Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 1 of 26
👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
_*page*_ *1-2*
Ibrahim Khaleel Matashin saurayi d'an kimanin shekaru Ashirin da takwas,mazaunin unguwar zoo road.
Dogo ne me matsakaiciyar k'iba, kalar fatarsa bak'a ce amma ba mai duhu sosai ba,fuskarsa cike take da gargasa tare da gashin baki, wanda y'an zamani ke kira da 'quarter million' yana da cikar gemu amma ba mai tsayi sosai ba, bashi da girman idanu sai dai baza'a kira su da mitsimitsi ba,bashi da dogon hanci amma baza'a ce mishi me fad'in hanci ba,yana da sanyin murya tare da sanyin hali.
Tsohon telan mata ne, wanda ya fara d'inki tun yanada shekaru goma sha biyar,har izuwa yanzu bashi da wata sana'a bayan d'inkin mata.
Ya yi karatunsa na N.C.E a kwalejin tarayya da ke kano wato F.C.E.
Yana da sani a b'angaran islama dai dai gwargwado.
Duk wanda ke zaune da Ibrahim zai bada shaidar shi mutum ne ba mai zafi ba,komai nasa cikin sanyi ya ke yinsa.me yawon kyauta da tsananin zumunci. Mahaifiyar sa ta rasu kimanin shekaru goma da suka wuce, suna zaune ne a gidansu dake unguwar zoo road kan titin hausawa sabon titi. Su hud'u mahaifansu suka haifa,babban yayan su namiji Yaya Muktar sai shi Khaleel,sai k'anwarsu Mace Zakiyya dake gidan mijinta,sannan autan su Jabir me shekaru goma sha takwas.
Mahaifinsu Malam Sule na raye sai dai girma daya kamashi ga lalurar yau da kullum wadda ba'a raba tsofaffi da ita.
Gidansu gida ne da yake da girma Wanda ya tara tarin d'akuna.hakan yasa Yaya Muktar yake zaune da iyalinsa cikin gidan,daga farko kana shiga d'akin Mahaifunsu ne jere dana Ibrahim da Jabir tare da k'aramin band'aki a gefe,sannan in ka shiga cikin gidan kuma d'akuna shida ne,wasu rufe wasu a bud'e, duk wanda suke bud'e Sakina ke amfani dasu ita da y'ay'anta hud'u,akwai wadatar tsakar gida me d'auke da babban bayan gida da d'akin girki. Kwanan abuncin Ibrahim da Jabir da mahaifnsu duk yana tukunyar Sakina.wadda suke zaune lafiya da ita matsayin ta na matar yayansu kuma tamkar uwa ce gare su duk da ba wani yawon shekaru gare ta ba amma suna girmamata sosai.
********
Tsaye yake bakin tebur d'in da yake yanka d'inki cikin zagayen farko dake Shagon d'inkin nasa,wanda yake bakin titin shiga gidan zoo.
Su'ada tai sallama ta shigo shagon cikin fara'arta ta fara gaisawa da Jabir da ke tsugunne yana fifita gawayi cikin dutsen gugu.
D'ago kai Ibrahim yai tare da mata mirmishi ya maida kansa ga yankan da yake. Ita kam ciki ta shige ta gaggaisa da sauran telolin da ke cikin shagon sannan ta dawo in da yake tsaye taja kujera ta zauna tana fad'in "Yallab'ai barka da yamma, ya aiki?"
Bai bar yankan da yake ba ya amsa mata cikin fara'a "Barkanki dai Yallab'iya,ya school d'in?"
"Hhhhmmm school gata tana garamu saura k'iris dai insha Allah mu huta.Allah yasa dai an gama min d'inkina."
Cikin tsokana yace "D'inkinki ko yanka shi ba'ai ba sai zuwa gobe ko jibi."
D'an zaro ido tai tare da marairecewa tace " Wai da gaske Khaleelee? gobe ne fa dinner d'in, kuma bazan samu fitowa ba goben don zanje k'unshi da gyaran kai."
Jim yayi kamar yana tunani can yace "Gaskiya akwai matsala,don kinga duk su Musa akwai d'inkuna a wajansu dana yanka musu sun had'e miki zuwa dare ko da safe."
K'ara marairaicewa tai tana fad'in "Haba Khaleelee kasan fa ni ban jin dad'in d'inkin kowa in ba naka ba,ni dai don Allah kasan yanda zakayi ka d'inka min zuwa gobe da yamma kaji."
Gyad'a kai yai yana kallon cikin shagon yace "Umar mik'omin waccan ledar in gani."
Fito da kayan ciki ya farayi yana y'ar dariya yace"kamar ma Wannan ne kayan ko?"
D'an turo baki tai mirmishi kan fuskarta tace" Allah Khaleelee ka maidani ma abar tsokana,wallahi har kasa jikina ya mutu. "
"A'a kar ya mutu don Allah ga kayanki nan maza d'auki ki je gida."
Cikin fara'a ta amshi ledar tana mik'o mai cikon kud'in d'inkinsa naira dubu uku. Sannan tai musu sallama ta fita a shagon fuskarta d'auke da fara'a. Ita kam bata san me yasa Khaleel ke birgeta ba,komai nasa sha'awa ya ke bata,musamman tsananin tsaftar sa, Allah yayi shi da tsafta kullum tsaf zaka same shi, haka ma shagonsa ko yaushe a gyare ga k'amshi in ka shiga kamar karka fita.
________________
Sa'adatu Mustapha Sarki Darki matashiyar budurwa me shekaru goma sha tara a duniya, Kowa na kiranta da Su'ada, fara ce ba sosai ba,bata da tsayi kuma bata cikin gajeru,amma dai za'a iya kiranta me k'aramin jiki, kallo d'aya zaka mata ka gane kamanninta da fulanin asali. Su'ada tana da matuk'ar hak'uri da yawon fara'a.haifaffiyar garin kano ce a unguwar sharad'a,a can tai primary d'in ta da secondary da islamiyya. Daga nan Suka dawo unguwar Medile k'aramar hukumar kumbotso.yanzu tana karatun ta a Aminuddeen college of education.
Cikin gidansu su bakwai ne,yayar ta d'aya tana da aure sai ita,sannan k'annanta mata guda hud'u sai autansu Ibrahim Wanda suke kira Khaleelee.(don haka take kiran Ibrahim tela da Khaleelee) wanda ya kasance shi kad'ai namiji a cikinsu.don haka suka d'au son duniya suka d'orawa Khaleelee.
Mahaifinsu bafulatanin garin darki ne dake kano,kasuwanci ya fito dashi daga k'auyansu.
d'an kasuwa ne me safarar takalma da les daga legos zuwa kano.
Mahaifiyar su kuma cikakkiyar bahaushiya ce y'ar unguwar gwale gudundi. ma'aikaciyar lafiya ce a asibitin yara da ke kano wato ASIYA BAYERO.
Akwai wadatacciyar tarbiyya a cikin gidansu,don mahaifiyarsu jarumar mace ce me tsaye a kan lamarin iyalinta,kasancewar Allah ya wadatata da yaya mata yasa duk motsinsu ke idonta. Wayayyiyar mace ce ba ruwanta da wani kauda ido akan d'a,tana jansu a jikinta sosai don haka basa iya b'oye mata sirrinsu. Wani sa'in in kaje gidan kaga yanda take mu'amala da y'ay'anta zakai tunanin k'annanta ne ba y'ay'a ba.bata da abokan hira ko shawarar da suka wuce y'ay'anta, don haka suma dukkan shawarar su tare da ita suke yi.
_*da yuyuwar nan gaba ya koma na kud'i*_🥰
*Ku biyoni yanzu na fara* 👌
*Taku ce*
*y'ar mutan Ja'oji*🙋
👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.