Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 26
_*page*_*21-22*
Yau satin Su'ada guda gidan Ibrahim,zuwa lokacin wata shak'uwa da tsantsar k'auna ce ta lullub'e rayuwar su,ko yaushe su na manne da juna,kulawar da su ke bawa juna dole ta birgeka, don ko motsi d'aya ya yi to a kan idon d'ayan ne.
Kullum da safe Su'ada in ta gama aikin ta za fito su gaisa da maman Abba,sannan ta je d'akin Baba ta gaida shi,to wani sa'in ta kan tsaya su d'an yi hira sama sama,ta koma wajanta,musamma da ke ko yaushe da rana cikin yin bak'i ta ke da dare kuma ta na tare da Oga.
B'angaran abinci kullum in ta dafa na rana za ta kaiwa Baba, sannan da dare ma za ta kai mishi,haka na Jabir ta sa mai kwano a wajanta duk da ya na sa kwano a a tukunyar Sakeena.haka ma yaran Sakeena duk wanda ya shigo cikin au hud'un za ta zuba mai ya ci ya k'oshi.
Yau da rana Su'ada tai girki tare da had'a lemon kwakwa, ta d'auko sabon food flask d'in ta da ta warewa Baba shi,ta zuba mai jalof d'in shinkafa da waken da tai,sannan ta d'auko wani juck ta zuba mishi lemon, a tire ta jera ta d'auka don kai mai.
Ya na bacci ma sallamar ta ta tashe shi,bayan ta ajiye abincin ta ke mai barka da rana ,ha amsa cikin fara'a sosai, "Sannu Sa'adatu, sannu da k'ok'ari, ya bak'unta? Ko dake yanzu kin zama y'ar gida ko."
Kanta a k'asa ta na d'an mirmishi,ya fara bud'e abincin, k'amshin kad'ai ne ya cika hancin Baba amma ya ji wani nishad'i ya saukar mai,duk da shekarun da su kaiwa Baba yawa amma harshen sa na son d'and'ano,da ke da an yi arzik'i komai ci ake kamar a banza,to sa karayar arzik'in ta zo sai tazo dai dai da rashin me d'aki, wannan yasa komai ta cakud'e,abinci sai Wanda suruka ta dafa ta bashi, ba shi da ikon fad'in kalar abincin da ya ke so,ba wai don BA za'a mishi ba,a'a kawai yakana kawaici irin na iyayen da,ba su son takura suruki ko kad'an.
Ganin zai fara cin abincin ya sa Su'ada tashi ta fita.
A tsakar gida ta sami Sakeena ta na ta fama da gwawayi yak'i kamawa gaba d'aya, ga shi lokacin tafiyar yaran makarantar Islamiyya ya kusa,sai k'orafi su ke yi.zama tai kan kujera y'ar tsugunne ta na fad'in, " Maman Abba wannan gawayin anya ba ruwa ne ya tab'a shi ba?.
Cikin b'acin rai da gajiya tace "Su'ada wane ruwa,yaushe ma damunar ta zauna kawai dai mara cin ne,tun ranar da aka kawo buhun gawayin nan nace wa Abbansu ba mai kyau bane,nace ya maida amma taurin kai ya sa ya kafe da fad'in me kyau ne,yanzu kinga tun sha d'aya na ke fama na kunna ya mutu na kunna ya mutu gashi har d'aya ta yi."
Cikin mamakin kalmar da Sakeena ta fad'awa mijinta wai tsabar taurin kai,ta jinjina kai da fad'in " Ba mamaki ruwan ne ya tab'a, tunda kinga da ga kudu a ke kawowa kuma su tuni ruwa yai nisa mu ne dai ruwan bai zauna ba, to ki kunna risho ki hak'ura da gawayin."
"Wane risho Su'ada, ai tun tuni yaran nan su ka mirjemin shi ya lalace."
Karaf Abba yace" To Umma ki d'ebo wancan sauran icen da a kai amfani da shi da biki ki kunna mana."
Zaro ido tai tace "Wa? so kake yau a silleni kenan,ka na ganin da bikin ana girki Ibrahim na k'orafin hayak'i na b'ata gida,tun tuni ka san ya tsani yaga an hura ice a gidan nan,balle yanzu da ya sa kud'in sa yai wa gidan fenti."
Haushi da mamaki su ka k'ara cika Su'ada, wato ita dai Sakeena ba ta iya tauna magana, kawai duk abunda ya zo bakinta fad'in shi take yi,cikin basarwa tace " To ai lalura ne,za'a zauna ba'ai girki bane,tunda gawayin ya k'i kamawa kuma akwai icen ki kunna mana."
Tashi Sakeena tai da ga durk'ushen hura gawayin ta na fad'in "To k'ila tunda kinsa baki ba zai k'orafi ba,bari na hura icen."
Su'ada kam binta tai da ido kawai,tun zuwanta gidan ta fahimci Sakeena a kwai raunin tsafta a tare da ita,don da ga zanin da take yawo dashi a tsakar gida ma kawai za ka gane k'azantarta,sannan ga ga yaranta ma,wani lokaci sai su Kai yamma ba wanka,su yi ta yawo cikin datti.
Maganar Islam ce ta dawo da ita nazarin da ta tafi, "Aunty ki bani abinci unwa ike ci."
dariya ta baiwa Su'ada yanda take maganar,cikin tsokanar ta tace "Ni ba zan baki abincina ba,y'an makaranta zan zubawa su ci kar su makara."
Kuka ta tsanyare da shi,ai kuwa yaran su ka sa dariya Su'ada ma tai d'an mirmishi tana mik'ewa tsaye ta rik'e hannunta "zo muje in baki to karki tara mana jama'a."
Kulan da ta cikawa Jabir ta juye musu a wani babban plate ta k'walawa Abba kira, ya zo ya d'aukar musu.
Taliya ta dorawa Jabir don ta san yanzu zai shigo gidan shima,abinka da aikin gas nan da nan ta dahu,ta na tacewa ta jiyo muryar Ibrahim a tsakar gida.
D'an lumshe ido tai ta na fad'in "My Khaleelee."
Ya na shigowa ta na fitowa a kitchen d'in,tsayawa yai harde da hannayensa a bakin k'ofa,ita ma ta hard'e hannu ta tsaya k'ofar kitchen, sun Kai y'an mintuna su na kallon juna a haka,da ga bisani ya tako a hankali gareta,bud'e hannayenta tai ta fad'a jikinsa,bayan ya yi hugging d'in ta na d'an lokaci ya cikata yana fad'in " Na gaji da yawa yau fa."
Cikin sanyin murya da kissa tace " Me ya faru ?"
"Na sha wahala a gurin gyaran keken nan fa."
D'an marairaice murya tai tana shafo sajensa zuwa gemunsa tace "Eyya sannu my Choice, zo muje in had'a ma ruwan wanka ."
Rik'o Hannayenta yai ya na kashe ido yace "Ba wanka kad'ai na ke buk'ata ba fa."
"To da me kake buk'ata ?"
Rank'afowa ya yi yana mata magana cikin kunne,y'ar k'ara ta saki ta na janyewa baya tace "A'a ni dai bari a gama da wannan d'in."
Kai tsaye ta wuce kitchen ta d'auko mai ruwa me sanyi da cup's, Bayan ya sha ya koma ya kwanta kan kujera,ita kuma ta shiga toilet ta had'a mai ruwan wanka, sannan ta fito da towel, mik'a mai hannu tai ya tashi zaune,ta tsugunna ta na balle mai botir d'in gaban rigar,shi kam idonsa na kanta,duk motsinta ta cikin idonsa.
Bayan ta taimaka mai ya cire kayan duka ya d'aura towel d'in, rigima irin tasa ya dage sai dai tazo ta taya shi wankan.k'wayar idonsa ta ke kalla cikin wani salon so tace "Rigima ko?"
D'an b'ata fuska yai da marairaicewa yace "Ni ba rigima ba,ai kin san na gaji da yawa,ba zan iya wanke bayana ba,ba inda ma zan k'ara fita sai gobe."
Y'ar dariya tai tace "Da wa yake wanke ma bayan in ka gaji."
Haka na ke barinsa,amma yanzu ai da a kwai me wankewa ,kuma ma ai nata ne,tafi kowa amfana dashi yanzun."
Da sauri ta juya ta na fad'in "To bance amin tonon silili ba ni,zo muje na tayaka amma fa ni ba zan yi ba."
Gyad'a mata kai ya ke cikin mirmishi su ka shige toilet d'in.
Rashin wayo irin na Su'ada ya hillaceta itama sai da yai mata wankan.
Bayan sun gama k'ailulansu su ka shirya,ita kam k'aramar riga ta sa mara hannu,tsayinta iya gwiwa,shara shara ce,sabida zafin da ake,shi kam ko riga bai sa ba wando kawai three quarter ya sa.
Su na zaune su na cin abincin ta jiyo muryar Jabir ya na wa Islam wasa, mik'ewa tai zuwa kitchen ta d'auko flask din abincin da ta zuba mai,ajiyewa tai gaban Khaleelee tace "Don Allah ko zaka mik'awa Jabir, ka ga Maman Abba ba ta dad'e da d'ora girki ba,abincin sa ma na bawa su Abba au kaci zasu tafi islame,shi taliya na k'ara dafa mai."
Hankakinsa ba ga abincin sa yace " Sa Hijab d'inki ki je ki kai mai."
D'aki ta koma ta d'aura zani sannan ta saka katon hijab ta fito,binta yai da kallo harta fita a falon.
A tsakar gida ta same shi ya na cin sauran abincin da ta kaiwa Baba,cikin fara'a ya d'ago ya na fad'in "Aunty na barka da gida ."
"Sannu da dawowa, ga abincin ka harka fara cin wani,amma wannan taliya ne fa."
"Wallahi kinga yunwa na ke ji ,kuma Maman Abba bata k'arasa ba kawai na d'auko sauran na Babah,amma kawo taliyar ma duk zata shiga ai,kin san cikina na maza ne ba kalar na angonki ba."
Ya k'arasa da tsokana,
Dariya tai ta ajiye mai kulan ta na fad'in "Ba ruwana ai ya na jiyo ka."
Sakeena ta saki wani tsaki tana fifita wuta.
Juyowa tai ta kalleta har za tai magana taga ta wani d'aure fuska,don haka bata tanka ba ta juya ta koma wajanta.
Bayan sallar Magriba Su'ada na kwance jikin Ibrahim ya kamo kunnanta yana magana k'asa k'asa " Ke ce kika bada damar a kunna ice a gidan nan ko?"
Rik'e hannun da ya kama mata kunnan tai cikin kukan shagwab'a tace "Wayyo Allah, Abbana mamana,kun kawo ni za'a cire muku kunne na."
Sosai maganar ta bashi dariya yace "Yanzu wannan kunnan ai nawa ne,ko na cire ni zan yi kuka, amma kin San me?"
"Um um sai ka fad'a."
"Ban san inga ana kunna ice a gidan nan tun asali,sabida matar gidan tana da rauni wajan gyarawa,in ta kunna ice sai ki ga duk gidan ya fita hayyacinsa, don haka ma shi kansa Yaya Muktar ya hana,sai gawayi ta ke amfani da shi,to d'azu da nazo naga ta kunna ice nace ga gawayi me yasa ta kunna ice ,shine tace wai ya k'i kamawa sai kika ce ta kunna icen kawai."
Gyara kwanciya tai a jikinsa tans wasa da gashin da ke kwance a Hannayensa,
Cikin sanyin murya tace " Ka kan wani abu ne? Gawayin da take amfani da shi bai ci,ya sha ruwa kuma lokaci na ta k'urewa ba ta d'ora girki ba,shi ne Abba ya ke ce mata ga sauran icen biki ta d'iba,to sai na ga ta nuna ko za kai fad'a ne ni kuma na ce mata me ne ai lalura ce don ta kunnna ice kamawa tai."
Shafa kanta ya ke cikin wani salo ya fara magana " Su'ada wlh Maman Abba ba ta kulawa da gidan nan,sai ta Kai yamma ba tai wanke wanke ba,shara kuwa ba batunta,sai kwana biyu ake yi,sai dai in an b'ata waje a tattare iya gun,ga yara dole gida ya rink'a buk'atar gyara kullum,Wannan dalilin yasa na d'auke sharar gidan nan ta dawo kaina,kin ga band'akinmu ba d'aya ba amma haka nake wanke namu na wanke na su, wanke wanke ma don Baby ta kawo girma ne ake yinsa a kan kari,to kinga shekarar ta takwas yarinyar amma ita ke wanke wanke safe da yamma,wani lokaci da safe ina jinta ta ba kuka tana wanke wanke sabida ga makaranta ga aiki,wankan yara wahla ya ke mata,na sha kama yaran nan nai musu wanka,in naga su na yawo da datti,Maman Abba ta na da son kiji da k'iywa,ni kuma na tsani kazanta,duk rashin son maganata ba na shiru in naga k'azanta ,to in kin jini da ita k'azanta na gani,ban so ban so wlh."
Juyi Su'ada tai a jikinsa Wanda ta san dole zai tsirga mai,da sauri ya Tsantsameta ya na fad'in "Kan kujera fa mu ke sai kin fad'o ko?"
Mik'a ta k'ara yi sannan tace "To in na fad'o ai laifinka ne.
Kasan me? Maman Abba mace ce,kuma duk mace ta na buk'atar uziri cikin rayuwar ta,maybe abubuwa ne su kai mata yawa,ga yara ga aikin gida,amma Yanzu tunda yaranta sun fara girma za ka ga komai ya dai daita,k'azanta ba ta dad'i ko kad'an amma wani ta zame mai jiki."
Kiran Sallar isha'i ya sa su ka mik'e don yin salla.
Bayan sun dawo daga masallaci ya shiga yiwa Babs sai da safe,zai mik'e yace ya zauna.bayan gyaran murya ya fara magana "Ibrahima daman batu ne kan abinci,ka ga tun zuwan matarka gidan nan ta samin kwano itama,ga ba wajan Sakeena, to abincin ya na min yawa,kuma duk wadda ban ci nata ba zata ji ba dad'i, kaga d'azu ban ci na Sakeena ba sabida na k'oshi a lokacin da ta kawo,nace yaran su cinye,to hakan bai mata dad'i ba har ta kaiwa mijinta k'orafi, d'azu da magriba ta ke min zancan, don haka shima na fad'a mai ko wacce ta rink'a kawo min abinci sau d'aya, wata da rana wata da dare,kaga hakan zai fi ko?"
Jinjina kai ya yi da cewa "Hakan yayi Baba, amma ita Su'ada sai ta rink'a kawo ma na dare,sabida kaga tana koyarwa kuma da safe ne,yanzu ma hutu su ka bata,kafin ta dawo ta d'ora girki lokaci zai rink'a k'urewa,amma na daren ta na gida."
Gyad'a kai Baba yai da fad'in "Hakan ya yi,Allah ta yai muku albarka ya hore muku abinda za ku kula da iyalenku."
"Ameen Ameen Baba,Allah ya tashemu lafiya."
Sai da dafe ya yi mai ya fito.
Sai da su ka zo kwanciya ya kewa Su'ada maganar da su kai da Baba,ita kam mamaki ne ya cika ta,amma sai ta basar kawai tace "To ai ba damuwa,duk d'aya ne."
********
Da safe Baba ya na jiran abun karyawa har wajan goma Sakeena ba ta kawo mishi ba,ya saba tun wajan takwas take kawo mishi,tunda mijinta da wuri ya ke fita tare da yara ya saukesu a makaranta,to yau har yaran su ka fita shiru,har ya koma baccin safe ya tashi ba labari, bai ce komai ba ya shirya ya fita k'ofar gida, a nan ya samu yara masu wucewa da abun siyarwa ya sai kunun gyad'a ya sha.
Su'ada kam daman ita na rana da dare ta ke bashi,to kuma yanzu ance sau d'aya, ba ta san Baba bai karya ba balle ta aiko mai.
Ibrahim ya gama shirin sa zai tafi shago, ta rako shi kamar yanda ta saba,d'akin Baba su ka shiga don gaisheshi, sai su ka samu bai ciki,bakin soro ta rakoshi su kai sallama ya tafi.
ganin Sakeena ba ta tsakar gida ya sa Su'ada tsayawa k'ofar d'aki tana gaisheta, a dak'ile ta amsa mata,Islam ta d'aga labule ta na mata surutu,ta tsaya ta na tsokanar yarinyar,ta rik'e hannunta su ka wuce wajanta, ba ta bi ta kan uwar ba.
Tsawon kwana uku Su'ada ta ga Sakeena ta canja mata sosai,abun na bata mamaki,ita dai ta san ba abunda tai mata amma sai cin magani take.
Ganin haka ya sa ta tsantsame jikinta,don duk kirkin Su'ada ba ta d'aukan wulakanci sam.
B'angaran Baba kuwa kwana uku ya na fama da yunwar safe,ba wanda ya kula cikin yaransa,dalili Jabir daman da safe ya ke fita school,Yaya Muktar ma tun bayan sallar asuba in ya shiga su ka gaisa to sai yara sun yi shirin boko ya ke fitowa su tafi tare,to anan ma in ya shiga mai sallama ba dad'ewa ya ke ba,shima Ibrahim in su ka gaisa bayan dawowa daga sallar asuba to sai goma in zai fita ya ke k'ara shiga wajansa.
Hak'uri kawaici irin na mutanan da ya sa cikin kwana ukun Baba bai magantu ba,sai dai kullum in hantsi ya d'aga ya fita k'ofar gida ya zauna,in masu kunu sun zo wucewa ya siya ya sha. Ganin da yai yunwa na neman mai illa ya sa yau yai magana,lokacin da Ibrahim ya zo mai Sallama zai fita ya tsaida shi.
"Ibrahima in babu takura ka cewa me d'akinka ta sa kwanan safe da ni,ita Sakeena sai ta rink'a kawo min na rana kawai."
"To Baba ba damuwa,na ranar ma don ka k'i ne wallahi."
"A'a a yi hakan kawai,na safe da na daran ma Allah ya yi albarka ya bud'a muku."
"Ameen Baba, Allah ya k'ara lafiya ya k'ara nisan kwana."
Nan yai mai sallama ya tafi.
*******
Da dare ya sanar da Su'ada ta rink'a girkin safe da Baba,ta amsa da to, ba ta k'ara cewa komai ba,cikin ranta ta ke nazarin al'umuran da ke faruwa,tabbas in haka zaman gidan zai rink'a tafiya ba zai dad'i ba.
*Taku ce*
*y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 12:05 AM] LAYUZA KABIR: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
_Allah ya k'ara maka lafiya my Grandfather, Allah ya tashi kafad'arka ya sauk'ak'a maka_🙏🙏🙏
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.