn namu ya fara wahalar dake ne?"

D'an zaro ido Su'ada tai da fad'in "Wa? rufa min asiri ni ba ruwana,bari kiga na gudu ma."

Daga haka ta juya tana dariya.

Sakeena da ke zaune ta tab'e baki fa fad'in " Tab' d'in,ke kinga alamar wani Baby anan? Ai y'ar boko ce ita,kinsan y'an boko basa haihuwa da wuri."

Ita kam Zakiyya bayan ta kai lomar abincinta baki ta had'iye tace "Yo boko tana hana haihuwa ne sai dai in Allah bai kawo ba,kuma ni tsokanar ta ma nake,don naji tace zata huta ne,ai tana ma k'ok'ari koyarwa akwai wahla,don yau Friday ne ma ta samu ta dawo da wuri.gashi daga dawowarta har ta d'ora abinci ta gama dole ta bu'kaci hutawa."

Cikin jin takaici Sakeena tace "To k'ok'arin me take? in kud'in yazo aljihun wa yake shiga? kuma da kike gani da safe abin karin kumullo kawai take musu ta shirya ta fice ko in ce ma ya kaita.sai bayan ya kaita ga dawo sannan yazo yai wanke wanke ya gyara gidan ya wanke sannan shima ya fita shago."

Gane inda zancen ya dosa yasa Zakiyya k'ara 'k'ular da ita ta hanyar cewa "Ma'auratan gaskiya kenan,su rink'a taimakawa juna,wallahi Yaya Ibrahim ya birgeni. Kinga da baya tayata da wasu ayyukan ai da yanzu sai ta dawo kuma tayi ga girki duk ita kad'ai."

Cikin 'kulewa da yanda Zakiyya ke so dole dai sai ta kare Su'ada, tace "Ba wani fa hutawa da za tai,wallahi shiryawa zata je tai ta tari miji ai yanzu zaki ganshi lokacin zuwa cin abincinsa yayi,ba ta so ne wani ya shigar mata yasa tace bacci za tai."

Kafin Zakiyya ta kai ga bata amsa su ka jiyo ihun yaran Zakiyya na fad'in "Kawu Ibrahim Oyo yoo."

Cikin fara'a ya fara d'aga k'ananan yana fad'in "Su Mamana da Babana da Humaira da Zainab da Salama duk ina musu oyo yooo."

Dariya duk yaran su ka sa, Zainab tace "Kawu Ibrahim ba kaiwa Ummanmu ba fa."

Labulen falon da ya jiyo muryar Zakiyya tana mishi sannu da zuwa ya d'aga,cikin fara'a sosai yace "To inaiwa Y'ar Uwata Ummansu Zainab Oyo yoo."

Sosai yaran ke dariya da murnar ganin shi, don shi akwai wasa da yara da jansu a jiki, shi yasa su ka saba dashi sosai.

Zakiyya ta gaidashi cikin fara'a itama,yana tambayarsa ya aiki ya iyali,duk ya amsa mata da Alhamdulillah. ya d'an dad'e wajansu sannan ya rik'e hannun Zainab da ta cikwikwiyeshi yace "Zee zee muje in baki abun dad'i."

Da sauri sauran 'k'ananun biyu suma su ka rirrik'eshi,manyan kuwa Ummy da Ummu Salama su na gefe su na dariya.
Shima dariyar ya ke ya sa hannu ya d'aga Islam yana fad'in "Ni duk kun hana ma Isy tazo wajena,kun kakkare mata Babanta ko."

Islam ta d'aga kai cikin dariya da murna.
Duk jansu yai wajansu.

Zama yai kan Kujera suna baibaye dashi yace "Su'ada kawo min alawar nan na basu."

Bayan ta kawo mai duk ya basu yana musu yana ta musu wasa.can yace "To kuje Ku barni na huta,anjima in na fito sai aje kantin Mahrazu a siyo wani abu."

Da murnarsu su ka fice su na tsalle."

Su'ada da ke tsaye hard'e da hannayenta tana kallonsa cikin sha'awar yanda yake wa yaran,tai mirmishi da fad'in "Sannu da zuwa Kawun yara."

K'arasowa yai gareta yana kawota jikinsa yace "Um Sannu da gida Aunty Amarya in ji yara."

Y'ar dariya tai tana shafo gefan fuskarsa tai k'asa da murya sosai tare da kashe ido tace "Ka yi kyau sosai fa,ban tab'a ganin namijin da manyan kaya kewa kyau irinka ba."

Cikin farin ciki yace "Don kina ganin kyana ne kike ganin komai namin kyau,kince k'anan kaya namin kyau kince manya namin,kince Babbar riga tafi min kyau sama da komai, kinga alamun son kai yasa kike ganin hakan,wata ma haka take ganin mijinta,umm nama manta rannan ma haka kika ce, inna d'aura towel zan yi wanka kyau nake miki kamar ki had'iyeni."

Y'ar k'ara tasa cikin wani salon k'issa ta kai hannu tana rufe mai baki tace "Ni dai yaushe nace haka? Ni fa ban fad'a ba,ba ruwana."

Cikin dariya sosai ya rik'o hannayenta yana k'ara sata cikin jikinsa yace " To naji biki fad'i haka ba,wasa ne,amma rannan kin fad'i abunda yafi haka fa."

Cikin wani jan hankali ta d'an ware idonta akan nasa tace "Yaushe m kuma me na fad'a?"

K'asa sosai yai da muryarsa yana sa bakinsa a kunnanta yai mata rad'a.

Ai kuwa ta cikwikwiyeshi tana d'an bugunsa a k'irji tace "Ni dai ban fad'i ba,gaskiya in ma na fad'a to ban cikin nutsuwata."
Ta k'arasa maganar da dariya.
Shima dariyar ya ke sosai yace "Eh daman a wannan lokaci ai ba batun wata nutsuwa tare da ke,ke don fa ina rufa miki asiri ne,amma wasu maganganun ma da kike ai bazasu fad'a ba."

Ture shi tai a jikinta tana d'an mai hararan soyayya tace "A'a Allah kaine me surutai kai ta sambatu,wani sa'in ma sai na toshe ma baki,amma shine zaka mak'ala abun a kaina."

Baya shima yai yana d'an d'age kafad'a alamar bai damu ba yace " To ni ko zaki kwana kina fad'in nai surutai nai sambatu sabida ke ai bazan damu don kuwa nasan ina yi,kuma kin kai kinma zarta ai kukan dad'i sabida ke."

Juyawa tai zuwa d'aki tana dariya tace "Ni kam nai shiru yau naga duk da tsokana ka tashi, an jima ma had'e kawai."

Bin bayanta yai zuwa d'akin yana k'ara tsokanarta da cewa " A'a yanzu zamu had'e yasin ba wani anjima."

Ita kam bata k'ara biye mai ba ta taimaka mishi ya rage kayan jikinsa,sannan ta had'a musu abinci,bayan sun gama ci ta tattaro duk hankalinta gareshi ta fara magana "My Khaleelee, daman zanma magana ne kan Zakiyya, na fuskanci kamar suna cikin matsin rayuwa,a yanayin hirar da mukai d'azu,shine nace don Allah me zai hana mu had'a Mata kayan abinci,kaga dai kayan abincin mu kullum kamar bama tab'awa kar ma su zo su lalace, gashi kuma y'ar uwarmu na buk'ata."

Wani dad'i ne ya lullub'e Ibrahim, a ransa yake k'ara tabbatarwa lalle ya sami matar rufin asiri, ta sami mace ta gari abokiyar shiga aljanna,don duk macen da ke son y'an uwanka ai dole ka d'aga mata kafarka ta shige aljanna zuruf.

Rik'o hannunta yai cikin mirmishi yace "Na gode angle, na gode yanda kike kula da lamuran y'an uwana, Allah ta saka miki da alkairi, kiyi duk yanda kika ga ya dace kinji,Allah yai miki albarka mace ta gari."

Fara'a sosai a fuskarta ta amsa da "Ameen nima na gode da bani dama mijin wuce sa'a."

A tare duk su kai dariya.

Lokacin da zai koma shago ya bata dubu biyu yace ta bawa Zakiyya su yi kud'in mota.

Da ya fito ya tsaya su kai sallama da Zakiyya,sannan ya bawa yaran d'ari biyu yace su je kanti su siyo biscuit.

Su'ada kam ta sami buhu ta zubawa Zakiyya shinkafa kwano uku,tasa mata ta tuwo kwano biyu,Sannan taliya guda biyar macaroni guda biyar,cous cous ,ta auna mata man gyad'a da manja,su magi da dai duk abun buk'ata, sannan ta d'auko dubu uku ta d'ora kan dubu biyun da Khaleelee ya bayar a bata ta had'a su ka zama 5k.

Bayan sallar la'asar Zakiyya ta lek'a zatai mata sallama,tace "Au daga bakin k'ofa ma? to bazan amsa sallamar ba gaskiya."

K'arasawa ciki tai tana fad'in "To ai yamma tayi ne Amarya,kuma zamu je mu d'ora tuwon dare,ga masu d'orawar kafin na dawo to duk sun biyoni.

Bayan ta zauna Su'ada ta jawo buhun da ta had'a duk kayan a ciki tare da kud'in ta bata tace inji Khaleelee.

Murna ta cika ran Zakiyya tai ta godiya bakinta yak'i rufuwa.

Su ummi ta k'walawa kira su ka zo su ka ja buhun,kud'in ko ta ninkesu a jaka.

D'akin Baba taje ta nuna mai kayan da kud'in yai mirmishi cikin jin dad'i yace " Masha Allah, an godewa Ibrahima da matarsa,don tabbas na san wannan aikinta ne,Allah yai musu albarka gaba d'aya."

Ta amsa da amin tana mai sallama.

Sakeena har soro ta rakasu tana k'ara kallon buhun,don bata san meye a ciki ba,kuma Zakiyya bata ce mata komai ba,amma koma meye tasan kyauta aka bawa Zakiyya don yanda ta fito daga gun fuskarta fess cike da fara'a tasan samuwa tai.
Don haka da tai mata rakiya soron tace "Zakiyya me aka samu ne haka?"

Zakiyya tace "Wallahi kayan abinci ne da dubuta biyar,ai yau nayi farin zuwa gidan nan,ki tayani godiya wajan Amarya don Allah."

Tab'e baki tai tana juyawa ciki tace "Ku gaida gida."

A ranta tana fad'in 'kinibibi da neman gindin zama.

Zakiyya kuwa tana zuwa gida ta kira Ibrahim a waya tana mai godiyar kayan abinci da dubu biyar d'in daya bata.cikin mamaki yace "Dubu biyar ko biyu?".

Tace mai biyar Su'ada ta bata.
Yace To Su'ada ce dai ta k'ara mata amma shi biyu ya bada.

Godiya sosai tai mishi,sannan ta kira number Su'ada tai ta mata godiya itama.

Bayan Ibrahim ya dawo gida da dare yake ma Su'ada maganar kud'in da ta bawa Zakiyya ta had'e rai tana d'an turo baki tace "To sai dai in so kake ka nunamin y'ar uwakka ce kai kad'ai banda."

Godiya sosai yaita mata,yana k'ara sa mata albarka.

*Taku ce*
*'Yar Mutan Ja'oji*🙋

[2/23, 11:56 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_*Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun.Ha'ki'ka dukkan me rai mamaci ne,Wannan aya ta tabbata a kan mahaifin malamina, ina rok'on Allah ya jik'ansa ya gafarta zunubansa ya kyautata makwancinsa,Allah yasa mutuwa hutu ce gareshi*🙏🙏🙏😢

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.